Sashe 44
Hasashen Soyayya Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Sayyid Legendspen
Amanar-Janafty
Shafi na Hamsin (50)
Bhatool ta juyo da sauri. Ganin Senate tsaye a bakin kofa, sanye da riga mai launin toka, fuskarsa ta canja kala, ya sanya ta jin wani irin shock. Ta mike tsaye da kyar saboda nauyin jikinta, ta rike gefen kujera.
Senate bai sake kallon Ahmad ba, idanunsa duka suna kan Bhatool, musamman ma yadda ya ga cikinta ya girma sosai. Wani irin tausayi da bakin ciki suka hadar masa.
"Bhatool... me kike yi haka?" Senate ya fada cikin muryar dake nuna tsananin rauni da bacin rai. "Dama ashe tun kafin iddarki ta kare kin riga kin maye gurbina da wanda kike so?"
Ahmad ya matso kusa da shi ya fara magana. "Haba Senate."
Senate ya daka masa tsawa. "Karka kuskura ka sanya baki a tsakanina da matata! Ko ka manta har yanzu akwai igiyar aure a kanta?"
Bhatool ta ja numfashi, ta share hawayen da ya fara zubo mata. Ta kalli Senate, sannan ta ce "Senate, ka kira ni 'munafuka', ka kira ni 'muguwa', sannan ka sake ni ta waya. Me kake nema a nan yanzu? Mutumin da kake gani, shi ne ya share mini hawaye lokacin da kake Abuja kana jin dadinka. Don haka, don Allah ka fita mana daga gida!"
Senate ya yi turus, kalaman Bhatool sun dake shi kamar saukar aradu. Falon ya rikice da wani irin yanayi mai nauyi. Senate ya dubi Ahmad, idanunsa sun yi jajur, jijiyoyin kansa sun fito radau saboda tsananin kishi da raWadi. Bai sake cewa uffan ba, ya dam™i wuyan rigar Ahmad da ™arfi, yana huci tamkar zaki.
"Dama ashe jira kake saSani ya shiga tsakani ka bayyana kanka? Kai na laSe kana kunno masifa daga gefe domin rugujewar gidana?" Muryar Senate ta fito a shake.
Ahmad bai yi yunkurin ramawa ba, sai dai ya ri™e hannun Senate yana ™o™arin kwatar kansa.
"Senate, ka yi bincike kafin ka yi hukunci. Karka ™ara kuskure a kan wanda ka riga ka yi..."
Kafin Ahmad ya ™arasa, Bhatool ta ™wala wani uban ihu wanda ya sanya Senate sakin rigar Ahmad ba tare da ya sani ba. Ta matso tsakiya, duk da nauyin cikin dake jikinta, ta tsaya tana kallon Senate ido cikin ido babu sauran ™auna a cikinsu, sai dai tsantsar tsana da jin haushi.
"Ya isa haka Usman!" Ta kira sunansa na yanka, wanda hakan ya fi kowane mari zafi a wurinsa.
"Karka kuskura ka taSa shi. Shi ba irinka ba ne. Shi mutum ne mai daraja, mutumin da ya tsaya mini a lokacin da mijina ya gudu ya bar ni. Mutumin da ya yarda da ni a lokacin da kai kake kirana da karuwa kuma kake watsar da ni!"
Senate ya ja baya, ya dafe ™irjinsa, ya ji kamar an soka masa wu™a a zuciya. "Bhatool... kina nufin yanzu Ahmad kike so? Bayan dukkan soyayyar da muka yi? Bayan kwanakin da muka shafe na so da ™aunar juna eyee Bhatool?"
Bhatool ta saki wani murmushi na takaici, hawaye ya wanke mata fuska. "Soyayya? Soyayyar da ba ta da amana ai ba soyayya ba ce, guba ce. Tabbas, ina son Ahmad. Ina son shi fiye da yadda na taSa tunanin zan iya son wani namiji. Domin shi ya gani, ya sani, kuma ya tabbata ni mace ce ta gari. Kai kuma Usman, ka riga ka mutu a zuciyata. Ka tafi Abuja ka ci gaba da rayuwarka, ka bar ni in haifi Wana a cikin natsuwa tare da mutumin da zai zama uba na gari a gare shi."
Wani irin sanyi ne ya ratsa ko'ina a jikin Senate. Ya kalli Bhatool, ya kalli cikin dake jikinta, ya tuna ranar da suka ji labarin samun cikin nan ranar da suka rungume juna suna murna. Yanzu kuma ga shi, ita ce take gaya masa cewa wani namijin ne zai zama uba ga Wansa.
Senate ya dur™usa a ™asa a tsakiyar falon, ya rufe fuskarsa da hannu biyu, ya fashe da wani irin kuka mai ban tausayi, kukan irin na mijin da ya gane kuskurensa a ™urarren lokaci. Sautin kukan nasa yana fita a shake, yana nuna tsananin nadama.
"Bhatool... don Allah karki yi mini haka. Na yarda na yi kuskure, na yarda makirci aka yi mini... amma don Allah karki ce kin daina sona." Ya faWa cikin muryar kuka, yana sheshshe™a kamar ™aramin yaro.
Bhatool ta kauda kanta, ta nuna masa hanyar waje da hannunta dake rawa. "Ka tafi Usman. Karka sake dawowa gidan nan. Ba na son ganinka, ba na son jin muryarka. Ka rabu dani, nima kuma na rabu da kai."
Ahmad ya matso ya taSa kafaWar Senate cikin tausayawa, amma Senate ya harzu™a ya ture hannunsa, ya mi™e da ™yar. Ya kalli Bhatool a karo na ™arshe, fuskarsa ta jike da hawaye, sannan ya juya ya fice daga falon yana layi kamar mashayi.
Yana fita waje, bai tsaya ko'ina ba sai cikin motarsa. Ya kife kansa a kan sitiyarin motar, ya ci gaba da kukan da ya kusa raba shi da numfashinsa. "Na rasa Bhatool na har abada saboda wautata."
Kukan da yake yi ya toshe masa ma™ogwaro, ganinsa ma ya fara dishi dishi saboda hawaye da kuma wani irin jiri dake Wibansa, ya kifa kansa a kan sitiyari, numfashinsa yana fita da ™yar. Bai san tsawon lokacin da ya Wauka a haka ba, kafin ya tada motar ya nufi gida.
A can falon kuwa, Bhatool ta koma kan kujera ta zauna, ta ci gaba da kukan da ya fi na Wazu ciwo. Ahmad yana tsaye a kusa da ita, ya rasa abin da zai ce mata, sai dai tausayinta da yake ji yana sake ratsa shi. Daidai wannan lokacin ne Umma ta shigo gidan, ta iske falon a hargitse, ga kukan Bhatool yana tashi.
Umma ta tsaya cak, tana kallon Bhatool sannan ta kalli Ahmad. "Lafiya? Me yake faru a gidan nan?" Umma ta tambaya cikin muryar firgici da damuwa.
Ahmad ya sauke numfashi, ya gyara tsaiwarsa. "Umma, tsohon mijin Bhatool ne yazo. Ya iske mu muna hira, shine ya tada hankalinsa har aka samu saSani."
Umma ta zaro ido, ta kalli Bhatool dake faman kuka. "Senate? Me ya dawo da shi kuma?" Ahmad bai iya ™ara cewa uffan ba, ya ga yanayin ya canja. Ya kalli Bhatool cikin tausayi, sannan ya kalli Umma. "Umma, bari na tafi. Zan dawo an jima mu gaisa."
Bayan ficewar Ahmad, Umma ta ™arasa kusa da Bhatool ta zauna a gefenta, ta fara shafa bayanta cikin lallashi. "Kiyi shiru Bhatool. Ya isa haka nan."
*****
A can gidan Mom kuwa, Senate yana shiga gidan, bai ko bi ta kan kowa ba ya nufi falon sama. Mom tana ganinsa ta mi™e tsaye saboda yanayin da ta gani a tare da shi. "Senate? Lafiyarka?"
Senate bai iya ba ta amsa ba, sai wani irin nishi mai nauyi da yake yi. Ya dafe ™irjinsa, ya kalli Mom da idanuwan da suka canja launi zuwa jawur, sannan kafin ya ce komai, idanunsa suka rine, ya tafi luuu ya faWi a ™asa tim!
Wani irin uban ihu Mom ta saki dake nuna tsantsar firgici. "Usman! Senate!" A guje ma'aikatan gidan suka shigo. Ganin Senate a ™asa shame-shame ya sa kowa ya rasa natsuwa. Cikin gaggawa aka Wauke shi aka sanya shi a mota, aka nufi asibiti da shi, Mom tana kuka tana kiran sunansa.
****
A gidan Umma, falon ya yi tsit bayan Bhatool ta Wan lafa daga kukan da take yi. Umma ta kalli Wiyarta, sannan ta gyara zama, fuskarta Wauke da wani irin yanayi na nazari.
"Bhatool, tashi ki wanke fuskarki ki zo mu zauna. Akwai maganar da nake son mu yi, magana mai muhimmanci," Umma ta faWa cikin muryar dake nuna cewa ba wasa take ba.
Bhatool ta tashi ta je ta wanke fuskarta, ta dawo ta zauna a ™asa gaban Umma. Umma ta nisa, sannan ta ce, "Bhatool, na ga abin da yake faruwa tsakaninki da Ahmad. Ina so ki sani, ni mahaifiyarki ce, kuma ba zan taSa so miki abin da zai cutar da ke ba. Amma akwai abubuwan da ya kamata mu fuskance su da hankali, ba da fushi ba."
Bhatool ta Wago kai tana kallon mahaifiyarta, tana jiran jin abin da Umma za ta ce.
Legendspen
08129553971
HASASHEN SOYAYYA (BOOK 2)
By
Sayyid Legendspen
Amanar-Janafty
Shafi na Hamsin da Waya
(51)
Umma ta ja numfashi mai nauyi, ta kura wa Bhatool idanu cikin tausayawa. Ta mika hannu ta kamo hannun Wiyarta, ta ji shi a sanyaye.
"Bhatool, na san raWadin da kike ji a zuciyarki. Na san yadda kike jin tamkar an ci amanarki, amma ina so ki buWe kunnenki ki ji maganar nan da zan gaya miki a matsayina na mahaifiyarki, kuma uwar da take tsoron miki fushin Allah."
Bhatool ta sunkuyar da kanta ™asa, muryarta a shake ta ce, "Ina jinki Umma."
"Bhatool," Umma ta kira sunanta cikin muryar lallashi. "Allah (S.W.T) Ya tsara mana rayuwa da dokoki a cikin Alkur'ani. Kina sanye da iddar Senate ne a yanzu tunda kina da juna biyu. Addini ya haramta miki sauraren wani namiji ko yin soyayya da shi a wannan lokacin. Allah Ya ce a cikin Suratul Baqarah: 'Kuma kada ku ™ulla ™udurin ™ulla auren a cikin zuciyarku har sai idda ta ™are.' Wannan yana nufin koda a zuciya ne, bai kamata ki sanya soyayyar wani ba har sai kin sauke abin da yake cikinki."
Umma ta ci gaba da bayani, "Annabi (S.A.W) ya yi hani akan mace ta dinga tattaunawa ta soyayya da wani namiji alhali tana cikin iddar wani.
Ahmad mutumin kirki ne, ya tsaya miki, amma duk abin da kuke yi yanzu kuskure ne a addini. Idan kika bari soyayya ta shiga tsakaninku a yanzu, kuna sanya wa rayuwar ku sharri ne kuma kun cire k albarka."
Jikin Bhatool ya yi wani irin sanyi ™alau. Ta ji kalaman Umma suna ratsa kowace jijiyar jikinta. Tabbas, fushin da take yi da Senate ya rufe mata idanu har ta manta da wasu iyakoki na Ubangiji.