← Book details Hasashen Soyayya Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 12 OF 51

Sashe 12

Hasashen Soyayya Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Mai machine yana ajiye ta ta bashi kudinsa ta nufi get, bugawa ta shiga yi tana fadin. Zaka bude ko sai na balla get din.

Da gudu mai gadi ya bud e yana cewa. Ina band aki ne ayi hakuri Hajiya.

Hararan shi tayi tana cewa. Yanzu zaka matsamin ne ko sai na buge ka?.

Da sauri ya matsa mata ta shige tana masifa, a falo ta wurgar da handbag dinta tana kwalawa Yaya Karima kira. Yaya Karima!!.

Yaya Karima tana daki ta kwanta kenan taji kiran, da sauri ta fito tana cewa. Bhatool lafiya?.

Fashewa tayi da kuka tana zama a k asa, da mamaki Yaya Karima ta iso gurin ta tana dafata ta zauna ta ce. Me ya faru?.

Kasa tsayar da kukan nata tayi tana fadin. Yaya ni na hakura da Makarantan nan.

Cike da mamaki ta ce. Me kuma ya faru? Me aka miki?.

Nan ta bata labarin komai bata boye mata ko daya ba, ta karashe tana kuka.

Shuru Yaya Karima tayi, gefe guda na zuciyarta na tuna mata da Senate, kafin ta sauke ajiyar zuciya ta ce. Dago fuskarki ki kalle ni Bhatool.

Da idanunta da suka danyi ja ta dago tana kallon ta.

Yaya Karima ta ce. To ke waye kike so?.

Yaya burgeni kawai yake yi.

Waye ne shi din?.

Shuru tayi kafin tayi magana suka ji sallaman Juraij da Senate, lokaci daya zuciyarta ya tsinke ta kalli Yaya Karima wacce ke sakin murmushi tana fadin. Yau Senate ne a gidan.

Murmushi ya mata suna k arasowa cikin falon, gaishe da ita suka yi ta amsa tana tambayar su Momi suka ce tana lafiya.

Idanunsa na kan Bhatool da taki juyowa dan kukan da tayi ya saka idanunta ja.

Yaya Karima ta ce. Bari na dauko muku ruwa ko. Ta fada tana nufan fridge.

Juraij yayi saurin dakatar da ita ta hanyar cewa. Anuty da kin bari daga gida muke fa, dama gurin Bhatool muka zo.

Dum-dum haka taji zuciyarta na bugu, yayin da Senate yayi saurin dafe saitin zuciyarsa yana karanto addu a duba da yanda lokaci daya ya harba masa.

Yaya Karima ta ce. Laifi ta muku ko?. Ta fada tana dariya.

A a mun isa ta mana laifi.

Dubanta Yaya Karima tayi tare da cewa. Bhatool baki ji ance anzo gurin ki ba.

Jinjina kai tayi tana cewa. Naji Yaya. Kafin ta mike ta ce. Ina zuwa bari na shiga daki na fito. Tayi sauri ta yanda kar a ce ta tsaya.

Yaya Karima ta zauna tana duban su ta ce. Me ya faru?.

Kallon Senate Juraij yayi kafin ya ce. Anuty wannan na rako fa. Ya nuna Senate kafin ya cigaba da cewa. Wai Bhatool& .. Saurin katsai shi yayi ta hanyar buge k afarsa yana marairaya ido.

Tsaki Juraij yayi yana cigaba da cewa. Wallahi Anuty hauka ya fara yi akan Bhatool.

Runtse ido Senate yayi saboda kunyan da yaji lokaci daya ya kama shi, Yaya Karima ta ce. Ikon Allah, wai Senate har yanzu tsoron ne da kai? Tsoron ma na Bhatool?.

Juraij ya ce. Hmmm!!! Shi ne yau na jawo shi nace yazo ya fada mata ko zamu samu sauki.

Yaya Karima ta dubi Senate da kyau ta ce. To idan kana tsoron ta taya zakuyi zaman aure kenan? Ko ka taba ganin inda miji ke tsoron mata?.

Girgiza mata kai yayi, ta cigaba da cewa. Ka cire tsoro ka ajiye shi a gefe ka tunkare ta da zancen.

Gyada mata kai yayi kafin ta mike ta ce. Bari na kira ta. Ta nufi dakin da Bhatool ke ciki.

Da sauri ya dubi Juraij zai yi magana ya ga ya ciro waya yana tashi da alama kiransa aka yi.

Inna illahi!! Ya furta a zuciyarsa kafin yaji wani bangare na zuciyarsa na ce masa. Zaka iya, idan baka fada mata ba wani ya rigaka fa kamar yanda wancan ya rigaka Ji yayi wani kishi ya tokare masa makoshi lokacin da yaji ta ce. < Ce masa nayi ina da wanda nakeso>.

Ko da Yaya Karima ta shiga dakin ta same ta zaune da waya a hannu tana dannawa, kusa da ita taje ta zauna tana cewa. Bhatool!!!. Ta kira sunanta.

Mayar da hankalinta tayi zuwa gareta baki daya tana amsawa.

Bhatool baki fadamin wanda kikeso ba?.

Yaya burgeni kawai yake yi.

Waye ne shi din?.

Dan Momi ne. Ta fada tana turo baki gaba ta dauke kai.

Ke bana son shirmen kin nan fa, dan Momin bashi da suna ne.

Yaya Karima Senate ne fa.

Sakin baki tayi tana kallon ta. Shi sonta yake, ita kuma burge ta yake, me hakan ke nufi?. Sanin babu mai bata amsa ne ya saka ta dubi Bhatool me kyau ta ce. Ke ko dai son shi kike?.

Da sauri ta juyo tana girgiza kai.

Yaya Karima ta yi murmushi tana rike hannunta ta ce. Bhatool kin san Senate baya surutu, kuma baya kula mata ko?.

Yoo to ni Yaya taya zan sani.

Ungo naki=ØÝ ai fada miki nake yanzun ba wai kin sani ba.

To ina ji. Ta ajiye wayanta ta zuba mata ido.

Tsaki Yaya Karima tayi tana tashi ta ce. Ki je falo yana neman ki.

Dariya tayi tana cewa. Allah yasa outing zamu fita ya kashe min zuciya da kudi.

Kallon ta Yaya Karima tayi tana tsaki ta fita.

Mayafin Abayan jikinta ta yafa ta fito falon.

Yana zaune yayi shuru kamar maraya, kamar mutuniyar kwarai ta iso da sallama a bakinta.

Amsawa yayi ba tare da ya dago ya ganta ba, a kujeran dake kusa da nashi ta zauna bayan ta gaishe shi ya amsa.

Shuru ne ya biyo baya babu wanda yayi magana tsawon mintuna, kafin da kyar ya dago da kai ya kalle ta yana fadin.

Legend's pen 08129553971

14-

*HASASHEN SOYAYYA*d'þ
=Ø%Ý>ØyÝ

_Imagination of love_

_Stroy and written_

By

Sayyid (Legend's pen)


*FUTURE WRITERS ASSOCIATION*

*(FUWA)=Ø‹Ýþ=ØÚÜ*

*The Fearless Writers Team*

_Marubuta masu tsage gaskiyya_

*BISMILLAHI RAHAMANIN RAHIM =ØOÞ=Ø«Ü*

_Page 14_

Da sauri ta d aga kai ta kalle shi, jinjina mata kai yayi yana cigaba da cewa. Za ki iya aure na?

Uhm& . Uhm& . Ni wai?. Ta nuna kanta tana kallon shi.

Gyada mata kai yayi yana mikewa tsaye ya zuba hannunsa a aljuhun wandonsa ya ce. Kiyi shawara kafin ki yanke amsa, na baki daga yau har zuwa lokacin da kika ji kin amince. Ya ajiye mata kudi da bai san nawa ba ya tafi.

Da ido tabi bayansa har ya fita kafin ta kalli kudin, dariya kawai tayi dai-dai lokacin da Yaya Karima ta fito.

Yaya wai fa tambaya na yake zan iya auren shi, can t believe it wai wannan handsome guy din ke cewa zan iya auren shi, to ai ko baya gani ne sai na aure shi balle kuma yana kallo. Ta karashe da wani murna a tattare da ita.

Dariya ita ma Yaya Karima tayi tana fadin. To ke me kika ce masa?.

Yaya me zance masa kuwa, barshi na dan wainasa a tunkunyar masa tukun, na ja masa aji sosai kafin nayi accepting.

Murmushi kawai Yaya Karima tayi ta ce. Kar ajin dai ya tsinke.

Tashi tayi ta nufi dakinta bayan ta bawa Yaya Karima kudin ta ce ta ajiye mata.

*Senate*

Yana fitowa a falon ya sauke wani lafiyayyar ajiyar zuciya yana dafe saitin zuciyarsa, lumshe ido yayi yana jin wani karfin guiwa.

Dafa sa da akayi ne ya saka shi bude ido ba shiri yana sauke su akan Juraij, dariya Juraij ya fara masa yana cewa. Wani irin tsoro ne haka Senate.

Hararan shi yayi yana nufan hanyar fita, shi ma ya mara masa baya yana tsokanan sa amma ya mantar dashi har suka shiga gidan su.

A falo suka tarar da Momi, Anas da Salman sun zuba tagumi suna jiran me zai je ya dawo.

Momi na ganinsa ta mike ta iso gurin shi tana zuba masa ido alamun tanaso taji karin bayani.

Dariyan da Juraij ke yi ne ya saka Anas cewa. Ya kwafsa ko?.

No bai kwafsa ba. Ya fada yana dariya kafin ya ce. At last ya fada mata yana sonta.

Lokaci daya suka saki murmushi, Momi bata san sanda ta rungume shi ba tana cewa. Babana ya zama jarumi.

Murmushi kawai yayi yana fadin. Momi dama jarumin ne tun a baya, kuma In Sha Allah ta sanadiyarta na canza, na zama jarumi.

Sakin shi Momi tayi tana jan kumatunsa ta ce. Better.

Salman yayi murmushi ya ce. Shikenan ai yanzu sai kar ka kashe kanka ko.

Rarumo filon kujera yayi yana wurga masa, da sauri ya matsa yana dariya da fadin. Senate na Bhatool.

Dariyan da ya dade bai yi ba yayi yana shafa sumarsa ya ce. Fadi da k ara Senate na Bhatool kuma Bhatool na Senate.

Dariya falon suka saka kafin aka zauna ana hira ana zolayan shi, har su Salman da Juraij suka tafi

*Washe gari*

Rawar kai, ya mantar da Bhatool tashin hankalin dake makaranta. Hakan yasa ta shirya tun wajen ™arfe bakwai, so take taje ta kaiwa ™awayenta gist Winan.

˜arfe 7:45 a bakin gate Win YSU tayiwa Bhatool, tana tafe tana danna wayarta. So take takira wata cikin ™awayenta taji ko sun ™araso cikin school. Horn din taji anayi mata a baya, hakan yasata waigawa a fusace, wa zata gani?.

Dr Hashim. Ya Allahu. ta furta kaman tayi kuka, a hankali ya kawo motar kusa da ita. Bhatool. Ya maganar mu. Murmushin dole ta jawo tayi sanan tace. Nayi shawara, zanzo office Winka anjima.

Okay. kawai yace yaja motarsa, da harara tabi motar tasa. Wayarta ce tayi ™ara alamun kira.

Wai Suhaima ina kikasa wayarki ne.

Ina kan mashin. sai yanzu na sauka, Kinzo school din ne?.

Da banzo ba, zan kiraku?.

Okay gani nn shigowa.

Kashe wayar tayi ta nufi wajen da suke zama kafin su shiga hall. A wajen ta tarar da su Janah suna zaune, dan su tsarin su sai sun hadu baki daya zasu shiga class tare, yanzu ma takirasu sabida tayi tunanin ko sun shiga. Sabuda bata ce dasu zata zo ba.

˜arasawa tayi ta zauna, tare da fadin. Amarya wace zatayi miki make-up?.

Da kallo suka bita, su sunanan cikin tashin hankali da fargaba, ita tana nan tana musu zancen make-up.
Chapter 12 · 0% Book details