← Book details Hasashen Soyayya Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 37 OF 51

Sashe 37

Hasashen Soyayya Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

"Tun ranar da na fara ganinsa a gidansa naji a jikkna kamar nasan shi, kwanaki da muka zuana a gidan ni da Senate, na shiga babban falonsa kai masa fruit da Mom tasa Senate shi kuma yasani, log book Winsa dake kan table na bude hoton Umma ne a farko amma tun ba ta kai shekaruna ba, sao dgaa baya ma na yu tunanin yana sane yasa naga hoton sabida na fahimci komai."

"Ikon Allah." Yaya karima ta faWa, Abdul kam cewa ya yi. "To sai mene, a yanzu dai yasan baza ta taSa auren sa ba." 

"Abduk kai yaro ne bakasan soyayya ba, kai nufinka hawayen da ka ga Umma na yi na mene idan ba na soyayya ba." Bhatool ta faWa. "Nine yaron dan ubanki abinda nasani baki sani ba."

"Dan Allah ku bar wannan maganar haka, ni hankalina yana kan mutuwar auren Bhatool." 

"Wallahi ni Yaya mamaki abun yake bani fa." Abdul ya faWa. "Ni kaina haka me yake damun Senate." 

"Yaya ba abin mamaki ba ne idan kika duba hotonan da ya turumun." 

"Wanne hotona?."

"Shi yasa na tambaya ina wayata, hoto ne a zaune cafteria kuma asalin hoton ni da Jannah da Amrah ne, amma aka yanke su, sanan wani kuma  ina rungume da namiji." 

"Rungume kuma, innullahi wainna illahir raji'un." Yaya karima tafaWa, Abdul kama ta shi ya yi ya fice. "Ina zaka?."

"Zanje na Wakko wayarta ta ne." 

"Eyh yakamata kam." Kuka Bhatool ta fashe da shi, gaba Waya abun ya dawo ma ta sabo, wane irim abu ne haka me aka shirya ma ta haka. 

"Ki yi hakuri Bhatool, komai zai zo da sau™i." 

"Yaya me na yi haka, waye yake son kashen aure haka?." 

"Koma wane komai zai bayyana in sha Allah."

*****

Amrah ce zaune kan gadon Wakinta wayarta na ri™e a hannu ta kara ta a kunne. "Salamu alaikum." Ta faWa bayan an Waga wayar, bayan amsa ne ta ce. "Anty aiki ya cika, Senate ya saki Bhatool." 

Mun dawo bayan sallah, littafi ya kusa kammala, ina fatan kunyi sallah lafiya, Allah Ya maimaita mana ya kuma sa munyi ibada karSaSSiya. 

Legendspen

08129553971.

HASASHEN SOYAYYA (BOOK 2)

By

Sayyid Legendspen

Amanar-Janafty

Shafi na Arba'in da biyu (42)

Amrah ce zaune kan gadon Wakinta wayarta na ri™e a hannu ta kara ta a kunne. "Salamu alaikum." Ta faWa bayan an Waga wayar, bayan amsa ne ta ce. "Anty aiki ya cika, Senate ya saki Bhatool."  Shiru ta yi na 'yan mintuna sannan ta ce. "Anty ya nawa sa™on." 

"Zakiji ni." Matar ta faWa, Amrah ta yi wani murmushin jindaWi, Bayan kusan mintuna talatin da amsa kiran "Anty", Amrah ta zauna a gefen gado tana duba wayarta, zuciyarta fara ™al , idanunta kawai zaka kalla ga wani irin farin cikin da ba za a iya misalta shi ba. Ta dade tana jiran wannan ranar, ranar da za ta ga rugujewar auren Bhatool. A ganinta, Bhatool ba ta dace da Senate ba, kuma ba ta dace da dukiyar da take ciki ba. 

"Ke wacece da zaki mallaki zuciyar Senate, mutumin da tun ranar da na fara ganinshi a makaranta ya mallake zuciyata?" Ta fada kasa-kasa tana huci.

Wayarta ce ta sake yin ruri alamun sa™o ya shigo, ta Wauka ta duba ta ga sunnan Jannah.

"Amrah, ina kike? Na ji labari wai Bhatool ba ta da lafiya tana asibiti, kuma na kira wayarta ba ta shiga, kina ina kizo muje ki kirani, idan na kiraki ba ta tafiya."

Tsaki Amrah ta ja, ta watsar da wayar gefe. "Ke dai nan kika sani Jannah, baki san sauran ba. Ai yanzu an wuce wurin jinya, gidan miji ne aka raba ta dashi daman ba na ta ba ne." Ta sake murmushin mugunta, ta tashi ta nufi banWaki tana jin kanta kamar wata da ta ci nasara a babban ya™i.

A can gidan Yaya Karima kuwa, dakin ya yi tsit, Bhatool ce kawai ke kuka sama sama, wanda yake fitowa a hankali. Yaya Karima tana zaune gefenta tana shafa mata baya, amma ita kanta Yaya Kariman zuciyarta ba daWi.

"Bhatool, dakata da kukan nan haka. Kin san fa kina da juna biyu, kuma likita ya ce kina bu™atar hutu." Yaya Karima ta faWa cikin muryar lallashi.

"Yaya, ta yaya zan yi shiru, wani irin hutu kuma? Ta yaya zuciyata za ta samu natsuwa bayan anyi mini ™azafi a wajen mijina. An zubar mun da mutuncina? Senate ya kira ni 'munafuka', 'muguwa', sannan ya ce bai yafe mini hakkinsa ba. Me na yi masa Karima? Me na yi wa Senate?"

"Kiyi hakuri, kishi ne ya rufe masa idanu. Amma babban abin dubawa a nan shi ne. Waye ya dauki hotunan nan? Kuma waye ya tura masa? Kinsan Senate yana Abuja, wani ne yake leSe dake a yake kai masa rahoto."

"Yaya baki ga hoton ba fa, har da wanda nake rungume da namiji da zallunci." 

Bhatool ta share hawayenta, ta tashi zaune da kyar. "Yaya, kin san abin da nake tunawa? Ranar da muka je cafeteria da Amrah da Jannah. A ranar ne kawai na sanya wannan lace Win da aka nuna a hoton, sai dai kuma Amrah da na arawa lace din ta je biki dashi, kuma ma ta ce bata saba sabida ta yi ankon." 

Yaya Karima ta zuba wa Bhatool ido. "Amrah? Bhatool, kina nufin Amrah ta ari kayanki?"

"Kwarai kuwa Yaya, kuma ranar tare muka je cafteria ita da Jannah ne kawayen da nake tare da su."

Shiru dakin ya sake yin, kowacce cikinsu tana juya tunani a ranta. Yaya Karima tana son halin Amrah tun a lokacin bikin Bhatool, ta ga yanayinta kamar mace ce mai son kai, amma ba ta taSa tunanin za ta iya kaiwa ga ruguza auren kawarta ba.

A Abuja kuwa, Senate yana zaune a cikin dakin hotel dinsa, dakin ya yi kaca-kaca da takardu da rabobin ruwa da ya watsar. Gaba daya aikin da ya kai shi ya fice masa a kai. Duk lokacin da ya rufe idonsa, hoton Bhatool yake gani tana murmushi, amma sai hoton da aka turo masa ya dishasha wannan murmushin.

Anas ne ya shigo dakin, ya dade yana bugawa ba a bude ba, sai da ya sanya ma'aikatan hotel din suka bude masa. "Senate! Me kake yi haka? Ka duba kanka kuwa?"

Senate bai dago ba, muryarsa ta fito a shake. "Anas, na sake ta. Na raba kaina da ita."

"Kayi hauka ne? Saki? Akan hoton da baka tabbatar da gaskiyarsa ba? senate, kasan fa makiya suna da yawa. Kasan yadda kake da kudi da daukaka, mutane da dama ba sa son ganin ka rasa afarin cikinka."

"Anas, hoton fa na gani da idona. Tana sanye da lace din da na saya mata, lace din da na kwaso mata da kaina daga gida. Ta yaya zan karyata abin da idona ya gani?"

"To amma baka ga fuskar namijin ba, kuma baka ga babu fuskar macen a jikin namijin ba. Me zai hana ka jira ka dawo? Me yasa ka yi gaggawa?"

Senate ya tashi tsaye, idanunsa sun yi jawur. "Saboda ina son ta Anas! Ina son ta fiye da yadda kake tunani. Zafin soyayyar ne ya sa nake jin kamar ana huda zuciyata da mashi. Ba zan iya jure ganin wani namiji ya taba ta ba."

"To idan ta kasance ba ita ba ce fa? Idan sharri aka yi mata fa? Usman, ka tuna tana da juna biyu. Ka taba tunanin halin da za ta shiga?"

Anas ya girgiza kai, ya san halin abokinsa idan kishi ya taba shi, baya gani baya ji. Ya juya zai fita, sai ya tsaya ya ce, "Mom ta dade tana kiran wayarka ka ki dagawa. Tana can asibiti wurin Bhatool. Idan kana son kanka da alheri, ka kira mahaifiyarka."

Can gidan Dad kuwa, Mom ta samu Dad a daki zaune yana kallon wani tsohon hoto. Tunda suka bar asibiti Dad ya shige daki ya ki fitowa, har abincin dare ma cewa ya yi ba ya bukatar sa.

Mom ta karasa kusa da shi, muryarta a sanyaye. 

"Alhaji, mene ne tsakaninka da Maman Bhatool? Na ga yadda kuka rude lokacin da kuka hada ido."

Dad ya sauke ajiyar zuciya mai nauyi, ya mika mata hoton dake hannunsa. Hoton Umma ne tun tana budurwa, tana murmushi dauke da littattafai a hannunta. "A'isha, wannan ita ce 'First Love' dina da nake fada miki. Wannan ita ce Habiba da na shafe shekaru ina nema, wadda nake tunanin ta rasu."

Mom ta ja numfashi, ta zauna a gefen gado. "Kace min mahaifiyar sirikarka ita ce macen da kake so ka aura?"

"Ban sani ba Zainab. Ban taba sanin cewa diyar Habiba ce Usman ya aura ba. Sai yau da na ganta a asibiti, na ga kamaninta da Habiba suka kasance daya. Tabbas, Habiba ita ce rayuwata ta baya, kuma har yanzu ina jin muryarta a cikin zuciyata."

"Amma Alhaji, kasan fa yanzu 'ya'yanku sun yi aure? Kasan irin sar™a™iyar da wannan zai haifar?"

"Na sani. Amma ai yanzu Usman ya sake ta, ko ba haka ba?" Dad ya tambaya yana kallon Mom.

Mom ta gyada kai cikin damuwa. "Eh, ya sake ta. Amma ina kyautata zaton akwai makirci a ciki. Alhaji, idan har kana son Habiba, kuma Usman yana son Bhatool, ta yaya zamu daidaita wannan lamarin ba tare da kowa ya ji ciwo ba?"

Dad ya yi shiru, tunaninsa ya tafi can shekaru ashirin da suka wuce, lokacin da aka raba shi da Habiba. Yanzu kuma ashe Wansa ne ke fuskantar kaddara irin tasa?

Abdul ne ya shigo Wakin fuskarsa babu fara'a. Su Bhatool na ganin shi suka mi™e. "Lafiyanka Abdul?." Yaya karima ta tambaya. "Bhatool, na je na Wakko miki wayar taki, amma kuma naga Screen Win wayar ya fashe gaba Waya, alamar ya bugu ne lokacin da kika yanke jiki kika faWi."

Bhatool ta kalli wayar, ta ji wani sabon takaici. "Abdul, dan Allah ka kai mini gidan gyara, ina son ganin hotunan da ya tura mini, ina son sanin yadda aka kulla mini wannan makircin."

"Karki damu, yanzu zan kai ta kasuwa a gyara screen Win, kafin nan ki kwanta ki huta," Abdul ya faWa tare da ficewa da wayar a hannunsa.

"Bhatool na tambaye ki mana." Yaya karima ta faWa. "Ina jinki Yaya?." 
Chapter 37 · 0% Book details