← Book details Hasashen Soyayya Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 40 OF 51

Sashe 40

Hasashen Soyayya Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Amrah ta kalli Mom cikin tsoro, sannan ta Wauko wayarta ta kunna wani sauti (recording). Muryar Anty (Maman Anas) ce ta fito sarai tana faWin: "Amrah kinyi mini aiki mai kyau. Kin san fa Senate Wana ne, kuma ba na son ganinsa da wannan yarinyar tun farko. Ke kin yi amfani da kishinki, ni kuma na yi amfani da hikimata wajen ganin na raba su..."

Wani irin jiri ne ya kwashi Mom, ta koma ta zauna da sauri. "Anty? Maman Anas? ˜anwata ce take son ruguza farin cikin Wana?" Mom ta faWa cikin wani irin murya mai ban tausayi, hawaye ya wanke mata fuska.

Abdul ya daka wa Amrah tsawa. "Muguwa! Kalli irin abin da kika aikata. Kin ruguza aure saboda kishin banza."

Bhatool ta mi™e tsaye, tana kallon Amrah cikin wani irin yanayi na tsana da tausayi lokaci guda. "Amrah, na gode da kika faWi gaskiya. Amma ki sani, kin riga kin illata zuciyata. Kin raba ni da mutumin da na fi ™auna a duniya."

Barrister Al-Amin ya mi™e ya karSi wayar Amrah dake Wauke da recording Win. "Wannan ita ce shaidar da muke bu™ata. Yanzu saura abu Waya, dole ne Senate ya ji wannan muryar, kuma dole ne ya ga wannan gaskiyar."

Amrah ta rushe da kuka tana neman gafarar kowa dake wurin, amma kowa ya juya mata baya, domin abin da ta aikata ya wuce duk yadda ake tunani.

"A'a tunda har Senate bai sami yarda dani ba, ya yarda da wani abu daban, har ya iya sakina nima na hakura da Senate har Abada."

Legendspen

08129553971

HASASHEN SOYAYYA (BOOK 2)

By

Sayyid Legendspen

Amanar-Janafty

Shafi na Arba'in da Biyar  (45)

Bayan kowa ya saurari muryar Anty (Maman Anas) a cikin rikodin Win da Amrah ta kawo, falon ya sake yin tsit na wasu da™i™o, Kowa yana sarrafa abin da ya ji a cikin ransa. Bhatool kam ta daina kukan da take yi dazu, fuskarta ta koma wani iri, babu sauran alamar karaya ko wani yanayin damuwa, dan ba ta ma san abinda zai dame ta ba, shin ™awarta da ta ci amanrta ko kuma mijin da ya kasa yarda da ita?. 

"Yanzu ke Amrah mene ribarki a wannan abun da kika aikata, gwanda ma ita Maman Anas din ta yi ne da burin ta raba auren dan 'yar uwarta dan tana ganin kamar bai dace da ita ba, da ta ta 'yar ya dace, ke fa?." Yaya Karima ta tambayi Amrah. "Nasani na kasance azzaluma, maci amana, mai fuska biyu na cuci kaina na cuci ™awar da ta Aminta dani." 

"Tabbas kincuci kanki, kincuci yarda da aminci amma baki cuci Bhatool ba, sabida ubangiji ya riga da ya tsara mata hakan, sannam Bhatool tun a farkon auren ku na nuna miki cewaer ki dinga ri™e sirrinki amma sai kika watsar dani, karshe ma kika daina nemana, har ita Amrah ta fira sabgata a makaranta sai dai ni na me ta, yanzu wa gari ya waya, na fada miki cewa ba kowanne murmushi ba ne soyayya." Jannah ta faWa. "Ki yi ha™uri ki yafe mini Bhatool dan Allah dan Annabi." 

"Amrah ni bazan ri™e ki ba, sabida na zauna dake da zuciya Waya na yarda dake, amma kika ci amana, na barki da ubangiji ya yi miki duk sakkayar da ya ga dama, muddin kina doran duniya bana jin zan yafe miki, amma daga ranar da na riga ki mutuwa tabbas kam na yafe miki." Kuka Amrah ta fashe da shi, Mom kam ta ce. "Ni Amrah banda bakin da zance na yafe miki ko a'a, abun kunyar da 'yar uwata tabar mini ka Wai ya isheni." 

Jannah ce ta mi™i tsaye sannan ta ce. "Amrah idan kina da tunani yanzu lokaci ne da zaki gyara rayuwarki, ki tuba kafin ki koma ga mahallinci ki, ni baki yi mini komai ba a zaman mu dake, idan ma kin yi to bansani ba kuma na yafe miki, amma  kanwance kamar da na gama in sha Allah."  Taba fadin haka ta fice, Bhatool ta kalli Abdul. "Ka mayar dani gida wajen Umma zan koma, duk kayana da suke gidansa a dawo dasu kawai." 

"Me yasa Bhatool?." Mom ta tambayeta. "Mom duk abun nan da ya faru ba zai canja abin da Senate ya yi mini ba. Ya yarda da kowa, ya ™aryata ni. Ya yarda da hotuna, ya yi watsi da amanar da ya ce yana da ita a kaina."

Mom ta matso kusa da ita, muryarta a sanyaye. "Bhatool, kiyi ha™uri. Kina gani yanzu asiri ya tonu. Kowa ya san gaskiya yanzu. Senate ya yi kuskure ne saboda tsananin kishi, amma idan ya ji wannan gaskiyar, na tabbata zai dawo ya ro™i gafararki."

Murmushin takaici Bhatool ta yi, ta girgiza kai. "Mom, don Allah kiyi ha™uri. Ni kam na ha™ura da Senate tun da har shi ma ya iya ha™ura da ni cikin sau™i haka. Ba zan koma gidan da aka wulakanta ni ba. Zan raini cikina a duk inda nake har Allah Ya sa na haife shi lafiya, amma batun Senate na riga na cire shi a raina. Yanzu abin da nake so, Abdul ka Wauko mini kayana, gidan Umma zan koma yanzu."

"A'a Bhatool! Kar kiyi haka. Kina cikin idda fa, kuma kinsan idan kika koma gida kowa zai ta yamaWiWi ne da zancen," Yaya Karima ta faWa cikin tashin hankali tana son ba ta baki, dan duk sunyi mamakin hukuncin da ta yanke. Amrah dai simi simi ta faki ido ta tashi ta fice, Bhatool kam ta ce

"Yaya Karima, na riga na yanke shawara. Ba na son zama a inda zan dinga tunawa da wannan cin amana. Abdul, don Allah ka shirya mu tafi," Bhatool ta faWa cikin murya mai nuna cewa ba za ta canja ra'ayi ba.

"Tashi to mu tafi." Abdul ya faWa. "A'a fa Abdul anan zata zauna." Yaya karima ta faWa. "To muje wjen Umma duk hukunci da ta yanke shikenan." Ba musu kowa ya tashi, Mom ma ta tashi ta yi na ta gidan, a falo ta tarar da Dad yana zaune, tana shiga ta zauna akan kujera ta hada hannu da kai. "Lafiya dai?." 

"Ina lafiya." Mom ta fada tare da fara zubar da hawaye. "Me yafaru ne?." Dad ya faWa hankali a tashe yana matsowa kusa da ita, kuka ta fara kamar ™aramar yarinya domin tabbas abun yana cinta a rai. "Wai yanzu ace kamar 'yar uwata ce za ta yi wa Senate asiri, za ta sam duk yadda zata yi ta raba aurensa, duk akam tana son ya auri Ikilima." 

"Ki yi hakuri, karki sa damuwa ki jawa kanki ciwo don abin da wata ta aikata," Dad ya faWa yana tausar kafaWunta.

"Alhaji, yaya zan yi ha™uri? ˜anwata ce fa! Matar da nake gani a matsayin jini na, ita ce ta sa aka raba auren Wana. Kuma ga shi yanzu Bhatool ta ce ta ha™ura da shi gaba Waya. Alhaji, idan Senate ya dawo ya iske ya rasa Bhatool, yaya kake jin zai kasance?" Mom ta faWa cikin kuka.

Dad ya numfasa, ya ce, "ki kyale ta da Allah. Ita kuma Bhatool, karki damu da fushin da take yi yanzu. Ai mace ce, kuma tana cikin raWadi ne. Ga shi kuma tana da juna biyu. Kina ji ai yadda likitoci suke cewa, mai ciki tana saurin fushi. Amma kiyi tunani, akwai idda mai tsayi a gabanta tunda tana da juna biyu. Har sai ta haihu kafin lokacin auren ya ™are gaba Waya. Kafin wannan lokacin, Senate zai dawo ya san gaskiya, ita kuma za ta sauko daga fushin da take yi. Mu ba ta lokaci kawai."

Nasiha mai ratsa jiki Dad ya dinga yi wa Mom, yana nuna mata cewa komai lokaci ne, kuma Allah zai daidaita komai tunda asiri ya riga ya tonu.

Bhatool ta takura lallai sai an kai ta gidan Umma. Abdul ya kasa musa mata ganin yadda take cikin matsanancin fushi. Yaya Karima ta ga ba za ta iya barin su su tafi su kaWai ba, ta kalli mijinta. "Barrister, mu tashi mu tafi gaba Waya kawai. Ba zan iya barin Bhatool ta tafi a wannan halin ba."

Haka kowa ya shirya, suka sanya Bhatool a mota suka nufi gidan Umma.  

A cikin gidan Umma kam, tana zaune tana gyaran kayan miya ta ji sallama, murya har xa ta Goggo Larai, a ranta ta ce. "Kana tsaka da tashin hankali zasu zo su ™ara ma wani." Shigowa suka yi Umma ta mi™e da faWin. "Goggo sannunku da zuwa." Cike da hawaye Goggo ta ce. "Yawwa, Yawwa Habiba, Habiba dan girman Allah, dan girman maaiki, dan daraja, dan ™udura, dan zatin...." 

"Goggo lafiya wai?." Umma ta katse ta cike da tashin hankali da fargabar abinda zata faWa. "Habiba ki yafe mini, kisa 'ya'yanki su yafe mini, na cutar dake dasu cutarwa da banga amfanin ta ba, cutarwa da ba ta yi mini rana ba dan Allah ki yafe ni." Shiru Umma ta yi na 'yan mintuna sannan ta ce. "Tabbas kun cutar damu, amma bakomai ta ni na yafe muku suma 'ya'yana nasan zasu yafe muku." Goggo Larai ba ta kai ga yin magana ba Su Bhatool suka shigo. 

Baki sake suka kallon Goggo Larai dur™ushe gaban Umma a gefe kuma ga Fure da Habi nan, Yaya Karima ce ta ce. "Umma Lafiya? Goggo mai ya faru?." Rarrafowa Goggo Larai ta yi zuwa inda suke, sannam ta ce. "Ku yi wa Allah ku yiwa Girman ma'aiki ko yafe mini dukkan cutarwa sda na dinga yi muku, da irin tsanar da na yi muku." 

Legendspen

08129553971

Jama'a ba ™arya na gaji da Littafin nan

HASASHEN SOYAYYA (BOOK 2)

By

Sayyid Legendspen

Amanar-Janafty

Shafi na Arba'in da Biyar  (46)

Baki sake suka kallon Goggo Larai dur™ushe gaban Umma a gefe kuma ga Fure da Habi nan, Yaya Karima ce ta ce. "Umma Lafiya? Goggo mai ya faru?." Rarrafowa Goggo Larai ta yi zuwa inda suke, sannam ta ce. "Ku yi wa Allah ku yiwa Girman ma'aiki ko yafe mini dukkan cutarwa sda na dinga yi muku, da irin tsanar da na yi muku."
Chapter 40 · 0% Book details