← Book details Hasashen Soyayya Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 29 OF 51

Sashe 29

Hasashen Soyayya Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Tun Mom na jiran kiran Senate har tagaji ta kirashi, ta yi matu™ar mamakin ganin taki kirashi bai Wauka na, hakan yasa ta yi masa na biyu shima bai Waga ba, wasa-wasa sai gashi ta masa kira goma bai Waga ba nan-da-nan hankalinta shi ya ta shi, ta mayar da kiranta ga Anas. Anas kuna tare da Senate?. Ta faWa bayan ya Waga wayar. No Mom. Ya bata amsa. Kana ina yanzu?, je gidansa ka dubamun shi.  

Okay Mom. Ya faWa tare da saita motarsa zuwa hanyar gidan Senate, dai-dai lokacin kuma Yaya Karima ta kira ta. Karima ta zo?.  

A a Momi ba ta zo ba wallahi, yanzu Umma ma ta ce ba ta zo ba.  

Innullahi me yake faruwa da yaran nan, shima kinga senate Win wayarshi baya Wagawa tun Wazu.  

Ya salam, To ko dai naje gidan nasu nagani?.  

Na tura Anas ya tafi.  

Innullahi, bara natura Abdul. Yaya karima ta faWa sanan ta kashe wayar, ta shiga lalubar ta Abdul. Bugu Waya ya Wauka da faWin. Yaya Karima yanzu Umma ke cemun wai Bhatool ba ta gidanta.  

Eyh wallahi Abdul, mijinma kaga ana kiran wayarsa baya Wagawa ko zakaje gidan nasu ne?.

Yanzu abinda Umma ta faWamun kenan.  

To katashi kaje, duk yadda akayi kafaWamun kafin ka fara faWa mata.  

Toh shikenan.   Ya faWa tare da kashe wayar, motarsa ya Wauka ya nufi gidan Bhatool Win sai dai a bakin gate yaco karo da Anas, fitowa ya yi daga motarsa suka yi musabaha sanan ya ce. Suna ciki?.  

Basa ciki fa, yanzu ma naga wayarshi a ciki da tarin Missed calls ni ina tsorom ma faWawa Mom.  

Itama Bhatool Win wayarta tana ciki, tun da idan an kira bata Wauka mu shiga aduba. Abdul ya faWa. Okay mu shiga.  

Wayar Abdul ya fara kira tun da suka shiga gidan, can suka juyo ™arar ta a cikin bedroom, ita ma da tarin missed calls sosai, Anas ne ya kalli Abdul sanan ya ce. Me kake tunani?.  

Ni wallahi duk kaina ya kulle, amma an ce Bhatool Win ce ta fara fita, ina tunanin shi bai yi nisa ba ya shiga Anguwa dubawa ko zai ganta.  

To mu ta shi mu shiga Anguwan muma. Anas ya faWa, Abdul ya ta shi suka shiga zaga Anguwan. Kana ganin ba zamu fara tambaya ba?. Abdul ya faWa ganin sun zaga Anguwan sosai. Mu fara, amma wanan abun na Bhatool ne. Ya faWa yana tsugunnawa ™asa, braclet ya Wakko wanda yasan ya™in da sukayi da Bhatool a kan shi. Mu tsaya anan muyi tambaya to. Anas ya faWa. Wa zamu tambaya ko ina babu mutane.  

Bayin Allah lafiya. Mai gadin da ya yi wa su Senate magana Wazu ya faWa. Dan Allah Baba muna cigiyar yan uwan mune mata da miji, yanzu anan mukaga abun hannun matar.  

Ayyah, Wazu macen ta tawo tana kuka shi kuma mijin na binta a baya, cikin rashin sa a yaro ya fito daga gidan da kuke tsaye a mota ya buge matar, amma sun tafi kai ta asibiti.  

Innullahi, Baba wani asibiti?. Abdul ya faWa kamar zai yi kuka. Nima bana ce ba, amma nasan asibiti mafi kusa zasu je.  

Wanne ne mafi kusan?. Anas ya faWa. Akwai wani a farkon Anguwan nan. Abdul calm down, everything will be okay. Anas ya faWa ya taSa Abdul ganin ya shiga damuwa sosai. Bhatool fa amanace a hannuna. Abdul ya faWa ™walla na zubowa daga idonsa. Ka yi ha™uri kazo muje mu duba. A hankali ya fara tafiya yana bin Anas a baya har suka isa inda motar Abdul Win take, kasancewar ta Anas na cikin gidan. Ina key Win ka?. Anas ya tambayeshi, hannu yasa a aljihu ya fito da shi ya mi™a mai. 

A hankali Anas ke jan motar, zuciyarsa cike da tunanin me ya faru da Bhatool da Senate har ya kai ga ta fito waje yana binta, a haka suka ™arasa asibitin. Mu fara duba emergency. Anas ya faWa, bayan sun fito daga motar. Tom. kawai Abdul ya faWa suka nufi emergency Win, dai-dai lokacin da Likitan ya mi™ama Senate wayar da ya tambayeshi. 

Senate!. Anas ya kira sunanshi, juyowa Senate ya yi kalleshi a take ya mi™a ma Likitan wayar tare da cewa. Thanks you.  

You re welcome. Likitan ya faWa tare da hucewa. How is she?. Abdul ya faWawa likitan. Tana cikin ™oshin lafiya. Likitan ya faWa. Me yasa me ta?.  

Kai kuma mene ala™anka da ita?. Likitan ya tambaya, dam shi abun ya fara Waure masa kai, wan can ya ce mijinta ne, wan can ya ce shi ya bugeta. Šan-uwanta ne na jini, yayanta ne.  

Okay bata da wani rauni sosai, hasali ma bugewar bai wani taSa ta ba daman dai tun farko tana cikin damuwa ne.  

Damuwa kuma wane kala?.  

Wanan mijinta zaka tambaya kuma. Likitan ya ba shi amsa tare da hucewa. Waje Abdul ya samu ya zauna, dai-dai lokacin da wayarsa ta fara ringi.

Sai da ya fara sai ta nutsuwarsa, sanan ya Waga wayar da faWin. Umma anganta suna tare da mijin. Ajiyar zuciya Umma ta sauke sanan ta ce. Kai Alhamdulillah, ba ni ita.

Legendspen

08129553971

*HASASHEN SOYAYYA*d'þ
=Ø%Ý>ØyÝ

_Imagination of love_

    _Stroy and written_

             By

   Sayyid (Legend's pen)


   *FUTURE WRITERS ASSOCIATION*

*(FUWA)=Ø‹Ýþ=ØÚÜ*

    *The Fearless Writers Team*

  _Marubuta masu tsage gaskiyya_

*BISMILLAHI RAHAMANIN RAHIM =ØOÞ=Ø«Ü*

_Page 34_

*HASASHEN SOYAYYA*d'þ
=Ø%Ý>ØyÝ

_Imagination of love_

    _Stroy and written_

             By

   Sayyid (Legend's pen)


   *FUTURE WRITERS ASSOCIATION*

*(FUWA)=Ø‹Ýþ=ØÚÜ*

    *The Fearless Writers Team*

  _Marubuta masu tsage gaskiyya_

*BISMILLAHI RAHAMANIN RAHIM =ØOÞ=Ø«Ü*

_Page 34_

"Umma na fito waje zan kira ku kenan kika kira, bara na fara kiran Yaya na faWa mata duk ta damu, sai in shiga gidan." 

"Hakane kuma Abdul kira ta, Allah Ya yi muku albarka." 

"Amin ya Allah Umma." Ya faWa tare da kashe wayar, sao da ya goge ™wallan da ta sakko daga idonsa sanan ya tafi kiran Yaya Karima, kamar jira take kiran ya shigo dan bai gama ringi va ta Wauka. "Hello Abdul ya ake ciki?." 

"Yaya angansu duka." 

"Kai Alhamdulilalh, amma sai na ci uban Bhatool wallahi, duk ta wahalal damu." 

"Yaya tana asibiti." Ya faWa kamar zai yi kuka. "Bangane asibiti ba, me take yi?." 

"Yaya wai motane ya bige ta." 

"Innullahi wa'ina illahir raji'un garin Yaya kuma, ya salam." Ta faWa tana kuka. "Nima bans sani ba Yaya amma alamun sun nuna matsala suka samu." 

"Eyh matsala suka samu tun safe ta faWamun, yanzu wani asibiti kuke?." 

"Zan tura miki live location ki duba, danni ma ban sani ba." 

"Turumun yanzu, bara nasa ya kawo ni."  

"Sannu bawan Allah." Abdul yaji an faWa, Wagowa ya yi yaga wane. "Nine na buge ™anwarka, nazo hucewa yanzu naga kana waya."  Mi™ewa Abdul ya yi sanan ya ce. "Garin ya haka ta faru Wan-uwa?." 

"Wallahi bisa tsautsayi, ta tawo da gudu ne shi kuma wan can yana binta a baya, na yi duk ™o™arina amma haka Allah ya ™adddara." 

"Waye yake binta kuma?." 

"Wan can mana da ya ce Mijinta ne." Ya faWa yana nuna Senate. "Eyh Mijinta ne." Abdul ya faWa. "Gashi wanan na yi payment na duk kuWin da suka caza, sanan na ™ara musu dubu Wari biyu ko zasu bu™aci wani ™arin, zaka samun lambarka anan, zan dinga taSa akai-akai in sha Allahu, yanzu zanje Wakko mahaifina a filin jirgi ne." 

"Ayyah ka bar shi kawai, hakan ma da ka yi mun gode sosai da sosai." 

"A'a baza a yi haka ba Wan uwa, kasamun dai lambar taka sanan Sunana Ahmad." Ya faWa yana mi™ama Abdul waya, amsa ya yi ya rubuta mai lambar sanan ya ce. "Sunana Abdul." 

"Na gode, Allah yabata lafiya." 

"Amin ya Allah." Abdul ya faWa. 

"Kagani ko Anas, wanan gayen akwai wani abu a ransa." Senate ya faWa yana kallonsu. "Wane abu ne a ransa wai, mutumin da ya yi muku wanan abun kake cewa haka." 

"To shi Abdul Win mene zai kulashi, har ya ba shi lambarsa." 

"Kaga Senate bazan iya da wanan abun naka ba, gaka ga Abdul Winan kaje ka tambayeshi mana." Anas ya faWa yana kiran lambar Mom. "Ban ce ka yi mun rashin kunya ba." Banza dai Anas ya yi masa ya mayar da hankali ga kiran Mom, sai da ya kira sau uku sanan ta Wauka. "Anas na yi salla ne, kun gan su." 

"Eyh Mom, gamu a asibiti wai mota ta buge Bhatool Win." 

"Ya salam! Garin ya kuma." 

"Wallahi banda masaniya." 

"Turamun location Win inda kuke, gani nan."

"Tom." Ya faWa tare da tura mata, zama suka yi jingun-jigun kusa mintuna goma sha biyar sanan Senate ya ce. "Ban card Winka, zan ayi payment." Mi™a mai ya yi ba tare da ya ce ko ™ala ba, shi kuma ya amsa ya huce wajen biyan kuWin. "I'm sorry sir, your payment is already done." Abinda ma'aikaciyar wajen ta faWa kenan. "Banagne ba, who paid it?." 

"Someones named Ahamd." Ta faWa, tsaki ya yi sanan yabar wajen ya koma ciki, lokacin Abdul ya tashi zai shigo da Yaya Karima da mijinta. "Abdul, me wan can gayen ya ce da kai?." Senate ya tambayeshi. "Nothing, kawai ya ce shi ya bugeta ya bada hakuri, sanan ya ce ya yi payment har ma da extra kuWi ya bari." 

"Mun ce mushi muna bu™ata ne?."Ya faWa a fusace. "˜ila yaga kun yi kala da masu bu™atar ne." Abdul Win ya bashi amsa ya huce, tun da dai yaga ba ubansa ba ne shi dai zai zo yana mai tsawa, Senate kamar ya haWiye zuciya haka ya ji. "Me wanna yake nufi?." Ya tambayi kan shi. "Yana jin haushinka ne, a kan abinda ya sami ™anwarsa." Wani Sari daga zuciyarsa ya faWa masa. "To kuma nina ja?."Ya sake tambayar kan shi. "Ai kai ka biyo ta gudu, da kazo a nutse duk haka ba lallai ba ne ya faru." Tsaki yaja sanan ya ce. "Rubbish." Abdul kam a waje ya tarar da su Yaya Karima, kana ganin idonta zaka san ta ci Kuka ta gaji. "Ya salam Yaya mene yasaki Kuka haka?, jikin na ta fa da sau™i.  

Yanzu Abdul idan Umma ta ji ya za ta yi?. yaya Karima ta faWa. Ai baza ta ji ba in sha Allah.  

Kana nufin za aSoye mata ne?.  
Chapter 29 · 0% Book details