← Book details Kwantan Bauna Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 5 OF 55

Sashe 5

Kwantan Bauna Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

"Sarkin mu na gobe, kaine yarima mai jiran gado, masarautar katagum taka ce, kai sarki, mahaifin ka sarki, kakan ka sarki, mahaifin mahaifiyar ka sarki. Allah ya ja zamanin Aliyu gadanga k'usar yak'i, daga kan ka an gama sarauta, kaine zakayi ko basa so sai ka hau karagar mulkin katagum." Lumshe idanu yayi jin kirarin da yake masa bai san lokacin da murmushi ya sub'uce masa ba ya kalle shi sai kuwa ya sunkuyar da kai yace, "Duk mai shirin bamu matsala akan hawa karagar mu zamuyi maganin sa ko waye, kar yarima ya damu muna tare dashi za kuma mu bashi goyan baya duk wahala duk dad'i, ko da tsiya koda tsiya-tsiya sai Aliyu ya gaji katagum koda Za'a rasa rai."

Jin hakan sai Aliyu ya bud'e bakin sa a hankali yace, "Asad."
"Shi d'in wa? Ana zancen mutanen k'arfafa wa yake zancen rago Asad?, mulki naka ne sai dai Asad ya duk'a a gaban ka ya kwashi gaisuwa, shi waye da zamu duk'a masa?, wane mutum balle aljan?. Mulki na k'arfafa ne ba irin Asad ragwaye ba, mulki na madu dakakkiyar zuciya ne ba irin Asad maau rauni ba. Allah ya ja zamanin yarima bai kamata Asad ya dinga damun ka ba domin ta ko ina kaine a sama bashi ba, waye zai d'auki mulki ya bawa kurma...?" wanda yake amsa sunan Hashim yake fad'a yana kallon sa cikin girmama irin wacce ake yiwa sarakai.

Murmushin jin dad'i Aliyu yake yi duk duniya babu abinda yake k'auna sama da hawa karagar mulkin gidan su, babu abinda yake so sama yaga manya da yara suna duk'awa suna gaishe shi duk tsufan su haka duk yarintar su, yana so yaji ana buga masa tambari ana buga masa bindiga ana bud'e masa lema ana binsa a guje ana yi masa fifita. Asad yana neman zama cikas a cikin lamarin sa, burin sa da yake mafarki kullum Asad yana k'ok'arin ganin ya tafi a banza ba tare da ya tabbata basketball, sake kallon Hashim yayi har zaiyi magana sai kuma ya fasa ya d'auki wani pack a gefen sa ya bud'e ya d'auki kwayar da take bugar dashi yasha ya kora da ruwa yana sauke ajiyar zuciya. Murmushi Hashim yayi ya mik'e ya fita dan yasan ba kasafai yake son magana ba shi kuma ya lumshe idanun sa zuciyar sa na kawo masa abubuwan da ya kamata yayi a kan Asad.

*ASAD.*

A zaune yake a k'aramin falo ya hard'e yatsun sa waje d'aya yana kallon wani wajan daban idanun sa a kulle kamar mai tunani, wanda yake zaune kusa dashi kallon sa kawai yake yi kafin yace, "Asad hak'uri zaka yi fa babu yadda zakayi." Numfashi ya sauke ya buɗe idanun sa ya kalle shi kamar zai magana sai ya fasa ya koma ya jingina da kujera ya d'ora k'afa kan d'aya yana kad'awa.

"Kai kad'ai ne ka dace da sarautar garin nan ka fi kowa ilimi da girmama talakawa, kai kad'ai ne kaf gidan nan baka yiwa bawa tsawa sai dai murmushi koda bakayi magana ba, kai kad'ai ne zaka cigaba da gunadar da mulki kamar mai martaba, matuk'ar sarautar nan ta bar hannun ka sarautar garin ta lalace gabad'aya" wanda yake zaune kusa dashi ya fad'a yana kallon sa. Lumshe idanun sa yayi ya buɗe ya kalle shi a hankali ya furta, "ni kuma bana so, why sai ni?."

Jin yadda yayi maganar ya saka Suhail yayi murmushi yace, "kamar ba yanzu na gama fad'a maka qualities d'in ka ba?, bazan b'oye maka ba ko mahaifi na da yake k'ani a wajan mai martaba matuk'ar ya karb'i sarautar nan sai ya lalata komai, domin kansu kawai suke hange ba talakawan su ba, kaine ka dace dole ka hak'ura." Jijiyoyin kansa ya dafe yana murza wajan a hankali zuciyar sa na kawo masa abubuwa da yawa. _Meyasa ma suke zancen shine zaiyi sarki bayan mahaifin sa na raye kuma yana kan mulkin?._ ya tambaya a zuciyar sa yana so ya furta a bakin sa amma baya tunanin zai iya hakan ya saka shi ya sake yin ajiyar zuciya baice komai ba.

Mik'ewa Suhail yayi ya k'arasa wajan fridge ya d'auko fresh milk ya had'o da glass cup ya dawo kusa dashi ya zuba masa madarar ya mik'a masa yace, "karb'i ka sha zaka ji dad'i a zuciyar ka." Bai motsa ba kuma bai karb'a ba hakan ya saka Suhail yace, "please ka karb'a." Baya son magana hakan ya saka shi ya karb'a ya rik'e a hannun sa ba tare da ya sha ba.

Cigaba da magana Suhail yayi yace, "burin Mama ne ka daure ka cika mata shi nasan an tauye ka da yawa, burin ka na zama babban malamin addini a k'asar Saudia ya rushe ta dalilin sarautar nan amma ya zakayi abinda Mama take so ne, kayi hak'uri ka dinga bin abinda tace in Allah fa yayi baza kayi mulkin nan ba sai kaga baka yi ba."

Dai-dai lokacin da ya kai kofin madarar bakin sa zai kenan daga bayan sa aka ce, "Asad!." A firgice ya fasa sha ya juyo yana kallon wanda ya shigo ya juya idanu dan daman yasan sai shi d'in ya d'auke ido daga kan sa dan ya tsorata shi. Abokin sa Hafiz kuma MD na kamfanin Asad ya fad'a yana shigowa cikin falon yana kallon sa yana kuma kallon Suhail.  Zama yayi a nesa dashi yana kallon sa yace, "lafiya kake?."

Fuska ya d'aure sosai domin yasan Suhail da Hafiz basa jituwa ko kad'an koya suka had'u zasu so suyi hayaniya shiyasa baya so su kasnace waje d'aya suna bashi ciwon kai,  ganin hakan sai Suhail ya murmusa ya mik'e yace, "Deaf zamu had'u anjima." Fita yayi daga falon Hafiz ya kalle shi yace, "u know what deaf?, sam zuciya ta bata amince da wannan Suhail d'in a kusa da kai ba, u have to be very careful kasan yanzu kowa kai zai dinga hari tunda mai martaba ya furta zai sauka a mulki ya baka kowa burin sa yaga ya kawar da kai."

Kallon Hafiz kawai yake yi kafin ya tab'e baki yace, "I trust him."
"Kai ai daman zuciyar ka ta amince da kowa shiyasa ake cutar ka a ko wanne lamari, lamarin sarauta ba abu bane mai wasa kar ka manta mahaifin sa na neman mulkin nan za'a iya had'a baki dashi a cuce ka." Kallon sa yayi har ya bud'e baki zaiyi magana sai ya fasa ya d'auke kansa kafin ya d'auko waya yana dubawa.

Hafiz ya kuma cewa, "ya dai kamata ka nutsu kasan abinda kake yi yanzu da kake gani kowa neman ganin bayan ka yake yi. Baka san komai ba a gidan kasancewar rayuwar ka Madina ka yita shiyasa kake d'aukar yarda ka bawa kowa."
Nan ma bai amsa masa ba yasan daman bazai bashi amsa ba hakan ya saka shi baice komai ba shima ya cigaba da danna wayar sa. Gajiya da zaman Asad yayi ya mik'e ya shiga ciki bai sake magana ba shima kuma Hafiz bai kuma ba.

Da daddare kamar yadda mai martaba yace yana neman sa bayan sallar i'sha ya tabbatar yana cikin gida ya nufi cikin gidan da yake da girman gaske, tun daga k'ofar da zata kai ka B'angaren mai martaba dogarai ne bila adadin har da jami''an taaro da suke gadin wajan sabida abinda zai zo wanda zai cutar dashi. Tunda Asad ya doshi wajan ake kwasar gaisuwa sai dai ya d'aga kai kawai har ya iso babbar k'ofar da zata kai shi falon mai martaba, Sai da aka bashi izinin shiga sannan ya shiga da sallama a nutse yake takawa har cikin falon.

Bai ma kula da wacce take zaune ba ya duk'a ya kai gaisuwa kafin ya zauna har lokacin bai d'ago ba, "Asad!" Mai martaba ya kira shi ya d'ago yace, "Na'am, Allah ya ja da ranka."
"Gobe in Allah ya nuna mana zamuyi tafiya zuwa Kaduna dakai."
Kai ya d'aga kafin yace, "Allah ya nuna mana goben."
"Amin. Kaje shine neman da nake maka daman."
"Nagode, a tashi lafiya" ya fad'a yana mik'ewa ya fita.

Da kallo uwar gidan sarki ta bishi tana murmushi ta kalli mai martaba tace, "Takawa in Asad ya karb'i mulkin garin nan talakawa zasu huta zasu ji dad'i domin kuwa har ya fika zuciyar tausayi." Murmushi jin dad'i yayi babban burin sa a nuna masa kulawa ga Asad shiyasa koda yaushe Sa'adatu take burge shi tana son Asad sosai tana kuma yabon kyawawan halin sa yace, "Shine fatan da nake yiwa masarautar nan domin Asad shine kad'ai zai gyara duk wata b'arakar da take cikin ta, amma sam baya so shiyasa na dakata da batun ajjiye sarautar zuwa nan gaba."

"Zai so ma tunda yana jin maganar ka na tabbata zai so, mu kam mu Asad ya karb'i mulkin garin nan ai jin dad'in mu ne balle kuma talakawan sa." Murmushi mai martaba ya kuma yi yace, "zai kasance in sha Allah."
"Muna fatan hakan, shiyasa tun yanzu na fara nema masa maganin tsari daga garin mudan maganar da ka furta na zaka bashi mulki Allah kad'ai yasan magautan da suka sako shi gaba. Nasan mai martaba yana nema masa shima kuma yana yiwa kansa tawa gudunmawar nake so na bayar."

Mai martaba yace, "Shiyasa nake alfahari da kasancewar ki babba cikin matana, kinyi tunani mai kyau dan a yanzu haka Allah kad'ai yasan adadin jifan da ake masa."
"Allah zai kare mana shi koma waye zai koma kansu."
Shiru tayi kafin kuma tace, "Takawa in an bamu izini zan shiga gida na dawo." Kallon ta yayi ya d'aga kai tayi godiya ta tashi ta fita.

          B'angaren ta ta koma ranta a matuk'ar b'ace jikin ta har rawa yake sabida bak'in ciki da hassada ta wuce cikin d'akin ta hannu na rawa ta d'auki waya, duka biyu aka d'auka tace, "Matuk'ar ba kawar da Asad mukayi daga doron duniya ba tabbas masarautar nan sai ta gagare mu shigowa nan gaba, mai martaba yana nan a kan bakar sa na bashi mulki ya dakata ne sabida wani dalili nasa amma ko gobe yaso zai sauka ya bashi karagar ya hau, bana fatan wannan bak'in labari ya tabbata ina raye ka san abin yi."
Chapter 5 · 0% Book details