← Book details Kwantan Bauna Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 28 OF 55

Sashe 28

Kwantan Bauna Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

         Masallaci ya fara wucewa yayi sallah kafin ya nufi d'akin sa jikin sa duk babu dad'i, zuciyar sa na bugawa sosai yana jin bak'on abu yana zaga jikin sa kamar yadda jini yake zaga jijiyoyin jikin sa.  Yana tsallaka k'ofar d'akin yaji kansa yayi mugun sarawa ya tsaya cak yana bin wajan da kallo amma baiga komai ba ya runtse idanun sa.
"Lafiya?" Aliyu ya fad'a daga bayan sa ganin yanayin sa duk ya canja. K'arasowa Aliyu yayi yana kallon sa yace, "baka da lafiya?." Asad ya cize bakin sa ya kalle shi yace, "Kaina" abinda yace kenan ya shiga ciki shima yabi bayan sa.

          Suhail da yake lab'e a bayan babban gate d'in da ya raba apartment d'in su da gidan ya fito yana murmushi ya bar wajan da sauri ya fiddo waya daga aljinun sa ya danna kira ana d'auka yace, "An zuba masa kuma tabbas ya taka yanayin sa ma ya canja." Waziri yace, "Good boy." Daga haka ya yanke wayar yayi saurin barin gidan gabad'aya.

       Shigar Asad falo keda wuya kansa yayi mugun nauyi ya rasa me yake masa dad'i bai san lokacin da yayi saurin dafa bango ba yana furta, "Ya salam!." Ganin hakan ya saka Aliyu ya rik'o hannun sa yace, "you're not okay deaf, zauna" ya fad'a yana jan sa kan kujera ya zaunar dashi yana juya kansa. Yadda kansa yake mugun ciwo da sarawa fita yayi daga hankalin sa idanun sa suka firfito waje ya saka hannayen sa biyu ya dafe kansa yana ji kamar ana saka guduma ana dukan kansa.

         Aliyu ganin abin yayi yawa sai hankalin sa ya tashi ya zauna kusa dashi ya rik'e kan nasa jin yadda jijiyoyin kan nasa suke bugawa a guje sune ya sake tayar da hankalin sa yace, "oh my God wannan wanne irin ciwo ne?." Da sauri ya lalubo waya ya kira Dr Yasir amma bai same shi ba ya tashi tsaye ya kira number Mama ya sanar da ita halin da ake ciki.

        A gigice Mama ta tawo apartment d'in nasu gab da zata shiga Hafiz ya tsaya a gaban ta yace,"Mama kar ki wuce nan wajan." Hararar sa tayi kafin tace wani abu yace, "Wani abu aka zuba masa ya wuce ta wajan, kalli kiga" ya fad'a yana nuna mata wani bak'in ruwa a wajan ga garin magani a cikin sa har yellow yake yi.

Kallon wajan take gaban ta na fad'uwa da sauri ta k'arasa ta kunna hasken wayar ta ta sake haska wajan ta kalli Hafiz tace, "Waye ya shigo nan b'angaren?." Hafiz yace, "ban sani ba Mama."
"Kuna ina! Kuzo nan" ta fad'a cikin d'aga murya sosai masu tsaron wajan suka k'araso a guje suka zube kafin suyi magana tace, "Kafin Asad ya shigo wajan nan waye ya shigo?." Jikin d'aya yana rawa yace, "Ranki ya dad'e Suhail ne ya shigo."

"Suhail again" ta fad'a tana dafe kanta kafin ta juya da sauri ta nufi falon Asad d'in, bata sake bi ta kan maganin dake wajan ba ta tsallaka ta shiga ta same shi a zaune hannu sa duka biyu a kan sa jikin na rawa sosai. Da sauri ta k'araso ta rik'e shi ta d'ora hannun ta a akan sa tace, "Aliyu kayi wani abun please." Aliyu yace, "Mama na kira Dr yana hanyar zuwa yanzu."
"Sannu Asad" ta fad'a kamar zatayi kuka tana kallon sa.

      Ya canja lokaci d'aya jijiyoyin kansa sun fito radau jikin sa na rawa sai juya kai yake alamun yana cikin azabar ciwo, hankalin Mama ya sake tashi ganin numfashin sa yana k'ok'arin tsayawa ta kalli Aliyu da yake a tsaye hannun sa rik'e da waya shima duk ya rud'e. Shigowar Dr Yasir ya saka Mama kallon sa tana fad'in, "yi sauri kazo ka duba shi." A guje ya k'araso ya tab'a kan Asad jin yadda yake bugawa sai da ya d'auke hannun sa da sauri.

         Hannun sa har rawa yake ya saka masa ruwa ya kuma yi masa allura ya fara auna bp sa, abinda ya bashi mamaki komai normal yake dan yadda yaji kansa yana bugawa ya d'auka ko jinin sane yayi k'asa hakan ya saka ya kalli Mama itama shi take kallo duk rauni ya bayyana a tare da ita kamar zatayi kuka. Hannu Asad ya saka ya cire ruwan da yake shiga jijiyoyin sa sabida ji yake kamar azaba tana shiga cikin jikin sa. "A'a Asad ya zaka cire?" Mama ta fad'a tana kallon sa hankali a tashe.

Juya kan nasa yake yi cikin tsawa Mama tace, "Dr kana ganin abinda yake yi ka tsaya kana kallon sa!?." A firgice ya kalle ta yace, "Ranki ya dad'e na rasa gane kan matsalar, bara nayi masa allurar bacci" ya fad'a da gaggawa yana yi masa allurar bacci amma ko gezau baiyi ba.

Aliyu yace, "Dr muje asibiti kamar zai fi." Hafiz yace, "No prince zaman sa a nan yafi safe, dan Allah Yasir kayi iya k'ok'arin ka a samu yayi bacci."  Gabad'aya sun rud'a Dr ya rasa ma abinda zaiyi yayi masa allurar bacci baya son sake yi masa wata dan tabbas zai zama cikin risk domin abubuwan zasu yi masa yawa a blood d'in sa. "Prince in aka sake masa another injection abubuwan zasu yi masa yawa" ya fad'a yana kallon Aliyu.

"Kayi masa mana, ko meye kayi masa abinda zai bar wannan condition d'in!" Mama ta fad'a a fusace tana kallon sa dan hankalin ta a tashe yake, bai san sanda ya balle kan allurar ya ja a sirinji ya dannawa Asad a jijiyoyin jikin sa. Lumshe idanu Asad ya fara yi har lokacin yana rik'e da kansa idanun sun k'i rufewa yadda ake so.

      Abin mamaki da al'ajabi Dr ya tsaya yana kallon ganin har lokacin bacci bai d'auke sa ba sai kansa ya kulle ya rasa abinda zai bashi kuma nan gaba. Domin allurar da yayi masa bata second biyar a jikin mutun bata saka shi bacci ba. Hafiz da yake tsaye ya lura da yanayin Dr hakan ya saka ya k'arasa wajan fridge da sauri ya d'auko ruwa ya bawa Mama yace, "Mama ki masa tofi ya sha zai fi samun sauk'i." Ba musu ta karb'a ta fara tofa masa duk ayar da tazo bakin ta kafin ta bashi yasha ta shafa masa ragowar a fuskar sa. Komawa gefe Dr yayi yana kallon ikon Allah har lokacin bacci bai d'auke Asad ba kuma kansa bai daina ciwo ba.

      "Hafiz kama shi mu kai shi d'aki ya kwanta" Aliyu ya fad'a yana kallon Hafiz. Tare suka d'aga shi aka kai shi kan gado ya kwanta har lokacin hannun sa na dafe da kansa idanun sa kuma a bud'e. Mama na zaune a gefen sa hannun ta guda d'aya ta rik'e nasa tana tofa masa addu'a a hankali, sun kwashe sama da mintina arba'in a wajan kafin bacci ya d'auke shi.

     Ajiyar zuciya Mama tayi ganin yayi bacci ta kalle su da suke tsaye har lokacin bata ce komai ba ta mik'e aka ja masa k'ofar aka fita ta kalli Dr hakan ya saka shi yace, "Ga magani na koma na d'auko masa in ya farka sai ya sha. Nayi mamakin ciwon nan nasa ban tab'a karo da ciwon kai irin wannan ba gaskiya" ya fad'a yana ajjiye maganin akan table.

Bata ce komai ba ta fita da sauri ta dinga kiran masu tsaron wajan suka k'araso a guje suka zube ta kalle su tace, "Daga yau ban amince a sake barin kowa ya shigo wajan nan ba, ko waye ko wace ban amince ba in kuma aka sab'a abinda na fad'a....." Bata k'arasa ba ta girgiza yatsan ta guda kafin ta bar wajan da sauri.

       Tana shiga b'angaren ta d'akin da Hydar yake ta shiga yana kwance inda yake ta fita ta koma d'akin ta. Waya ta d'auka hannu na rawa ta zauna jikin ta duk yayi sanyi ta nemi number mahaifin ta ta kira shi. yanke kiran aka yi hakan ya bata tabbacin zai kira ta kenan bata ajjiye wayar ba kuwa kiran ya shigo, da sallama ta d'auka muryar ta na rawa sosai kafin tace, "Barka da dare Abbie." Jin maganar ta a haka ya saka yace, "Ban saba jin rauni a muryar Rabi'atu ba, me ya haifar da hakan?."

          Kuka ta fara yi mara sauti kafin tace, "Abie suna neman su kashe min Hydar da Asad. Hydar na kwance har yanzu baya motsawa ga Asad can yanzu na baro wajan sa kansa na ciwo dak'yar aka samu yayi bacci. Ban san me suke nema a wajan su ba so suke suga bayan su."
Abie ya murmusa yace, "Babban kuskuren mijin ki da ya furta zai sauka daga kan kujerar sa ya bawa Asad wannan shine kuskure babba da ya tafka. A yanzu zakiyi mamakin adadin wad'an da suke harin rayuwar Asad sabida son mulki, mulki yana sakawa mutane suyi komai a kansa, mulki yana sakawa idon mutane ya rufe suga in basu samu abinda suke so ba zasu iya ganin bayan kowa. Baza su barki kiji dad'i ba sai kin dage da addu'a sosai dan itace maganin ko wanne mugu. Kiyi hak'uri ki bar lamarin a hannun Allah, nima kuma ina taya ki addu'a bama ke kad'ai ba dukka y'an uwan ki."

"Allah yaja da ran mahaifina lamarin nasu ne yayi yawa na rasa inda zan saka kaina."
"Zama uwa ga sarki ai ba abu bane mai sauk'i ba Rabi'a, duk inda kike tunanin wahalar sa ya wuce nan sai kin jure dole. ki cigaba da addu'a kawai ban amince kiyi shirka ba Allah kawai zaki rok'a zai miki maganin komai. Zan bada sak'o a kawo miki kuyi amfani da maganin dukkan ku."
"An gode Takawa, Allah ya ja kwana, Allah ya tsare, Allah ya rufa asiri" ta fad'a da girmamawa kafin suyi sallama ya katse kiran ta sauke numfashi, ko babu komai hankalin ta ya kwanta da kalaman mahaifinta masu sanya nutsuwa.

*☆☆☆*
        "Umma k'afa ta ciwo take min" ta fad'a tana hawaye mai zafi tana cize bakin ta. Umma hankalin ta duk ya tashi ta kunna k'aramar fitilar hannun ta tace, "Sannu Rauda, kiyi hak'uri kita yiwa k'afar addu'a zata daina in sha Allah." Kai take juyawa kawai sosai k'afar take ciwo rashin shan maganin da bata yi ba.
Chapter 28 · 0% Book details