← Book details Hasashen Soyayya Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 24 OF 51

Sashe 24

Hasashen Soyayya Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Kizo ki kawo abincin nan kafin na sumar dake, mara tarbiya. Šan-ladi da Iliyasu suka haWa baki suka faWa. Idan da kuWin ku a ciki sai ku ci. Ta faWa dai-dai lokacin da ta fice, bata ™arasa fita ba taga almajirai waje ta juye musu, kuma gaba daya gidan babu komai sai tuwo, an basu shinkafa sun cinye sunci basu ™oshi ba kuma ba za su ci tuwo ba, shine aka dafa musu taliya leda biyar, taji kayan haWi ko gama zuba ta cikin faranti basuyi ba. Umma ce ta fito daga Waki tana cewa. Ungo sha na maganinki. Dai-dai lokacin Bhatool ta shigo da kula babu komai ciki. Bhatool mene haka?. Ummah ta faWa. Amma anyi tsinanniyar yarinya a duniya, yanzu kin zubar da abincin?. Goggo larai ta faWa. Ai sai kunga jami an tsaro zaku tabbatar da tsinanniya nake.  

Wai Bhatool mene haka, me kike aikata?. Umma ta yi mata wanan tambayar. Umma su ta shi subar gidannan, tun da su harkar arzi™i bata kawo su waje.

Gidanku Bhatool, ina kika kai abincin?.  

Na bawa almajirai.   Salati suka saki baki Waya, Goggo larai ta fashe da ihu tare da faWin. har abada bazan manta da wanan cutar da kika mun ba, wanan taliya ta ji jar miyar, taji nama, ta me star amma kika bayar, Allah wadaranki. Su sauran ma ba su iya magana ba sabida mamki da alhini. Bhatool fita ki bar gidannan. Umma ta faWa dai-dai lokacin kuma wayarta ta fara ringi, sunan Senate ne hakan yasa ta fice zuwa mota. 

Ba wata doguwar tafiya suka yi na zuwa wajen bikin, lokacin kowa ya iso wajen ya shiga shida abokansa, cikin wami irin salo wanda yadauka hankali, ya karaWe mediya domin abokansa sun yi watsin dala, sun yi watsin nera. 

˜awayen Amarya ne a gaba, bayan yan taku sai kuma Amarya tare Yaya Karima da Abdul sun ri™e mata hannu, Mc ta yi gyaran murya ta fara maganaa. 

Legendspen 08129553971

*HASASHEN SOYAYYA*d'þ
=Ø%Ý>ØyÝ

_Imagination of love_

    _Stroy and written_

             By

   Sayyid (Legend's pen)


   *FUTURE WRITERS ASSOCIATION*

*(FUWA)=Ø‹Ýþ=ØÚÜ*

    *The Fearless Writers Team*

  _Marubuta masu tsage gaskiyya_

*BISMILLAHI RAHAMANIN RAHIM =ØOÞ=Ø«Ü*

_Page 28_

Zinariyar tana tafe a baya cikin ™asaita, cikin isahhhhh a tare da yan uwanta. 

Ga aji& .. ga ilimi.

Ga isa da kwalliya kaman wata Wawisu.

Ga nasaba& & . Duk a gurin Senate Winan ke kaWai gayya.

Kin kira taro an amsa, kin tara gari, garin ya haWu gaba Waya. 

Amasu kyawu ita Win mai kyawu ce ajin farko.

Irin kyan da zaka ji masana na bada labarin guda Waya akeyi a nahiya. 

Kyawunta ya kai kyawun da mutum zai bada labari, ya doki ™irji ya ce ga mai kyawu ta iso. 

Murmushinta kaWai abun ka kalla ka ™ara kallo ne. 

Murmushin da yake sanyaya zuciyar dukkan wani masoyi. 

Murmushi da ko a hanya idan ka kalli murmushin nan sai ka ce wayyo Allah kalon Senate bai isheni haka ba. 

A kyawu keWin za a bada labarin kina sa kyawu. 

A aminci, amintaciyace a cikin bayi. 

Muna ™arai muku lale, muna ™arai muku marhabun, muna ™arai muku sallama Assalamu alaikum, warahmatullahi ta ala wabarakatuhum.

Yau kuma da wanan kirarin Bhatool ta ™arasa mazauninta, Masu hoto da bidiyo sun cika wajen kamar za ayi daukan film, banda manyan wayoyi da suke ta shi wajen, daga Sari daya adon da ™awayen Mom su ka yi yau, ya ninka na jiya dau dari dan kamar anyi musi gorin gwala-gwalai, kowacce fantamawa take da Gwala-gwala da leshi mai tsada. 

Abincin yau har ya fi na jiya, li™in da aka yi yau ma ya fi na jiya, komai ci gaba aka samu.

Sai wajen ™arfe 12:30 na dare aka tashi, kowa ya nufi makwancinsa. 

Washe gari kasancewar bawani babban events ba ne, Amarya ce zata yi da ™awayenta shima Ango zai yi na shi daban da abokansa. Anam gida kuma Mama ta haWa saukar al™ur ani mai girma, haka ma Sangaren Mom ta Wakko manyan malamai suna sauka wasu anam gidansu, wasu kuma can gidan da amarya da ango zasu zauna. 

Duk masifar su Goggo larai ds su Ilyasu sai da suka kwana gidan, abun kunya har da su mazan, sai shago aka nema musu a waje wai sun zauna a ci arzikin dan-uwansu da su, Goggo Larai tun safe take faman zuga Furee da habi, amma sun™i sauraronta sai ma ce mata da sukeyi. Yanzu babu ™yashi babu hassada a tare da mu, kalli yadda mukayi ™iba muka murmure, dan haka mu zama nan yanzu muka fara har karatun boko zamu koma, mu samu gina gobe mai kyau.  

Eyh lallai ne asararru, to ku sani wyaanan iyayen ba™ar zuciyar ba zasu taSa son ku ba. Goggo larai ta faWa musu. Ni kinga tafiyata. Furee ta faWa, habi ma ta ce. Kuna cin arzikinsu kuna musu hassada.  

Haka Goggo larai taita sababi tai ta masifa, kowa kuma ya yi mata banza, har ™anwar Mama autarsu ta ce zata ci mata mutuncin amam sauran suka hanata, wacce ita Bhatool ta gado sak a wajen rashin mutunci, basa shakkar kowa ba sa shayin kowa. 

Yau a S Twinkles zasuyi Ladies night Win nasu, kawayen sun yi ankon ba™i ita kuma ta yi na fari sun bada style mai kyau da daukan hankali, sun yi abu a gayyacin, cike da ilimi da wayewa. ˜arfe tara dai-dai suka ta shi abunsu. 

Washe gari kuma Kamun Ummah, shima Hall Win da suka kama yana cikin manyan hall a garin Yobe, sun yi ™o™ari sosai wajen abinci da tsarin wajen, sanan ™awayen Mom da ita sun samu hallarta, an mutunta sosai sama da yanda suka yi suma, duk da suma sun yi matukar kokari, abokan amgo sun xo amma sai daga baya, Abdul da abokansa ne suka cika wajen kuma suma sun zuba li™i, sai ga ™awayen Bhatool da wata sabuwar al ada wai suma sun siya wankam ango naira miliyan Waya, wajem da ya yi trending sosai a social media, bidiyon ya zaga ko ina tare da burge mutane, wamsa karshe ma abokan angon sai da suka bada sama da kuWin da suka amsa. 

Washe garin kuma suka yi Cockail, anan ne aka zuba biki, ango da abokansa amarya da ™awayenta babu mafaWi, Ashe senate ta™adirin kansa ne, sai yanzu ya sami dama har mamaki yake bawa Bhatool na irin rawar da yake yi a wajen shi da abokansa, itama Bhatool da ™awayenta suka sha rawa abunsu. 

Washe gari yakama ranar ™arshe, Mom za ta yi nata event Win amma na rana uku za a ta shi a huce da amarya gidansu, su yi nasu yini kafin daukan amarya, yau ™awayen amarya basu da anko, kowacce dress Win ta za ta yi, kuma iya ™awayen amrayar ne zasu su ™awaye da yan uwan mama suna gida suna yininsu, wasu ™awayen ma na Bhatool gida zasu. 

Tun takwas suka fita gidan kwalliya, amma ba su suka isa wajen ba sai ™arfe Waya na rana. Yau komai na wajen kamar na sarauta, ga basu da algaita kayan da suka saka, ango har da rawani amaryar da alyabba, kirarin Mc ya da ce da komai na wajen. 

Wanan busar idan ba Saraki ba, ko an busa ta ba za ta hau ba. 

Algaita iya algaita, busar Wan gidan Saraki ango senate, da busar ™asaitaciyar basarakiya zinariya abar adon yan mata. 

Zinariya abun alfaharin kowa ya ri™e. 

Lu u-lu u abun alfahari ba gidan kowa ba.

Takowar da ake a gurinan, da ango ne Senate da Amarya Bhatool, da Anti Fauza matar ministan kuWi, da Anti Shuwa ™awar da ta zama yar uwa, da Momin Amarya momin Ango, Yau Bhatool ta zama zinariyar mata. 

Lu u-lu u abun adon da ba kowa yake taSa gani ba

Lu u-lu u abun adon da kowa sai dai ya gani a addu a. 

Haka kike ko acikin al umma. 

Kainuwa ce dashen Allah. 

Itace kalmar da ake kira kyawu.

Idan aka kalli wasu za ace masu kyawu ne.

Itako idan akace kyau, dukkan wata fassara da ake nema a duniya itace fassarar kyau. 

Bata taSa zama mai kama da model ba.

Domin ita da kanta model ce.

Kuma role model ce. 

Idan katara mace Wari.

Guda hamsin sai tace maka Bhatool nake kwaikwayo.

Dukkan Wabi unta cassain da takwas a cikin Wari.

Dabi une da kowane mahaluki yake cewa yana son irinsu.

A cikin mu amala, ba kowa kake samu mai halinta ba.

Idan ka kallesu a tare ka kwana kana kallo, Bhatool ne da senate. 

Bazaka gaji da kallonsu ba.

A cikin alfarma ta uwa.

Acikim albarka uwa.

A soyayya ta yan uwa.

A karamci irin na uba mahaifi.

A haka suka rayu. 

A haka aka haife su.

Saboda haka dukkan rayuwarsu aminci ne cikin aminci. 

Aminci da muke kara nema a yarda da amincin Allah. 

Daren su Bhatool, masu algaita, sarkin busa, da sauran yan-uwa muce Allah ya kyautata makwancin mahaifin Bhatool. 

Kukam da Bhatool ke ri™ewa ne ya fito, da sauri Senate ya rungumeta, tun lokacin da aka fara ambatar kalamar mahaifi Bhatool ta fara zubar da hawaye, ita shikenan nata ya mutu, da yana raye haka za a dinga faWin sunanshi tana jin daWi, amSa yanzu babu shi, ba ta taSa kuka daga cikin zuciyarta ba tun rashin Abbanta ba sai yau, daga cikin zuciyarta take yin shi, tana matu™ar kaunar abbanta, amma tun tana ™arama ya mutu. 

A hankali senate ke shafa mata bayanta, har tasamu sauki daga kukan da take. Gaba Waya Bhatool ba ta ji daWim event Win ba, mussaman da ta ™ara tunawa yau fa zata bar gidansu, zata bar Umma za ta tafi wani wajen tayi ta rayuwa a can, zama bana kwana daya ba bana biyu ba, ba irin zaman da take yi gidan Yaya Karima ba, ji tai kamar ta kwanta a ™asa ta fashe da kuka taita burgemi a ™asa. 

A haka aka lallaSa aka ™arasa Senate ya dawo da ita, a lokacin gidansu ya cika ma™il, Yaya Karima ce ta tsaya a kanta ta shirya sabida Senate ya sanar da ita kukan da ta yi wajen, daga nan ta kawo mata abinci ta dole ta cusa shi, daga nan ta fito aka dinga gaisawa da yan uwa da iyaye. 
Chapter 24 · 0% Book details