← Book details Kwantan Bauna Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 50 OF 55

Sashe 50

Kwantan Bauna Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

A fusace tace, "Hydar ba da kai nake magana ba dashi nake magana, ka fice ka bani waje." Hydar yace, "Allah ya wuci zuciyar ki, ina neman afuwa in abinda na fad'a ya b'ata miki rai" ya mik'e ya kalli Asad yace, "kazo muje takawa yana son ganin ka."

Jin abinda Hydar yace ya saka Asad mik'ewa Mama tana rik'e da hannun sa har lokacin tace, "kar ka amince Asad, na yadda zan bar ku kuyi mata ko wanne irin taimako amma banda aure tsakanin ku bazan iya jure ganin wannan ranar ba, zuciyata zata iya bugawa a lokacin da hakan ta faru. Na rok'e ka matsayina na mahaifiyar ka Asad ka sanar dashi baka sonta." Kai Asad ya girgiza kawai ya fita Hydar yabi bayan sa.

Hanyar wajan mai martaba Asad ya nufa Hydar yace, "Zo muje ba wani kiran mu da yake yi, na fad'a ne dan ka taso kalaman ta zasu karya maka zuciya ka hak'ura da abinda kake so" ya fad'a yana jan hannun sa suka nufi hanyar apartment d'in su. Bayan sun shiga Asad ya kalli Hydar a sanyaye sosai yace, "Hydar zan hak'ura kamar yadda Mama take so, bazan iya ganin Mama a halin da take ciki ba ina da damar cire ta kuma na barta; zan hak'ura kawai kome nake ji a zuciya ta zan jure Hydar; ba yau ne na fara rasa abinda nake so ba" ya fad'a a sanyaye yana zama akan kujera ya dafe kansa.

Tausayin sa ya kama Hydar domin yasan soyayya tayi masa mugun kamu lokaci d'aya ba tare da ya shirya ba ya zauna kusa dashi yace, "Baza ka hak'ura ba deaf, sai ka mallake ta domin itace wacce kake so ba Jidda ba. Kana fa da hakki akan Mama ba itace kawai take da hakki a kanka ba tauyen ka da take yi yayi yawa a ko yaushe kanta ta sani bata duba kai halin da zaka shiga in ka rasa abinda kake kawai cikar burin tane a gabanta." Ya juyo ya fuskanci Asad ya rik'e hannun sa yace, "Deaf u lovers her right?."

Ya lumshe ido yace, "Hydar!." Hydar ya katse shi yace, "Na tambaye kane kawai ka amsa min." Shiru yayi yana tunani kafin yace, "eh ina sonta Hydar, but yanzu na bar batun ta sabida Mama."
"Baza ka bari ba abu nawa ka bari sabida Mama a duniya? Meyasa ita baza ta yi maka adalci a wannan lokacin ba?. Tana so ka auri wacce take so kaji zaka aura amma kaima zaka auri wacce kake so ba shikenan ba anyi equal why zata ce kai sai ka hak'ura?."
"Hydar mu bar maganar nan dan Allah" ya furta yana dafe kansa da hannu d'aya kansa yana harbawa yana ajiyar zuciya.

Hydar yace, "Na bari; amma inaso ka sani bazan zuba ido ka rasa abinda kake so a karo na babu adadi ba deaf, zanyi iya yina wajan ganin ka mallake ta" yana fad'a ya tashi ya fita daga falon ya bar Asad a zaune yana sauke numfashi.

_Suna zancen wani Asad ni meye had'ina da wani Asad?._ kalaman Rauda suka fad'o masa a zuciyar sa ya runtse idanu zuciyar sa na bugawa da sauri-sauri ya lumshe idanu yana tuno yadda fuskar duk taji ciwo, wani abu yaji yana masa suka a zuciya ya runtse idanun sa da k'arfi yana cize baki, bud'e ido yayi ya kalli falon kamar mai neman wani abun kafin ya tashi ya shiga d'aki jikin sa duk a sanyaye.

*☆☆☆*

Umma da take sauraron abinda Baba yake fad'a mata da mamaki take binsa da kallo jin abu kamar a shirin film ko a hausa novel tace, "Malam wai auren Rauda ake nemawa Asad d'in? Nifa ban gane ba ka saka ni a duhu wallahi." Baba yace, "Abinda kika ji na fad'a shine, Asad d'in ne da kansa yace yana son tane shiyasa mahaifiyar sa ta turo ayi mana wannan aikin dan daman nasan labarin ta ana cewa bata son had'a jini da talaka; shiyasa ta d'auki wannan matakin kafin abin yayi nisa."

Umma ta rik'e baki tace, "Tabd'ijam, ni kuma fa gani nake kamar da wata manufa akace yana sonta in badan haka ba ina matsayin sa ina Rauda...?, banda abin su ina shi ina Rauda? Kalli yadda take fa?" Ta fad'a tana kallon Rauda da take zaune a gefe. Baba yace, "to Allah ne masanin gaibu ni bana ce komai ba." ya fad'a cikin rashin sanin mai zaice.
Umma tace, "Ina zamu kaita inda za'a wulak'anta ta?, da ta aure shi azo ana wulak'anta ta wallahi gwara ta auri talakan da bashi da komwi zai kula da ita. To ita da bama sonsa take ba ina maganar aure?."
"Ke kinji illar ki wallahi, meye to in ta aure shi? ai tunda yana sonta ko ita bata son shi magana ta k'are, kuma kaf dangin ki da nawa wacece ta taka matsayin da Rauda ta taka in ta aure shi?. D'an sarki fa kuma mai kud'i ki kuma tuna shine sarki gobe wannan ai abin alfahari ne a gare mu gabad'aya."

Umma ta kalle shi da mamaki ta girgiza kai tace, "Shi kuma yanzu Anas ka dawo daga rakiyar sa kenan ko?." Baba yace, "ke muna so mu shiga aljanna amma a aljanna ma firdausi muke nema" ya fad'a yana wara hannayen sa. Umma ta d'auke kai daga kallon sa tace, "to ke Rauda wanne tunani kike akan wannan?."

Rauda tace, "Umma wanne tunani zanyi?." Umma tace, "kece kike da tunani Rauda, amma a zahiri ina ke ina Asad?, Ga k'iyayayar da babar sa take miki tun kafin aje ko ina har ta fara turowa har gida ayi miki wulaƙanci dan kiji tsoro ke kya shiga gidan nan?. Ga badaqalar da take cikin gidan sarauta, da karancin shekarun ki a haukata min ke ko a kashe ki a barni da zubar da hawaye, bana fatan ma ki aure shi wallahi." Baba yace, "Sai ki hana ai in an tashi auren, ko in Allah ya rubuta kije ki goge." Umma bata ce komai ba Baba ya tashi ya fita ta kalli Rauda tace, "Rauda ke kina ji a ranki zaki iya zama dashi?."

Rauda tace, "Bana kawo hakan Umma, hasalima ni haushi yake bani duk abubuwan nan da suke faruwa bai tab'a cemin yi hak'uri ba a haka kuma zan zama matar sa?. Bada ni ba yaje can ya nemi wata ni kam bazan iya ba dan ni zuciya ta ma hasaso mun take akwai wata manufa a son da yace yanayi min wata k'ila amfani zasu yi dani daga baya su wulak'anta ni dan sun ga suna da mulki da kud'i. Bana sha'awar hakan ma ni sam Umma."

Umma ta sauke ajiyar tace, "ashe kin hango abinda nake hangowa. Meyasa ya zabe ki bayan tarin matan da suke son su aure shi? Dan nasan bazai rasa ba duba da girman da yake dashi a idanun mutane, duka ya tsallake su yazo kanki kuma yana tunanin zamu amince da zuciya d'aya yake son ki...?. ga rigimar gidan sarauta musamman ma ta katagum d'in nan da kowa yasan badaqalar da take ciki, Allah ya kawo miki wani daban amma ba shi ba yaje ya samu daidai shi amma ke kam yafi k'arfin ki."

"Sabida tsabar mulki da sarauta bai tab'a min kallon arzuk'i bama sa wani ce yana sona dan kawai suna ganin zamu amince tunda suna da kud'i?, to ba haka muke ba yaje ya nemi daidai ahi nikam a kai a kasuwa."
"Kedai tunda bakya ra'ayi ai shikenan babu wanda zai miki dole, amma yau kiyi addu'a ki kuma yi istikhara kafin ki kwanta wata k'ila akwai abinda Allah ya b'oye wanda mu bamu san dashi ba."

Da to kawai ta amsa ta jingina da bango tayi shiru tana tunanin abubuwan da suka faru tsakanin ta da Asad d'in har kawo wanda ya faru yau sai taji tsigar jikin ta ta tashi har gashin kanta sai taji abin.

Da daddare Asad yana zaune ya dafe kansa yana kallon wani waje daban b'acin ran da Mama take ciki gabad'aya ya dame shi ko yaya ya motsa ita yake gani tana kuka akan abinda yake da ikon rabuwa dashi, kuncin sa ya shafa ya tuna marin da tayi masa wanda ko yana yaro baya tunanin ta tab'a marin sa amma sai gashi yau sabida wata mace daban ta mare shi.
"I'm sorry mah" ya furta a hankali yana sauke numfashi zuciyar sa nayi masa d'aci da k'una.

Hydar ne ya shigo d'akin nasa ya kalle shi ya ganshi sanye da doguwar riga kalar orange mai hula a baya tayi masa kyau sosai yace, "Deaf ko zamu iya zuwa wani waje mu dawo?." Asad zai musa yayi saurin katse shi yace, "Please yanzu zamu dawo kaima kuma zaka ji dad'i stress d'in nan da kake ciki." Mik'ewa kawai yayi suka fita suka shiga mota Hydar yaja Asad bai san inda suka nufa ba.

Babu zato yaga sun tsaya a k'ofar gidan da suka ajjiye su Rauda d'azu kafin Asad yace wani abu Hydar ya fita daga motar a lokacin Baba ya fito ganin su ya saka ya k'araso da fara'a yana fad'in, "A'a Hydar kaine tafe?."

Hydar yace, "Eh, tare muke da Asad ma, ka fito mana" ya fad'a yana kallon glass d'in motar dole Asad ya fito badan yaso ba. Baba yace, "to ku shigo mana ciki ai bakwa tsaya a waje ba." Daman abinda Hydar yake so kenan suka yi gaba Asad ya tsaya a baya bai da niyar tawowa Baba yace, "Asad baza ka shigo ba kai?."
Jin hakan sai ya tako ya biyo bayan su yana jin sa wani iri kamar bashi ba.

Rauda na zaune da hijjabi tana nunawa Ummulkhairi assignment kasancewar gidan akwai hasken wutar sola ba duhu ko ina haske tarr suka ji sallama, amsawa sukayi kafin su kalli wanda suke shigowa. Asad shine k'arshe shigowa yana shigowa ya had'a ido da abar sonsa nan take yaji duk wata damuwa na yayewa a zuciyar sa a hankali tana tafiya kamar daman bata samu mazauni a ransa ba.
Chapter 50 · 0% Book details