← Book details Kwantan Bauna Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 34 OF 55

Sashe 34

Kwantan Bauna Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Walida tace, "An ce sarkin garin nan ma dashi akayi." Habiba tace, "A'a yanzu fa daga gidan sarkin nake bai zo ba baya jin dad'in amma ya turo wakilan sa Asad da Aliyu. Kuma shi ai yana da k'okari wallahi ko ba masu kud'i ba yana zuwa jana'iza, ki tuna ta gidan su Salima da baban su ya rasu shine ma ya ja sallar gawar, yanzu ne ance baya jin dad'i shiyasa ya turo wakilan sa kuma na jiki."

Jin hakan sai gaban Rauda yayi mugun fad'uwa ta kalli Habiba tace, "Waye Asad a y'ay'an nasa waye kuma Aliyu?." Habiba ta kalle ta tace, "ke dai kina son labarin gidan sarkin nan. Aliyu shine babba shine baya ji bashi da mutunci ko kad'an bai d'auki talaka a bakin komai ba, shine ya mare ki ranar nan badan nayi masa wannan kirari ba wallahi sai yace a kai ki ki share turken dokunan da kike jin tsoro kuma wallahi sai kin yi in ba haka ba a zane ki" ta fad'a tana kallon Rauda ta cigaba da fad'in,

"Bashi da mutunci ko kad'an ya raina talaka ganin talaka yake kamar ba mutum ba, in fa ya tawo bayi ko dogarai suka tawo wallahi sai kin koma can baya duk nisan wajan ya wuce sannan zaki wuce, ga shi kowa ya shaida a gidan shaye-shaye yake da neman mata shiyasa basa shiri da mai martaba. Naji ance a da yafi son Aliyun amma rashin jin sa ya saka ya fita a ransa tunda yayi yayi Aliyu ya shiryu yak'i kullum sake wastewa yake yi, gashi baya yafiya ko kad'an. akwai wani labari da naji y'ar sarkin Zamfara tayi masa rashin kunya ya saka aka d'auko masa ita yayi mata fyad'e na wulak'anci ya azabtar da k'arshe yarinyar rasa ranta tayi, amma da yake babar sa ba kanwar lasa bace wallahi tuni an manta da maganar."

Habiba bata kula da halin da Rauda ta shiga ba tace, "Asad kuma shine Kamili mai kirki duk da baya fara'a amma kowa ya shaida a gidan nan shine ya fita zakka kamar ba jinin sarauta ba in yayi miki wani abun, bazai ga ana wulak'anta d'an adam a gaban sa ya k'yale ba, bazai ga ana cin zarafin wani a kyale ba, shiyasa ko hukunci Aliyu ya saka a yiwa wani da sun ga Asad zasu daina domin tasu tukunyar ce zatayi zafi a wajan sa. Ga taimako ko a hanya yaga tsoho zai tsallaka titi Asad yana iya parking mota ya fito ya tsallakar dashi ya bashi kud'i sannan ya koma mota yaje inda za shi, labari in yaji na gidan ku baku dashi ko kuna neman wani taimako sai ya taimaka muku wallahi, wani lokacin baza ma kusan shine yayi ba. Kuma kaf gidan nan babu mai kud'in sa hatta mai martaba bashi da kud'in da Asad yake dashI, sai dai mai martaba ya nunawa Asad kadarori amma zunzurutun kud'i Asad ne yake dashi tunda shi bada Nigeria yake aiki ba. Kullum fa sai ya bawa su Gwaggona dubu d'aya sadaka, sama da mata d'ari a gidan nan kowa sai ya samu yara da manya, in kana da buk'ata ma in Allah ya had'a ku ka nemi taimakon sa an gama shiyasa kullum yake gaba baya b'ata yin baya a rayuwar sa."

"Shi bar shi da baya magana dan ya kwana uku ma bai fito daga d'aki ba abu ne mai sauk'i a gare shi tunda ba zaman k'asar yake so ba, duk inda kike tunanin miskili mara son magana da hayaniya ya wuce nan, shiyasa y'an gidan da dama kurma suke ce masa domin ance sai su zauna meeting na cikin gidan su a tashi bai ce kanzil ba, sam baya k'aunar magana shi yafi son shiru shiyasa ko gaishe ki kayi a hanya sai dai ya d'aga hannu in yaga dama yayi murmushi. Amma fa naji ance duk tsiyar Aliyu in Asad yayi fushi bai kama k'afar tasa tsiyar ba, ance duk ya fisu zafi ta Aliyu ce ta bayyana."

Walida tace, "shi na ukun fa?." Habiba tace, "Hydar kenan gidan fara'a, shine kuma basa kama da y'an uwan in kika ganshi ma baza kice y'an ukun su bane, wad'ancan sune masu kama kwabo da kwabo kika ga Asad kika ga Aliyu baza ki banbance ba. A da adon gemu ne yake banbanta su na Asad bak'i ne sosai na Aliyu kuma ya shirka da ja, cikin kwanakin nan shima ya mayar da nasa bak'in kafin ki gane su zaki sha wahala. Hydar halin su d'aya da Asad kawai shi yana da wata cuta ce da in ta tashi sai ya shafe wata a kwance kamar yadda na fad'a muku ranar nan, yanzu haka ma ciwo ya tashi yana kwance ya jima ance ko motsi baya yi."
"Allah sarki Allah ya bashi lafiya."
"Amin. Ke Rauda lafiya kike kuwa?" Habiba ta fad'a ganin kamar ta fita a hayyacin ta.

Rauda ta firgita ta kalle su hawaye ya wanke mata fuska tace, "fyad'e kika ce ya yiwa wata dan tayi masa rashin kunya fa, kuma y'ar uwar sa mai kud'i da mulki; Innalillahi wa'inna ilaihir raji'un, Habiba na shiga uku ni yanka ni zai saka yi, bakina ya jawo min abinda yafi k'arfin dangin mu gabad'aya." Walida da mamaki tace, "Me kike nufi?."
Sai kuma Raudan ta saita nutsuwar ta tace, "Wai da ranar da ya mare ni na tanka masa."

Habiba tayi dariya tace, "ke me zai had'a ki da wannan? Yadda ya raina talakawa wallahi Allah kad'ai yasan mai zai miki. Banza matsoraciya shine har da kuka?" Ta fad'a tana kallon ta sukayi dariya ita da Walida. Habiba ta kuma cewa, "kuma baku san wani abu ba, a kaf gidan babu mai taka masa burki kamar Asad d'in, basa shiri fa amma kamar ba y'an uku ba sam Aliyu da Asad basa jituwa amma kuma in ya tsawatar akan abu ance Aliyun yana shayin aikatawa, dan Asad akwai slicent treatment."

Walida tace, "Ke wai a ina kike jin wannan labaran?."
"Ina fa kwana a gidan, kuma kin san labarin gidan sarauta baya tab'a b'uya ko me aka aikata sai ya bayyana."

Basu lura da yanayin ta ba suka cigaba da tafiya har aka zo gida Rauda ta shiga gida suma suka wuce nasu gidan. Umma na zaune taga shigowar Rauda a gigice ta bita da kallo tace, "ke kuma lafiya?." Jikin ta har rawa yake tace, "babu komai Umma" tana fad'a ta shiga d'aki ta zauna gefen gadon Umma ta ajjiye sandinan ta a gefe kawai ta fashe da kuka.

"Na shiga uku ni Rauda na jawowa kaina bala'i" ta fad'a a hankali gudun kar Umma taji. Bugawa k'irjin ta yake cikin tsoro da fargabar abinda zai je ya dawo hankalin ta ya mai k'arshe wajan tashi k'irjin ta har d'agawa yake sabida tashin hankali.
Umma da ta d'aga labule ta shigo ta kalle ta tace, "Ki sanar dani abinda yake damun ki."

Kuka take sosai bata ce komai ba Umma na tsaye tana kallon ta ganin yadda take kuka sosai sai tayi mata shiru tana kallon, sai da ta gaji da kukan sannan ta kalli Umma tace, "Tausayin kaina nake Umma lokaci guda na nakasa." Umma ta girgiza kai tace, "Wani lokacin kamar bake ba, kina mantawa da Allah yana canjawa bawa halittar sa komai tsufan sa, indai ba mutuwa kika yi ba'a gama canja miki halitta ba. Indai baza kiyi imani da k'addara ba kuka yanzu kika fara" ta fad'a tana komawa da baya ta barta.

Kwanciya Rauda tayi cikin tashin hankalin da ya hana zuciyar ta sukuni, hangowa take ya saka an kamo ta itama anyi mata fyad'e kuma an kashe ta lokaci d'aya sai taji hankali ta ya kuma tashi. Tana kuka bacci ya d'auke ta bata sani ba.

*☆☆☆*

Tunda ya shiga falon Mama ya zauna bai ce kala ba ganin hakan sai Mama ma ta share shi ta cigaba da danna wayar ta dan duk a tunanin ta Asad ne ba Aliyu ba, shigowar Asad ya saka ta kalle shi taga fuskar sa tayi kama da ta Asad ta dawo da kallon ta ga Aliyu taga sak iri d'aya dai ta Asad d'in ce a d'aure ko wanne da alamun b'acin rai a tare dashi.
Sanda Asad ya zauna lokacin ta kalle su ta ajjiye wayar a gefe tace, "Ikon Allah." Nan ma babu wanda ya tanka mata a cikin su sai suka sake rud'a ta.

"Lafiyar ku kuka shigo min ko wanne fuska a d'aure? taz'aziyar da mahaifin ku ya tura ku kenan?."
Nan ma shiru babu amsa ko wanne na kallon wani wajan daban sai suka fusata ta tace, "Malamai bakwa ji ina muku magana ne? Wanne irin iskanci ne wannan ina magana kunyi banza dani kamar sa'ar ku?. Ku banbance min kan ku tunda kun d'auko sabon iyayin saka kaya iri guda, banbancin ma da yake fuskar Aliyu ya shafe shi."

Tab'e bakin da Aliyu yayi ya skaa ta kalle shi tace, "Kaine Asad kenan" sai ta kalli Asad taga bama ita yake kallo ba nan ta sake rud'ewa dan gabad'aya ko wanen su acting d'in Asad yake yi. Ganin ranta ya fara b'aci ya saka Asad yace, "Allahbya wuci zuciyar Mama, ya jikin Hydar?." Yana fad'ar hakan sai ta gano waye dan Asad yafi damuwa da jikin Hydar akan Aliyu daman kuma tun farko tasu tafi zuwa d'aya, ta kalli Aliyu tace, "baku tab'a rud'a ni kamar yau ba, kamar ku ta fito a zahiri sosai har ta bani tsoro tabbas Aliyu ka koma min Asad a yau."
Chapter 34 · 0% Book details