← Book details Kwantan Bauna Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 25 OF 55

Sashe 25

Kwantan Bauna Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

"Na'am Yaya Asad" ta bashi amsa tana kallon sa shima kuma ita yake kallo da mamaki shinfid'e a kan fuskar sa. kallon k'ofar falon yayi ya dawo da kallon sa gare ta sai tace, "Mama ce ta bani fresh milk tace na saka maka a fridge shine nake waya nace na saka." Kai ya jinjina kafin yayi gaba sai kuma ya tsaya ya juyo ya kalle ta yace, "bayan yau ta tab'a aiko ki?." Kai ta girgiza alamun A'a tace, "bata tab'a ba, yau d'in ma dan bata fito bane ba ya saka ta bani, ni kuma bazai koma ciki ba shiyasa nake sanar da ita a waya."

Baice komai ba ya shiga d'akin wajan fridge ya nufa ya bud'e yaga madarar a ciki ya kulle ya shiga d'akin sa yana k'are masa kallo kamar wanda yake neman wani abun kafin ya sauke ajiyar zuciya ya tsaya a jikin mudubi yana kallon kansa. Wani abu ya gani ya gifta ta bayan sa bai juya ba ya cigaba da kallon mudubin ya sake ganin giftarwa abu hakan ya saka shi ya juya da sauri amma bai ga komai ba.
Wajan da yake ganin abun yake nufa amma baya ganin komai hakan ya saka shi kulle idanu ya bud'e tunda ya fara mafarkan nan sai ya dinga ganin abun kamar a zahiri ne yake faruwa.

Bai jima sosai ba ya kuma fita yaje masallaci ya dawo suka had'u da Hafiz a k'ofar shiga falon suka shiga tare, suna zama Suhail ya shigo da sallama Asad ne kawai ya amsa banda Hafiz ya samu waje ya zauna yana fad'in, "kwana biyu kowa ya b'uya." Asad girgiza kai kawai yayi Hafiz ya kalli Suhail yace, "ko zaka iya bamu waje magana zamuyi." Suhail ya kalli Asad ya kalli Hafiz ya murmusa ya mik'e tsaye yace, "okay babu damuwa."
"Noo zauna" Asad ya fad'a yana danna wayar sa jin hakan Suhail ya koma ya zauna Hafiz takaici ya sake kama shi ya girgiza kai amma baicr komai ba

Shiru wajan ya sake d'auka dan shi dai Hafiz bazai yiwa Asad magana Suhail yana nan ba shi kuma Asad bazai yi maganar ba, Suhail ya mik'e yace, "Sai da safe" yana fad'a ya fita Hafiz kamar jira yake ya kalli Asad yace, "Abinda kake yi fa sam ba mai kyau bane ba, kasan manufar Suhail a kanka amma ka dinga zak'ewa kana barin sa kusa dakai bayan nida kai mun san dama kad'an yake nema a kan ka ya halaka ka amma kake bashi fuska har haka."

Shiru yayi kamar bazai amsa ba jikin sa wani iri yake ji cikin kwanakin gabad'aya baya son zaman gidan yana jurewa ne kawai sabida Mama amma da tuni ya bar k'asar, "Ka nunawa wanda yake neman ka da sharri baka san yanayi ba yafi riba" ya bashi amsa yana kallon sa shima yana kallon sa.
"Amma kasan....." dakatar dashi Asad yayi yace, "Bana son magana a kan hakan. Muyi abinda nace."
"Okay better" ya bashi amsa shima kafin ya mik'e ya fita dan bazai yi maganar ba shima ya fasa.

Murmushi Asad yayi bayan ya fita cikin su biyun shi dai ya rasa wanda yafi sonsa ko wanne burin sa ya bashi kariya shiyasa yake ji dasu baya so yaga an tozarta wani a gaban sa. Duk da shi ba wani sakewa yake da abokai ba amma babu laifi su kan danyi hira sama-sama.

Tashi yayi ya fita daga apartment d'in gabad'aya yana takawa a hankali kamar ko yaushe ana zubewa ana kwasar gaisuwa yana amsawa a ciki, zaga gidan kawai yake badan akwai abinda zaiyi ba sai dan haka zuciyar sa take bashi umarni, har yazo b'angaren da yake da duhu sosai har ya gota sai kuma ya dawo da baya jin abinda ake cewa, "ku bari kawai shima Asad d'in maganin sa zamuyi yadda muka kwantar da Hydar shima haka zamu kwantar dashi, ko muyi masa kurciya ya bar k'asar gabad'aya bazai sake dawowa ba har abada." Dariya yaji anyi kafin yaji ance, "Allah yaja zamanin Master planer, Asad bazai tab'a mulkar garin nan ba in sha Allah, jinin Rabi'atu baza suyi sarauta ba in Allah ya amince."

Motsi yaji alamun za'a fito ya tsaya a wajan cak yana jiran yaga wacce zata fito, rad'ad'in da ya kawo masa ziyara a idanun sa ya saka shi kulle su ba tare da yayi niya ba yana juya kansa yana so ya bud'e amma ya kasa idanun nasa ruwa suke yi, hannu ya saka a aljihu ya d'auko tissue yana goge idanun nasa hankalin sa na wajan da yake jin maganar amma baya gani sosai, sai da ya d'an samu sauk'in idon ya d'auko wayar sa ya kunna haske ya sake haska wajan amma babu kowa alamun da gangan aka saka masa abu mai yaji a idanun sa.

"Asad me kake yi a nan?." Jin tambayar daga bayan sa ya saka shi ya juya yaga Hajiya a tsaye tana kallon sa. Mamaki ya kama shi uwar gidan sarki mai zai kawo ta wajan a wannan lokacin da ba kowa yake yin hanyar ba..? amma bai nuna mata mamakin sa ba sai ya goge idanun sa yace, "babu komai" yana fad'a ya wuce tabi bayan sa da kallo ta murmusa kafin ta bar wajan.

D'aki Asad ya koma yana zagaye hankalin sa a tashe matuk'a, bai tab'a jin tashin hankali akan abubuwan da suke faruwa ba kamar yadda yake ji yau. Babban tashin hankalin sa sunan Hydar da yaji suna ambata kenan duk rashin lafiyar da yake yi sune suka jawo hakan?. Suna saune suke kwantar dashi dan rashin imani..? Su waye ma a tak'aice....?. Kama k'ugu yayi ya furzar da iska mai zafi yana sauke numfashi, "me ya kai Hajiya wajan a yanzu?" Ya tambayi kansa nan ma babu amsa ya had'd'iye  saliva a jikin sa yake jin lokaci yayi da kowa ya kamata yasan waye Asad.

*Bayan wasu kwanaki.*

"Malam dan Allah in ka fita ka biya ta wajan sarkin d'ori ku tawo da ko yaron sane yazo a duba k'afar Rauda. Gashi dai ta samu lafiya amma k'afar ta nakasa yazo ya gani in akwai abinda za'a yi" Umma ta fad'a tana kallon Baba. Baba da ya gama saka takalmi yace, "in aka d'auko sarki d'ori ke zaki biya shi?."
Umma ta buɗe baki tana kallon sa shima yana kallon ta yace, "Nidai bazan biya ba in zaki biya yanzu za'a tawo dashi."

Umma tace, "Shikenan azo dashi sai na biya d'in."
"Zab'i mai kyau, kuma kin san dai biyan da tsada tunda gida zai zo sai ki tanadi kud'i."
"Zan bayar ko nawa ne."
Ya k'are mata kallo yace, "Da uwar kud'in ki a k'ugu amma asahana in ta kare sai a turo min yaro" ya fad'a yana fita ta bishi da kallo kawai.

Ba jimawa ya shigo yace, "ku gyara gashi mun zo dashi" ya fad'a yana komawa suka shigo tare aka shiga d'akin Umma ya fara duba k'afar Rauda da take zaune.

Mai gyaran k'afar da yake kusa da Rauda yana duba k'afar ta ya kalli Umma da Baba da kuma Inna yace, "Akwai sauran gyara a k'afar nan tata dole sai dai ayi mata aiki." Baba yace, "Aiki kuma?."
"Eh aiki Baba, amma kuje asibiti ayi hoton k'afar a kaiwa likita shi kuma zaiga inda za'a gyara sai ya fad'i kud'in ku biya." Umma ta girgiza kai tace, "to kuma zata iya tafiya?."
"Eh zata iya amma sai dai a bata sandina guda biyu, inda dama yanzu kuje asibitin ayi gaggawar duba k'afar tata in ba haka ba zai zama silar da za'a ce zata nakasa gabad'aya."

Baba yace, "to mun gode." Fita yayi Baba ya kalli Umma yace, "ke kina da kud'in zuwa asibitin ne?." Umma ta girgiza kai a raunane tace, "bani dashi. Suke nan na hannuna kuma na bayar yanzu." D'an k'aramin tsaki yaja ya kawar da fuska gefe yna jin haushin ciwon nata kawai za'a saka shi kashe kud'i kafin ya fita. Inna tace, "abu kad'an zai zama sanadi." Umma tace, "Allah ya yaye." Rauda dai tana jin su jikin ta yayi sanyi ta tabbatar ta rasa k'afar ta kenan sabida tasan kud'in aikin da za'a fad'a babu mai kud'in da zai iya biya.

Baba ya dawo yace, "ta tashi ta d'auki sandinan muje yanzun." Ba musu Umma da Inna suka kama ta ta tashi aka bata sandinan nata tana tafiya dasu a hankali har suka fita suka ga taxi Baba ya taro aka kwantar da ita a baya Umma ta rab'a ta zauna Baba ya shiga gaba suka tafi. Wajan hoton k'afar suka fara zuwa suka hau layi abin mamakin Baba baiyi k'yashi ba ya bada kud'in akayi hoton suka shiga asibiti wajan likita. Tun safe suke zaune har azahar layi bai zo kansu ba duk sun gaji da zama gata ita kuma a kwance tunda k'afar ba kwari tayi ba.

Bayan azahar layi yazo kan su suka shiga duka su ukun aka bawa likitan hoton yana kalli hoton sosai ya gama Nazarin duk abinda yake jiki ya juyo ya kalle su bayan ya gama dubawa yace, "Akwai wani k'ashi da ya tsage a k'afar ta yanzu kuma nama ya shiga tsakiya jini ya shiga sosai dole sai anyi aiki zan cire an had'e wannan k'ashin." Baba yace, "to kuma aikin yana kaiwa nawa?." Likitan yace, da yake bani zanyi aikin ba amma dai gaskiya yana kaiwa miliyan d'aya da dubu d'ari biyu koma yaje miliyan biyu. Aikin babba ne gaskiya dan ba'a jima da fara yin sa Nigeria ba Egypt ne da Germany da India kawai suke yin sa." A tare gaban su ya fad'i suka kalli juna Rauda idanun ta tuni sun wanke da hawaye Umma tace, "Tabd'ijam."
Chapter 25 · 0% Book details