← Book details Kwantan Bauna Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 48 OF 55

Sashe 48

Kwantan Bauna Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Mum tace, "Innalillahi wa'inna ilaihir raji'un. mun shiga uku, me yarinyar nan ta yiwa Asad ne haka?." Mama ta fusata tace, "ko me tayi masa dole ya sake shi bazan lamunci abinda yake niyar tunkaro ni ba, wannan raini ne da k'askanci a idanun mutanen gidan nan a gare ni. ya zama dole Asad ya bar maganar nan matuk'ar yana son zaman lafiya a cikin gidan nan." Aliyu yace, "ko kuma Mama ta hak'ura ba ta bar shi da ita domin kuwa da zarar maganr taje gaban Takawa zancen ta ya k'are kuma yanzu haka suna kan hanyar zuwa gare shi."

A haukace Mama tace, "Kira min shi Aliyu, maza ka kira shi" ta fad'a jikin ta har rawa yake tana zaga falon tana ji kamar zuciyar ta zatayi bindiga ta fashe. "Mama baiyi picking ba nasan daman ko Mama ce ta kira shi yanzu bazai d'auka ba balle kuma ni" yana fad'ar hakan ya fita daga falon hankalin Mama da Mum ya sake tashi Mama kamar ta zubar da hawaye haka take ji.

A b'angaren su Asad ana idar da sallar la'asar Asad ya shiga b'angaren su Hydar ya fita bai wuce ko ina ba sai wajan mai martaba ransa a b'ace. Basu san mai ya faru ba dukkan su sun samu kiran gaggawa daga gare shi har Asad suka isa b'angaren nasa ba tare da sanin abinda ya faru ba. A zaune Asad ya tarar da Mama ga Hydar a gefe nan take gaban sa ya fad'i abinda ya faru yazo ransa ganin su kad'ai ne a ciki ya samu waje ya zauna Mai martaba yace, "Asad abinda Hydar ya sanar dani haka ne?." Shiru Asad yayi dan bai san mai Hydar yace ba ya d'ago ya kalli Hydar d'in kafin ya girgiza kai yace, "Haka ne takawa."
"To ma sha Allah. Bazan ce komai ba a yanzu zan tura aje a tawo min da mahaifin yarinyar da kuma ita yarinyar, Hydar kaje kazo dasu ka kai su b'angaren baya dan bana son cikin gida su san abinda yake faruwa in yaso in kazo dasu ka sanar dani zan zo da kaina."

Hydar ya amsa da to ya tashi ya fita babu wanda ya kuma magana a cikin su mai martaba baice komai ba ran Mama a b'ace tana ta hararar Asad shi kuma kansa na k'asa baya ganin me take yi. Ba jima Hydar yazo da girmawawa ya sanar dashi gasu can yazo dasu ya yace, "Ku je can gani nan zuwa." Tashi sukayi Mama kamar ta shak'e wuyan Asad haka take ji sai binsa take da kallo tana kwafa suka fita shi kuma ya kasa ma had'a ido da ita.

Ta wata k'aramar k'ofa mai martaba ya fita babu wanda ya lura da fitar sa sai gashi ya bayyana a harabar b'angaren da yace a ajjiye su ya shiga falon kowa ya mik'e tsaye banda Rauda da take k'okarin tashi ya kalle ta yace, "yi zaman ki" ya fad'a yana k'arasowa ya zauna a akan kujera duk suka zauna a k'asa.

Mai martaba ya kalli Baba yace, "Malam Adam mun same ku lafiya?." Baba jikin sa har rawa yace, "Allah ya ja da ran mai martaba, lafiya lau."
"To ma sha Allah. Ya akaji da abinda ya faru kuma?."
"Mun gode Allah ranka ya dad'e."
"Muna sake baku hak'uri akan abinda aka yi muku tabbas ba'a yi muku adalci ba. Meye sunan naki?" Mai martaba ya fad'a yana kallon Rauda.

"Rauda" ta furta a hankali mai martaba yace, "Kiyi hak'uri kinji Rauda duk abinda aka aikata muku ga wacce ta saka nan, babu babu wanda yasan abinda ya faru sai bayan ta saka an aikata d'in da baza mu bari hakan ya faru ba" ya fad'a yana nuna Mama da take zaune a gefe kana yace, "Mahaifiyar su ce komai ya faru itace ta saka ayi muku. gaku gata nan in kun yafe mata a k'yaleta in baku yafe ba kuma a yi mata hukunci daidai da ita kowa yasan mulkina baya lamuntar zalunci koda jinina ne ya aikata."
Rauda zatayi magana Baba yayi saurin katse ta yace, "Allah ya k'arawa sarki lafiya, babu komai mu hakan ma da akayi mana an nuna mana mahimmacin mu, an nuna mana muna muna da darajar da Mai martaba da kansa sai bamu hak'uri,ya wuce mun gode sosai." Mai martaba yace, "ka barta tayi magana ita aka yiwa ba kai ba, Fad'i abinda yake ranki."

Rauda ta kalli Baba yana kallon ta tace, "Babu komai ya wuce." Mai martaba yace, "kin tabbatar ya wuce ba'a takura ki ba?."
Rauda tace, "Ya wuce ranka ya dad'e."
Mai martaba yace, ma sha Allah. Rabi'atu basu hak'uri" ya fad'a yana kallon Mama.

A firgice ta kalli Mai martaba suka had'a ido kallon da yayi mata ya saka ta d'auke kai tana girgiza kai tare da taune leb'en ta na k'asa cikin wani abu wai shi bak'in ciki da taikaici ta kalli Rauda da take kallon ta itama ido cikin ido ta cize bakin ta kafin tace, "Ayi hak'uri." Murmushin jin dad'i Rauda tayi har cikin zuciyar ta taji abinda aka yi musu ya wanke tass ko babu komai mace mai izza ta basu ko iya nan sun ci riba.

Baba ya washe baki yace, "babu komai ranki ya dad'e, ya wuce." Mai martaba yace, "mun samu labarin an buge wata yarinya kwanaki amma bamu san ba'a kula da lafiyar ta ba tunda Hydar ya kwanta ciwo, Shima muna neman afuwa a kan hakan kuma nasan Asad zaiyi duk abinda ya dace in sha Allah." Baba yace, "Allah ya taimaki Mai martaba, komai ya wuce mu a wajan mu. Kamar yadda mai martaba yace Asad yana iya bakin k'okarin sa akan rashin lafiyar Rauda."

Mai martaba ya girgiza kai yace, "mun gode da karamcin ku a gare mu baki d'aya, muna tabbatar muku da babu abinda zai sake samun iyalan ku ta k'ark'ashin wannan gida in sha Allah."

Shiru babu wanda yayi magana kafin mai martaba yace, "Tunda hakan ta kasance ina neman wata alfarma a wajan ka." Baba yace, "A wajena kuma Ranka ya dad'e?."
"Eh wajan ka."
"Umarni shine naka a gare ni ba alfarma ba."
"Alfarmar dai nake nema ka amince na fad'i abinda nake so."
"A shirye nake da sauraron ka, Allah ya ja zamanin ka."

Mai martaba ya kalli Asad yaga kansa yana k'asa ya kalli Mama yaga tana kallon sa kafin ya kalli Baba yace, "D'ana Aliyu wanda nakewa lak'abi da Asad gashi a gefe yaga y'ar ka Rauda ya yaba da hankalin ta da kuma tarbiyyar yace yana so. Bama shi ba ni kaina na yaba da ilimin ta da kuma tarbiyyar ta da nuna b'acin ranta a kan abinda zai tab'a iyayen ta. Muna neman alfarmar a bashi ita inda damar hakan!." A take k'irjin mutane hud'u suka buga a wajan, Mama, Asad, Rauda, da Baba. A tare suka kalle shi shi kansa Asad d'in ya gigice bai san abinda zai fad'a ba kenan dan bai shiryawa hakan ba a lokacin kwata-kwata.

Baba baki na rawa yace, "Allah yaja zamanin mai martaba, maganar da naji ce nake kokwanto anya ba mafarki nake ba?." Mai martaba yace, "ba mafarki kake ba Malam Adam abinda kaji gaskiya ne. Amincewar ka da tata amincewar nake so a d'aura auren ranar juma'ar nan mai zuwa dan bana son a d'auki lokaci. amincewar ku kawai nake nema amma babu dole in taga bai mata ba karta takura kanta, in kaga kaima baza ka iya bashi auren ta ba duka ba abin damuwa bane. Ina tambayar ka a matsayin siriki ne ba matsayin shugaba a gare ka ba, ka kalle ni matsayin sirikin ka ka fad'a min amsar da take zuciyar ka. Zaka iya bawa Asad auren Rauda ko A'a?!."

Tirk'ashi!🏃🏼‍♀️😂

#Vote
#Share
#Comments

*KWANTAN ƁAUNA*
Fitattubiyar 2023

             ©️ *Nana Haleema.*

*Book 1*
*023.*

Kallon kallo ake tsakanin Baba da Rauda da kuma Mama kowa fuskar sa d'auke da rud'ani, Asad dai kansa yana k'asa ko motsin kirki ya kasa balle ya iya d'ago idanun sa yace wani abun yayi shiru yana jiran yaji abinda za'a ce dan zuciyar sa duka take kamar ana doka ganga. Baba ya kasa magana shud'ewar wasu dak'ik'u kana Baba yace, "Allah yaja da ra. mai martaba, abin ne naji shi wani iri shiyasa na kasa magana."

Mai martaba yayi murmushi irin nasu na manyan mutane yace, "Kar ka damu na baku lokaci kuje kuyi shawara in tana sonsa Alhamdulillah haka muke fata, in kuma bata so kar ayi mata dole a barta da ra'ayin ta. Ina sauraren ku nan da wasu kwanaki da kun yanke hukunci a sanar dani ayi komai a gama cikin watan nan bana so a d'auki lokaci mai tsaho."

Baba yace, "angama ranka ya dad'e, in sha Allah zaka ji komai daga bakina kamar yadda ka umarta. Allah ya k'ara lafiya da nisan kwana, ya jiqan iyaye ya sanya suna Aljanna." Da amin suka amsa dukkan su kafin mai martaba ya kalli Hydar yace, "A mayar dasu gida, a kuma tabbatar an basu kulawar da ya kamata bana so su nemi wani abun su rasa." Ba musu Hydar ya tashi suma suka tashi akayi godiya suka fita.

Falon ya rage daga Asad sai Mama sai mai martaba babu mai magana a cikin su kowa ta ciki na ciki, hawayen bak'in cikin da Mama take b'oye ne suka zubo mata daga idanunta ta share tana kallon wani wajan daban zuciyar ta nayi mata zafi da k'una sabida k'askantar da akayi a gaban talakawa.
Chapter 48 · 0% Book details