← Book details Hasashen Soyayya Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 9 OF 51

Sashe 9

Hasashen Soyayya Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Bayan ta samu sau™i. Shiru Bhatool tayi tana son tace bazata ba, sai kuma ta tuna dole zata ga Senate Mutumin da kyansa da sautin muryarsa ya tsaya mata arai. Shikenan bari na haWa kayana. ta faWa tare da tashi.

Cikin ™an™ani lokaci ta haWa kayanta da kuma jakar makarantar ta, fitowa tayi tsakar gidan ta tarar da Mama da Yaya karima, Mamace ta kalleta sanan tace Bhatool kinga bata da lafiya ki nutsu dan Allah. Cikin sanyi murya tace Insha Allah Mama, ki gaishe mun da Abdul Wina. Daman haka Bhatool take tana da rigima amma tabbas bata son nisa da Mama ko Abdul, Kasancewar Yaya Karima na da mota kuma a ita tazo ba mijinta bane zaizo ya Wauke ta kuma ga Yamma yara sun kusa dawowa daga school, daman tun safw tazo sunje duba Goggo Larai ita da Mama.

Ko a mota ma Bhatool ba tace uffan ba, har suka ™arasa Gida tayi nisa a cikin tunani taji Yaya karima tace Dan Allah je gidan Momi kice mata nadawo ta aiko da saqon. Tabbas Bhatool taji dadi sosai domin tunanin da takeyi kenan tinda suka tawo har tazo, Tom Yaya. ta faWa tare da nufar hanyar gidan.

~~~~~Yana zaune cikin gidan Yau bai samu ko yaje makarantarsu Bhatool ba sabida gaba Waya ita yake gani da ya rufe idonshi, bama yaso yayi tafiyar da zaiyi nisa har yakasa rufen idon, kuma abunda ke sa mai jindadi shine idan ya ganta murmushi take masa, kuma Salman ne da juraij sunzo a gidan suka yini, sun tattauna kan bikin ™annen Salman da kuma company da zasu buWe, Rabin kuWin da za a bude company Win Abban Senate ne ya bashi sanan shima ya haWa da nashi, shi ke da kaso 75 cikin Wari na campanin sai Kuma juraij da yasa kaso 25 wanda yasawa Salman ne domin Juraij Dad Winshi ya bashi company shi dake Cyprus shiya ba cika zama nigeria ba.

Sunyi ja inja sosai wajen saka sunan kamfanin inda Senate yadage sai dai asa Bhatool, Shi Salman bai cika hayaniya ba Juraij ne dai yayi ta ja dashi,shima kuma wasa yake mai sabida yana so yaga Senate na doguwar hira kuma a rayuwar Senate dasu kaWai yake iya hirar sakamakon sanin halinsa da Juraij yayi hakan yasa yake janshi da doguwar hirar, ™arshe dai suka amince a haka.

Bayan tafiyarsu ne yadawo falo, su na zaune tare da Mom suna hira sama-sama,sai kuma Anas da bai daWe da daowa ba, Anas Win ne ke tsokanar Senate yana cewa Ango mijin Amarya. Wani kallo senate ya watsa mai ba tare da yace komai ba. Angon Batula. kallonshi ya ™arayi sanan yace Stop. cikin sasanyar muryarshi. Na batula. Anas ya sake faWa yana dariya, kallon Mom senate yayi wacce take zaune kamad ba ta jinsu. Mom! kiyi masa magana. Harara ta makawa Senate Win sanan tace Komai ni zan maka ko?. Hannu yasa ya fara sosa ™eya shi kuma Anas ya ™ara cewa Senate Bhatool. .

Mene yasa ba zaka kira ta da Anty ba. Daga Mom har Anas juyowa sukayi suka kalleshi, jin yanayin da yayi magana kamar bashi ba,Murya cike da ™arfi da ™warin gwiwa da kuma kwar jini,son ™ara tabbatarwa ne yasa Anas ™ara cewa Bhatool senate. .

Anas ba kai naiwa magana ba?. Tabbas shi yayi maganar wallahi,Mom ce tace Senate, daman ka iya magana haka?. cikin fushi yace Mom mai yasa bazai kirata Anty ba,ai na girmeshi dan haka mata ta ta girmeshi. kallon ikon Allah Mom ta tsaya yi, kenan idan yana cikin Sacin rai shine yake magana haka lallai ne. I'm sorry. Anas ya faWa Sorry for your self. Senate ya faWa tare da tashi.

Rufe idonshi yayi da ™arfi tare da ri™e ™irjinshi..

Legend's pen 08129553971.

10-

*HASASHEN SOYAYYA*d'þ
=Ø%Ý>ØyÝ

_Imagination of love_

_Stroy and written_

By

Sayyid (Legend's pen)


*FUTURE WRITERS ASSOCIATION*

*(FUWA)=Ø‹Ýþ=ØÚÜ*

*The Fearless Writers Team*

_Marubuta masu tsage gaskiyya_

*BISMILLAHI RAHAMANIN RAHIM =ØOÞ=Ø«Ü*

_Page 10_

Rufe idonshi yayi da ™arfi tare da ri™e ™irjinsa, dai-dai lokacin da tayi sallama ta shigo falon, da sauri ya bud e manyan idanunsa yana sauke su akanta.

Momi ta mike tsaye tana murmushi ta amsa sallaman tare da cewa. Daughter k araso mana.

Murmushi tayi tana shigowa cikin falon, har yanzu idanunsa na kanta ya gagara daukewa.

Har k asa ta durkusa tana fadin. Momi ina kwana?.

Lafiya Daughter ya gida? Kin zo lafiya? Tashi ki zauna a sama. Momi ta fad a tana murmushi.

Da lafiya ta amsa tana zama a kan kujeran kafin ta kalli Anas ta furta. Ina kwana?.

Washe mata baki yayi yana cewa. Lafiya kalau Bhatool ya Makaranta? Yasu Mama da kowa da kowa an same ku lafiya? Ya&

Hararan da Senate ya masa ne yasa yayi dif bai ce komai ba sai dariyar da yake yi ™asa-™asa, kallon Senate din tayi ta ce. Yaya ina kwana?.

Sanyayyen murmushin nan nasa ya yi ya ce. Lafiya. Yana komawa ya zauna yana facing nata.

Momi ce ta nufi fridge ta dauko mata ruwa da juice ta ajiye a gabanta tana fadin. Daughter ki sha ruwa ko.

Murmushi tayi bata ce komai ba, Senate sai murmushi yake yi kamar wanda ya zauce, kafin ya ce. Bhatool ruwan gidanmu ne bazaki sha ba?.

Da sauri ta kalle shi dan batayi tunanin zai sake yin magana ba har taji zazzakar muryansa mai kwantar mata da hankali, wani sanyi taji a zuciyarta kafin ta ce. A koshe fa nake.

Haba daughter dan ban dibo miki abinci bama ko?. Cewan Momi tana bata fuska.

Momi Wallahi na koshi yanzu nasha ruwa, dama Yaya Karima ce tace nazo za ki ban sako. Ta karashe suna hada ido da Senate.

Ok to ina zuwa bari na dauko miki. Cewan Momi ta nufi dakinta.

Tashi Senate yayi ya dawo gujeran da take kai yana fadin. Za ki dade a nan ko?.

Eh nazo taya Yaya karima zama ne bata da lafiya.

Hannunsa ya saka a cikin sumarsa yana shafawa kafin ya kalli Anas ta gefen ido yana sakar masa murmushi, girgiza kai kawai Anas yayi bai ce komai ba.

Momi ce ta dawo hannunta dauke da bakin leda, mikawa Bhatool tayi tare da fadin. Gashi nan Daughter.

Karba tayi tana mai tashi tare da cewa. Momi sai anjima.

To Daughter ki gaishe da Karima.

Da sauri Senate ya mike yana mara mata baya da fadin. Momi bari na taka mata zuwa gidan. Ya fita da sauri dan ya isa gurinta.

Momi ta dubi Anas tana fadin. Naga Senate ya canja ne lokaci kadan, daga yanayin maganar zaka gane yana magana tamkar zaki, ina nufin muryansa da kausashi. Momi ta karashe da dan mamaki, dan Senate idan zai yi magana duk a cikin sanyi yake sai dai daga dazu ya canja ya zama cikekken na miji, amon muryansa ma ya isa ya sa jikin mutum ya dau rawa.

Anas ya ce. Momi kila dan ya fara soyayya ne ya chanzu.

Maybe. Kafin ta nufi kitchen.

Bayan ya iso inda take suka jera suna tafiya, fuskarta dauke da murmushi haka ma nasa, kamar ba zaiyi magana ba kuma sai ya ce. Bhatool. Ya kira sunan a wani irin voice.

Ji tayi babu wanda ya kai shi iya kiran sunan ta, a wani irin yanayi ta kalle shi ta furta. Na am Senate.

Tsayawa cak suka yi babu wanda ya motsa, kafin ya ce. Kina da wanda kike so ne?.

Girgiza kai tayi, wani naunauyar ajiyar zuciya ya sauke kafin ya saki murmushi ya ce. Muje ko. Suka cigaba da tafiya babu wanda ya cewa wani kala.

A bakin get ya tsaya ta shiga, ganin ya tsaya yasa ta ce. Ka shigo ku gaisa da Yaya mana.

Girgiza mata kai yayi ya ce. A a yanzu kunyar ta nakeji, akwai lokacin da zan shigo har mu gaisa muyi hira da ita.

Ok nagode ka gaishe min da Momi. Ta fada tana masa bye bye ta shiga falon.

Har sai da ta bace kafin ya sauke numfashi yana furzar da iska ya ce. Yau na mata magana, yesss God kasa kar tayi wani saurayi har ta gane inason ta. Ya fada yana tsalle da murmushi kafin ya koma gida.

Tana shiga falon ta fara ihu wanda ya tsorata Yaya Karima ta fito da gudu daga kitchen.

Wallahi sona yake, yess na kamu da soyayyar Kyakkyawan saurayi fari ajin farko irin na fita cikin kawaye da shi, na kece raini.

Cike da haushi Yaya Karima ta ce. Shi ne zaki shigo da ihu?.

What the fuck, Yaya Karima ki barni kawai. Ta fada tana fadawa akan three seater ta lumshe ido.

Filo Yaya Karima ta dauka tana buga mata, da sauri ta tashi tana dariya ta nufi dakin da ta sauka ta ce. Sai hakuri idan zaki iya, kisan wanda ya fada soyayya baya jin shawara.

Yana komawa gida ya shigo falon da gudu yazo ya rungume Momi.

Babana Lafiya? What s wrong?.

Momi babu wanda ya kai ki sona a duniya, ina kaunar ki Momi.

Dariya Anas yayi yana ciro waya ya fara musu video yana fadin. Cigaba mana da maganar, irin yau kaga bugun zuciyarka, ai har yaran ku sai sun ga video nan In Sha Allah.

Turo baki gaba Senate yayi yana hade fuska ya nuna Anas yana kallon Momi ya ce. Momi ki ce ya daina bana so.

Anas ka daina baya so. Cewan Momi tana dariya.

Ke ma dariya kike min Momi?.

A a kuka nake.

Juyawa yayi ya tafi dakinsa yana guna-guni kamar yaro karami.

*Bhatool*

Tun bayan da ta shiga dakinta bacci ya dauke ta, sai kusan mangarib ta fito tana bata fuska.

Yaya Karima ce da Barrister a falon yaran sun tafi wasa, kallon ta Barrister yayi yana cewa. Yar dakina nazo kina bacci.

Sakin fuska ta yi tana cewa. Uncle ina wuni?.

Lafiya ya gajiya.

Alhamdulillah.

Tashi yayi yana cewa. Ni kam na wuce masallaci kar na makara.

A dawo lafiya. Yaya Karima ta fada tana masa murmushi, da haka ya fice.

Duban Yaya Karima tayi tana yamutse fuska ta ce. Yaya abinci.

Ni zan kawo miki kenan?.

Ni bance haka ba, naga bakon ka Annabin ka.

Da mamaki Yaya Karima ta ce. Ke ce bakuwar kenan?.

Eh mana.
Chapter 9 · 0% Book details