← Book details Hasashen Soyayya Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 34 OF 51

Sashe 34

Hasashen Soyayya Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

"Ki yi shiru Bhatool, zan kira shi gobe ku zo gaba Waya."

"Tom Mom." Ta faWa tana kuka. "Ki daina kukan kin ji zaki koma karatunki kin ji?."

"Na daina Mom." Ta faWa, Mom takashe wayar ita kuma Bhatool ta kwanta.

Washe gari da safe ta tashi ta fara aikinta na gida, tana cikin kicin ya shigo ya ce. "Kishirya zamuje gidan Momi."

"Tom." TafaWa tana kashe gas Win. A mota ta same shi yana jiranta, sai dai suka yi nisa da tafoya sannan ya ce. "Bhatool mene matsalalki?." Da mamaki Bhatool ta kalleshi, a ranta ta na maimaita kalmar Matsalalta. "Shin ni ce mai matsalal?." Ta tambayi a kan ta. "Eyh BhatooW?."

"Babu." Ta faWa ba tare da ta ™ara kallonshi ba, shiru shima ya yi bai ™ara ce ma ta komai ba har suka isa gidan, tun da suka shig gidan Senate ya ji wani irin sanyi a ran shi, a fili ya furta. "Sweet Home Sweet." Ita dai Bhatool ba ta kula shi ba ta shige ciki, Mom na zaune a falo Bhatool ta yi sallama ta shigo, fuskar momi fal da fara'a ta amsa ma ta. "Momi ina kwana?."

"Lafiya kalau daughter." Mom ta amsa dai dai lokacin da Senate ya shigo. "Momina." Ya faWa yana shigowa ciki. "Uhm da bamu da uwar da munyi kuka." Bhatool ta faWa a cikin ranta tana taSe baki. "Ina kwana Mom." Ya faWa yana zama kusa da ita. "Lafiya Kalau."

"Mom yana ga bakya murna da zuwana." Hararshi ta yi sanan ta ce. "Kawai ka hana yarinya komawa makaranta, sabida me?."

"Au shine ta faWa miki?."

"Bazata faWa mun ba?."

"A'a."

"To me yasa ka hana ta?."  Kallon Bhatool ya yi sanan ya ce. "Mom ta faWa miki abinda take mun a gidan, komai tana mun a gutsire, magana a gajrace. "Gashi, zaka ci, sannu da zuwa, zan koma makaranta, Momi Babu girmamawa babu kulawa, babu soyayya." Kallon Bhatool Mom ta yi sanan ta ce. "Me yasa Bhatool?."

"Mom, ko abinci bai fiya ci ba, da ya shigo xai fara haWe rai yana cin magani, idan na ce mai ya yi hakuri sai ya ce wai me na yi?."

"Mom har ni yarinyar nan za ta ce wai daman ba son ta nake ba na aureta."

"Oh Allah, ashe ba zaman daWi kuke yi a gidan ba kenan, to kusani kuna dauke da Ša, Bhatool na da cikinka, ke ma kina Wauke da ciki a jikin idan kuka ci gaba da hauka ku kuka sani." Har cikin zuciyar Bhatool ta ji wani abu, wai tana Wauke da ciki. "Mom did you mean she is pregent."

"Yes, tana Wauke da ciki."

"Kai Alhmadulillah." Senate ya faWa yana kallon Bhatool, fukarsa fes da farin ciki. "Mom ki yi hakuri ta ci gaba da zuwa makarantar."

"Allah Ya yi muku Albarka, ya baku zaman lafiya mai Worewa." Mom ta faWa suka amsa da baki. "Mom zanje gidan Yaya Karima." Bhatool ta faWa. "Okay Bhatool." Tashi ta yi ta fice, Senate ya mi™e zai bi ta Mom ta kama hannunsa ya tsaya, sai da Bhatool ta yi nisa da fita sannan Mom ta ce da Senate. "Kasan wani abu?."

"A'a sai kin faWa." Ya bata amsa yana zama. "Wai Abbanka aure yake son ™arawa."

"Aure Kuma?." Ya tambaya. "Eyh, wai aure." Mom ta ba shi Amsa tana taSe baki. "To shi yanzu wace zata aureshi?."

"Wai wata frist love Win shi ce, daman already ya taSa bani labarinta.  Amma haka ya ce ta mutu, to yanzu ya gano mijinta ya mutu shine yake so ya aureta, yayata uku ma."

"ChaS, Dad ya fiya matsala."

"Kabarshi kawai Allah Ya ba shi sa'a, amma wallahi ya jamun surutun da bazai ™are ba cikin ™awayena, tun da yarinta ba ayi mun kishiya ba, sai yanzu da girmana har na kusa fara ajiye jikoki."

"Gaskiyya Mom bai kyauta ba, amma zan yi magana da shi."

"A'a kar ka fara, kar ma ka nuna mai kasan maganar ka barshi kawai."

"Okay."

Yaya Karima na zaune a Waki ta ji an faWo a kan ta, ba ta kai ga tantance wand aya faWo ba ta ji anfashe da kuka, a firgrcr ta Wago Bhatool tana faWin. "Ke lafiya?." Kuka Bhatool ta ci gaba da yi. "Bhatool bana son iskanci, kawai zaki shigomun babu sallama ki fara kuka."

"Shine baki ™ara zuwa gidana ba, da nice da tuni nazo kamar mara mafaWi har kwana nake yi a gidanki." Dariya Yaya Karima ta yi sannan ta ce. "To bikiga banda lafiya ba, haihuwa ta fa ta kusa."

"Amma ai bai hana ki zuwa unguwa ba."

"To wai ma ke Bhatool me ya fito dake da wannan safiyar?."

"Gidan Momi ya kawo ni."

"Shine kika bar gidan kika tawo nan?."

"To me zan musu, ashe haka auren yake duk wahala, gashi har na sami ciki. Ni bana wani farin ciki wallahi."

"To ai daman a ko da yaushe ana faWa miki aure gaba Wayanshi Wan ha™uri ne, ke ce daman kile wami Hasashen soyayya zalla a gidan mijin, bawai ba a samu ba ne amma tana Wauke da ™alubale kala kala."

"Uhm, to Allah Ya kyauta." Bhatool ta faWa tare da kwantawa a kan kujera. "Yaya soyamun ™wai."

"Ba ki ga banda lafiya ba ne?."

"Nima ai ba lafiyar ce dani ba, ciki gareki ciki gareni." Dariya Yaya Karima ta yi sannan ta ce. "Allah Ya shirye ki Bhatool, bara na sa mai aikin nan ta yi miki."

"Ni kinga Momi ta aikon mu da masu aiki, amma iya share share na ce suna yi sai su tafi, idan Waya ta yi na safe, Wayar ta yi na yamma."

"Eyh hakan ma ya yi, ni dake cikin nawa ya tsufa ai."

"Aini Yaya cikina ya na fitowa zan tafi gida, ko ya yarda ko bai yarda ba."

"Wai ke waya faWa miki a aure ana cewa ko ya yarda ko bai yarda ba."

"Ni dai tashi kika soyamun, Wan cikina yunwa yake ji." Bhatool ta faWa tana danna wayarta, ta shi Yaya karima ta yi fa shiga kicin, ta lallaSa ta soya mata ™wan, tana addu'ar Allah Ya kawo Senate yazo ya kwashe ta su tafi. Bhatool kam na gama cin ™wan ta mi™e ta kwanta, ba ita ta tashi ba sai azhar, lokacin zuwa Senate biyu, amma ganin tana bacci sai ya ce abarta. "Yaya Shinkafa." Bhatool ta faWa tana mi™e ido. "Ki tashi ki bi mijinki." Sai a lokacin Bhatool ta kula da Senate dake zaune yana kallonta. "Ni anan zan kwana." Wata uwar harara ya watsa ma ta sannan ya ce. "Sannu cin kai." Ba ta ba shi amsa ba ta sake mai da kan ta ga Yaya Karima. "Ni yunwa nake ji."

"Bhatool tun Wazu fa yake jiranki, idan kun je gida kwanci. Kinga ni nan ban Wora shinkafa ba, kunnun gyaWa na yi."

"To zan sha." Ta shi Yaya Karima ta yi ta shige kicin. "Ke ta shi mutafi."

"Nifa na dawo gidan yar uwata, idan ba za a dinga hula™anta ni ba."

"Na daina fa, ki ta shi dan Allah."  Ya faWa yana karyar da kai. "Sau nawa kana cewa ka daina?."

"Bhatool ke zuma ce sai da huta."

"A'a sauro ce, ka ta shi ka tafi gidanka ni ba inda zani, daga nan ma gidanmu zan tafi, bari na kira Abdul ya zo ya Wauke ni." Ta faWa tana Waukar wayarta, ganin tana shirin Sa ta masa rai ya sa ya mi™e tsaye to na tafi. "Kafi ruwa gudu." Ai ba ta yi aune ba ta ji ya kinkice ma ta, ya Waga ta cas kamar wata yar baby ya yi waje da ita. Yaya Karima na fitowa taga sun fice. "Kai ma shaaa Allah, Bhatool ko rigima."

Ko Sangaren Mom bai kai ta ba ya tura ta a mota suka bar gidannan,  tun da suka fara tafiya ran ta a haWe yake ko kallon inda yake ba ta yi, ™asa ma ta mayar da kan ta. "Ki yi ha™uri Habibty." Ba ta Wago ta kalleshi ba ta ce. "Yanzu muna komawa gida zaka daina duk wannan murmushin, duk wannan dariyar, ka wani haWe rai." Dariya ya yi sannan ya ce. "Na ce fa na daina gaba Waya in shaaa Allah."

"Tom Allah Ya yarda."

"Kalli inda muka zo." Šagowa ta yi, ina zata gani idan ba gidansu ba, yau za ta ga Umma. Ko™arin buWe motar ta fara, ya ri™e ma ta hannu. "Ki jira ni mana."

"Thom." Ta faWa, sannan ya cika ta ya buWe suka fito, hannunshi cikin na ta suka shiga cikin gidan, sai dai shi kaWai ya yi sallama ita ba ta yi ba sakamakon jirin da ta ji yana Wibarta. "Ash." Ta faWa. "Bhatool are you okay?." Ya tamabaye ta, girgiza kai ta fara yi sannan ta ce. "Kai na."

"Me ya samu kan?." Ba ta iya buWe baki ba ta ji jikinta ya sake, shuuu ta faWa. Da sauri ya ri™o ta ta faWo jikinsa. "Bhatool! Bhatool." Ya shiga kiran sunnanta, amma ba ta ko numfashi bare motsi. "Bhatool!." Ya sake faWa, Umma dake xaune Waki ba ta san me yake faruwa a tsakar gidanta ba sai murya ta ji daga sama kamar ana kuka. "Umma! Umma!! Umma!!!, Bhatool." Mi™ewa tsaye Umma ta yi tare da faWin. "Subhanallahi." Amma ba ta kai ga ™arasawa ba ta ji ansake kiran sunnan na ta. "Umma! Bhatool." Da sauri ta fito, tsaye ta yi turus ganin Senate da Bhatool a kwance.

*HASASHEN SOYAYYA*d'þ
=Ø%Ý>ØyÝ

_Imagination of love_

_Stroy and written_

By

Sayyid (Legend's pen)


*FUTURE WRITERS ASSOCIATION*

*(FUWA)=Ø‹Ýþ=ØÚÜ*

*The Fearless Writers Team*

_Marubuta masu tsage gaskiyya_

*BISMILLAHI RAHAMANIN RAHIM =ØOÞ=Ø«Ü*

_Page 40_

"Subahanallahi, mai yafaru daku?." Umma ta faWa tana ™arasowa inda suke, cikin kuka Senate ya ke magana. "Umma yanzu mun shigo, mun shigo kawai ta faWi ™asa."
Chapter 34 · 0% Book details