Sashe 45
Hasashen Soyayya Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
"Umma," Bhatool ta kira sunanta da ™yar. "Na gode da kika tunatar da ni. Na yi kuskure, kuma zan janye daga dukkan wata hira ko soyayya da Ahmad har sai na haihu. Amma Umma, ina neman alfarma guda Waya; ranar da na haihu, ina son a Waura mini aure da Ahmad. Ba na son sake komawa rayuwar baya."
Umma ta sauke ajiyar zuciya, ta rungume Wiyarta. "In dai wannan ne, Allah Ya nuna mana ranar lafiya. Amma yanzu, kiyi ha™uri ki fuskanci Ubangijinki."
*****
A can babban asibitin kuma, yanayin ya sauya.
Gaba Waya maaikatan gidansu Senate kowa ka ganshi fuska babu fara a, Mom tana zaune sai kuka take, shi kuma Senate yana ciki, manyan likitoci kusan su biyar suna kansa, kowanne yana ™o™arin ganin numfashinsa bai tsaya ba.
Daga ™arshe, babban likitan ya fito yana goge gumin dake goshinsa. Mom ta ruga wajensa tana kuka. "Doctor, yaya jikin nasa? Don Allah ka gaya mini."
Likitan ya kalli Mom cikin damuwa. "Gaskiya numfashinsa yana neman agajin gaggawa. Zuciyarsa ta kusa bugawa ne sakamakon wani babban abu da ya danne shi lokaci guda. Dole ne mu mayar da shi sashin kulawa na musamman (ICU) a yanzu haka. Kuma muna bu™atar addu'arku, domin sa'o'i ashirin da huWu na gaba sune za su tabbatar da rayuwarsa."
Mom ta saki wani kuka mai ban tausayi, ta zube a ™asa tana kiran "Usman! Usman!". Dad da suke waya da Mom tana fada masa komai liktan ya fito ya ce kar ta kashe, ya runtse idonsa, yana ambaton sunan Allah.
An tura gadon Senate zuwa dakin ICU, fuskar nan tasa dake cike da kwarjini ta yi fari fat, injina ne kawai suke taimaka masa wajen jawo numfashi. Masu aikin gidansu Senate dake waje duk sun zubar da hawaye ganin yadda mai gidansu gashi kwance matacce ko rayayye ba a sani ba.
A gidan Umma kuwa, Bhatool ce ga dauki waya ta kira bayan ta Waga Yaya karima ta ce. Yana ji kin yi wani jugum. Ita kuwa Bhatool tunanin maganganun Umma da kuma yanayin da Senate ya fita daga gidan suna ta yawo a ranta.
Zama ta gyara sannan ta ce . Senate yazo.
"Mene ne ya faru? Da Senate ya zo Win?"
Bhatool ta sauke numfashi, ta kwashe dukkan abin da ya faru ta gaya wa Yaya Karima. Ta gaya mata yadda suka yi faWa da Senate, kalamai masu zafi da ta gaya masa, da kuma yadda ta fito fili ta nuna tana son Ahmad a gabansa. Ta ™ara da gaya mata nasihar da Umma ta yi mata na janye soyayyar Ahmad har sai ta haihu.
Yaya Karima ta yi shiru na wasu mintuna, sannan ta ce, "Bhatool, gaskiya Umma ta faWi gaskiya. Dokar Allah ta fi ™arfin komai .Amma ina so ki sani, kalaman da kika gaya wa Senate a halin da yake ciki na nadama, suna da nauyi sosai. Na san yana da kuskure, amma zuciyar namiji idan ta karye tana da wuyar gyara. Kiyi ha™uri ki fuskanci addu'a yanzu, ki bar maganar Ahmad tukunna har lokacin da Allah zai sauke ki."
Bayan sun jima suna tattaunawa, Yaya Karima ta yi mata sallama ta kashe wayarta, zuciyarta ba daWi.
Tun da suka yi waya, Yaya Karima ta kasa samun natsuwa. Ta sanya mayafinta ta nufi gidan Mom don gaishe ta da kuma jin halin da ake ciki. Tana shiga, ta iske gidan shiru, ma'aikatan gidan suka shaida mata cewa gaba Waya su Mom suna asibiti tun Wazu domin Senate ya yanke jiki ya faWi.
Wani irin uban razana Yaya Karima ta yi. "Asibiti kuma? Me ya faru?" Ba ta tsaya jiran amsa ba, ta kira mijinta Barrister Al-Amin ta gaya masa halin da ake ciki. Shi ma hankalinsa ya tashi, ya zo ya kwashe ta a mota suka nufi asibitin.
Suna isa, suka iske Mom a waje tana kuka, Yaya Karima ta ™arasa wajen Mom tana tambaya. Mom ta nuna mata dakin ICU da hannu, muryarta a shake ta ce, "Usman yana neman mutuwa Karima... zuciyarsa ce take kumbura."
Yaya Karima ta le™a ta gilashin dakin ICU. Ganin Senate kwance, an yi masa rubdugu da wayoyin na'urori, fuskarsa ta yi fari tamkar gawa, ya sanya ta jin wani irin tsoro da firgici. Ta tuna yadda Bhatool ta gaya mata kalaman zafin da ta gaya masa Wazu, sai ta ji jikinta ya yi sanyi.
"Wannan sharrin na Maman Anas ya kai Usman ga rami," Yaya Karima ta faWa a cikin ranta, hawaye yana zubo mata. Ta san cewa idan wani abu ya sami Senate, rayuwar Bhatool ma ba za ta taSa natsuwa ba saboda nauyin nadama.
Legendspen
08129553971
HASASHEN SOYAYYA (BOOK 2)
By
Sayyid Legendspen
Amanar-Janafty
Shafi na Hamsin da biyu
(52)
Bayan dawowar Yaya Karima gida daga asibiti, ta kasa zaune ta kasa tsaye. Tana shiga Waki ta iske mijinta Barrister Al-Amin zaune a gefen gado, shi ma fuskar nan tasa cike da damuwa. Ta zube a kan kujerar dake Wakin, ta rufe fuskarta da hannu biyu.
"Barrister, gaskiya halin da na ga Senate ya kr ciki ya tsoratar da ni. Mutumin da kake gani jiya yana takawa da ™afafunsa, yau gashi kwance numfashinsa ma na inji ne," Yaya Karima ta faWa cikin murya mai rauni.
Barrister Al-Amin ya nisa, ya gyara zamansa. "Karima, lamarin nan akwai nauyi. Kin ga dai kalaman da Bhatool ta gaya masa su ne suka zama sanadiyyar rugujewar lafiyarsa. Gobe ina so ki koma gidan Umma, ki zauna da Bhatool ki sake yi mata nasiha. Ki bayyana mata halin da yake ciki na mutuwa-ko-rayuwa. Ba don lallai ta koma gare shi ba, amma don ta san cewa tana da nauyi a kanta idan wani abu ya same shi."
Haka kuwa aka yi, washe gari tun safe Yaya Karima ta nufi gidan Umma. Ta iske Bhatool zaune tana gyara wasu kayan sanyi na jariri, fuskarta babu alamun damuwar abin da ya faru jiya.
"Bhatool," Yaya Karima ta kira sunanta cikin sanyin murya. "Ina so ki buWe kunnenki ki ji ni. Jiya na je asibiti, na ga Usman. Yana can kwance a ICU, zuciyarsa ta fara kumbura saboda kalaman da kika gaya masa. Likitoci sun ce sa'o'i ashirin da huWu ne kawai aka ba shi na rayuwa idan bai farfaWo ba."
Bhatool ta dakata da abin da take yi, ta Wan yi shiru na wasu da™i™o™i, sannan ta Wago kai ta kalli Yaya Karima sannan ta ce "Yaya Karima, na ji dukkan abin da kika faWa. Kuma ina mishi addu ar Alllah ya bashi lafiya idan zai tashi. Amma ina so ki sani, ni na riga na gama da shafin Senate a rayuwata. Mutuwar sa ko rayuwarsa ba ta gabana dan bazan sake komawa dgareshi ba. Shi ya zaSi ya yarda da ™arya, ni kuma na zaSi in yarda da gaskiyar da Ahmad ya kawo mini."
Yaya Karima ta ji jikinta ya yi sanyi, ta kasa sake cewa uffan ganin yadda Bhatool ta rufe idonta baki Waya.
Bayan ficewar Yaya Karima, Bhatool ta Wauki wayarta ta kira Ahmad. Muryar Ahmad ta fito a sanyaye lokacin da ya Waga. "Bhatool, kina lafiya? Na damu tun jiya ina kiranki ba ta shiga."
Bhatool ta nisa, sannan ta gaya masa nasihar da Umma ta yi mata na su janye maganar soyayya har sai ta haihu don gudun fushin Allah. "Yaya Ahmad, don Allah karka ga laifina. Ina son mu bi dokar Allah ne don aurenmu ya sami albarka."
Ahmad ya yi shiru na Wan lokaci, sannan ya ce cikin muryar ro™o, "Bhatool, na yarda da duk abin da kika faWa, kuma zan bi umarnin Umma. Amma ina ro™onki don Allah, karki guje ni. Kar kice tunda tsohon mijinki ya dawo kuma yana asibiti, hakan zai sa ki fasa aurena. Ba zan iya jure rashinki ba."
Wani irin karsashi Bhatool ta ji ya dawo mata. Ta danne dukkan wani rauni, ta ce, "Yaya Ahmad, karka damu. Na riga na ba ka zuciyata. Ina sake ba ka al™awari, komai rintsi, komai wuya, kuma ko ma mene ne zai faru da kowa, ina tare da kai. Ranar da na haihu, ina jiran ganinka a matsayin mijina."
Ahmad ya sauke numfashi na jin daWi. "Na gode Bhatool. Na gode da kika zaSe ni."
Haka suka kashe wayar, kowanne yana jin daWin amana da al™awarin dake tsakaninsu.
A can dakin ICU na asibitin kwararru, na'urorin dake jikin Senate suka fara bada wani sauti na daban. Likitoci suka taru a kansa cikin hanzari. Senate ya fara motsa yatsunsa, sannan a hankali ya buWe idanunsa dake dishi-dishi. Abin da ya fara fitowa daga busasshen bakinsa shi ne sunan da ya zame masa abincin zuciya.
"Bha... Bhatool... Bha... tool..." Ya faWa muryarsa tana rawa, kafin ya sake lumshe idanunsa ya koma wani dogon bacci sakamakon magungunan da aka ba shi ta hanyar allura da ruwa.
Babban likitan ya fito ya kalli Mom. "Hajiya, muna bu™atar wadda yake kira a kusa da shi. Wacece Bhatool? Domin a yanzu, jin muryarta ko ganin fuskarta shi ne kaWai zai iya sanyaya kumburin zuciyarsa."
Mom ta fashe da kuka, ta rufe fuskarta. "Matarsa ce da ya sake ta a cikin fushi Doctor."
Dad ne ya shigo asibitin a daidai wannan lokacin. Mom ta tare shi cikin kuka ta gaya masa duk abin da likita ya faWa. "Alhaji, don Allah ka taimaka ka je gidansu. Ka yi amfani da damarka tun da Mahaifiyartatana ganin mutuncinka. Idan kai ka je, ba za ta ™i ba. Rayuwar Senate tana cikin haWari, xuwam Bhatool a yanzu a yanzu zai taimaka."
Dad ya yi shiru, ransa bai so zuwa ba saboda kuskuren da Wansa ya yi, amma ganin halin da Senate yake ciki, ya gyada kai ya nufi gidan Umma.
Dad ya isa kofar gidan Umma, zuciyarsa tana wani irin bugun da ya daWe bai ji irinsa ba. Haka ma Umma dake zaune a falo, tana jin fakin Win motarsa, ta ji wani irin faduwar gaba. Kusan mintuna biyar sannan almajiri ya shigo yana faWin. Wai Akwai ba™o a waje. Da™yar Umma ta iya cewa. Ka ce yab shigo.
Tana fitowa ta iske shi tsaye. Idanunsu suka sarke a cikin na juna na wasu da™i™o, wani tsohon so ya ratsa tsakaninsu.