← Book details Hasashen Soyayya Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 49 OF 51

Sashe 49

Hasashen Soyayya Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

"Gaskiya na gaji da wannan zaman gidan Umman. Na matsu in haihu lafiya, in ga jaririnmu, sannan mu koma gidanmu mu ci gaba da rayuwarmu. Ina son in ri™a tashi a kusa da kai, in ri™a kula da kai kamar yadda ya kamata."

Senate ya yi murmushi, ya sunbaci goshinta. "Bhatool, nima abin da nake jira kenan kullum a raina. Amma kin san dokar Mom; tace sai kin gama jegonki sannan zaki dawo. Ko kina son mu karya dokar Mom ne?"

Bhatool ta Wan yi fushi na wasa, "A'a, ba karya doka ba, amma gaskiya kewarka tana sanya ni kuka wani lokacin idan dare ya yi."

Senate ya ji daWin wannan kalaman nata. Ya rungume ta, yana jin yadda zuciyarsa take bugawa don ™aunarta. "Kiyi ha™uri ragowar kwanaki ne suka rage. Insha Allah duk yadda kike so, haka za a yi. Zan sake gyara miki gidan nan ya fi yadda kika sani, domin ke ta musamman ce a gare ni."

Haka suka ci gaba da nuna wa juna soyayya mai tsayawa a rai. Kowa ya gansu yakan yi musu fatan alheri, domin sun zama ababen koyi wajen ha™uri da yafiya. Amma a tsakanin wannan annurin, Bhatool tana yawan jin wani irin bacci da kasala dake ziyartar ta, wanda take gani tamkar nauyin ciki ne kawai.

Washegari da safe, Senate ya dira a gidan Umma da wani irin hanzari. Fuskarsa dake cike da annuri ta bayyana cewa akwai wani abun farin ciki dake tafe. Bhatool tana zaune a falo tana shan kwanon tatacciyar madara, ta kalle shi tana murmushi.

"Wannan annuri haka? Ko an kara maka girma ne a wajen aiki?"

Senate ya yi dariya, ya kamo hannunta ya mike da ita. "Tashi mu fita waje, ina son nuna miki wani abu."

Bhatool ta mike tana dambarwa saboda nauyin jiki har suka isa kofar gida. Tana fita, idanunta suka sauka akan wata hadaddiyar mota kirar Lexus 2024, fara sol, wadda aka yi mata ado da furanni da kuma rubutun "For My Queen" a jiki.

Bhatool ta zaro ido, ta rufe bakinta da hannu biyu saboda mamaki. "Senate Wannan motar fa?"

"Kyautar ki ce Bhatool. Kyautar hakurin da kika yi da ni, da kuma farin cikin da kika shigo mini da shi. Ina so ko da yaushe kije asibiti ko wani waje, kije cikin girma da mutunci," Senate ya fada yana mika mata makullin motar.

Tana cikin murnar nan, ashe Umma tana tsaye a bakin kofa tana kallonsu tana dariya. Ganin yadda Senate yake ta faman sosa keya da nuna damuwa akan Bhatool, sai Umma ta katsa musu hira cikin barkwanci.

"Wai kai Usman, yaushe ne zaka daina wannan rashin kunyar taka? Ka dame mu, kullum kana gidan nan tamkar a nan aka haife ka. Na gaji da ganin fuskarka kullum!" Umma ta fada tana boye murmushin dake fuskarta.

Senate ya yi dariya, "Umma, ai kece kika ce na jira sai ta haihu."

Umma ta tabe baki a wasa, "To na janye maganar nan. Na gaji da takura, zo ka dauke matarka ku tafi gidanku kawai, tunda gani nake yi kusan tare kuke kwana."

Bhatool ta fashe da dariya, ta rufe fuskarta da mayafi saboda kunya. Senate kuwa ya saki wani uban murmushi na jin dadi. "Umma gaskiya kika fada? To yanzu ma zan dauke ta mu tafi!"

Haka suka yi ta barkwanci, inda Umma ta kara nuna musu cewa ta yafe wa Senate kuma tana kaunarsa matsayin danta. Wannan ranar ta kasance ranar farin ciki mara misaltuwa. Senate ya dauki Bhatool a sabuwar motar suka zagaya gari, suna jin dadin haduwar kawunansu.

Amma a cikin wannan murnar, Bhatool ta kalli Senate ta ce, "Usman, na gode sosai. Amma ina so ka sani, babban burina ba mota ba ne, babban burina shine mu rayu tare cikin aminci har karshen rayuwarmu."

Suna tsaka da wannan murnar ta sabuwar mota da kuma barkwancin Umma, farat Waya sai yanayin Bhatool ya sauya. Ta saki wani Wan gajeren nishi, ta dafe ™ugunta yayin da zufa ta fara keto mata a goshi. Senate ya kalle ta cikin firgici, "Bhatool, lafiya? Ko nakuda ce?"

"Usman... marata... marata tana murWawa," ta faWa cikin murya mai rauni.

Ba tare da Sata lokaci ba, Senate ya sungume ta ya sanya ta a sabuwar motar nan, Umma ma ta rigo ta Wauki jakar kayan haihuwa suka nufi asibiti a guje. Senate yana tu™i yana addu'o'i, hankalinsa gaba Waya ya tashi, yana kallon yadda Bhatool take ta faman nishi da ambaton sunan Allah.

Suna isa asibiti, ma'aikatan jinya suka karSe ta suka kai ta Wakin bincike. Bayan kusan mintuna talatin, likita ya fito yana murmushi. Ya kalli Senate da Umma dake jiran jin bayani.

"Alhaji, ku kwantar da hankalinku. Wannan  alamun nakuda ne ba na™udar ba. Duban da muka yi mata ya nuna cewa lokacin haihuwarta (EDD) bai cika ba, akwai sauran mako guda cur. Yanzu za a iya mayar da ita gida ta ci gaba da hutawa."

Legendspen

08129553971

HASASHEN SOYAYYA (BOOK 2)

By

Sayyid Legendspen

Amanar-Janafty

Shafi na Hamsin da takwas

  (58)

Wani irin ajiyar zuciya Senate ya sauke, ya kalli Umma suka yi murmushi. Haka suka sake loda kayansu suka dawo gidan Umma.

Dawowar nan ya sanya aka ™ara shiga wani sabon shafin na soyayya da kulawa. Senate ya ™i tafiya gida, ya ce shi a falon Umma zai kwana har sai Bhatool ta haihu. Kullum yakan zauna a ™asa kusa da ™afafun Bhatool, yana shafa cikinta yana yi wa jaririn magana.

"Ka ga yadda kake wahalar da mahaifiyarka ko? Muna jiran ka ka fito mu nuna maka duniya," Senate yakan faWa yana dariya, yayin da Bhatool take shafa kansa cikin tsantsar ™auna.

Wannan satin ya zama tamkar karni a wajen Senate. Kowanne motsi na Bhatool yana sanya shi tashi tsaye. Sun ™ara shakuwa fiye da kowane lokaci, suna musayar kalaman soyayya dake ratsa jini da Sargo. Bhatool tana jin wani irin daWi a ranta, tana jin tamkar dukkan matsalolin rayuwarta sun ™are.

Mako guda ya wuce cif cikin kwanciyar hankali da annuri, makon da Senate da Bhatool za su dade suna tunawa da shi a matsayin makon da suka fi kowane lokaci shakuwa a rayuwarsu. A duk tsawon kwanakin nan bakwai, Senate bai bar gidan Umma ba. Ya zama tamkar inuwar Bhatool; idan tana daki, yana kofar dakin, idan tana falo, yana zaune a gefenta.

Soyayyar da suke nuna wa juna ta kai matsayin da ko Umma idan ta gansu, sai ta sauke ajiyar zuciya tana musu addu'ar Allah Ya bar su tare. Senate ya riga ya gama shirin komawarsu gida, har ya sa an sake yanayin gidan, komai ancanja kujeru da komai da komai, fenti ma kalar da Bhatool take so, sannan ya cika dakin jariri da kayan wasan yara na zamani.

Wata rana da yamma, sa'o'i kadan kafin cikar makon, suna zaune a falon Umma a kan sallaya daya. Bhatool ta jingina bayanta a kirjin Senate, tana jin yadda bugun zuciyarsa yake bugawa cikin natsuwa.

"Senate," ta kira sunansa cikin murya mai dadi.

"Na'am masoyiyata," ya amsa yana wasa da yatsun hannunta.

"Ina so ka sani cewa, duk abin da ya faru a baya na yafe maka duniya da lahira. Kuma ina so ka sani cewa kaine babban burina. Idan Allah Ya sauke ni lafiya, ina so ka san cewa ba zan taba manta da irin soyayyar da ka nuna mini a satin nan ba. Ka sanya na ji ni tamkar mace mafi daraja a duniya."

Senate ya kara kankame ta, ya sunbaci gefen kanta. "Bhatool, ni ne ya kamata in gode miki. Kin ba ni damar gyara kuskurena, kuma kin karbe ni da dukkan raunina. Allah kadai Ya san yadda nake sonki. Yanzu dai addu'armu daya; Allah Ya kawo ranar nan lafiya mu ga danka a hannunki."

Bhatool ta gyada kai, "Amin. Insha Allah komai zai zo da sauki."

Haka suka yini cikin farin ciki da nuna wa juna kauna. Dare ya yi, kowa ya kwanta, amma Bhatool ta kasa bacci. Ta dinga kai-komo a daki, tana jin wani irin canji a tattare da ita.

Tana kallon agogo, karfe biyu na dare ya buga, daidai cikar mako guda da suka dawo daga asibiti. Farat daya, Bhatool ta ji wani irin nauyi ya sauka mata, wanda wannan karon ta san cewa lallai bako ya iso. 

˜arfe biyu na dare, shiru ya mamaye ko'ina sai ™arar injinan sanyaya Waki da kukan tsuntsayen dare. Bhatool ta mi™e zaune tana jan numfashi da ™arfi. Wannan karon, marar ta ba murWawa take yi ba; ji take yi tamkar ana raba ™asusuwan ™ugunta gida biyu.

"Us...man... Usman!" Ta kira sunansa cikin muryar dake nuna tsananin wahala.

Senate dake kwance a kan doguwar kujera a falon Umma, ya farka tamkar wanda aka watsa wa ruwan zafi. Ya faWo Wakin Bhatool a guje, ya iske ta tana zufa duk da sanyin AC.

"Bhatool! Me ya faru? Nakudar ce?" Ya tambaya yana ri™o kanta, hannunsa yana rawa.

"Usman... ta zo... yanzu take... daban take da ta wancan karon," ta faWa tana kankame hannunsa, har yatsunta suna nutsewa a cikin fatarsa.

Senate bai tsaya wata-wata ba. Ya kwala wa Umma kira, ita ma ta fito cikin gaggawa. Nan take aka nufi asibiti. Senate yana tu™i, amma wannan karon idanunsa sun cika da ™walla yana jin kowane nishi na Bhatool a cikin ransa. Suna isa asibiti, likitocin dake kan aiki suka karSe ta cikin gaggawa.

"Alhaji, yanzu lokaci ya yi. Ruwan jikinta ya fashe," in ji wata nurse yayin da suke tura gadon Bhatool zuwa Labour Room.

Bhatool ta ri™e hannun Senate gam kafin su shiga. "Usman... don Allah ka yafe mini. Ka kula da kanka... ka kula da jaririnmu idan wani abu ya faru."

Senate ya girgiza kansa, hawaye ya zubo masa. "Bhatool, ba abin da zai faru! Zaki fito lafiya, mu koma gidanmu. Don Allah karki faWi haka."

Haka aka raba hannunsu, aka tura Bhatool cikin Wakin da yake zaman rayuwa ko mutuwa. Senate ya dube ™ofar Wakin, ya ji wani irin sanyi ya ziyarci zuciyarsa. Ya zube a kan kujerun corridor Win asibitin, ya rufe fuskarsa da hannayensa yana kuka mai cin rai.

Umma tana gefe tana faman jawo carbi, tana addu'o'i. Senate ya kalli hannunsa dake har yanzu akwai alamar kankamen da Bhatool ta yi masa, ya ji tamkar ransa yana son fita.
Chapter 49 · 0% Book details