← Book details Hasashen Soyayya Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 22 OF 51

Sashe 22

Hasashen Soyayya Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Ai Bhatool ta jawo jama a. Jannah ta faWa tana dariya, sai da Habi ta fice sanan Amrah ta ce. Wai wayanan zaman me suke yi basu tafi ba, basu ne marasa mutuncin nan ba?. Dariya Bhatool ta yi sanan ta ce. Ai sun canja wallahi, kuma Mama ce ta ce kawai su zauna har biki, jiya ta ce da Yaya Karima idan abun arzikin ta dore ai sai ta ri™esu kafin suma su yi aure, kinsan Furee bazawara ce to naji ma ta ce ita karatu take son komawa.  

Ai kam dai Mama ta kyauta wallahi. In ji Jannah ita dai Amrah ba ta ce komai ba kiran Senate ya shigo,bayan sun gaisa ne ta ce. Annur wai su Amrah ne ke tambayar Events Win sabida muna son fito da Ashobe.  

Hakane Fulani, dazu mun yi magana da Mom ta ce ita dai nata events Win na kanta guda uku ne, sanan ™awayenki gaba daya mutum sha biyar ake so, akwai Ashobe din da aka tanadar musu na dukka events Win, za aka wo su gida ko zuwa gobe, sauran kuma bansan yadda za ayi ba, mu guda nawa zamuyi?.

Legendspen 08129553971

*HASASHEN SOYAYYA*d'þ
=Ø%Ý>ØyÝ

_Imagination of love_

    _Stroy and written_

             By

   Sayyid (Legend's pen)


   *FUTURE WRITERS ASSOCIATION*

*(FUWA)=Ø‹Ýþ=ØÚÜ*

    *The Fearless Writers Team*

  _Marubuta masu tsage gaskiyya_

*BISMILLAHI RAHAMANIN RAHIM =ØOÞ=Ø«Ü*

_Page 26_

Ni gaskiyya bansan nawa za ayi ba, kai nawa kake so?.

Ina da abinda nake so ne bayan wanda kike si Fulani.

Zan iya shawara ko?. Dariya ya yi sanan ya ce. Ki yu shawarar ki, zuwa Anjima zamu zo ni da su Anas gaba dayanmu, sai ki kara su Amrah.  

Tom Annur, Allah ya kawo ku lafiya.  

Amin Fulaninah.

Shegiya soyayya, Allah ka aurar damu. Jannah ta faWa, dariya suka yi baki daya  sanan Amrah ta ce. Fulanin Annur, ya aka yi?.  

Ya ce Events din Mom guda uku ne, kuma ™awayena sha biyar ake so, duk ashobe da kayan da zansa za a akwo su yau zuwa gobe. Wata uwar guWa Jannah ta saki sanan ta ce. Kaji masu yi dan Allah.  

Ke banza ki bari mu™arasa ji. Amarah ra faWa, sanan ta ce. Naki fa.  

Ya ce wai guda nawa muke so, muyi shawara.  

To yanzu dai Bhatool ai inaga baki da ™awaye sama da sha biyar ko?. Jannah ta faWa. To ai ko sunfi sha biyar Win cire su za ayi. Amrah ta faWa. Kunga dangin Abba za a dauki Furee da Habi, dangin Mama akwai guda uku, sai kuma Na ima da wata Rukayya yan nan unguwar.  

Bakwai. In ji Jannah. Wai shikenan?. Amrah ta faWa. Gaskiyya su nake tunanin xan iya sawa a harkar bikina, sai dai ko wata fauziya dake kusa da gidan Yaya Karima.  

A a ™yale ta, ni su Furee din ma da an ciresu.  

Ke Amrah gaskiyya abarsu, ni wallahi Bhatool kin burgeni da kika sunansu, yanzu ragowar takwas din sai a haWa, idan ansami extra sai asa Fauziya Win ko?.  

Ta ina za a sami extra?. Amrah ta sake faWa. Ke jarabar duniya, yanzu ya zamu yi da bakwai.  

Nima ai kallonta kawai nake. Bhatool ta faWa. Dalla malamai, ko a makaranta biyar sun fita, sabida ina so mu bayar a cikin team din su Hafsa al™ali, kinsan idan muka bayar muka ce Free Ashobe wallahi zasu je kuma kinga su biyar ne, muka bawa biyu ai sai mun haWasu faWa.  

Mene ribar mu dan mun haWa su faWa, mu bar su suje da muguwar aniyarsu ko banza yanzu cikinmu biyu sun yi aure, kuma sauran biyun ma in Allah yayarda muna hanya. Jannah ta faWa. Idan ma za a bayar a cikinsu Fadila za a bawa ita kaWai muke mutuncin da ita, har a waya ta kirani jiya, amma wallahi sauran babu shegiyar da zan bawa dan ubansu. Bhatool ta faWa. To yanzu dai kinga Amrah ke, Sai ni, sai kuma Suhaima, sai Fadila, to asa Fauziya Win, biyar kenan.  

Kun manta da su Lawisa?. Amrah fa faWa, dariya sukayi sanam Jannah ta ce. Aikuwa da muncika butulu, bikin Labiba mukaje har aka ce munfi kyau a akan su namu kuma mu manta da su. Dariya suka sake yi sanan suka yanke shawara. Yanzu bara naje na ji yadda zamuyi da Mama akan nata event Win sai mu tsayar da namu ko?. Bhatool ta faWa tana mikewa. 

Ke Bhatool fita idona, babu wani event da zan yi.  

Haba Mama,gaskiyya a a ko daya ne ki yi.  

Zaki mun dole ne?. Waya Bhatool ta dauka ta kira Abdul. Kai na ina?.

Ina inda kika aike ni Uwata.  

Dalla maganar serious nake maka.  

Munfita ni da Yaya Karima, muna nan muna bauta miki kina mana iskancin, kayan gado Set uku muka siya miki wajen 7million duk jarin shago na ya ™are. Dariya ta yi sanan ta ce. Ai daman danni kake fita neman dan albarka, yanzu wai Mama ce ba zata yi event ba.

A a wasa take miki zata yi.  

Zaka mun dole ne. Mama ta faWa daga inda take. Ni na isa Hajiya Mama, amma dai zakiyi inji babbar Yaya.   

Zai zo ne anjima zamuyi magana yadda za a tsara komai, su za su yi guda uku shine ya tambayeni Mama fa.  

Kece za ta yi guda Waya, yanzu ma zamu biya mune mi Hall.  

Shikenan dan albarka. Daga haka ta kashe wayarta ta ta shi zuwa Waki. Bayan ta yi zauna ne ta ce. Mama daya, yanzu shi zamu fitarwa da Ashobe, sai ladies night namu ko?.  

Eyh Bhatool, amma ba za ayi cocktail ba harda abokan Ango. Amrah ta faWa. Eyh gaskiyya dai zai yi kyau, amma bara muji dame suka zo.  

~~~~~Red bricks. 

Senate ne da team din abokansa baki daya, wansa ya haWa da Anas, Juraij, Salman, sai kuma Faruq. Senate ne ya ce. Duk wasu events na Mama already ta gama da komai, sanan yanzu Anas ya ce zai haWa night party da ™awayenta, i think komai ya isa haka kar bidi a ya yi yawa.   Faruq ne ya ce. Yanzu ka ta shi muje wajen nasu, a tsayar da komai ba mu da enough time fa. Mikewa suka yi zuwa inda Mom take, itama duk ta yi busy ba™i ta ko ina, bayan sun gaisa ne ya ce. Mom zanje gidansu Bhatool, zamu tattauna yadda events Win zasu kasance.  

Okay, ita kayan da zata sa an kawo su Wazu gaba daya, na ™awayen na ta ne ba a kawo ba har yanzu. Amma ga cards nam kowanne events ga 50cards nan, banda ™awayenta masu Ashobe.  

Okay Mom, kawo cards Win kayan nata idan an kawo wancan a haWa gaba daya.  

Okay. Ta faWa tare da ta shi, kallon jama ar dake gidan ya yi, yau saura kwana goma cif Bhatool ta tare a gidansa. Gaskiyya ina cikin alheri. Ya faWa yana murmushi. Ungo sanan ka ce mata, kar su wahalal da kansu akan cards din mu na na su event Win, idan bai da yawa.  

Tom Mom. Ya faWa tare da amsa ya fice, a waje ya sami abokan nasa kowa cikin motarsa. Ina zamu da motoci haka kuma?.  

Zamu raka ango ne.  

Dan Allah kar su yi yawa, daya ma ta ishemu duka?.  

Allah Senate A a, kai ka shiga ta Anas amma mu duka daga nan gidajen mu zamu huce. Juraij ya faWa, sauran kam duk suka shige nasu motocin, ba dan ya so ba ya shiga suka tafi. A hanya ya yi mata text gasu nan sun tawo. Kun ji gasunan sun tawo, sai mu ta shi mu gyara. Ba musu suka ta shi suka hau shiri. 

Ba daWewa suka kara so, gaba dayansu suka zauna a barandar gidan kan kafet, bayan an cika gabansu da kayan ciye-ciye ciki har da Furee da Habi, su Amrah dai sai ™ara kame jiki ake. Amare namu. Anas ya faWa yana murmushi. Angwaye namu. Amrah ma ta faWa, nan suka kwashe da dariya gaba dayansu, daga nan suka shiga tattauna yadda komai zai kaya musu, har da sanye cocktail din da zasu yi da abokan ango da ™awayen amarya, sanan suma suka ware Backlorate party da za suyi abokan Angon ranar da zasu yi ladies night, sanan Faruq ya dauki nauyin duka rogowar Ashoben ™awayen Amarya, suka yanke matsayar gobe zasu shiga kasuwa da Jannah da Amrah su zaSo komai, bayan sun gama ne aka bar Senate da Bhatool ya bata cards da kuma mukkin gidan sabida masu zuwa Kafi (jere), sanan ya ce zai a aiko da kayan da zata sa da na ™awayenta zuwa gobe har da Mint (kuWaWen li™i). 

Sai yamma su Abdul suka dawo, lokacin duk ™awayen Bhatool sun tafi sai su Furee da hari, komai da aka siyo ya yi kyau sosai sanan aka yanke shwarar gobe zasu a afara zuwa ayi jerin jibi kuma a ci gaba, cikin daren aka aiko da kayan nata da Ashoben ™awayen, kuwa ya ji daWin lissafi da ta yi mussaman da tasa Furee da Habi. 

~~~~~~Washe gari

Masu kafi sun sha matukar mamakin ganin girman gidan, domin kuwa a iya part daya Bedroom uku ne, falo ya kai biyar ga maka-makan kitcehn guda biyu, hala ma daya part Win, Yaya karima ce ta ce. ChaS, ai wallahi mu zuba abinda muke da shi.  

Daman ai abinda za ayi kenan, kar ma asanar da wancan fitinanniyar yarinya, bare ta tayar mana da hankaki. Anty Sailuba ™anwar Mama sa ta zo daga Jigawa ta faWa, suna cikin jerin ne wata motar kayan ta shigo, itama dauke da kayan gado seat biyu, kujeru seat uku, waya Yaya Karima ta dauka ta kira Abdul ta tambaye shi ko shi ya kawo, amma ya ce A a, nan ta kira Umma ita ma ta ce A a, Bhatool ta kira itama ta ce A ah. To kira mijinki ko shine?.  

Banajin shine Yaya, ko Wazu mun yi waya kuma bai faWan ba.

Kirashi dai.  

Tom. Ta faWa tare da kiransa, bayan ya Waga ne ta ce. Wai kai ne ka tura da kaya gida?.  
Chapter 22 · 0% Book details