← Book details Hasashen Soyayya Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 48 OF 51

Sashe 48

Hasashen Soyayya Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Ranar Waurin auren Amrah, gidan ya cika da murna. Amrah tana kuka tana sake neman gafarar Bhatool yayin da take shirin tafiya gidan mijinta. "Bhatool, kaddara ce ta sa na yi miki kishin hauka, amma yau gashi zan tafi nawa gidan. Don Allah karki daina sanya ni a addu'a."

Bhatool ta rungume ta, "Allah Ya sanya alheri a aurenki Amrah. Komai ya wuce."

Bayan an tafi da Amrah, Senate ya zo ya Wauki Bhatool don mayar da ita gida. Suna cikin mota, ya kalle ta cikin sanyi. "Bhatool, yanzu kowa ya fara samun natsuwa. Saura mu kadai. Ina so ki sani, ina jiran ranar da zaki ce mini kin yafe mini baki Waya."

Bhatool ta yi murmushi ta kalli titi. "Zuciyata tana kan hanyar hakan, Senate."

Soyayya tsakanin Senate da Bhatool ta koma sabuwa ful, tamkar yanzu aka fara zancen. Duk da cewa tana gidan Umma, amma Senate ya mayar da gidan tamkar nasa. Kullum yana nan, idan ya zo ba ya tafiya sai dare ya yi, hira suke yi ta natsuwa inda Senate yake ta ba ta ha™uri tare da nuna mata tsantsar nadama.

Sai dai, duk da wannan shau™i, Mom ta tsaya a kan matsayarta na cewa: "Babu maganar Bhatool ta koma gidan Senate har sai ta haihu lafiya, ta yi jegon ta ta gama." Wannan hukunci ne Mom ta yanke wa Senate a matsayin horo na rashin bincike da gaggawar da ya yi wajen sakin mata ta wayar tarho. Senate ba shi da yadda zai yi, ya amshi wannan hukunci cikin sanyin jiki, yana mai cewa, "Mom, zan jira koda shekara nawa ne, muddin zan sake samun Bhatool a matsayin matata."

Legendspen

08129553971

HASASHEN SOYAYYA (BOOK 2)

By

Sayyid Legendspen

Amanar-Janafty

Shafi na Hamsin da shida

  (56)

A Sangaren Abdul kuwa, labari ya sauya. Ganin yadda Ahmad ya nuna halin girma da sadaukarwa, sai sha™uwa ta ™aru tsakanin iyalansu. Cikin ikon Allah, Abdul ya ga ™anwar Ahmad, mace mai natsuwa da tarbiyya. Ba tare da Sata lokaci ba, aka shiga maganar magabata.

Cikin ™an™anin lokaci, aka ™ulla auren Abdul da ™anwar Ahmad. Ganin yadda kowa yake son ™ulla wannan zumunci, aka sanya lokacin auren a gurguje wata guda kacal! Wannan lamari ya sanya farin ciki a zukatan kowa, musamman Bhatool dake jin daWin cewa zumuncin da ta so ™ullawa da Ahmad ta hanyar aure, yanzu zai tabbata ta hanyar Wan'uwanta.

Kwanaki sun fara gudu tamkar walkiya. Shagalin bikin Abdul ya kankama, yayin da cikin Bhatool shi ma ya ™ara girma, ya shiga watan ™arshe wanda daga shi sai watan haihuwa. Senate ya dage wajen ganin bikin Abdul ya ™ayatar, domin yana jin nauyin yadda Ahmad ya janye masa fage.

Wata rana, suna zaune a tsakar gidan Umma, Senate ya kalli Bhatool wadda take fama da  jikinta saboda nauyin ciki. Ya kamo hannunta, ya dube ta cikin ™auna. "Bhatool, saura kwanaki kaWan biki, kuma saura kwanaki kaWan mu ga jaririnmu. Ina addu'ar Allah Ya kawo ranar lafiya, domin ranar ita ce zan fara rayuwa ta gaskiya da ke."

Bhatool ta yi murmushi, wanda ya bayyana kyakkyawar fuskarta dake cike da annuri. "Insha Allah Senate. Komai zai wuce lafiya. Amma karka manta, ka yi mini al™awarin ba zaka sake saurarar maganar kowa a kaina ba."

Senate ya rungume hannunta a ™irjinsa. "Na miki al™awarin dake tsakanin rai da numfashi, Bhatool. Ke ce tawa har abada."

Mom tana zaune a falo tana nazarin wasu takardu, sai ga Anas ya faWo gidan yana kuka mai ban tausayi, muryarsa tana rawa. Mom ta mi™e cikin firgici tana tambayarsa abin da ya faru.

"Mom! Anty ce... ba ta da lafiya! Daga Abuja aka kira ni ake gaya mini wai tun safe take surutai, ta haukace gaba Waya!"

Mom ba ta Sata lokaci ba ta kira Senate, nan take suka garzaya Abuja tare da sauran yan uwa. Suna isa gidan, abin da suka gani ya tsoratar da su. Maman Anas ce zaune a tsakar Waki, gashin kanta ya hargitse, ta yayyage kayan jikinta tana ta surutai marasa kan-gado. Tana ganin Senate, sai ta mi™e tana nuna shi da yatsa, tana wata irin dariya mai ban tsoro.

"Usman! Ka zo ganin aikina ne? Ni ce na sa Amrah ta yi dukkan abin da ta yi! Ni ce na raba ka da Bhatool! Na tsani ganin farin cikinku!" Ta fara ihu tana kiran sunan Bhatool da Amrah, tana bayyana dukkan makircin da ta ™ulla na raba aurensu.

Senate ya tsaya cak, jikinsa yana rawa saboda jin tsantsar muguntar da yar uwar mahaifiyarsa ta aikata. Kafin kowa ya yi yun™urin kamata, Maman Anas ta daka wani uban tsalle ta fice daga Wakin da gudu. Su Mom da Senate suka biyo bayanta suna kiranta, amma ta riga ta fita har kan titi tana gudu ba tare da kallon hagu ko dama ba.

A daidai lokacin, wata mota mai gudu ta taho, direban ya yi ™o™arin taks birki amma abin ya faskara. Motar ta bige ta, ta yi sama ta faWo. Kafin su ™arasa kanta, rai ya yi halinsa. Maman Anas ta mutu a take, tana girbar abin da ta shuka na sharri da ma™ar™ashiya.

A can kuwa, rayuwa ta ci gaba da gudana cikin farin ciki da annuri. Bikin Abdul ya kankama, inda aka yi shagali na gani ta faWa. Abin farin cikin shi ne, ashe shi ma Ahmad, bayan janyewar da ya yi, Allah ya haWa jininsa da wata kyakkyawar Cousin Winsa, inda aka haWa aurensu lokaci guda da na Abdul.

Bhatool, duk da nauyin cikin dake jikinta, ita ce ta zama "Uwar Biki" a wajen Abdul. Ta dage wajen ganin kowa ya ci ya sha, fuskarta Wauke da murmushin jin daWin yadda dangantakarsu da Ahmad ta koma zumunci mai ™arfi.

Tana tsaye a tsakiyar mata, tana raba abinci, sai ta ji wata fWuwar gaba. Ta dafe ™irjinta, ta tuna da Maman Anas ba tare da ta san abin da ya faru ba. Amma ganin yadda Abdul da Ahmad suke cikin murna a matsayin ango da ango, sai ta share damuwar ta ci gaba da taya Wan'uwanta murna.

Bata sani ba cewa a can Abuja, Senate yana tsaye a kan gawar wadda ta zama silar rugujewar farin cikinsa na wani lokaci

Senate ya dawo Kano cikin wani irin yanayi na nauyin zuciya. Ko da ya isa gidan Umma, ya iske Bhatool tana cikin hidima da shagalin bikin Abdul. Tana ganinsa, ta fahimci akwai damuwa tattare da shi. Senate ya zauna a gefen gado, ya kasa boye abin dake damunsa, nan take hawaye ya fara zuba a idanunsa.

Cikin muryar kuka da rawar jiki, ya kwashe dukkan abin da ya faru a Abuja ya gaya mata. Ya bayyana mata yadda Maman Anas ta haukace, da kuma yadda ta fadi asirin cewa ita ce ta rura wutar kiyayya tsakaninta da Amrah har ta raba aurensu, sannan kuma ga mutuwarta mai ban tsoro a kan titi.

Bhatool ta dade tana kallonsa, zuciyarta tana wani irin bugawa. Maimakon ta nuna farin ciki akan mutuwar, sai ta sauke numfashi, ta share wa Senate hawayensa.

"Allah Ya jikanta. Ya riga ya kai ta inda babu sauran ma™arkashiya. Gaskiya ta bayyana, kuma wannan shi ne babban abin farin ciki na," Bhatool ta faWa cikin nutsuwa. "Yanzu don Allah ka bar kukan nan, mu ci gaba da shagalin bikin Abdul cikin farin ciki, tunda Allah Ya wanke mu."

Duk da mutuwar ta girgiza ta, Bhatool ta ji wani irin natsuwa a ranta. Sanin cewa ba kuskurensu ba ne ya ruguza aurensu a baya, sai dai tuggun wani, ya sa ta ™ara jin son Senate yana ™aruwa a ranta.

Amrah ma acan gidanta ta sami labarin mutuwar Maman Anas. Ta girgiza matu™a, ta dinga kuka tana tuna yadda Anty ta dinga zuga ta tana ba ta shawarwarin banza. Ta yi nadamar yadda ta bar kanta a matsayin kayan aiki a hannun wata, har ta kusan ruguza rayuwar Bhatool. Ta kira Bhatool a waya cikin kuka sukayi ta jajantawa juna, inda Amrah ta sake ro™on gafararta a kan dukkan abubuwan da suka faru a baya.

Bikin Abdul da Ahmad ya ci gaba da ™ayatarwa. Kasancewar Bhatool ce uwar biki, ta dage sosai duk da nauyin jikinta, Ko'ina aka ga Bhatool, za a ga Senate a bayanta tamkar inuwarta, yana ™o™arin kare ta daga kowace irin wahala.

A daren ranar walimar su Abdul, an yi taro mai cike da albarka. Ahmad ya zo har kusa da Senate da Bhatool, ya gaisa da su cikin mutunci da ™auna. Ganin yadda Ahmad ya rungumi ™addara har ya auri Cousin Winsa, ya sanya Senate jin wata irin kunya da kuma girmama Ahmad a ransa.

"Alhaji Usman, Allah Ya bar zumunci," Ahmad ya faWa yana murmushi.

Senate ya dafa kafaWarsa, "Ahmad, kai jarumi ne. Na gode da komai."

Bhatool tana kallon su, tana jin daWin yadda rayuwarta ta fara fuskantar haske. Gaskiya ta bayyana, ma™iyi ya tafi, sannan masoya duk sun sami natsuwa. Sai dai kuma, a duk lokacin da ta juya, tana jin wani irin nauyi a cikinta, alamar cewa lokacin da kowa yake jira na saukar numfashi ya riga ya ™arato.

Legendspen

08129553971

HASASHEN SOYAYYA (BOOK 2)

By

Sayyid Legendspen

Amanar-Janafty

Shafi na Hamsin da bakwai

  (57)

An kammala bikin Abdul da Ahmad lafiya cikin nasara da albarka. Amaryar Abdul, wato ™anwar Ahmad, ta tare a gidanta dake kusa da su Umma, yayin da Ahmad shi ma ya tare da tasa amaryar cikin kwanciyar hankali. Wannan aure ya ™ara dan™on zumunci tsakanin gidajen guda biyu, inda kiyayya ta koma soyayya, zargi kuma ya koma yarda.

Bayan bikin, hankali gaba Waya ya koma kan Bhatool. Senate ya ware kusan dukkan lokacinsa a kanta. Babu inda yake zuwa idan ba asibiti ko wajen aiki ba, to yana gidan Umma. Soyayyar da suke nuna wa juna a wannan lokacin ta zarce kowace irin soyayya da suka yi a baya. Senate yakan zauna ya yi ta yi mata tausa a ™afarta, yana mata hirar yadda gidan nasu zai kasance idan ta dawo.

Wata rana da yamma, suna zaune a tsakar gidan Umma, iska mai daWi tana kaWawa. Bhatool ta jingina kanta a kafaWar Senate, tana kallon cikinta dake ta motsi.

"Senate," ta kira sunansa cikin muryar dake cike da natsuwa.

"Na'am rayuwata," ya amsa yana ™ara gyara mata zaman mayafinta.
Chapter 48 · 0% Book details