← Book details Kwantan Bauna Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 12 OF 55

Sashe 12

Kwantan Bauna Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Zama tayi kusa da ita tace, "Zan jira ki a nan." Suna nan zaune ga abincin bai k'are ba Rauda taji jiri yana d'aukar ta ta mik'e tace, "Khairi d'auki kular nan muje kawai." Ba musu ta tashi ta d'auka suka tafi. A hankali suke tafiya dan sosai Rauda take jin jiri sabida yadda kanta yake sarawa.
Titi suka zo tsallakawa Khairi ta tsallaka ta barta tana fad'in, "kya tsallako da kan ki dan nasan halin ki da tsoron titi bazan jira ki ba."

Rauda bata ce komai ba ta saka k'afa a kan titi da niyar tsallakawa  sai da tazo tsakiya ba zato babu tsammani taji anyi sama da ita an dawo da ita k'asa ta fad'i a gaban motar, wata razananniyar azaba taji a dukkan ilarin jikin ta musamman k'afar ta dalilin hakan ya sanya ta sumewa a wajan. Ihuu Khairi tayi a haukace tace, "Anty Rauda!" Ta fad'a a guje tana tsalkawowa daidai lokacin wanda yake zaune a cikin motar ya fito a gigice yana kallon Rauda da take kwance cikin jini hankalin sa a tashe............

*KWANTAN ƁAUNA*
        FitattuBiyar 2023.

          ©️ *Nana Haleema.*

*Book 1*
*006.*

A guje Ummulkhairi ta tsallako a lokacin Hydar yayi inda take kwance hankalin sa a matuk'ar tashe ya d'auke ta cak ya saka a bayan mota bai ma kula da Ummulkhairi da take kuka ba ya shiga motar ya ja a guje a hankalin sa tashe. Kasancewar titin babu jama'a sosai babu wanda ya lura da abinda ya faru Ummulkhairi ta kwasa a guje ko ta kan kwanikan abincin bata bi ba ta tafi gida.

Babban asibitin kud'i na garin ya wuce da ita jikin sa gabad'aya rawa yake fuskar ta ta tasa lokaci d'aya har lokacin bata motsin kirki, k'ara gudun motar yake yi har ya isa asibitin nan take yayi waya akayi sa'a likitan da yake nema yana nan aka fito a guje aka d'auke ta aka wuce ciki. Gabad'aya ya kasa nutsuwa yana zaune a office d'in Dr amma zuciyar sa bugawa take da sauri, bai tab'a buge koda kaza ba tunda ya fara tuka mota sai wannan lokacin, shiyasa hankalin sa ya tashi sosai.

Sun jima matuk'a a kan ta kafin Dr ya shigo yana ganin sa ya kalle shi alamun k'arin bayani nake nema, Dr ya zauna yace, "Prince ta samu karaya a k'afar ta munyi x-ray na k'afar mun gano k'ashin da yake rik'e k'afar ta baya wanda ya kasance bashi da k'wari ya karye shima, k'afar ta d'aya lafiya take sai dai buguwa da tayi amma d'ayar gaskiya tana da matsala munyi iya abinda zamu iya a yanzu in abin baiyu ba gaskiya dole sai anje Egypt."

Hydar ya sauke numfashi ya lumshe idanun sa ya bud'e ya kalli likitan yace, "Yanzun jiran me za'a yi baza a tafi can ba?." Dr yace, "dole za'a jira ciwon ya warke in ka lura karaya ce mai jini ma'ana karaya ce mai had'e da ciwo, in ciwon ya warke in abinda muka yi  bai ba shine za'a fitar da ita." Baice komai ba ya mik'e ya fita ya shiga d'akin da take yana kallon fuskar ta da ta kunbura amma kamannin ta basu gushe ba.

Kallon ta yake k'irjin sa na bugawa ga k'afar ta a d'aure haka goshin ta ma an manne shi sabida ciwon da ta samu, numfashi yake fesarwa dana sanin fitowar sa daga gida gabad'aya ta damalmale masa zuciya ya fito daga d'akin suka had'u da Dr d'in a k'ofar d'akin yace, "A nemo family nata but bana so a sanar dasu nine na kad'e ta, a tabbatar musu da za'a tsaya ta samu lafiya ko nawa ne za'a kashe" abinda ya fad'a kenan kawai ya fita daga wajan bai jira ma yaji mai likitan zai ce masa ba.

A can gida kuwa a guje Ummulkhairi ta shiga gida tana fad'in, "Umma! Umma!!" Umma da take tsakar gida ta kalle ta tace, "Khairi lafiya wannan wanne irin kira ne?." Jikin ta har rawa yake tace, "Anty Rauda!, Umma Anty Rauda!" abinda take maimaitawa kenan tana haki alamun ta sha gudu.

Hankalin Umma ya tashi ta k'araso kusa da ita tana fad'in, "me ya sami Rauda d'in? Tana ina?, me ya same ta?."
"Wani ne ya kad'e ta a mota tana kwance bata numfashi Umma, jini yana ta zuba daga jikin ta Umma" ta kuma fad'a har lokacin bata dawo dai-dai ba tana hakki.

"Innalillahi wa'inna ilaihir raji'un, wani ya kade ta fa kika ce Ummulkhairi?."
"Eh Umma, ya d'auke ta a mota sun tafi."
"Hasbunallahu wani'imal wakil, Innalillahi wa'inna ilaihir raji'un!" Abinda Umma take fad'a kenan jikin ta na rawa itama Inna Babar su Rahma kenan ta fito itama tana salati tace, "To banda shirme kuma irin naki sai ki bari su tafi baki bisu ba?."

"So nake nazo na fad'a muku, Umma Anty Rauda jikin ta duk jini ko motsi bata yi" ta k'arasa fada tana fashewa da kuka ta zube a wajan. "Kukan me nake ji haka?" Baba ya fad'a yana shigowa yana kallon su. Ba wanda ya iya magana yace, "Ya naga kunyi cirko-cirko kamar wad'an da aka yiwa mutuwa?, ke ina Rauda?."

"Baba wani mai babbar mota ne ya kad'e ta ya d'auke ta suka tafi a mota." Baba yace, "Ya kad'e ta fa kika ce? A ina ya kad'e ta?, waye shi?."
"Baba ban san shi ba, ya dai kad'e kuma ya saka ta a mota sun tafi."
"Innalillahi wa'inna ilaihir raji'un" abinda Baba ya furta kenan ya fita daga gidan hankalin sa a tashe.

Dukka mutanen gidan Hankalin su a tashe yake sun kasa koda zama musamman Umma Khairi kuma har lokacin kuka take sosai hankalin ta ya kasa kwanciya tunda a gaban ta akayi ba kuma ta tab'a ganin hatsari a zahiri ba sai a kan wannan. Baba ya jima da fita ya dawo Umma tace, "Malam an same ta?." Baba yace, "ban samu komai, inda aka buge ta d'in tabbas ga jini nan har yanzu yana wajan amma babu wanda yazo ya bada sanarwa koda y'an uwan ta zasu neme ta."

Umma ta dafe kanta tace, "Innalillahi wa'inna ilaihir raji'un, yanzu a ina zamu same ta gashi har dare yayi?." Baba yace, "ki kwantar da hankalin ki ko waye ya buge ta zai nemi dangin ta ai kodan kula da lafiyar ta, kiyi hak'uri."
"Ka gani ko?, kaga illar tallan da suke fita ko? Yanzu da basu je tallan ba da babu abinda ya same ta."
"Tsautsayi ne ko tana gida sai ya same ta" ya fad'a yana fita daga gidan gabad'aya.
Umma kasa magana tayi sai tagumi da tayi kawai zuciyar ta na k'una da zafi domin bata san halin da y'ar tata mai tausayin ta take ciki ba.

*◇◇◇*
Lokacin da Hydar ya shiga gida b'angaren mahaifiyar sa ya wuce a nan ya same ta a zaune ita da Asad ta saka shi a gaba tana ta jero masa tambayoyi amma guda d'aya ya gaza bata amsa, yadda ya shigo ya saka ta bishi da kallo tace, "Hydar lafiya?." Kusa da Asad ya zauna yayi shiru kafin ya kalle ta yace, "Accident nayi."

Suhaima tace, "Accident a ina?." Kafin yayi magana Mama tace, "Babu abinda ya same ka?."
"Babu Mama, but na buge wata yarinya yanzu haka ta asibiti unconsciously."
"Da ranta dai ko?" Suhaima ta tambaya tana kallon sa. Kai ya d'aga alamun eh Mama tace, "A ina take yarinyar?."
"I don't know, but zata tsallaka titi ne kawai sun fito daga kasuwa, I think tana sai da abinci ne."

"Mtswww, to meye na damuwa? Ba ka kaita asibiti ba?" Ta fad'a tana kallon sa ganin yadda ya wani damu akan y'ar talakawa. Hydar yace, "Ranki ya dad'e Dr ya tabbatar min in abinda akayi bai yi ba sai an kaita Cairo an yi gyaran a can, taji ciwo sosai a k'afar ta kuma nine sila dole na damu." Mama ta tab'e baki tace, "Is okay tunda dai kai lafiya kake, kaje ka huta." Jikin sa a sanyaye ya mik'e sai a sannan Asad yace, "Sorry Bro." Kai ya girgiza kawai ya fita daga apartment d'in.

"See him akan wata yarinya yar talakawa yake wannan damuwar, I hate dis" ta fad'a tana bin sa da kallo tana yatsine fuska kafin ta dawo da kallon ta ga Asad da yake kallon ta tace, "Dis time bazan d'aga maka k'afa ba Asad dole kaje ka nemo auren Jidda itace zab'ina a wajan ka sai kuma ka aure ta." Kai ya girgiza baice komai ba dan bai san me zaice mata ba.

Baiyi magana ba Suhaima taji wayar ta na k'ara ta mik'e ta fita daga falon gabad'aya ta nufi can k'arshen gidan ta hango wanda ya kira ta a tsaye yana jiran ta, "Hello Suhail, I hope lafiya kake nema na haka?" Ta fad'a tana kallon sa. Kallon ta yayi yace, "lafiya lau Auta, akwai wani abu da nake so na baki ne ban sani ba ko zaki karb'a."
"Meye shi?."
"Magani ne nake so ki bawa Asad ya sha ba tare da ya sani ba." Wara idanu tayi tana k'are masa kallo mai cike da harara da mamaki ganin hakan ya saka shi yin murmushi yace, "bazan cutar da Asad ba kin sani, tunda kika ga na kawo masa kin san naji wata magana ne da take shirin faruwa."

Hannu ta d'aga masa tace, "Bana daga cikin wad'annan shirmen naku kai ka sani, baza kuma ka hani wani abu kace na bawa Asad ba tare da ya sani ba, baza ka had'a kai dani a cutar dashi ba." Ya matso kusa da ita yace, "ba cutar dashi zanyi ba Suhaima, ke kin san baza'a tab'a had'a kai dani a cutar da Asad ba because he's my favorite cousin and he's my friend, wannan maganin da zan baki in ya sha zai karya dukkan abinda za'a aiko masa dashi, u know rayuwar Asad tana cikin hatsari a yanzu, kowa neman ganin bayan sa yake ki taimaka ki karb'a ki taimaki Yayan ki."
Chapter 12 · 0% Book details