← Book details Idan Kaya Ya Gaji Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 14 OF 47

Sashe 14

Idan Kaya Ya Gaji Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Wai garinma yaya kaji irin wannan ciwon ne?"
"Kar ki damu.

Ki daure ki kiramun likita hannuna tsami yake yi mun"
ewa tayi ta fita, yabi bayanta da ido kawai.

Takamaimai ya rasa tunanin me zaiyi ma zuchiyarshi a cunkushe take sosai.

Haka dai wannan daren ya kasance musu dare dubu da
MRS BUKHARI
Babangida yana ruwa
IDAN KAYA YA GAJI...

GAMMO MA YA GAJI
LITTAFI NA BIYU
SHAFI NA SHIDA
BADIAT IBRAHIM MRS BUKHARI B4B GIDAN
AMSHI
ARIN SHAFI ALLAH YASA ZUKATANKU SUYI SANYI.

SABUWA:.

Haka dai lamura suka ci gaba da tafiya suna jiyawa.

Matan Babangida suka ci gaba da jinyarshi yau wannan ta kwana gobe waccan.

Amarya dai tana turakar mijinta.

Yadda na fuskanceta bata da ha
uri kamar zawayi haka take, shi yasa kusan kullum ita da
ar shuwa sai sun hau sama sun duro, gata da gadara da girman kai.

Ni dai tun daga wannan ranar kafata bata sake taka asibiti ba.

Malama Babba ma har aka sallamota banje ba.

Baba Malam kam naje har sau biyu gida na duba shi.

Shine ma ya sanar dani a tsanake in tattare kayayyakina waje guda, in
alle gado da komai nawa dai.

Bai mun bayanin komai ba, nima ban tambaya ba na dai bi umarninshi nida su Labbai mukai ta kaye_kaye.

Sai da su Sa'a suka zo gidanne
ar Shuwa ta rakouu barayina ko zama sun kasa yi.

"Ku ha
a kayayyakinku waje guda zaku tashi a gidan.

Za'ayi ma gidan gyara sosai ne"
Bata bari na amsa ba suka fice.

Amman jikina yana bani matsala ba tun yau ba, dan na fahimci su Kawu Manga sai kai kawo suke yi hatta motar
ar shuwa babu.

A zuwa na duba Baba malam na ukunne ma na tarar an sallamo Malama Babba sai na shiga na dubata da jiki.

Ta rame ta koma
e sosai.

"Sa'a ku bamu waje inaso zanyi magana da Sabuwa"
Bani ka
ai ba harsu Kudidi suma sun yi mamaki.

Ni ko kaina cike da tambayar da babu wanda zai iya amsa mun.

Nan duk suka zame suka fita.

Cikin gadara Malama Babba tace.

"So nake ki janye wannan shar'ar da kika shigar da
ara kotu.

Na yi miki al
awarin ko nawa kike bu
ata zan baki"
Da mamaki na kalleta sai kawai nayi murmushi nace.

Bazan iya janye wannan
aran ba, ko da duniya da abinda ke cikinta zaki bani.

Takaddar sakina yafi mun komai"
A_a dai kije kiyi tunani nan da kwana biyu kinga lokacin shiga kotu ya kusa.

In kika janye zan baki ku
i masu kauri "
Daga sama muka jiyo muryar Baba Malam
"Babu mahalukin daya isa yasa ta janye.

Da kike maganar ku
i kuma a ina kika samesu ni bani da masaniya a kansu?

Ai dani kika bama kya samu lada.

Ke Sabuwa taso ki kama hanya ki tafi gidanki"
Sum_sum na ficewata ya suka
are sai Allah.

Ina isa gida a
ofar gidanmu naga wata
atuwar mota tana ta loda kayayyakin
aki harda gadona na hango a cikin motar.

Ban gama mamaki ba Labbai ta fito da
atuwar randa ta cike da kwanuka da su cokula.

Ga Hamida itama a gefe tanata zuba kayayyaki a buhu.

Gidan duk ya hautsine
Hannuna Labbai taja muka shiga cikin gidan"
"Kinga muna zaune Wawo ya le
o yace mu fito da kayanmu.

Lallai Sabuwa zaku sha gyara.

Amman naga gidannan babu abinda ya sameshi sai samannan da ake tadawa"
Jikina a sanyaye nace.

Sunce gyara za'ayi sosai a gabanki fa Sa'a ta fa
a mana.

Ina Adama fa?"
"Tana ciki tana fito da kaya muje daga ciki"
Ciki muka shiga muka ci gaba da harha
e kaya.

Motar ma ta cika har sun tafi kai kayan.

Ni ko har mun gama fitar da kab kayanmu waje, har Adama ta share
akunan, ni da Labbai mun goge komai da komai.

Har wajajen bayan la'asar yara suka shigo suka samemu muna jira, Adama dai tabi motar kaya da suka dawo.
ota duk an shisshigo dan jin ba'asi.

Da an fa
a musu gyara za'ayi mana sai su shiga taya mu murna.

Maman Safara,u ta da
e sosai tare damu taso binmu ma taga waje amman ganin har an kira magriba ba'a zo ba yasa tace.

"Maman Mardiyya ni kam zan tafi gida yau nice da oga, gashi dare yayi inaga sai zuwa gobe zan kiraki a wayar Labbai sai in zo in sha Allah.

Allah ya sanya alkhairi ya
ara arziki"
To Ameen Maman Safara,u nagode sosai Allah ya bar zumunci.

Sai zuwa goben.

Ta fita bata jima ba Wawo ya shigo yai kiranmu duk aka duramu a siyana muka
au hanya.

Motar tayi tsit kowacce da abinda take sa
awa.

Bamu tabbatar da akwai matsala ba sai da muka ga motarmu tasha kwanar wata unguwar da ka
an tafi unguwar da muka taso na da kyau.

Ga hanyar shiga unguwar bata da kyau ga ba wuta sai fa
awa ramuka muke yi.

A bakin get
in wani gida motar ta tsaya, get
in irin get
innanne da baikai har
asa ba, kai me wucewa kana iya hango har guiwar na tsaye gashi duk tsatsa.

"To masha Allah ga gidan da zaku zauna nan.

Muje in nuna muku
akunanku dan ba jere suke ba."
Wawo yayi gaba muka bishi a baya da yaranmu.

Gidan shiru babu hayaniya, babu ko macce
aya a tsakar gidan.

Gidane dogo ga
una a jere suna kallon juna.

Hagu
akuna hu
u dama ma haka, daga bakin get akwai wani lungu dana hango
akuna kamar hu
u suma a jere .

Wannan lungun shima lungu yake kallo da
akuna hu
u a jere suma kunji wata
udurar Allah.

"Ga
akinki Maman Fatima can na
arshen hagun dama.

Maman usama ga naki
akin na farkon hanun hagu, Amarya naki shine na tsakiyancan na hannun dama.

Maman Mardiyya naki na baya ta can kwanar muje in nuna miki sauri nake yi muna da meeting a gida.

Gashi muna sa ran gobe za'a sallamo Babangida daga asibiti ma.

Muna biye dashi har zuwa lungun
akina shine na
arshe a lungun.

Harma na hango Adama tana ta faman moping
in wata
ar baranda dake
ofar
akin, ko wanne
aki naga da baranda, kuma kamar babu kitchen a ciki dan naga duk a barandar naga iyakar
akunan dana hanga kitchen
insu yake.

Saida na shiga barandar naga harda kwanon wanke_wanke na turawa.

Adama sun jera mun durowowin kitchen
ina a wajen sun ciccikasu da kwanuka da tukwane da dai tsarkacen kayan kitchen namu na mata.

"Sai yanzu kuka shigo irin wannan jimawa me ya tsayar daku haka?"
Labbai ce taba Adama amsa.

Su Sadiya suna ciki sunata shewa.

"Wallahi Wawo ne baizo da wuri ya
ebo mu ba.

Yinwa kamar zata kashe ni."
"Yinwa?

Hmm muma ita muke ji.

Baku ha
u dasu Gaza ba?"
Sun zo ne?

Gaskiya bamu ha
u ba dake muna cikin mota"
Ciki muka shige yara dama tuni sun shige sai A
a'u da Malama sai murnar sabon gida suke yi.

Falon
aramine sosai gashi kujeruna suna da girma gabaki
aya sai suka takure falon, banga 1 sitter ba ma.
ofar da nake tunanin uwar
akine na shiga sai naga dogon falo ( Coridor) ne ga
ofofi guda biyu a jere, amman suna da taraza
ofofin.
aya ashe ban
akine
ayan
akin kuma
akin baccine.

Sai a falo kuma akwai wani
aramin
aki sosai yafi kama da store.

"Kinga wajen Lolo amman babu
akin yara.

Ma
ociyarki tace duk wannan
akin suke mayarwa na yaransu.

Amman asalinshi kitchen ne.

Sai mai gidan ya dawo da Kitchen
ar barandar waje.

Wasu ma da kansu suka yi aiki.

To kinga gadone ka
ai ya shiga, dorowarsu ta
i shiga, amman ta shiga
akinki.

Sai kayayyakin Babangida na turakarshi duk su Wawo basu sauke ba dashi suka juya
ila sabida babu wuri ne.

Amman dai tulin kayanshi mun jera a durowarki,
ankunnayen su Mardiyya da naki duka kuma suna
aramar jakarki."
Ajjiyar zuchiya na sauke tare da neman waje na zauna ina sake
arema falon kallo.

Sannunku Adama, Sadiya sannunku fa.

Ashe har kun garzayo.

Kinga
akinnan sai dai su Aminu su dinga kwana a ciki, ni da matan sai mu kwana a
akina"
Carab Aisha dake waya tace.

"Babansu in a
akinki yake kuma fa?"
Adama tace.

"Ato kema kya tambayeta."
Dana waiga naga yaran basa wajan sai nace.

Ai kunsan rabuwa zamu yi tunda saura kwana uku ma zaman kotu.

Kuma ai dama baya raba mana kwana da matanshi balle kuma yanzu kuma duk kun sani.

Yanzu dai su Aisha su siyo mana ko da biredi ne sai mu sha tea tunda akwai wuta.

Labbai muje ciki muyi Sallah "
Ciki muka shiga bayan na sallami su Aisha da ku
in biredi kayan tea ina dashi dama.

Ina rama sallolina maimakon in huta saina shiga tattare kab suturun Babangida da Adama suka jera mun.

Ko da suka shigo suka samu inata tarkace komatsenshi babu wacce ta tanka mun, kuma nasan dan sunga na mugun ha
e rainane.

Akwati uku na cika, banda manyan jakunkuna hu
u dana ciki, ga takalma cikin
aramin buhu.

Labbai taya ni muje mu kaima matan Babangida wannan kayan nashi, ni bana son Magana.

Ke Mardiyya Aisha ku taso"
Haka muka kinkimi kaya na
wasa
ofar Hamida duk muka jibge mata kayan a
ofa.

Da waya a kunnenta ta fito.

Ganin kaya yasa tace.

"Zan kiraka Baban Usama ina zuwa'"
Ta sauke wayar tana kallon kayan.

"Wannan kayan daga ina kuma?"
Kayan mijinku ne, ku ke da hakkin adana mishi"
Da harara da ta
e baki tace.

"Ni ina naga wajen da zan ajjiye wannan tulin kayan.
akuna tsukuku kamar kabari.

Sannan ai bani ka
ai bace matarshi ba.

Ga Ramatu me yasa ba'a raba an kai mata ba tunda Maman Fatima tana asibiti?"
Kallonta kawai nayi nace da su Labbai su tawo mu tafi dan bani da lokacinta
"Maman Mardiyya kizo ki debe mun wannan kayan daga nan duk bala'in da kike nema na dashi kin tara kin samu."
Babu wanda ya juyo balle ya tanka mata.

Tea da biredi harda tsire su Sadiya suka siyo mana.
Chapter 14 · 0% Book details