← Book details Kwantan Bauna Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 8 OF 55

Sashe 8

Kwantan Bauna Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Daga can inuwa ta hango motar Anas ta ja tsaki a zuciyar ta ta sake d'aure fuskar ta dan ma kar yaga fuskar da zai kulata, hango ta yayi ta tawo ya fito daga motar yana murmushi tazo zata gifta shi kenan ta jiyo amon sautin muryar Baba yana fad'in, "ki tabbatar sai kin biya ni hamsin d'ina ta jiya dan ba bar miki na yi ba!."

Runtse idanun ta tayi cikin takaicin dizgi irin na Baba ganin wanda yake tsaye ya saka Baba k'arasowa yana fad'in, "Anas yau kaine da rana haka?." Murmushi Anas yayi ya duk'a har k'asa ya gaida Baba ya amsa da fara'a yana fad'in, "Gashi mutuniyar zata tafi wajan sana'ar ta, kana jina da ita ko? Jiya ta yar min da hamsin shine nace sai ta biya ni shine duka ranta a b'ace."

Rauda kamar ta matse bakin Baba haka take ji amma babu dama ta d'aga k'afa zata bar wajan taji Anas yana cewa, "Baba har yanzu Rauda bata daina yawon siyar da abincin nan ba?."
"To ya za'ayi Anas dashi muka dogara ai."
"Bana son yawon Allah ya sani Baba, inda dama a siyar a gida in ya zama dole, in kuma akwai sana'ar da za'a canja a canja basai sun dinga fitowa ba."

Baba ya gyara tsayuwa yace, "Daman sana'ar keke napep d'in nake so to ance kud'i ne dashi tsububu shiyasa muka ganewa abincin."
"Babu damuwa Indai za'a daina bata abincin nan ta fita zan siya maka napep Baba."
"Kai amma nagode d'an albarka, wannan abu mai shegen kud'i za'a siya min? Wallahi na rasa ma me zance maka dan murna." Anas yace, "Babu komai ai Baba."
Baba yace, "talla ai daga yau ta daina zuwa yau d'in ma dan kar ayi asara ne" ya fad'a yana murmushi yana kallon sa.

Kallon Rauda yayi yace, "Rauda na nawa ne abincin?." Kafin ta bada amsa Baba yace, "Na dubu uku ne." Da sauri ta kalle shi shima ya kalle ta ya d'auke kai Anas ya zaro dubu biyar ya bawa Baba yace, "na siye na yau, dan Allah Baba a daina bata tallan nan bana so wallahi."

Hannun Baba har rawa yake ya karb'a yana zuba godiya Anas yace, "Babu komai Baba, zanyi tafiya yau bazan jima ba zan dawo dana dawo za'a kawo maka napep d'in in sha Allah, amma dan Allah a hak'ura da tallan nan dan Allah badan ni ba."
"Ai an gama Anas baza a kuma ba in Allah ya yadda."
"Na gode Baba."

Baba ya kalle ta yace, "bani kular na shiga ciki ku gaisa" ya fad'a yana karb'a ya wuce ya tafi gida ita kuwa ji take takaici kamar ya shek'e ta. Kallon ta Anas yayi yace, "kiyi hak'uri nasan na takura miki Rauda, Ina son ki ne da zuciya d'aya kuma auren ki zanyi." Bata ce komai ba ya kuma cewa, "Dan Allah kice wani abu mana Rauda."
"Me zance to? Na fad'a maka ni ba aure zanyi ba ka fita daga rayuwata ka nemi dai-dai kai amma kak'i."
"Kece dai-dai Rauda ko shekara nawa zakiyi nan gaba zan jira ki har ki shirya yin auren, Ina son ki Allah ya sani."

Bata ce komai ba yace, "ki bani number wayar ki zanyi tafiya ina so muryar ki ta dinga debe min kewa."
"Bani da waya, na gode da abinda ka bawa mahaifina Allah ya saka alkhairi, sai anjima" ta fad'a zata wuce yayi saurin cewa, "Dan girman Allah ki tsaya." Ba musu ta tsaya ya ya bud'e mota ya d'auko farar envelop ya mik'o mata yace, "ki karb'i wannan kya sha ruwa."
Kallon sa tayi ta kalli takardar tace, "na gode."
"Dan Allah ki karb'a."
"Kayi hak'uri bazan iya ba."

"Da hannu a jikin ki kice baza ki iya karb'a ba?, Rauda meyasa kike.mayar da hannun kyauta baya bayan kin san babu kyau hakan?!" Baba ya fad'a yana k'arasowa wajan yana kallon ta.

*KWANTAN ƁAUNA*
FitattuBiyar 2023.

          ©️ *Nana Haleema.*

*004.*

Runtse idanu Rauda tayi ji take ina ma k'asar wajan ta tsage ta shiga sabida kunya da takaicin abinda Baba yayi mata a wajan, ba'a b'ata yi mata abinda ta jishi a zuciyar ta kamar wannan lokacin ba, kafin ta gama wani tunani har ya k'araso kusa da ita daidai kunnen ta yace, "y'ar bak'in ciki baza ki karb'a ba?." Idanun ta ta bud'e ta kalli Anas da yake kallon su ta kalli Baba da yake ta yi masa murmushi.

K'arasowa yayi ya sake mik'a mata kud'in ta nok'e hannun ta idanun ta na kawo ruwa Baba yace, "Ki karb'a mana ai ba'a mayar da hannun kyauta baya." Hawaye ya sakko daga idanun ta ta mik'a hannu ta karb'a hannun ta har rawa yake Baba ya washe baki ganin kud'in sun shiga hannun ta yace, "Madallah Anas ana ta shan hidima Allah ya saka da alkhairi."
Murmushi yayi yace, "Babu komai Baba, zan koma a gaida mutanen gidan" ya fad'a da girmamawa har yana rage tsayin sa Baba yace, "to ba madallah, a gaida mutanen gidan dakyau."

Anas ya amsa yana wucewa ya shiga mota ya ja ya bar unguwar zuciyar sa kamar sake kwarara masa son Rauda ake yi domin ya tabbatar in ya same ta ya samu wacce ta aure shi ba dan kud'in shi ba.
A guje ya rufa mata baya ya tare ta a soro yace, "Ke Rauda! Bani kud'in mu ga." Ba musu ta mik'a masa ya b'are takarda ya ciro kud'in yana lissfawa. Dubu ashirin ne cif a ciki Baba baki yak'i rufuwa ya raba biyu ya d'auki dubu goma ya mik'a mata goma yace, "sai ku raba ke da babar ki badan na haife ki ba ai da baki samu ba" ya fad'a yana sokawa aljihu yana gyara zaman hular kansa.

Babu yadda ta iya ta karb'a ta wuce ciki ta shiga d'akin Umman ta fuskar ta a chucule, a zaune ta same ta zauna itama Umma tace, "kiyi hak'uri Rauda babu yadda zakiyi da halin mahaifin ki bazai canju ba shekaru sun riga sun tafi, yace min wai saurayin ki ya siye d'an waken gashi nan mu ci har gobe da safe." Rauda ta goge idanun ta tace, "haka yaje ya saka shi a gaba fa Umma har yace zai siya masa napep bayan nan ya bani kud'i naki karb'a Umma yazo ya saka dole sai na karb'a ya raba kud'in biyu ya d'auki rabi wai in da bai haife ni ba ai bazan samu ba. Yanzu Umma dan Allah ko Anas d'in na aura bai riga ya zubar min da mutunci a idanun sa ba?."

"To ya zakiyi ba'a canja mahaifi sai hak'uri, halin sane wannan mazajen yayyen ki ma da basu da kud'i ya suka cika dashi balle Anas mai kud'i?."
"Ga kud'in Umma, ni gidan Yaya Ummi ma nake so naje" ta fad'a tana mik'a mata kud'in ta karb'a tana kallon kud'in tace, "Allah ya sani bana son karb'ar kud'i hannun saurayi musamman ma irin Anas, a haka dai bashi da hali mara kyau amma.....to Allah dai ya kyauta" ta fad'a tana ajjiye kud'in jikin ta duk babu dad'i.

"Amin. Zanje gidan Yaya Ummi Umma, anjima zan dawo."
"To d'auki d'ari biyar ki hau motar zuwa da dawowa kar kije can ki d'ora mata nauyin kud'in mota itama ba k'arfi ne da mijin nata ba." Ba musu ta karb'a ta tashi ta saka talamin ta ta fita.

Bata jima ba ta samu abin hawa ta tafi gidan yayar tata, har k'ofar gidan ta abin hawan ya tsaya ta sauka ta basa kud'in sa ta shiga cikin gida. Tana tsakar gida tana aiki gidan shiru yara an tafi makaranta ta shiga da sallama, amasawa tayi ta d'ago tana kallon ta tana fad'in, "Maraba da amaryar Anas" ta fad'a  cikin zolaya tana dariya.
Sai kuwa ta d'aure fuska ta k'arasa kan tabarmar da ta gani a shinfid'e ta zauna tana fad'in, "Allah Yaya shiyasa bana son zuwa gida nan wani lokacin."

Dariya tayi ta bar abinda take yi ta dawo kusa da ita ta zauna tace, "to k'arya nayi? Ke a tunanin ki Baba zai bar Anas ya kufce masa bai bashi ke ba?, ai wallahi ko auren dole ne sai Baba yayi miki sai dai ki mutu."
"Hmmmm bari kawai Yaya, lamarin Baba sai shi."
"Yanzu dai ya Ummana tana lafiya?."
"Lafiya lau, tana gaishe ki."
"Yau ina tallan?."
"Na fito zan tafi Anas yana k'ofar gida shine fa ya siye har da ninkawa Baba kud'in yace a daina bani talla, wai Baba yace masa wai napep yake so ya siya kuma babu kud'i, a tak'aice dai yace zai siya masa."

Yaya ta girgiza kai tace, "Allah ya kyauta, lamarin Baba sai addu'a."
"Amin, kin san me Yaya."
"Sai kin fad'a."
"Mafarki nayi ina makaranta ina karantar aikin jarida." Yaya Ummi ta dara kad'an tace, "Wannan mafarki naki na aikin jarida Allah yasa ya tabbata Rauda."
"Badai a gidan Baba ba."
"Ha! Ha! Daman sai dai in kin auri Anas" Yaya Ummi ta fad'a tana dariya.

Rauda tace, "Kin san kuma kwana biyun nan sai na dinga mafarkin mutane masu fuska iri d'aya ko wanne da rawani a kansa, d'aya yana b'angaren dama d'aya hana haggu, a tsakiya kuma nice in na tafi wajan d'aya sai na kasa k'arasawa in na koma wajan d'aya ma sai na kasa zuwa. Ina yawan wannan mafarkin amma har yanzu na kasa rik'e fuskokin mazan guda biyu."

Yaya tace, "tofa, Allah mai hikima shi kad'ai yasan meya b'oye a cikin mafarkin naki, koma dai meye Allah yasa alkhairi ne shine fatan mu."
"Amin Yaya." Daga nan suka cigaba da hirar su.

*☆☆☆*

Tunda garin Allah ya waye ya samu labarin mai martaba da Asad sun fita hankalin sa yayi mugun tashi, safa da marwa yake a d'akin ransa a b'ace zuciyar sa yske so ta bashi mafita akan Asad amma har lokacin ya kasa samun matsaya.
Chapter 8 · 0% Book details