← Book details Hasashen Soyayya Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 51 OF 51

Sashe 51

Hasashen Soyayya Part 1 Complete Hausa Novel · about 6 min read

Jannah da Amrah suna can daga ™ofar gidansu Bhatool, kukan su yana tashi yana ratsa zukatan mutane. Babu wanda bai yi kuka ba a wannan ranar, har wadanda basu san Bhatool ba sun ji radadin mutuwar tata. Haka aka wuce da ita ma™abarta Kowane taku da ake yi, Senate yana jin tamkar ana kara nisa da shi ne daga duniyar farin ciki. Aka tafi da ita cikin kuka da addu'o'i, aka sanya ta a cikin kabarinta.

Lokacin da aka fara zuba kasa, Senate ya kalli Abdul suka yi ido hudu, kowannensu ya juya kansa gefe yana kuka.

An gama jana'iza, mutane suka fara rarrabuwa, amma Senate ya ki tafiya. Ya tsaya a kan kabarin, yana kallon sabuwar kasar da aka zuba. "Bhatool, na yafe miki duniya da lahira. Kuma na karbi amanar 'yarki da kika bar mini. Insha Allah zan rayu ina tuna kowace hira tamu," ya fada cikin murya can kasa.

Wannan rana ta kasance babban bankwana. Kowa ya koma gida da tunani daya "Ina ma ace Senate ya sani tun farko, ina ma ace Anty ba ta shiga tsakaninsu ba." Amma kaddara ta riga fata.

Legendspen

08129553971

HASASHEN SOYAYYA (BOOK 2)

By

Sayyid Legendspen

Amanar-Janafty

Shafi na Sittin (60)

Assalamu alaikum warrahmatullah! Yan uwa masoya ya kuke, ya hakurin rashin Bhatool? Ina mai baku hakuri akan hakan, nima ba wai nayi da Niya ba ne tsarin labarin ne a haka, kuma dama babu wamda yake dauwamme kowa Wan haka ne ya zo ya koma, ya zo ya koma, Allah MaWaukakin Sarki Yana cewa a cikin Littafinsa mai girma

"Kullu nafsin daikatul maut" (Kowannr mai rai WanWanar mutuwa ne).

Haka nan, Manzon Allah (S.A.W) ya koya mana cewa mu kasance a duniya kamar ba™i& . Rasuwar Bhatool a cikin wannan labari, ba wai ™eta ba ce ga masoyanta, face ishara ce gare mu duka cewa rayuwa baki Waya mai ™arewa ce, kuma duk abin da yake da mafari, tabbas yana da ™arshe.

Ina godiya da yadda kuka nuna damuwarku, hakan yana nuna yadda Bhatool ta shiga rayuwarku. Amma ina so ku sani, wani lokacin mutuwa ita ce take ba wa labari ma ana ta har abada.

Ku ci gaba da kasancewa da ni don jin yadda zamu ™arashe labarin. 

Naku,

Sayyid Legendspen (Amanar Janafty)

Bayan rasuwar Bhatool, rayuwa ta ci gaba cikin wani irin yanayi na jimami. Jaririyar da aka bari, wadda kowa ya shaida kyakkyawar kamanninta da mahaifiyarta, aka sanya mata suna Bhatool. Yaya Karima ce ta Wauki nauyin shayar da ita da kulawa da ita tamkar ita ta haife ta. Bayan an yaye Little Bhatool, sai ta koma gidan Ahmad da amaryarsa, inda suka ri™e ta cikin tsantsar gata da ™auna.

A gefe guda, ganin yadda zama ya kasance ga Umma mahaifiyar Bhatool da kuma yadda zumunci ya ™ara ™arfi, Mom ta dage wa Dad a kan lallai ya aure Umma. Bayan dogon nazari da tattaunawa, aka Waura auren Dad da Umma, wanda hakan ya sa dukkan iyalan suka koma gida Waya. Little Bhatool ta zama ´ar kowa; tana hutu a gidan su Mom, tana zama wajen Ahmad, amma zuciyarta gaba Waya tana wajen mutum Waya ne Mahaifinta.

Senate ya canza gaba Waya. Tun ranar da aka rufe Bhatool, Senate ya daina dariya, ya daina yawan magana, ya kuma janye jikinsa daga dukkan wata mu'amala ta duniya. Furfura ta fara fito masa a suma da gemu, amma bai taSa tunanin ™ara aure ba; ya ce Bhatool Waya ce a rayuwarsa, kuma ya riga ya kai ta makwancinta. Idan ka ga Senate yana hira, ko yana murmushi, to tabbas yana tare da Little Bhatool ne, wadda yake kira da "Little." Soyayyar dake tsakaninsu ta zarce tunanin mai tunani; tana son mahaifinta fiye da komai, shi ma kuma ita ce rayuwarsa.

SHEKARU GOMA SHA BIYU BAYAN HAKAN

"My mother died to give me life, and my father lived to give me love," Kyakyawar yarinya yar shekara goma sha hudu dake zaune a kan babban stage a babban Wakin taro na alfarma dake ™asar Amurka (USA), hasken lantarki ya mamaye ko'ina. Taron na musamman ne inda aka gayyato yara daga sassa daban-daban na duniya don su ba da labarai masu taSa zuciya (Inspirational Stories) yarinyar sanye take da doguwar riga ta alfarma, kamarta Waya da marigayiya Bhatool, idanunsu, hancinsu, har zuwa murmushinsu, babu abin da ya bambanta.

Cikin natsuwa da harshen Turanci mai sau™i da daWin saurare take magana.Hannunta ri™e da babban littafi mai suna The Journey of Bhatool Senate. Wanda mahaifinta ya Wauki tsahon shekaru yana rubutawa.

A cikin taron, a sahun gaba, ga Mom da Dad suna kuka. Umma da Yaya Karima suna share hawaye. Abdul yana zaune da matarsa da yaransu biyu (namiji Waya da mace Waya mai suna Bhatool). Ahmad ma yana nan da matarsa da ´arsa mai suna Bhatool. Hatta Jannah da mijinta sun kasa ri™e hawayen su.

A tsakiyar su, ga Senate zaune. Ya tsufa kaWan, furfura ta bayyana sosai a fuskar sa, amma kwarjininsa na nan. Yana kallon ´arsa a kan stage, hawaye na zuba a fuskarsa. Yana jin tamkar Bhatool Winsa ce take tsaye a wurin take yi masa magana.

Lokacin da Little Bhatool ta kammala labarin ta hanyar cewa, "My mother died to give me life, and my father lived to give me love," dukkan mutanen dakin taron suka mi™e tsaye suna tafi, yayin da kuka ya sar™e kowa.

Senate ya mi™e ya nufi kan stage Win. Yarinyar ta rugo ta faWa jikinsa, ya rungume ta tsam yana kuka. A daidai wannan lokacin, ya Waga kansa sama ya kalli silin Win Wakin, yana jin tamkar yana hango murmushin Bhatool.

"Mun gode Allah, Bhatool. Ga amanarki nan ta zama tauraruwa," ya faWa a cikin ransa.

Ni wallahi Allah sai an siya mini. Ta faWa tana burgima a ™asa. Tare da fara kuka. Mama kin mutu kin barni, kin bawa Wan uwanki amana ta amma yakasa cikawa. Little Bhatool ta faWa tana kuka, shi kam Abdul da ido yake kallonta, yana tuna yadda Bhatool take kuka tana kiran Mahaifinsu da ya rasu. Oh Allah! Bhatool ga abinda kika barmin nan. Ya faWa yana murmushi. 

ALHAMDULILLAH!

Tsokaci. 

Daidai da lokaci Waya Little ba ta bar komai na halin mahaifiyarta ba, duk ta kwashe su tana kuma yinsu, haka Abdul da Yaya Karima zasu sa ta a gaba su yi ta kallonta suna jjn dadin abinda take yi. 

Senate ya rasa Bhatool, amma tabbas ba ta tafi duka ba, domin ta bar masa little da take masa dukkam soyayyar da Bhatool take masa, girki, ruwan wanka, taje masa kai, fesa masa turare, har da zaSar masa kayan da zai sa, indai Little na nan ita ce zata yi masa. Yana jin kamar bai rasa Bhatool ba. 

Mom da Umma zama suke cikin so da mutunta juna, Dad yana ™o™ari wajen yin adalci a zamansu, amma soyayyar da yake yi wa Umma ta ninka wacca ya yi mata a baya. 

Amrah da Jannah da Suhaima suna rayuwa da rashin Bhatool, amma suna jin Little a ransu kamar su ne suka haife ta, ita ma tana ganinsu kamar sune suka haifeta. 

Haka gidan Ahmad Little ta dauke shi kamae gidansu, idan tana jin rigimarta har nan take zuwa tai ta bori.

Yaya Karima ce Uwar little, nan ta taso ta girma ta yi yawo, baka gane banbanci tsakaninta da ya yan Yaya Karima sai ma babban Wan Yaya Karima da ya ke son ta, ita ma take son sa, amma Senate ya™e™ashe ™asa ya ce, Little Bhatool Winshi yarinya ce ba yanzu za ta yi aure ba.

Daidai da rana Waya Senate bai taSa jin sake son wata mace ba, haka babu wanda ya takura masa akan hakan. 

ALHAMDULILLAH!

Wanan shine ™arshen a labarin Bhatool da Senate, kuskuren da cike ubangiji ya yafe mana, alherin dake ciki ubangiji ya bamu lada baki Waya. 

Na gode da bibiyar ku tun daga farko.

Mu haWu a labrin mu na gaba Sartse. 

Legendspen

08129553971
Chapter 51 · 0% Book details