← Book details Hasashen Soyayya Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 35 OF 51

Sashe 35

Hasashen Soyayya Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

"Ya salam, Wakko ta ku shigo."  Kamar wanu dutse haka Senate ya ji nauyinta, kamar ba ita ya Wakko daga gidan Yaya Karima har zuwa gidan Momi ba a hannusa. Da™yar ya kai ta Wakin, Umma ta ce dubu waccan akwatin ta saman sif, akwai zamzam a ciki ka mi™o mun. "Tom." Ya faWa tare da mi™ewa, ya kusa minti biyar yana dubawa kafin ya ganshi ya mi™o ma ta. Bayan ta yi addu'o'i ta shafa ma ta, a hankali ta fara sauke ajiyar zuciyar sannan ta buWe idonta. "Sannu Bhatool!." Senate ya faWa, gyaWa ma sa kai ta yi sannan Umma ta ce. "Ya jikin na ki?."

"Da sau™i Umma."

"Ku tashi ku tafi gida, ta na bu™atar hutu." UmSa ta faWa. "Dan Allah Umma na huta anan." Bhatool ta faWa kamar za ta yi kuka, dai dai lokacin wayar Senate ta fara ringing. "Ina zuwa Umma." Ya faWa yana mi™ew ya fita. "Hello Anas." Daga can Anas ya amsa da faWin. "Na siya maka ticket Win, na yi maka booking hotel da komai."

"Okay badamuwa, gobe ne ko?."

"Eyh gobe ne, amma me yake damunka na ji ka haka?."

"Ashe Bhatool na da ciki, kuma ka ga yanzu munzo gidan su kawai ta yanke jiki ta faWi."

"Ya salam! Kuna asibiti?."

"A'a ta farfaWo, ina tunanin ko zan barta gidansu zuwa na dawo."

"Eyh hakan ya yi sosai da sosai, amma ka faWa ma Mom."

"Okay." Ya faWa tare da kashe wayar ya kira Mom, tana zaune abin duniya duk ya isheta ta Waga wayar. "Son ya aka yi?."

"Mom munxo gida Bhatool za ta gaida Umma ta yanke jiki ta faWi."

"Ya salam! Kuna ina yanzu?."

"Muna gidansu, komai ya yi sau™i."

"Allah Ya ™ara sau™i."

"Amin-amin, daman zancen tafiyar nan ne."

"Gobe ne ko?."

"Eyh, na ce ko barin ta zan yi a gidansu?."

"Eyh, hakan ya yi, sai ka je gida ka Wakko mata kayanta, sannan idan ta ji sau™i ta fara zuwa makaranta."

"Tom shikenan Mom." Ya faWa tare da kashe wayar, bai koma gidan na su ba ya hau mota ya nifi gida, Wakin ta ya shiga ya hau haWo ma ta kaya, wayanda ya gani a cikin akwati, wayanda duk rabi na lefen ta ne ba ta ma da niyar sa su yanzu ya Webo ma ta, mayafai kam bai tsaya ya ga sun yi kala da kayan ba ko ba su yi ba ya Webo ma ta haka takalma, wani lace Win ta ya gani, yana son wannan lace Win tun da Mom ta nuna mai lokacin da ake haWa kayan lefenta, Waga shi ya yi yaga Winkin da aka yi ma ta. "So Ma shaa Allah." Ya faWa yana hango yadda Bhatool za ta yi kyau da shi. Haka ya haWa kayan ya fitowa ya sa su a mota ya tawo.

Mom na gama waya sa Senate ta kira Yayarta, Maman Anas. "Hello Yaya."

"Lafiyanki wai n ji muryar ki a haka?."

"Bakomai Yaya." Mom ta faWa. "Wane abu ya faru ne?." Mom ta sake faWa. "A'a naji muryarki kamar da damuwa."

"Oh! Wai matar Senate ce fa faWi a gidansu, ni Allah Yasa ma cikin bai sami matsala ba, yanzu dai na ce ya barta gidan nasu tunda shi zashi Abuja ya yi sati Waya."

"Eyh hakan ya yi kam, Allah Ya sawa™e."

"Amin, Amin." Daga nan suka shiga hirarsu.

Bhatool kam Kam Senate na fita ta kalli Umma ta ce da ita. "Umma dan Allah ko kwana Waya ne."

"Bhatool kin san dai ba zance da mijinki ya barki anan ba ko?, idan ya ga dama ya barki shikenan, idan kuma ya ce ku tafi shikenan." TaSe fuska ta yi tare da kawar da kai gefe ta kwanta. Kusan mintuna 20 babu senate babu alamunsa. "Umma kinga bai dawo ba."

"Ko ya barki anan ne?."

"Idan yabar ni ai zai faWamun."

"Ko yabarki zuwa ya je aiki ya dawo."

"Shima ya sani." Bhatool ta faWa tare da komawa ta kwanta, ba ta daWe da kwanciya ba ya shigo gidan, hannushi ri™e da akwati. Wani daWi Bhatool ta ji, sai dai kuma taji wani irin tsoro kar fa ya ce sakinta ya yi. Da ido ta bi shi har ya zauna. "Umma daman zanje Abuja, to na yi niyar nabarta ta zauna a can gidan namu, amma wannan abun da ya faru ya naga ya fi dacewa ta xauna anan, zuwa na dawo."

"Tom Allah Ya kai ka lafiya, ya dawo da kai lafiya."

"Amin Umma." Ya amsa dai dai lokacin da Umma ta ta shi ta fice. "Bhatool." Ya kira sunanta. "Na'am." Ta amsa kamar za ta yi kuka. "Babu matsala ko?."

"Me yasa baka faWamun zaka yi tafiya ba?."

"Ki yi hakuri, nima tafiyar ban so ma ta ba, amma ai kina tare da Umma babu abinda zai dame ki, ko missing Wina ba za ki yi ba."

"Ga shi tun yanzu na fara missing Winka, yaushe zaka dawo."

"Sati Waya ne cif, sannnan idan kin ji daWin jikin ki, zaki iya zuwa makaranta."

"Har sati Waya." Ta faWa tana goge idonta. "kina fa tare da Umma."

"Ni dai kawai ka tafi da ni."

"Ai baki da lafiya." Shiru ta yi ba ta ce komai ba, ya taso inda take ya ri™e hannunta. "Take care please, kin san kina da Baby."

"Take care too." Haka suka yi ta musayr kalaman soyayya, wayanda tun da suka yi aure ba su yi irinsa ba. Anan gidan ya yi magariba sannan ya tafi gidan Momi zai kwana can gobe da sassafe ya tafi, sun yi da Bhatool xai zo kafin ya tafi.

Kusa raba dare suka yi suna waya,  Bhatool har mamakin sauyin Senate ta yi, sai kuma ta yi tunanin ko ™ila sabida cikin dake jikinta ne, haka dai ta yi bacci da tunani kala kala.  Washe gari ™arfe bakwai da rabi ya zo, a tsaitsaye suka ga gaisa sabida jirgin takwas zai bi.

Wajen ™arfe goma da rabi, Bhatool na zaune Amrah ta kira ta a waya. "Allah sarki Amrah, duk lokacin da bana jindaWi sai ta kira ni." Bhatool ta faWa a fili sannan ta Waga wayat, tana faWin. "Amrah yakike."

"Lafiya ˜alau Bhatool, ya jikin?."

"Ah! Aina kika san banda lafiya?."'

"Ke ki jiki ki, kin manta ranan nan kin ce mun bakya jindaWi."

"Laa! ai nasami sau™i, yanzu ma dai gani a gida ya tafi Abuja zai yi sati Waya, kuma ya ce nakoma makaranta."

"Ya salam! Da fa kayan nan zan zo na amsa."

"Ai ya tawo mun da masu kyau kuwa, kizo ki xaSa kawai." Bhatool ta faWa. "Okay badamuwa."

"Ina Jannah kuwa?." Bhatool ta tambayeta. "Ni fa rabona da na kwana biyu, ta canja ™awaye fa ko a makaranta."

"Ai shi ke nan, nima dai gobe xan zo."

"Ah! Allah Ya kaimu."

"Amin, amin."

"Sai nazo." Amrah ta faWa, Bhatool kuma ta kashe wayar, tana nan zaune Abdul ta shigo hannunshi ri™e da ba™ar leda, washe baki Bhatool ta fara yi tare da faWin. "Šan Albarkan Umma, me aka samu mana?."

"Idon ma tambayi." Ya faWa yana zama. "Bamu mu ci." Mi™a ma ta ledar ya yi sannam ya ce. "Bhatool ya zaman gidan naku yake?."

"Komai yana tafiya yadda yakamata, tun da dai ance aure Wan ha™uri ne, to muna ta ha™urin dai."

"Allah Ya ™ara muki ha™uri, amma ni yanayin ki sai naga kamar ba wani daWin zaman kike ji ba, Bhatool ba fa zama a babban gida mai cike da kayan alato ba ne jindaWi, zama cikin soyayya da kulawa."

"Eyh, nasani Abdul."

"Tom Allah Ya dauwamar muku da zaman lafiya."

"Amin amin." Ta faWa tana kwance ledar, shi kuma ya ta shi ya fice. Sai yamma lis Amrah tazo gidan, suka shige Waki ita da Bhatool suka hau hira, nan Bhatool ta nuna ma ta kayan ita kuma ta zaSa, da faWin gobe kawai za ta yi amfani da shi, jibi za ta ba ta a makaranta.

Washe gari.

Bhatool da murnar zuwa makaranta ta tashi, bayan sunyi waya da Senate ya yi ma ta addu'a tare da jan kunne akan ta kula da kan ta, yanzu ita matar aure ce. Haka ta shirya cikin atamfa Super holland mai adon ja da touch din green, driver da Senate ya turu ma ta yazo Waukan ta.

Tunda driver yayi parking motar tasu wacce a wajen rubuta lamba aka rubuta *Senate* gaba Waya hankalin yan matan ya yo kan motar, driver ne ya fito daga wajen da yake tare da buWe mota ™ofar inda take zaune, hill sheo Winta ne ya fara fitowa kafin kuma ita ta fito, ai tuni wajen ya ruWe da faWin. "Fatima senate! Fatima senate!!."

*Cigaban labari*

Wani murmushi Bhatool ta saki, Allah Ya sani she miss alot from her school. Amrah ce ta tawo da gudu ta rungume ta, tana faWin. "Welcome back Bhatool." Nan da nan sauran yan ajin suka yo inda suke kowacce na cewa. "Welcome Bhatool." Cikinsu har da Jannah, da Amrah ta ce ba ta zuwa makaranta. Harara Bhatool ta makawa jannah, bayan sun ke Se su uku sannam ta ce. "Sannu Jannah, mara mutunci."

"Kai Bhatool rashin mutuncin me na yi kuma?."

"Baki zo inda nake ba kwata kwata, sai na nemi ki ke ba zaki nemi ni ba."

"Tun yaushe nake bin Amrah yaushe zamu zo sai daga baya ta ce wai ita ta zo."

"Ah to ba dole na naje ba, kullum ba a gane kan ki a school." Amrah ta faWa. "Bawani nan." Ita ma Jannah ta faWa, ita Bhatool mamakin yadda Amrah ta nuna ma ta basa tare da Jannah take, ita dai tun zuwan ta tare ta gansu, gashi yanzu ma suna hira tare. "Ai shi ke nan, yanzu me na yi missing a class."

"Oh! You missed alot, dan ma ina miki attendence, tun da Amrah ta ce mun zaki dawo na fara miki."'
Chapter 35 · 0% Book details