← Book details Kwantan Bauna Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 18 OF 55

Sashe 18

Kwantan Bauna Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Asad yana zaune a inda yake aka shigo da sallama ya amsa ba tare da ya kalli wacce ta shigo ba yaji an zauna kusa dashi bai kalle ta ba tace, "barka da hutawa my Asad." Bai kalli inda take bama balle ta saka ran zai amsa. Daman tasan za'ayi haka tayi murmushi cikin shagwaba tace, "Kayi min magana mana." Nan ma bai kalle ta ba idanun sa a kulle suke.

"Dan kai fa na baro gida nazo nan amma shine baza ka kula ni ba?" Ta fad'a a shagwab'e. Nan ma banza babu amsa ta kuma cewa, "My Asad please." Numfashi ya sauke ya juyo ya kalle ta baice komai ba ya sake d'auke kansa yana cize baki lokaci d'aya yaji cikin sa na k'ullewa.

Ganin hakan sai tayi shiru bata sake magana ba dan tasan kallo na kin ishe ni ne hakan ya saka ta yin shiru tana kallon sa yana yamutsa fuska. Sun jima a haka a zaune kafin ya cize bakin sa ya furta, "Ya salam!." Mugun ciwo cikin sa yake yi bai san sanda ya furta hakan ba idanun sa lokaci d'aya sun canja kala zuwa jajaye haka fuskar sa ma tayi ja jikin sa har rawa yake yi.

"Asad!, Asad me ya faru!?" Ta fad'a tana kallon sa ganin lokaci guda ya canja. Idanun sa da taga ya kulle yana sauke numfashi hannun ta na rawa ta kira number Mama tana d'auka tace, "Mama Asad zai mutu! Kizo Mama" ta fad'a da k'arfi tana kallon Asad da yake jingine a kan kujera kamar baya numfashi..
*KWANTAN ƁAUNA*
FitattuBiyar 2023

©️ *Nana Haleema.*

*Book 1*
*009.*

Tunda Mama tazo inda yake hankalin ta yake a tashe tana zaune kusa dashi tana fad'in, "Asad me kake ji a cikin naka? Kayi min magana dan Allah. Yaushe ya fara yi maka ciwo? Me kake ji?, zafi yake kome?." Bud'e idanu yayi ya zauna sosai yace, "Mama, I'm okay fa."
"Ban amince ba Asad, kalli face d'in ka fa yadda ya koma, tashi muje asibiti da sauri daman nasan babu ta yadda za'ayi kaci abincin Hajiya ba tare da ka samu wani abun ba."

Hannun ta ya rik'e duk da ciwon da cikin sa yake masa yace, "Mama kar ki tayar da hankalin ki."
"Ta yaya bazan tayar da hankali ba Asad? Abincin fa ta baka kaci gashi har kana ciwon ciki wanda baka tab'a yi ba, hankalina kake so na kwantar ko me?." Shiru yayi bai amsa na kafin ya lumshe idanun sa yace, "bacci zanyi."
"Baza kayi bacci ba Asad sai munje asibiti, kar ka kulle idanun ka ka bud'e mu tafi." Suhaima ce suka shigo tare da Dr Yasir Mama na ganin sa tace, "Zo da sauri ka duba shi." Da saurin kuwa ya k'arasa yana yanayin jikin nasa yana tambayar sa abinda yake ji duk da yasan babu lallai ya basa amsa.

Allurar ciwon ciki yayi masa kafin ya d'ago ya kalli Mama yace, "Ranki ya dad'e ba wani abin tayar da hankali bane nayi masa allura zai daina ciwom." Jidda tace, "are you sure zai daina?."
"I'm very sure." Mama tace, "in akwai damuwa muje asibiti ko scanning ne ayi masa."
"A'a ranki ya dad'e zai ji sauk'i." Kai ta d'aga shi kuma ya fita da sauri baya so tayi masa maganar Rauda da take asibiti.
Aliyu da ya shigo a lokacin ta kalls tace, "Ka rik'e shi ku shiga d'aki ya kwanta, please Aliyu take care of him bana so wani abun ya same shi."

Mik'ewa Asad yayi ya tafi d'akin da kansa Aliyu ya kalli Mama yace, "basai na taimaka masa ba kin gani" yana fad'a ya shiga d'akin da yake kusa da na Asad d'in ya kullo k'ofa. Fita Mama tayi suma su Suhaima suka fito suka ga ta mik'e alamun b'angaren mai martaba zata je su suka kuma koma ciki.
Mai martaba yana zaune shi kad'ai kamar ko yaushe aka mata izinin shiga ta shiga da sallama ta nemi k'asa ta zauna tana kallon wani wajan daban.

Ganin hakan sai ya murmusa yace, "Rabi'atul adawiya ya akayi ne?."
"Allah yaja da ran mijina burin mutanen gidan nan suga bayan y'ay'ana me suka tare musu? Hydar gashi can ciwo ya tashi, ga Asad ma Hajiya ta bashi zogale yaci gashi can a kwance yana ciwon ciki. Ya suke so nayi ne me na tare musu?." Mai martaba ya mik'e daga kashingidar da yayi yace, "Ciwon Hydar ya tashi baki sanar dani ba?." Ta kalle shi tace, "Na rud'e ne gabad'aya ana kira na naje asibitin da je duba wata yarinyar da ya buge a can ciwon ya same shi na dawo dashi nan, ga Asad ma a kwance ya suke so nayi ne?" Ta fad'a kamar zatayi hawaye.

Mai martaba yace, "kar ki zubar da hawaye ban sanki da raguwar zuciya ba ki daure kamar yadda kike daurewa a koda yaushe. Yanzu ya jikin Asad d'in?." Idanunta ta goge tace, "yayi bacci. zogale yaci wanda Hajiya ta bashi daman na tabbatar ba da zuciya d'aya ta bashi ba, yanzu gashi can a kwance babu lafiya, burin su suga Asad ya mutu sai sun kashe sa hankalin su zai kwanta."

Mai martaba ya kalle ta sosai yace, "bana son zargin da kike saurin yi ki fara tabbatar da abinda kika ga gani kafin ki yanke hukunci."
Bata ce komai ba hakan ya saka ce sake cewa, "kar ki damu duka zasu samu lafiya babu wanda ya isa yayi musu abinda Allah bai nufa ba, Asad yana da ibada sosai k'aramin abu ko babba bazai kama shi ba sai wanda Allah ya nufa. Hydar zai samu sauk'i nan kusa ki daina tayat da hankalin ki."

Bata ce komai ba a nan ma amma ta d'an ji sanyi a zuciyar ta yace, "muje na duba jikin su da kaina" ya fad'a yana mik'ewa tsaye ita kuma bata mik'e ba. Ganin hakan ya saka hannayen sa da kansa ya mik'ar da ita tsaye yana kallon fuskar ta da murmushi yace, "kar ki bada ni mana, ko yaushe ina fad'in ke jaruma ce samu mace mai irin tsayayyiyar zuciyar ki abu ne mai wahala ya zaki bani kunya kum?. Come on ban san ki da haka ba, muje."

Tare suka fito ganin fitowar mai martaba babu tsammani aka tawo a guje aka saka masa takalmi aka bud'e lema tana takawa a hankali tana gefen sa ana zuba masa kirari har cikin d'akin da Hydar yake. Daga shi sai ita sai shamaki a gefen sa wanda aikin sa duk inda sarki yake yana kusa dashi sune kawai a d'akin kowa yana waje ya kalle ta yace, "meyasa ba'a bar shi a asibitin ba?."
"Nan yafi safe."" ta bashi amsa a tak'aice tana kallon sa itama.

A tare suka kuma fitowa ana ta kallon su bayi masu gulma suna yi tuni har an kaiwa sauran labari tun kafin su gama ma abinda ya fito dasu. Inda Asad yake suka shiga har cikin d'akin sa, mai martaba ne ya shiga d'akin kawai bai jima ba ya fito daga d'akin ana kirari aka raka shi har b'angaren sa.

Bata zauna ba ta koma nata b'angaren mai martaba shi kansa abin ya d'aure masa kai sosai duk da yasan ciwon ciki lalura ce amma ya tabbata na Asad yana da sila baya so ya nuna mata ne ya sake tunzura zuciyar ta shiyasa yayi shiru.

B'angaren Hajiya da labari yazo mata Asad yana kwance sai ta damu tana ta zaga d'akin ta cikin tunani dan dai ita ta tabbatar bata sakawa Asad komai a cikin zogale ba wanda ta bashi ko ita zata iya ci, amma meyasa akace bayan yaci yana ciwon ciki?, meye dalilin ciwon cikin nasa?, Anya babu wanda ya jefi tsuntsu biyu da dutse d'aya?. Ta jima tana wannan tunanin kafin wayar ta d'auki k'ara, d'auka tayi taga sunan mai gidan ta Yana kiran ta ta d'auka a kunne ta saurari abinda yace kafin ta yanke wayar.
Numfashi ta fesar ta fito cikin takun isa da k'asaita ta tafi amsa kiran mai martaba.

Daga shi sai Wambai sai Mama a zaune ta shiga da sallama ta zauna gaban ta na fad'uwa sosai zuciyar ta duk ta cika da tsoro, mai martaba yace, "Rabi'atu gata." Mama ta kalle bowl d'in gaban ta da yake d'auke da ragowar zogalen a ciki ta fito da farar takarda tace, "wannan shine sakamakon gwajin ragowar zogalen nan da akayi ya tabbatar kuma an bawa Asad guba kuma itace wacce ta bashi yaci." Hajiya ta dafe k'irjin ta da yayi mugun bugawa fuskar ta tayi kalar tausayi ta kalli mai martaba shima ita yake kallo kafin yace, "Sa'adatu ya akayi haka?."

"Allah ya taimake ka wallahi Allah ban bawa Asad wani abu a cikin zogalen nan ba, inda nayi niyar cutar dashi bazan bari yasan nice na bayar ba sai dai yaci. Ko ni zan iya ci ban san ya akayi hakan ta faru ba, mai martaba yasan bazan rantse a kan k'arya ba" ta fad'a muryar ta na rawa sosai.

Mai martaba ya kalli Mama yaga ta kawar da kanta gefe alamun bata ma yarda ba kafin ya kalli wambai ya dawo da kallon sa a gare su yace, "zaku iya tafiya. Amma bana so na sake yin maganar nan a barta a wajan nan kar na kuma ji. Zaku iya tafiya." Ba musu suka tashi suka fita mai martaba ya kalli Wambai yace, "Mubarak mai ka fahimta game da lamarin nan?."
"Allah ya ja zamanin ka abu ne a bayyane kai tsaye baza'a ce Hajiya ce ta bashi gubar ba, kai tsaye kuma baza'a ce Fulani itace ta mata sharri ba. Komai zai uya faruwa kowa yana da gaskiya a cikin su." Mai martaba ya sauke numfashi yace, "Sa'adatu bazata bashi guba ba ni nasan da hakan, koda ma ace zata bayar d'in kamar yarda tace baza tayi yadda za'a gane ba ta taka sahun b'arawo ne tabbas akwai wanda yake son ganin bayan Asad a cikin gidan nan, amma waye?."
Chapter 18 · 0% Book details