← Book details Hasashen Soyayya Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 47 OF 51

Sashe 47

Hasashen Soyayya Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Yana shiga motarsa, ya dafe sitiyari. "Bhatool ba rabona ba ce," ya faWa a cikin ransa cikin murya mai cike da sadaukarwa. "Idan har mayar da aurenta shi ne zai ba ta natsuwa kuma ya ceci rayuwar Senate, to na ha™ura. Allah Ya ba su zaman lafiya, Allah Ya sanya hakan shi ne mafi alheri a gare ta."

Ahmad ya tada motarsa ya bar asibitin, ya bar zuciyarsa a can, ya tafi da wani babban nauyi aransa, shin nadama ce ko kishine shi dai yakasa  cewa komai, yasan dai ya yi jarumta ta ™arshe.

A cikin motar Dad kuwa, Bhatool tana kuka a jikin Umma har suka isa gida. tana isa gida, ta fada kan gado tana wani irin kuka mai cin zuciya. Kowane sassa na jikinta rawa yake yi saboda fushi da radadin kalaman Senate. Abdul ya shigo dakin, ya zauna a gefen gadon yana kallon kanwarsa cikin tsananin tausayi. Ya sa hannu ya dafa kafadar ta, muryarsa a sanyaye ya ce.

"Bhatool, kiyi shiru haka nan. Na san abin da kike ji, kuma na san yadda zuciyarki take tafasa. Amma ina so ki kwantar da hankalinki, na miki alkawari, muddin wannan auren zai zama silar damuwarki, zan tsaya miki da kaina wajen neman saki a wurin Senate. Ba zan bar ki a inda ba kya so ba, kiyi hakuri ko don abin da yake jikinki."

Jin kalaman Abdul ya sanya Bhatool jin wani dan sanyi, ta dan rage kukan amma har yanzu hawaye ba su daina zuba ba.

A can asibiti kuwa, bayan ficewar su Bhatool, Senate ya fara farkawa a hankali. Na'urorin dake jikinsa sun nuna cewa bugun zuciyarsa ya fara daidaita. Ya bude idanunsa, wannan karon babu dishi-dishi. Ya kalli Mom dake gefensa, ya yi wani dan gajeren murmushi na rauni. "Mom... ina Bhatool?" Ya tambaya murya can kasa.

Likitoci sun tabbatar da cewa kumburin zuciyarsa ya fara raguwa sakamakon ganin Bhatool da ya yi, wanda hakan ya ba shi karsashin rayuwa. Jikinsa ya fara sauki sosai, har aka fara cire masa wasu daga cikin na'urorin dake ma™ale da shi.

Bhatool tana kwance a gida, hannunta rike da waya. Ta kira Ahmad kusan sau goma amma bai daga ba. Zuciyarta tana wani irin bugawa, tana tsoron kar Ahmad ya fahimcita ba dai dai ba. Ta sake tura masa sako fuskarta Wauke da ™walla.

 "Yaya Ahmad, don Allah karka guje ni. Karka yarda da kalaman Senate, kai nake so..."

Ahmad, wanda yake zaune a cikin motarsa a gefen titi, yana kallon wayar tana haske. Hawaye ne ke zuba a idanunsa, amma ya daure ya kudurce wa kansa cewa sadaukarwa ita ce kololuwar soyayya. Ya dauki wayar, ya rubuta mata sako mai ratsa zuciya kamar haka.

"Zuciyata, Bhatool.

Na karbi sakonki, kuma na ji dukkan kukan dake cikin muryarki. Bhatool, soyayya ba wai mallakar masoyi ba ne kawai, soyayya ita ce ganin farin cikin masoyi a inda ya fi dacewa da shi. Senate ya mayar da ke dakinki a daidai lokacin da yake tsakanin mutuwa da rayuwa, hakan ya nuna cewa ke ce numfashinsa. 

Ni kuma, zan zama silar da zan janye domin ki sami natsuwa da danginki da kuma mahaifin abin da yake cikinki. Ba zan iya gina farin cikina a kan rugujewar rayuwar wani ba, musamman mutumin da yake neman yafiyarki a mawuyacin hali. Na yafe miki dukkan alkawarin dake tsakaninmu. Kiyi biyayya ga mijinki, ki raini danki a cikin soyayya. Zan kasance mai taya ki murna daga nesa. Allah Ya bar ku tare, Allah Ya sanya alheri a rayuwarki ta gaba. Salam."

Bhatool tana karanta wannan sako, ta saki wani uban kuka mai taSa zuciya. Ta kankame wayar a kirjinta, tana jin yadda Ahmad ya nuna mata tsantsar karamci da sadaukarwa.

Sakon Ahmad ya sauka a zuciyar Bhatool tamkar ruwan kankara, duk da radadin dake tattare da shi, amma ya sanyaya mata jiki sosai. Ta fahimci cewa Ahmad mutum ne mai daraja wanda ba zai taba zama silar rugujewar gidanta ba. Cikin kuka ta kira Jannah, ta kwashe dukkan abin da ya faru da kuma sakon Ahmad ta fada mata.

Ba a jima ba sai ga Jannah ta bayyana a gidan Umma. Ta zauna kusa da Bhatool, ta fara mata nasiha mai ratsa jiki. "Bhatool, kaddara ta riga ta gifta har wani abu ya faru tskanin ku da  Senate, amma Ahmad ya nuna miki girmansa, mutunci da karamci, kuma ya sauke miki nauyin dake kanki. Yanzu abin da ya rage miki shine kiyi hakuri ki koma ga mijinki, musamman yadda ya nuna nadama a lokacin da yake tsakanin rai da mutuwa."

Bhatool ta ja numfashi, ta goge hawayenta. "Jannah, na hakura. Zan zauna da Senate tunda haka kaddarar take. Amma ina so in nuna masa cewa na yafe masa ne don Allah."

Jannah ta yi murmushi, "To idan har hakan ne, tashi ki shiga kicin ki yi masa girki na musamman, ki kai masa asibiti. Wannan zai nuna masa cewa baki rike shi a zuciya ba, kuma zai kara masa karsashin tashi daga rashin lafiyar."

Legendspen

08129553971

HASASHEN SOYAYYA (BOOK 2)

By

Sayyid Legendspen

Amanar-Janafty

Shafi na Hamsin da biyar.

  (55)

Ahamd jiya ka kona mini rai, na so maka ka aure Bhatool, ka zauna da ita ka rabata da wancan Senate din, amma ka nuna kai ba haka ba, canka yanka.

Bhatool ta amince, ta shiga kicin ta hada wani daddadan girki wanda kowa ya gani yasan ta yi bajinta akansa. Lokacin da ta kai asibiti, kowa ya yi mamaki da murnar ganin Bhatool da abinci a hannunta. Wannan karimcin ya burge Mom, Dad, da dukkan dangin Senate.

Washe gari, garin Yobe ya dauki dumi da shagalin bikin Jannah. Dangi da abokan arziki duk sun hallara. 

A daren Ladies Night da ake yi a gidan Yayar Jannah, falon biki ya cika da mutane yan uwa da kawaye. Bhatool tana zaune a cikin wasu kawayenta, sai ga Amrah ta shigo.

Tana ganin Bhatool, Amrah ta kasa karasawa cikin taron. Ta tsaya daga nesa, idanunta suka cika da kwalla. Bhatool ta lura da ita, ta mike ta karasa wajenta. Amrah ta fashe da kuka, ta kama hannun Bhatool tana neman gafara.

"Bhatool, kiyi hakuri. Na san abin da na yi miki ya wuce misali, amma don Allah ki yafe mini. Zuciyata ba ta ™ara samun natsuwa ba tun ranar da kika bar gidan mijinki."

Bhatool ta tausaya mata, ta kamo hannun Amrah ta ce, "Amrah, komai ya wuce. Na yafe miki duniya da lahira. Allah Ya yafe mana baki daya."

Amrah ta ji wani irin dadi, ta gaya wa Bhatool cewa itama bikin ta ya rage saura sati biyu kacal. Suka gaisa cikin mutunci, abin da ya ba kowa mamaki ganin yadda suka yafe wa juna.

A can gidan Mom kuwa, Senate ya wartsake sosai. Kumburin zuciyarsa ya ragu, kuma likitoci sun ba shi damar komawa gida domin ya ci gaba da hutawa. Yana shiga gidan, ya iske ko'ina an gyara masa.

Zama ya yi a falon kasa, yana kallon hoton Bhatool dake manne a bango. Ya ji wani irin dadi a ransa jin cewa Bhatool ta duba shi har ta yi masa girki, kuma ya ji labarin yadda ta hakura da zama da shi.

"Zan nuna miki soyayya fiye da wadda na nuna miki a baya, Bhatool," Senate ya fada wa kansa, yayin da yake jin karsashin lafiyarsa na dawowa gaba daya.

Bikin Jannah ya ci gaba da ™awata gari Bayan taron Ladies Night da aka yi wanda ya zama silar sasanci tsakanin Bhatool da Amrah, washe gari aka gudanar da gagarumar Walima. Malaman addini mata sun gabatar da wa'azi mai ratsa jiki, inda suka yi bayani a kan ha™uri da zaman takewar aure. Bhatool tana zaune cikin sauran ™awaye, tana sauraren kowane kalma, tana jin tamkar kanta ake yi wa wa'azin. An tashi taro lafiya, kowa ya fito fuska cike da annuri.

Rana ba ta ™arya. Ranar Juma'a aka Waura auren Jannah da abokin Senate a babban masallacin Juma'a. Taron ya cika da manyan mutane, kuma an yi komai cikin tsari da albarka. Senate, duk da cewa bai daWe da fitowa daga asibiti ba, ya halarci Waurin auren, koda yake bai zauna ya sha wahala ba. An gama biki lafiya, amarya ta tare a gidanta na Abuja cikin so da ™auna.

Bayan kwanaki biyu da kammala bikin Jannah, Senate ya fara fitowa waje don ™ara samun natsuwa. Yanzu hankalinsa gaba Waya ya karkata ga neman gafarar Bhatool ta hanyar nuna mata tsantsar soyayya.

A karon farko, Senate ya nufi gidan Umma da yamma. Ya tsaya a ™ofar gida, ya kira wayar Bhatool. Muryarsa a sanyaye ya ce, "Bhatool, ina kofar gida. Don Allah ki ba ni dama ko da na mintuna biyar ne in ganki."

Bhatool ta Wan yi shiru, sannan ta sanya mayafinta ta fito. Ta iske shi jingine da motarsa, ya Wan rame amma kwarjininsa na nan. Ganin Bhatool ya sanya Senate sakin wani murmushi mai sanyi. Bai yi mata maganar baya ba, sai dai ya mi™a mata wata leda mai ™amshi.

"Na kawo miki abubuwan da kike so ne. Na gode da kika amince kika fito," ya faWa cikin girmamawa.

Haka Senate ya dinga zuwa kusan kowace rana. Wani lokacin yakan zauna da Abdul su yi hira, wani lokacin kuma ya samu damar zama da Bhatool na Wan lokaci. Yanzu ya daina nuna isa ko izza, ya koma tamkar wani sabon saurayi dake neman soyayyar budurwa. Wannan sauyin hali na Senate ya fara sanyaya zuciyar Bhatool, duk da cewa har yanzu akwai tabon abin da ya faru a baya.

A haka aka kwashe sati biyu, inda zumunci ya fara dawo wa tsakaninsu. Ahmad ma ya janye gaba Waya kamar yadda ya yi al™awari, wanda hakan ya ba Bhatool damar fuskantar rayuwarta ba tare da rudani ba.

Gari ya sake Waukar wani sabon dumin na bikin Amrah. Tunda amincinsu ya dawo, Bhatool ta tsaya tsayin daka wajen taya Amrah shirye-shiryen bikinta. An yi shagalin biki na gani ta fada, kowa yana mamakin yadda Bhatool ta ci gaba da mutinci da Amrah har ta taya ta abubuwan bikim ta , wanda ya nuna a tsakaninsu akwai wani aminci da zumunci mai ™arfi.
Chapter 47 · 0% Book details