← Book details Kwantan Bauna Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 40 OF 55

Sashe 40

Kwantan Bauna Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

"RAUDA!" ya furta a bayyane yana jin wani iri a jikin sa gashin jikin sa na rinsing ba tare da ya san dalilin hakan ba, wayar sace ta d'auki k'ara ta katse masa tunani ya kalle ta yaga sunan Hafiz ne yayi banza bai d'auka ba aka kuma kira ya kalla yaga d'aya daga cikin wanda ya saka su kai su Rauda ofishin yin fasko d'in ya d'auka, "Ranka ya dad'e, Allah ya taimaki yarima, Allah ya ja zamanin ka, ya baka tsahon rai ya taimake ka a duk inda kake."
"Uhum" ya furta kawai ba tare da yace komai ba.
"Ranka ya dad'e anyi abinda kace, yanzu haka mun sauke su sun shiga gida."
"Good" yana furta hakan ya katse wayar bai tsaya yaji mai zasu ce ba.

Lumshe idanu yayi ya tuno lokacin da take hawaye tana masa godiya sai yaji kasala ta saukar masa ya koma ya kwanta a akan kujera yana jin wani irin yanayi a jikin sa.
'You love her' yaji zuciyar sa ta furta hakan ya saka shi saurin tashi ya bud'e idanun sa yana ji zuciyar sa na gasgata masa abinda ta fad'a.

"A'a ba haka bane" ya furta yana cize bakin sa.
'Da gaske Asad haka ne ka yarda.' zuciyar sa ta sake fad'a ya dafe kansa da duka hannayen sa jin yana juya masa. Tashi yayi ya d'auki makullin mota ya fita daga gidan da sauri jikin har shaking yake yi.

*☆☆*

"Uncle ka kira ni then kayi shiru ina da abinda zanyi" Aliyu ya fad'a yana kallon waziri da yake zaune yana facing d'insa. Numfashi ya sauke yace, "Wato Aliyu abubuwan ne suke d'aure min kai, ace kamar ka babba kaine namijin farko da mai martaba ya samu amma a dinga mik'a sarauta ga k'anin ka?. Kasan jiya mai martaba ya zauna da Asad kuma ya tabbatar masa da shine zai mulki garin nan?."

Kafin Aliyu yayi magana yace, "ga kyau, ka k'ima, ga k'asaita, ga nagarta, ga izza, ga ilimi, ga wayewa, ga sanin ya kamata. Waye ya cancanci zama sarki in ba kai ba?. Kai ka san ina son sarautar nan amma sabida dacewar ka ya sanya na hak'ura na sallama; ranka ya dad'e wallahi inda zaka zama sarki zan cigaba da zama matsayin wazirin ka amma meyasa mai Martaba yake fifita Asad a kan ka? Meyasa kowa maganar sa a akan Asad take sab'anin ka?."

Zuuuuu haka Aliyu yake jin k'asaita da zugar da ake masa na shiga cikin jikin sa, kansa yake ji a sama kamar shine yake mulkin duka duniya, wani irin yarrrr yake ji a jikin sa har bai san ya cize bakin sa ya kalli Waziri yace, "Kana so kace min kana bayana? Kana so kace min kaima ni kake so na zama sarki a garin nan kenan?."
Murmushi waziri yayi yace, "Dari bisa dari, ni daman kaine nawa ai tun kana k'arami ba Asad ba, in kana musawa ka tambayi mahaifiyar ka zats baka labari."
Wani irin kallo Aliyu yake masa na ka raina min hankali amma sai ya murmusa yace, "Ta yaya zan yadda bayan kaima kana harin mulkin nan?."
"A bayyane yake ai ranka ya dad'e, indai kai zaka mallaka wallahi nidai na hak'ura."

Murmushi Aliyu yake na kana mayar dani yaro k'arami bai ce komai ba ganin murmushin da yake yi sai Waziri yace, "shine nace me zai hana baza mu samo mafita ba; matuk'ar Asad ya mallaki garin nan shiga gidan sai ya gagare mu, ya kamata mu san abinda zamu yi."
"Ina jinka."
Ya gyara zama yace,"Na shirya wani abu a raina amma ban sani ba ko zaka amince."
Da hannu yayi masa alama da yana jin sa.

Gyara zama ya sake yi yace, "Daman mafita ce na nemo amma ina jin shayin fada maka." Aliyu ya d'ora k'afa kan d'aya yana kad'awa yace, "Go ahead."
"Daman cewa nayi mai zai hana mu b'atar da Asad ya bar k'asar nan ma'ana ayi masa abinda bazai sake waiwayo mu ba, kai kuma sai ka koma acting d'in Asad a fad'awa duniya Aliyu ne ya b'ata ba Asad ba. Ni da kai mun san Aliyu ne yake nan amma duniya za'a ce mata Aliyu ne ya b'ata; kaga mai martaba zai mallaka maka mulkin katagum a matsayin Asad kaga shikenan ciki lafiya baka lafiya."

Wani irin kallo Aliyu yake masa gaban Waziri sai fad'uwa yake yi yana b'oye tsoron sa babban burin sa kar yak'i amincewa da batun sa hakan ya saka tsoro ya bayyana k'arara a tare dashi duk da yana so ya b'oye amma hakan ya gagara sai da tsoron ya kwanta a fuskar sa. Numfashi Aliyu yayi kafin ya saki dariya mai d'auke da izza da k'asaita kafin ya kalli waziri yace.......

*KWANTAN ƁAUNA*

             ©️ *Nana Haleema.*

*Book 1*
*019.*

Irin kallon da yake yi masa jikin Waziri yayi sanyi qalau kuzarin sa ya ragu amma duk da hakan bai nuna ba ya daure ya cije baya so ya bayyanar da raunin sa kar Aliyu ya gano shi, Aliyu wani irin murmushi yake yi ya sauke k'afar daga kan d'aya ya kalle shi ta k'asan idanu yace, "kana ganin hakan zai yu kuma?."
Jin abinda yace sai ya sauke ajiyar zuciya yace, "Mai zai hana ya yu ranka ya dad'e?, indai zaka bada goyan baya abu ne mai sauk'i faruwar hakan."

Ya juya manyan idanun sa ya sauke su akan Waziri kana ya mik'e tsaye yana kallon sa yace, "Zan yi tunani a kan hakan" yana gama fad'ar hakan ya fita daga falon bai sake kallon waziri ba. Waziri ya dafe k'irji gaban sa yana fad'uwa sosai ya d'auko waya da sauri jikin sa har rawa yake, kiran yake ba'a d'auka ba ya cillar da wayar akan kujera ya mik'e yana zaga d'akin.
"Me yaron nan yake nufi dani? Yaji sirrina a banza ya tashi ya tafi ya barni....? kenan yana nufin na jira shi?, in bai amince bafa?." Naushin iska yayi ya koma ya zauna jikin sa har b'ari yake sabida tashin hankalin da yake ciki.

Kamar kuma anyi masa allura ya mik'e da sauri ya shiga d'aki dan bai ga ta zama ba.

Aliyu lokacin da ya fita mota ya shiga ya zauna yana tuno abinda Waziri ya fad'a masa sai yayi murmushi yaja tsaki yace, "Wai ni zai yiwa wayo, an fad'a masa ni d'in shashasha irin sa?, ko kuma ya d'auka zuciya ta irin ta Asad ce?." Sai kuma ya tsaya da dariyar ya d'auki waya da sauri ya kira Waziri, kamar jira yake yaji an d'auka ya gyara murya yace, "Na amince da tayin ka." Yana jin ajiyar Wazirin a waya baice komai ba ya yanke wayar ya ajjiye wayar wayar yana kallon glass d'in gaban motar.

Asad bai koma gida ba sai da ya gama yawon sa har dare yaci abinci sannan ya koma, ko wajan Mama bai shiga ba ya shiga apartment d'in su ya tarar da Aliyu a zaune ya kunna sigari yana sha, har ya wuce ya dawo yana kallon sa har ga Allah baya son warin ta ko kad'an ya masa magana sau babu adadi amma yak'i.
"Aliyu ko a lafiyar ka abinda kake yi ba daidai bane" ya furta yana kallon sa. D'ago idanun sa yayi ya kalle shi ya murmusa ya sake zukar sugarin ya fesar kana yace, "lafiya ta kace ba taka ba, a gani na ai hakan ba damuwar ka bace ba."

Asad bai kuma cewa komai ba ya d'aga kafa zai wuce yaji yace, "kabi a hankali ka kuma taka tsan-tsan akwai lokaci Asad." Baice komai ba ya wuce ya k'yale shi ya shiga d'akin sa. Can k'arshen d'akin ya wuce ya janye labule sai ga k'ofa ta bayyana a wajan wacce in ba kasan da ita ba baza ka tab'a cewa tana wajan ba ya shiga ciki ya kulle k'ofar. K'aton wajan karstu ne mai d'auke da drawer na littafai manya-manya na addini dana karatun zamani, littafai ne sama da guda dari uku a wajan ko wanne rukuni da cover sa da sunan su a k'asa ga table da kujera mai guda d'aya a wajan da k'aramar lamp a kai.

Kujerar yaja ya zauna ya dafe kansa da duka hannayen sa biyu kansa na juyawa ya rasa dalilin da ya saka yake jin hakan da zarar ya shigo d'akin sa, daurewa yayi ya tashi ya k'arasa jikin cover ya d'auki littafai guda biyu ya k'araso ya zauna a kan kujerar ya fara dubawa. Karantawa yake a nutse yana bin rubutun daki-daki yana Nazariin abinda yake yi.
Rufe na farko yayi ya bud'e na biyun yana sake bi a hankali har ya kammala karanta inda yake da buk'ata ya kulle ya kifa kansa a kan littafin kamar mai bacci.

Juma'a ce gobe kuma shine zai gabatar da hud'uba shiyasa yake ta dube-duben littafai amma zuciyar sa ta kasa bashi topic guda d'aya da zaiyi hud'ubar a kansa, d'ago kai yayi ya saka hannu biyu ya d'an daki kansa a hankali ya furzar da iska waje yana kallon d'akin gabad'ayan sa. Zuciyar sa yaji yana bugawa da sauri har yana jin sautin ta a kunnen sa ya runtse idanun fuskar Rauda ta bayyana a gare shi.
"Hasbunallahu wani'imal wakil" ya furta a hankali yana dafe da kansa har lokacin bai kuma daina jin bugun zuciyar ba.

Cize bakin sa yayi ya runtse idanu kafin ya koma ya jingina da kujerar, sautin muryar ta yake tunowa a hankali tana shiga ilarin jikin sa, tasirin muryar da dad'in ta ya saka shi kulle idon sa yana sauke numfashi gashin jikin sa na tashi. sautin muryar yarinyar mafarkin sa yaji sai ya bud'e idanun sa; ya kasa banbance shin itace yake gani a mafarki ko kuma ba ita bace?, bai tab'a ganin waccan fuskar ta completely ba amma idanun ta da goshin ta irin na Rauda ne, akwai banbanci a maganar su waccan muryar ta tafi zak'i a kan ta Rauda, ita kuma ta Rauda tafi sanyi da taushi kamar mai mura in tana magana.
Tashi yayi ya kashe hasken d'akin ya fita daga cikin da ya dawo d'akin sa ya zauna a gefen gado ya rasa tunanin ma mai zaiyi.
Chapter 40 · 0% Book details