Sashe 50
Hasashen Soyayya Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Awanni sun fara shura. ˜arfe uku... huWu... har aka fara kiran sallar asuba, amma har yanzu shiru daga Wakin haihuwa. Duk lokacin da Senate ya ji nishin wata mace a ciki, sai ya mi™e tsaye yana zaton Bhatool ce, amma sai ya ji shirun ya ™ara yawa.
Lokaci ya tsaya cak a agogon asibitin, ko kwanakin da Senate ya yi a gadon rashin lafiya ba su yi masa nauyin waWannan awannin ba. An kusa kwashe sa'o'i biyar ana faman nakuda, amma har yanzu shiru kake ji. Likitoci da ma'aikatan jinya suna kai-komo, fuskokinsu cike da damuwa, domin jaririn ya ™i fitowa, yayin da ™arfin Bhatool ya fara raguwa sosai.
A cikin Wakin, Bhatool tana cikin wani hali na ban tausayi. Jikinta ya jike sharkaf da zufa, muryarta ta dashe saboda nishi da kiran sunan Allah. Tana jin tamkar ranta ne yake neman fita duk lokacin da marar ta ta murWa.
"Bhatool, ki ™ara ™o™ari! KaWan ya rage!" In ji babban likitan dake kanta.
Bhatool ta rufe idonta, tana jin yadda duniyar take juya mata. A ranta, addu'a Waya take yi Ya Allah, ko da raina zai fita, Allah Ka tashi jaririna lafiya."
A wajen corridor, Senate ya kasa zama, ya kasa tsayuwa. Ya dinga kai-komo, rigarsa ta jike da zufa duk da sanyin asibitin. Umma kuwa ta karkata a wani gefe, tana ta zubar da hawaye tana jan carbi. Duk lokacin da suka ji ihun wata mace a wani Wakin, sai hantar Senate ta kaWa, yana zaton ko Bhatool ce take cikin wannan halin.
˜arfe bakwai na safe ya buga. Daidai lokacin da hasken rana ya fara gauraye gari, sai aka ji wani irin nishi mai ™arfi daga cikin Wakin Bhatool, biyo baya kuma sai ga kukan jariri ya kara su!
Wani irin ajiyar zuciya Senate ya sauke, ya dur™ushe a wurin yana kuka, amma wannan karon kukan daWi ne. "Umma! Ta haifu! Alhamdulillah!"
Legendspen
08129553971
HASASHEN SOYAYYA (BOOK 2)
By
Sayyid Legendspen
Amanar-Janafty
Shafi na Hamsin da tara
(59)
Ba a jima ba, sai ga wata nurse ta fito tana murmushi, Wauke da wata kyakkyawar jaririya da aka naWe a cikin farin kyalle. "Masha Allah, an sami mace kyakkyawa. Jaririya tana cikin ™oshin lafiya."
Senate ya mi™e ya karSi 'yarsa. Tana kuka, amma ganinsa ya sanya ta yin shiru kamar ta san kowaye shi. Ya sunbaci goshinta, hawaye yana zuba a fuskarsa. "Masha Allah... kyakkyawa ce kamar mahaifiyarta."
Amma murnar tasa ba ta dore ba lokacin da ya ga nurse Win ta koma ciki da gudu ba tare da ta ce masa komai game da halin da Bhatool take ciki ba. Ya kalli Umma, sai ya ga ita ma fuskarta ta sauya.
"Nurse! Bhatool fa? Inna mahaifiyarta?" Senate ya kwala kira, amma ba wanda ya saurare sa.
Daga cikin Wakin, sai aka fara jin sautin injina da gaggawar likitoci. Senate ya ji wani irin sanyi ya ziyarci ™afafunsa, ya kalli 'yarsa dake hannunsa, ya ji wani irin tsoro ya ziyarci zuciyarsa, tsoron cewa wannan jaririyar ita ce kyautar da Bhatool ta bar masa kafin ta tafi.
Bayan kusan mintuna ashirin da haihuwa, likitan ya fito yana goge gumi, ya kalli Senate cikin wani yanayi na tausayawa. "Alhaji, tana son ganinka. Amma don Allah ka daure, karka nuna mata damuwarka."
Senate ya mika wa Umma jaririyar, ya shiga dakin jikinsa a sandarare. Ya iske Bhatool kwance, fuskarta ta yi fari sol, numfashinta yana fita da kyar, amma idanunta suna nemansa. Ya karasa kusa da ita, ya kama hannunta wanda ya riga ya fara yin sanyi.
"Bhatool... gashi nan kin tashi lafiya, kin kawo mana kyauta," ya fada yana kokarin hadiye kukan dake taso masa.
Bhatool ta yi wani raunannen murmushi, ta kalli Senate cikin ido. "Usman... lokaci na ya kusa... ina jin sa a jikina. Ina son ka sani cewa ina sonka sosai, na yafe maka komai..."
"A'a Bhatool, karki ce haka, zaki tashi, zaki warke mu raini 'yarmu tare," Senate ya fada yana kuka, hawayensa suna digawa a kan hannun Bhatool.
Bhatool ta girgiza kanta a hankali. "A'a Usman... ka saurare ni. Ina son ka kula mini da 'yata... Ka bawa Umma ko Abdul su rike mini ita, nasan za su so ta yadda nake so. Ka gaya wa Yaya Karima ina son ta, na gode da kula da ni da kuka yi... na gode da gatan da kuka nuna mini."
Ta danyi shiru tana neman numfashi, sannan ta ci gaba. "Ka gaya wa Abdul ina son shi sosai, ina masa fatan alheri a rayuwarsa da sabon aurenshi. Kowa ya yafe mini..."
"Bhatool kiyi hakuri don Allah, zaki warke, muna bukatar ki," Senate ya fada yana kukan dake cin rai, ya kankame hannunta tamkar hakan zai hana ranta fita.
Bhatool ta kara matse hannunsa da sauran karfin dake jikinta. "Usman... karka damu. Na tafi ina mai farin cikin cewa na bar maka gurbin da zai dinga tunatar da kai ni. Ka kira sunan Allah a kunne na..."
A lokacin ne Umma da Abdul suka shigo dakin. Abdul ya iske kanwarsa a wannan halin, ya durkushe a gefen gadon yana kuka. Bhatool ta kalli Abdul, ta yi masa wani kallo na karshe dake nuna tsantsar soyayya da fatan alheri.
Dakin ya cika da kuka, yayin da Senate ya fara karanto mata kalmar Shahada a kunne, muryarsa tana daukewa saboda zafin rai. Bhatool ta bi shi, tana motsa bakinta a hankali, idanunta suka fara lumshewa yayin da wani irin sanyi ya ziyarci dakin.
"La'ilaha illallahu..."
Wannan ita ce kalmar ™arshe da ta fita daga bakin Bhatool, tare da wani sanyayyan numfashi wanda ya fita bai sake dawowa ba. Hannunta dake ma™ale da na Senate ya saki, idanunta suka lumshe tamkar mai bacci, fuskarta kuma ta bayyana wani irin haske.
"Bhatool?" Senate ya kira sunanta, muryarsa tana rawa. "Bhatool don Allah ki buWe idonki. Gashi 'yarki tana kuka tana nemanki!"
Shiru! Babu amsa.
Abdul wanda yake du™e a gefen gadon, ya Waga hannun ™anwarsa ya ji shi tamkar auduga, babu sauran dumi. Wani irin ihu mai ban tausayi Abdul ya fasa, ya Wora hannunsa a ka. "Bhatool! Don Allah karki tafi ki bar mu! Wayyo ™anwata!"
Daidai nan, Yaya Karima ta faWo Wakin a guje, tana iske wannan yanayin, ta saki wani uban kuka ta zube a ™asa tana kiran sunan Allah. "Bhatool! Yanzu duk gatan da muka yi miki ashe na bankwana ne? Ashe dukan wahalar da kika sha a baya kika jure, ashe domin ki tafi ne yanzu?"
Asibitin ya ruWe da kuke kuke. Masu jinya ma kansu sun kasa daurewa, domin kowa ya shaida yadda Bhatool ta yi gwagwarmaya da rayuwa. Senate kuwa, ya kasa kuka, ya kasa magana. Ya kafe gawar Bhatool da ido, yana tunawa da hirar da suka yi a falon Umma mako guda da ya wuce. Ya tuno al™awarin da ya yi mata na cewa za su raini 'yarsu tare.
"Kin tafi kin bar ni da wannan nauyin, Bhatool," ya faWa a cikin ransa, yayin da wani irin daci ya ziyarci ma™ogwaronsa.
Umma kuwa, tana can a kusurwa, ta ™an™ame jaririyar a ™irjinta, hawayenta yana zuba a kan fuskar jaririyar. Jaririyar kuma ta fara kuka mai ™arfi, tamkar tana kiran mahaifiyarta dake kwance shame-shame, wadda ba za ta sake amsa kiran kowa ba har abada.
Wannan rana ta kasance ba™ar rana ga masoyan Senate da Bhatool. Mutuwar Bhatool ta zama wani babban darasi dake nuna cewa rayuwa ba ta da tabbas, kuma nadama takan zo ne a lokacin da gyara ba shi da amfani.
An fito da gawar Bhatool daga Wakin haihuwa, aka naWe ta a farin kyalle. Senate ya bi bayanta da kallo, yana jin tamkar ™ashin bayan rayuwarsa ne aka fitar da shi. Ya kalli Abdul dake kuka tamkar ransa zai fita, ya fahimci cewa wannan raunin ba na mutum Waya ba ne; rauni ne da zai dade yana raWadi a zukatan kowa.
Labarin mutuwar Bhatool ya karaWe garin Yobe tamkar wutar daji, musamman yadda kowa ya san wahalhalun da ta sha da kuma yadda yanzu take dab da samun natsuwa. Gidan Umma ya cika ya batse, mutane sun kasa gaskata abin da suke ji.
A gefe guda na falon, kawayen Bhatool na kusa da na nesa sun hallara, kowacce ka kalla fuskarta ta kumbura saboda kuka. Jannah dake kwance a kasa, kuka take yi tana kiran sunan Bhatool, tana tunawa da yadda suka yi biki kwanan nan.
Amrah kuwa, wadda take jin nauyin abin da ta yi wa Bhatool a baya, kukan nadama da tausayi ne ya cika ta tana jin kamar ba ta sami isasshen lokacin da za ta nuna wa Bhatool soyayya ba kafin wannan ranar.
Haka Suhaima ma, kuka kawai take yi. Gaggo Larai, Furee, da Habi, duk sun shiga wani irin tashin hankali. Kowa yana tuna wata hira ko wata hidima da Bhatool ta yi musu. "Bhatool ba mace bace mai rikon mutum, mace ce mai hakuri," in ji Habi cikin shesshekar kuka. Shuru ya mamaye falon duk lokacin da aka kalli jaririyar dake hannun Umma, wadda kukan ta ya ki tsayawa tamkar tana kiran mahaifiyarta.
Karfe biyu na rana aka shirya janizar Bhatool. Kowa ya hallara a babban masallacin dake layinsu Bhatool. Abdul yana tsaye, kansa a kasa, hawaye yana zuba a fuskarsa ba kakkautawa. Ahmad ma yana can a gefe, zuciyarsa tana tafasa da tausayin wannan baiwar Allah da kuma kaddarar dake tattare da ita.
Senate kuwa, tun asuba rabon sa da magana. Yana tsaye kusa da gawar Bhatool lokacin da aka sauke ta don yin salla. Ya dube ta a cikin makara, an nada ta a cikin farin kyalle, fuskar nan ta ta mai kyau yanzu babu sauran numfashi. A nan ne Senate ya ji cewa lallai rayuwarsa ta sauya har abada.
"Allahu Akbar!" Muryar liman ta karaWe ko ina.
Bayan an gama salla, aka dauki gawar zuwa makabarta. Nan fa kuka ya dawo sabo