← Book details Kwantan Bauna Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 53 OF 55

Sashe 53

Kwantan Bauna Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

A fusace Mama tayi kanta zata mare ta Mum ta rik'e tana girgiza mata kai Mama a fusace tace, "matuk'ar kika aikata haka zakiyi dana sanin da baki tab'a yi ba tunda Allah ya kawo ki duniya. Zan iya sakawa a b'atar dake daga duniyar gabad'aya wannan ba komai bane a wajena matuk'ar zan samu abinda nake so. Sai na tabbatar baki tako k'ofar gidan sarauta ba balle ki kasance a matsayin da kika lissafa domin yafi k'arfin kaf dangin ki gabad'aya. Zan miki biyu babu, babu Asad babu sauran wanda suka zo taimakon ki su aure ki tunda abin naki rashin kunya ce" ta fad'a tana nuna ta da yatsa cikin murya mai amo da alama kamar wani abun ma bata san tana fad'a ba sabida b'acin rai.

Rauda ta tab'e baki tace, "Ina jira na gani sirika ta, in kuma nice naci wasan na shigo gidan matsayin sirikar ki nice nayi nasara bake ba." K'wafa tayi fuskar ta har ja tayi sabida b'acin ran da take ji a zuciyar ta wanda bata tab'a jin irin sa ba sukayi hanyar waje kafin Mama ta tsaya ta juyo ta kalli Umma da Anty Ummi tace, "Duk abinda ya samu y'ar ku kuyi kuka da kanku.." Rauda ta d'aga murya tace, "babu abinda zai same ni sai alkhairi. Kii gaida min mijina kinji sirika ta!." Juyowa tayi ta kalle ta Rauda tayi dariya kafin ta girgiza kai ta fita daga falon a fusace.

Kallon Rauda Umma tayi bayan sun fita cikin fad'a tace, "Wannan wanne irin rashin hankali kike aikatawa haka Rauda?. Ke kuma babbar banza mai biye mata ina yi mata magana kina tab'a ni wai na k'yale ta tana yiwa wacce ta haife ta rashin kunya, Ni in aka yi min haka zaku ji dad'i ne?. Matar sarki ce fa bamu yi mata komai ba ta saka anzo gida an ci mana mutunci ina ga kun fad'a mata wad'annan maganganun marasa dad'i...? Ba kaina nake ji ba ke nake ji Rauda zata iya yi miki komai dan ganin bayan ki." Yaya Ummi tace, "Umma ai ke baza ki aikata abinda ita tazo tayi mana har cikin gida ba bayan wanda ta saka akazo har gida aka ji miki ciwo, ai wallahi munyi mata da sauk'i ma irin ta'asar da tayi kamata yayi mu kamata mu rama irin abinda ta saka akayi miki. gani take kud'i shine komai zata iya juya mu tayi mana rashin mutuncin da taga dama bata san bata isa ba wallahi. Dan tana matar sarki baza muji tsoron ta ba tunda ita ta d'auko k'afa tazo har inda muke ko zane ta mukayi itace ta jawo."

Umma ta kalle su tace, "ya dai isa haka bana son tashin hankali da yiwa na gaba rashin kunya. Ku tuna a gidan d'anta muke ko a yanzu mun ci albarkacin ta dan ba bata haife shi ba damu zauna ba, da badan yazo inda muke ba da wataƙila yanzu bamu san a inda muke zaune ba. Kar na sake ganin kin yiwa wani haka koda nan gaba ne, wannan ba tarbiyya ce." Umma ta fad'a tana kallon Rauda kafin ta tashi ta shiga d'aki.

Yaya Ummi ta kalli Rauda tace, "Ke me kika yanke game da auren shi Asad d'in?." Rauda ta kalle ta tace, "Ban yanke komai bani domin bana ra'ayin auren sa gabad'aya. Ya cika rainin hankali da yawa bazan jure ba."
"Kuna tare da Anas har yanzu?."
"Tun dai ranar yazo har yace min bashi ya aiko mana da kayan abinci ba ban sake jinsa ko a waya ba gaskiya."
"Kuma baki neme shi ba?."

"Na kira shi jiya amma layin a kashe." Yaya Ummi tace, "inda nice ke Rauda da Asad d'in nan zan aura badan yafi Anas kud'i da mulki ba sai dan na nunawa uwar sa ba'a ja da ikon Allah, duk k'ask'ancin mu da take gani in Allah yace yes bata isa tace no ba duk abinda take ji dashi sai dai tayi ta gama ta d'auki jikan da zaki haifar mata. Gurguwa, bak'a mai tallan abinci da take rainawa ta zama mata ga d'an nata da take ji dashi sai naga uwar abinda zatayi." Rauda tayi murmushi tace, "Nima zan so hakan Yaya kodan naga yanayin da zata shiga a wannan lokacin, amma sam ni bana ra'ayin auren sa."
"Kiyi ra'ayin yanzu Rauda, kar ki manta tun ba yau ba kina yawan ce min kinyi mafarki da namiji mai rawani a kansa wataƙila Allah ne ya nuna miki auren sa tun a mafarki. sannan istikhara da kika yi Allah ya nuna miki a mafarki ko?."

Rauda tace, "Haka ne Yaya Ummi amma hakan ba yana nufin shi zan aura ba. Nifa bazan iya zama matar sa ba gaskiya in na aure shi nayi ya da k'iyayayar mahaifiyar sa?." Yaya Ummi ta dawo kusa da ita ta dafa ta tace, "Shi zaki aura Rauda, ki saka a ranki shine mijin ki da zarar an tambaye ki kice kin amince." Rauda ta kalli Yaya Ummi tace, "Nifa bana son sa ta yaya zan amince?."
"Sabida mu nunawa babar sa iyakar ta, mu nuna mata duk abinda kake ji dashi baka isa kaja da ikon Allah ba."
"Ni tsoron gidan sarauta nake fa Allah ya sani."
"Ki ajjiye tsoron ki saka a ranki a nan aka haife ki."
Rauda ta kalle ta da mamaki tace, "Yaya Ummi in na amince da Asad Anas fa? Nayi masa adalci kenan duk tarin d'awainiyar da yayi dani dan na samu wanda ya fishi na watsar dashi...?."

#Vote
#Comments
#Share.

*KWANTAN ƁAUNA*
Fitattubiyar 2023

             ©️ *Nana Haleema.*

*Book 1*
*025.*

Yaya Ummi tayi shiru alamun tunani kafin ta sauke numfashi ta kalli Rauda tace, "Tabbas Anas ba abin yarwa bane ba, in muka watsar da Anas bamuyi adalci ba." Rauda rausayar da kai tace, "Abinda na gani nima kenan, zan iya auren Anas na zauna dashi duk da bana jin sonsa a zuciya ta har gobe, amma halayyar sa da yadda yake nuna tsantsar so a gare ni zata saka naso shi nan gaba."

Yaya Ummi tace, "Haka ne Rauda, ki cigaba da addu'a kedai kawai duk abinda ya zama alkhairi Allah ya zab'a maki."
"Ina yi sosai." Yaya Ummi zatayi magana kenan aka bud'e k'ofar aka shigo Baba ne da kuma maza guda biyu a bayan sa ganin su waye ya saka Yaya Ummi tashi tsaye tana fad'in, "Sannun ku da zuwa."

D'aya daga cikin su yace, "Yauwa Ummi, ya mai gidan naki?." Yaya Ummi tace, "Alhamdulillah." Gaisawa sukayi har Rauda kana d'aya daga cikin su yace, "Jiya nazo wucewa ta k'ofar gidan ku na tarar an baje gidan gabad'aya ya koma fili ana sabon gini na bulo, daman kuma ina ta ji a gari ban tabbatar ba sai dana gani da ido na; sai yanzu mahaifin ku yake shaida min abinda yake faruwa."

Kawu Badamasi yace, "Ke daman kin san shi ne tun a baya har ya furta yana sonki?." Rauda ta girgiza kai tace, "A'a Kawu bansan shi ba." Ya girgiza kai yace, "ikon Allah kenan, abinda baka tsammaci faruwar sa ba sai kaga ya faru." Kawu Lawan yace, "To ke meye a ranki kenan?." Rauda tayi shiru bata amsa ba Baba yace, "ita bata yanke hukunci ba har yanzu; akwai wani yaro Anas da yake sonta yana hidima da ita sosai ina tunanin shine a ranta."

Kawu lawan yace, "ba d'an gidan Alhaji Tasi'u mai farin gida ba?." Baba yace, "Shi." Kawu lawan yace, "to ai ni Alhaji Tasi'un ya aika min da mutane guda biyu na d'auka ma ko neman auren ta suka zo wajena sai suke shaida min shine ya turo su yace a sanar damu ya yiwa d'ansa mata kar a jishi shiru kwana biyu zai masa aure ne. Sun shaida min bazasu iya had'a ido da kai ba sabida kunya shiyasa suka je wajena kai tsaye." Baba yace, "ikon Allah! Amma baka sanar dani ba."
"Na d'auka shi yaron ai ya sanar dakai ko ya sanar da ita."

Baba ya girgiza kai ransa fari karr har hakan ya bayyana a kan fuskar sa yace, "basu zo inda nake bama shiyasa kwana biyu shiru babu motsin yaron, Allah sarki ni shaida ne yana son Rauda amma da alama iyayen sa basa son alaqar su tare shiyasa suka yanke wannan hukuncin, Allah ya zab'a mafi alkhairi." Kawu Badamasi yace, "Amin. Baza muyi saurin cewa iyayen ne basa son alaqar ba wataƙila alqawarin aure ne sukayi zasu had'a shi yaron bai san dashi ba shiyasa yake neman Rauds. Rauda karki yiwa kanki dole dan ganin kud'i ko dukiya ko kuma sarauta, yanzu maganar Anas ta k'are kinji duk abinda yake faruwa da kunnen ki, kar kice tunda babu batun Anas yanzu bara na amince da d'an sarkin kar kiyi haka kiyi addu'a ki kuma bi zab'in zuciyar ki."

Kai ta girgiza alamun gamsuwa Baba yace, "Ai ana ta addu'a duk inda na bayar ayi mana istikhara sai kaji ance auren sa da ita alkhairi ne ba kad'an ba. Daman Anas d'in nan nake ji tunda abin yazo da haka wallahi nafi kowa farin ciki  ya auri zab'in iyayen sa itama ta auri Asad d'in shikenan an huta." Kawu Badamasi yace, "A'a, ka barta ta zab'i abinda take so dan Allah kar abin duniya ya rufe mana idanu mu kaita inda zamu zo muna dama mun sani bamu kaita ba, dan ni Allah ya sani wani lokacin bana yi mata sha'awar shi yaron mai martaba sabida abinda zata tarar ba abu kad'a bane. Na farko da ga babar sa, na biyu ga sauran jama'ar gidan, na uku har abada gidan sarauta bazasu tab'a girmama ta ba k'ask'ance zata rayu dan su gidan sarauta indai ba y'ar gidan sarauta ka d'auko ba talaka sunan ka balle kuma Rauda."
Chapter 53 · 0% Book details