← Book details Kwantan Bauna Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 3 OF 55

Sashe 3

Kwantan Bauna Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Wanda aka kira da Mubarak yace, "zai iya mana ranka ya dad'e, Allah ya ja zamanin mai martaba ai kaf dangin mu Asad shine ya cancanci kujerar sarautar katagum sabida ilimi da halayen sa masu kyau. A madina fa yayi karatun addini suka rik'e shi suka hana shi dawowa sabida tsabar ilimin da ya tara, gana zamani gana addini. Allah yaja da ranka ina jin an manta da cewa Asad shine wanda k'asar Saudia ta yiwa takardar shaida zama d'an k'asa dan akwai basa so suyi asarar sa?."
"Haka ne wambai, amma baka duba yanayin sa na k'in magana, ta ya shugaba zai kasance baya magana da wanda suke k'ark'ashin sa?. Sai abu ya k'ure sannan yake iya furta kalma guda d'aya fa."

Murmushi Wambai yayi yace, "zai koya ne koya ne mai martaba. Allah yaja da ranka ai a haka ma maganar tasa ba kamar daba, tunda ya dawo Nigeria ai yana magana a can fa in ba karatun alkur'ani ba to yana masallacin madina yana limanci." Murmushi yayi mai cike da izza kana yace, "Sai yanzu nake ganin ganganci da nayi wajan furtawa y'an uwana Asad zan barwa mulkin Katagum, tabbas nayi kuskure a wannan b'angaren dana bar abin a zuciyata sai dai aji na aiwatar hakan zaifi."

Wambai yace, "Allah yaja da ranka abinda aka riga aka furta ya wuce, sai dai dole mu dage da taya Asad da addu'a dan wannan maganar da mai martaba ya furta wasu suna nan da ita suke kwana suke tashi burin su bai wuce su samu hanyar da zasu kawar dashi ba dan cikar burin su."

Mai martaba yace, "Nasan da wanann, makusanta na sune suke wannan k'ok'arin na san da hakan. Amma in Allah ya amince babu abinda zai faru sai alkhairi. Dan ma Asad d'in ba baya bane wajan addini da yanzu sun haukata shi. Allah zai kiyaye."
"Da izinin Allah." Daga haka suka canja hirar zuwa wata daban.

         A guje ta shiga cikin babban falon jikin ta na rawa sosai ta zube a gaban wata babbar mace mai ji da jiki  mara haske sosai tana fad'in, "Allah ya ja zamanin uwar gidan mai martaba, Allah ya ja zamanin ki, Allah ya ja da ranki ya saka ki fi haka, Allah ya albarkace ki da iyalan ki. Ranki ya dad'e" ta fad'a tana mata jinjina hannun ta na k'asa. Kallon ta tayi daga inda take zaune tace, "Ramma lafiya?."
"Ranki ya dad'e yarima mai jiran gado na gani........"
"Duk sanda na sake jin kin kira shi da wannan suna sai na saka an k'ona bakin ki" ta dakatar da ita a fusace.

"Allah ya wuci zuciyar ki, tuba nake, nabi Allah na biki ki yafe ni." Tsaki ta ja sannan tace, "Ina jin ki."
"Asad na gani a k'aramar fada shi da mai martaba sunyi ganawar sirri."
"Ganawar sirri?" Ta fad'a tana mik'ewa zaune sosai tana kallon ta.

"Na tabbatar ranki ya dad'e, domin daga shi sai wambai a ciki ko dogarai babu, kuma ya jima a ciki kafin ya fito." Jinjina kai take yi kafin ta mata alamu da hannu taje ta mik'e tana godiya ta fita. Tashi tayi tsam ta shiga cikin d'akin ta ta d'auki waya ta kira number Waziri.

Duka biyu aka d'auki wayar yana d'auka tace,  "Kana da masaniyar ganawar sirri da mai martaba yayi da Asad?." Daga can b'angaren yace, "Bani da masaniya, meya faru?. Waye ya kawo miki wannan labarin?."
"Na tab'a kawo maka mara tushe ne?."
"Baki tab'a ba."
"Nifa kwata-kwata bana son mulki yaje hannun jinin Rabi'atu, tana yi mana kallo y'ay'an talakawa dan kawai  ta kasance jinin sarauta, da zarar d'an ta ya zama sarki tabbas mun shiga uku zaman gidan nan sai ya gagare mu,  dole nida kai mu san abin yi domin kuwa Asad ne kawai burin ta shima mai martabar shine burin sa ya zama dole muyi maganin sa."

Dariya wanda ta kira da Waziri yayi yace, "Ina raye, ina numfashi, ina da wayo, ina ji, ina gani, ina da lafiya, wani bai isa ya mulki masarautar katagum ba face ni. Nine na dace kuma nine zan yi, babu wanda ya cancanta sama dani. Rabi'atun banza da wofi balle wasu y'ay'an ta?, ki bar ni dasu zaki ga yadda zan b'ullowa lamarin matuk'ar ina raye karagar nan tafi k'arfin ta!?."

"Haka kake cewa koda yaushe amma ka kasa yin komai, da zafi-zafi ake dukan k'arfe amma kana barin sa yana wucewa, tun kafin mai martaba ya furta maganar murabus kake fad'ar haka yau gashi har ya riga ya furta ya kuma ambaci sunan Asad, da zarar an tabbatarwa da Asad mulki nida kai dole mu bi babu yadda zamuyi. A daina d'aukar lokaci in za'a yi kawai ayi bana son a dinga mayar da hannun agogo baya." Daga can b'angaren yace, "ki bani lokaci Asad bai isa yayi mulki ina da rai ba, yaron akwai tsari a jikin sa sosai dama kad'an nake so na samu nayi masa shigar sauri, zamu gani za kuma muji, kema kuma zaki gani" yana fad'a ya yanke wayar tabi wayar da kallo tana sauke numfashi zuciyar ta tana tafasa cike da bak'in ciki da b'acin rai. A shirye take da ta salwantar da duk abinda ta mallaka wajan ganin jinin Rabi'atu bai mulki katagum ba, zata iya salwantar da rai da lafiyar wani domin burin ta ya cika.

*☆☆☆*
          K'aramin gida ne kana kallon sa kaga gidan talakawa wanda basu dashi yanayin sa da komai nasa ya nuna zallar talakawa ne suke rayuwa a cikin sa, ko a yanayin unguwar kasan ta masu k'aramin k'arfi ce amma tana da babbar hanya wanda mota zata zo har k'ofar gida. Daga cikin gidan tsakar gida ne mara girma duk turb'awa ko arzuki siminti babu sai d'akuna a tsakar gidan guda uku sai d'akin girki da kuma band'aki. "Rauda! Rauda!! Rauda!!" Gajeren Dattijo mai duhun fata da farar furfura ya ke fad'a yana shigowa gidan.

Maimakon mutum d'aya ta fito kamar yadda yake fad'a sai mata uku suka lek'o, biyu daga d'aki d'aya guda d'aya kuma daga wani d'akin daban. A hankali ta tako ta k'araso inda yake ta durk'usa tace, "Baba gani." Kallon ta yake cikin harara yace, "uban me ya hana ki fita wajan waccan yaron mai mota da yake son ki?." Shiru tayi ta sunkuyar da kanta k'asa ganin hakan ya saka shi ya fusata yace, "ba magana nake miki ba?."

D'ago idanu tayi ta kalle shi kafin tayi magana yace, "ke ba kyau ba amma ki dinga wulak'anta manyan mutane masu kud'i irin wad'an nan? Dan kin samu zasu d'auki irin ki....? a ka'ida a mai aikin gidan sa zaki je amma yayi miki adalci yana so ya d'auke ki matsayin mata kike ja masa aji, ina aji a wajan talaka..? Nace miki ina aji a wajan talaka...?." A hankali tace, "Baba kayi hak'uri."
"To tashi kije ki ku tattauna bana son jan magana." Bata musa ba ta mik'e taja mayafin ta a kan igiyar shanyar da take tsakar gidan ta saka takalmi ta fita.

D'akin da mata biyu suka lek'o ya kalla sai suka koma ya ja tsaki yace, "haka dai, ke munafuka y'ar ki ma munafuka." Rauda lokacin da ta fita ta tarar da wanda zuciyar ta ta bata tabbacin ganin sa a tsaye a jikin motar sa yana facing gidan su. Yana hango ta ya saki murmushi sab'anin ita da face d'in ta take a cushe ba walwala ko kad'an ta k'araso tace, "Ina wuni."
Sai da yayi murmushi sannan yace, "lafiya lau Rauda,  ya gida da mutanen gidan?."
"Lafiya."
"Kiyi hak'uri na saka Baba ya fito dake."

Bata bashi amsa ba daman yasan hakan yayi murmushi yace, "Ina son ki Rauda, Ina burin ranar da zaki ce min kema kina sona" Bata ce komai ba ta kalle shi tace, "Sai anjima." Har zata juya yace, "minti d'aya Rauda." Cak ta tsaya ya zagaya mota ya d'auko leda k'arama ya dawo ya mik'a mata yace, "ga tsaraba babu yawa." Kallon ledar tayi ta kalle shi tace, "na gode" daga haka ta juya ta shiga gida ko waiwayen sa batayi ba.

A kan idanun Baba komai ya faru tana shiga soron gidan ya yi mata dak'uwa yace, "uban me yasa baki karb'a ba?." Kamar zatayi kuka tace, "Umma ta hana ni."
"Keda Umman ba nine a gaba da ku ba? Dallah malama koma ki karb'o, ka ganar min yarinya y'ar bak'in ciki."

Idanun ta yayi rau-rau zatayi kuka tana kallon sa yace, "in baki koma ba sai na fyad'a ki da k'asa, ka jimin yarinya mai bak'in ciki, zaki koma ko sai na b'alla ki?."  Juyawa tayi hawaye na zubo mata ta kalli inda motar take taga babu shi alamun ya tafi ta sauke numfashi ta juyo ta dawo ta kalli Baban tace, "Ya tafi."

Harara ya banka mata ya ja tsaki yace, "a nonon uwar ki kika tsotsi bak'in ciki dan ni kam ba haka halina yake ba, na rantse da Allah duk ranar da kika sake aikata wannan kuskuren sai ranki ya b'aci. Banza mummanar banza da wofi, ke ba kyau sai tsinanan bak'in ciki da mugun hali. Duk wanda ya kwashe ki matsayin mata ya shiga uku."  Shiru tayi kanta na k'asa yace, "wuce muje ki d'auki d'anwake ki tafi bakin kasuwa rana tana yi."

Babu yadda ta iya haka ta shiga cikin gidan yana bayan ta ya wuce cikin madafar da kansa ya had'o mata kayan abincin ya fito dasu yace, "D'auki maza ki wuce kar lokaci ya k'ure, kuma wallahi kika dawo kika ce min baki siyar ba duk inda zaki nemo kud'i sai kin nemo kin kawo min, domin ke bak'in halin ki har akan kayan sana'a ta yake." Umman ta da ta fito daga d'aki tace, "Malam dan girman Allah ka daina d'orawa yaran nan tallah, yaran nan sun girma sun kai munzalin aure maimakon ka tura su makaranta sai ka dinga basu talla.....? Nace maka ni ka barni zan siyar maka a gida amma kak'i, gani kake kamar baza'a siya ba, tura yara talla kamar su Rauda ba komai zai jawo ba sai lalacewar rayuwar su."
Chapter 3 · 0% Book details