← Book details Hasashen Soyayya Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 42 OF 51

Sashe 42

Hasashen Soyayya Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Abu kamar wasa Ciwo ya tasarwa Mom,Yawan haki ga kuma tari, ciwon ya fara tsananta hakan ya sa Dad ya ce zasu huce ™asar india domin ganin babban likita, Mom ta hana a sanar da kowa cikin 'yan uwanta sbaida ma kar Senate ya sami labari, ga kuma Anty a gefe, shi kam Senate gaba daya ya watsar da lamarin gida da wata Bhatool, rayuwa yake baya tunawa da anyi wata mace wai ita Bhatoool, daman kuma Bokan Anty ya faWa mata indai Bhatool ta fita daga takaba Senate ko yasa ta a ido bazai taSa jin Sonta ya dawo ma sa ba, dan haka Amty tasa aka cire masa son gida da sha'awar gida har sai bayan wattanni uku, dan ita ba ta yi tunanin akwai cikim a tare da Bhatool ba. 

*****

Su Umma na zaune a falo Bhatool ta fito sanye cikin doguwar rigar atamafa, duk da ba ta yi wani hayaniya ba amma ta yi kyau, Wan ™aramin cikinta ya fara tasawa. "A'a Maman boy irin wannan kwalliya haka?." Abdul ya faWa yana washe baki ranshi fari ™al. "Kana nan zaune zan haifi kamarka." Bhatool ta faWa tare da wucewa, Umma ce ta ce. "Uwaki da baki da kunya." Dariya ta yi Ahmad kuma ya tashi. "To Umma zamuje mu dawo." 

"Ubamgiji Allah Ya tsare hanya." 

"Amin, Amin." Ahamad ya faWa, Abdul kuma ya ce." Na taso ne?."

"Duk yadda kagani." 

Daga wannan ranar fa wani sabo ya fara shiga tsakanin Bhatool da Ahamd, kamae yadda ya al™waranta duk weekend sai ya zo ya Wauki Bhatool sun fita, a yanzu damuwar dake zuciyar Bhatool ta ragu fiye da kaso saba'in cikin Wari, a hankali cikin jikinta yake ta sawa har ya shiga wata na haWu, ta ™ara kyau abinta, sannan ita kanta a yanzu ta san ta faWa cikin wata sabuwar rayuwar, ta kamo da kaunar abinda ke cikinta da kuma wata sabuwar kaunar ta Ahamd, tabbas ta a yanzu ta fara son Ahmad, ba wai kuma ta daina som Senate ba ne, amma ta yi ko™ari sosai wajen ya™i da soyyayyarsa a zahiri, dan a yanzu ko tunaninsa ma ba ta bari ta yi. 

Ahmad kam kulawarsa ga Bhatool kullum sai ™ara gaba take, Yanzu ba wai kulawar jinya yake ba mata ba, kowane mataki nasa yana nuna tsantsar ™auna ce dake tafasa a cikin zuciyarsa. Ya zama tamkar inuwar da ba ta rabuwa da ita. Duk lokacin da ya zo, sai ya sanya Bhatool ta yi farin ciki, taji daWi koda kuwa murmushin ya™e ne. Har kuma a kazo ita ma ta fara kamuwa da ™aunarsa. 

Wata rana da yamma, suna zaune a cikin motarsa bayan sun dawo daga zaga garinsu Wan kullum, da yanzu ba wai sai Weekend ba duk lokacin da yake free kawai zai zo ne su fita, wani lokacin ma harda Abdul suke fita, duk dan ganin a sanya mata farinciki. Ahmad ya kalli Bhatool wadda take wasa da yatsun hannunta. Ya nisa, sannan ya kira sunanta cikin muryar dake nuna tsantsar gaskiya.

"Bhatool, na san abubuwan da kika fuskanta sun yi miki nauyi. Na san kuma har yanzu zuciyarki tana jinin raWadin abin da ya faru. Amma ina so ki sani, tun ranar da na fara ganinki, ban taSa jin wata mace ta shiga raina kamar yadda kika yi ba. Bhatool, ina sonki. Ina son in zama silar farin cikinki na har abada, in zama mahaifi ga abin da kike Wauke da shi, in kuma share miki dukkan hawayenki idan kin ba ni dama."

Bhatool ta Wago kai tana kallonsa, idanunta suka cika da ™walla. Ba ta yi tsammanin furucin zai zo a wannan lokacin ba. Ta kasa cewa uffan, sai dai wani irin sanyi da ta ji yana ratsa ta. Furucin Ahmad ya zo mata a matsayin maganin radadin da take ji, ko da kuwa ba ta riga ta amince da soyayya baki Waya ba.

"Kuka kuma Bhatool ki yi hakuri bazan taSa miki dole ba, kowani abu da zai saki kuka."  Ta goge hawayen dake fuskarta sannan ta ce. "Bawai furucinka ya sani kuka ba, ina tuna Winbin alherinka gareni ne, Na gide sosai da dukkan abinda ka yi mini, kuma nima a shirye nake na yi rayuwa ta farin ciki da kai har Abada."

****

A Sangaren Amrah kuwa, tana cikin wani hali na nadama da kaWaici. Duk da cewa ta tona asirin komai, amma har yanzu tana jin nauyin abin da ta aikata. Tana yawan kiran wayar Bhatool don su gaisa, duk da cewa Bhatool tana amsawa ne a ta™aice, babu sauran waccan muryar ta abota da hira. Jannah ce kawai take yawan zama da Bhatool, tana ™arfafa mata gwiwa tare da raba mata damuwar da take ciki.

A yanzu Amrah dai ta canja dan hatta karatun ma ta watsar kamar yadda Bhatool ta watsar da na ta Jannah ce kawai ke zuwa makarantar, Amrah kullum cikin neman yafiya take wajen Ubangiji da Bhatool, cikin kwanaki kaWan wani bawan Allah mai rufin asiri ya fitowa Amrah, amma taki ba shi dama. Da ya matsa mata ne ma ta bashi labarin abinda ta aikata sannan ta tambayeshi cewar. "Kana ganin ya dace a aure mace mai muguwar zuciya irina?." Ya gyaWa mata kai, sannan ya ce. "Ai kin tuba, ko ubangiji muna masa laifi kuma mu tuba." 

"kana ganin kenan ya dace ni na yi aure bayan wacca na kashe mata na ta auren tana nan zaune?." 

"Shi ai aure nufine na ubangiji, kuma komai mu™addarine daga Allah." Amrah ta yi sannan ta ce. "Tom zan yi shawara." Daga haka ta shige gida, bayan ta shiga gidane ta kira Jannah a waya ta sanar da ita komai. Jannah ta ce. "To ai Amrah komai nufine na ubangiji, sannan rashin yin auren ki ba zai canja abinda ™addara ta tsara ba, ki yi addu'a idan har shi mafi alheri ne a wajenki to Allah zai tabbatar." 

"Shikenan Jannah Na gode."  Amrah ta faWa zata kashe wayarta. Jannah ta ce. "Šazu Sudais ya kirani ya dawo kuma suna so asa lokacin biki sati biyu, daman wancan lokacin sunyi da mahaifana da ya dwo daga tafiyarsa za a sa sati biyu." Murmushi Amrah ta yi sannan ta ce. "Kai Alhamdulillah, Allah Ubangiji Ya sanya alheri Ya kaWe fitina da sharri." 

"Amin Ya Allah." Daga haka suka kashe wayar, Amrah tana jin daWi a ranta ko ba komai Senate zai zo bikin, kuma zata san duk yadda zata yi ta gana dashi ta faWa masa komai, kuma tasan in sha Allah zai mayarwa da Bhatool auenta. 

Acan Sangaren Mom kam jiki ta Alhmdlh tum bayam zuwansu india, ta fara samu sau™i duk da dai damuwa ta kasa barinta, a kullum zancen ta Waya. "'Yar uwata da nake ganin ko babu raina xata kula da nawa, ashe ita ce zata kashe nawa." 

Legendspen

08129553971

HASASHEN SOYAYYA (BOOK 2)

By

Sayyid Legendspen

Amanar-Janafty

Shafi na Arba'in da Biyar  (48)

Acan Sangaren Mom kam jiki ta Alhmdlh tum bayam zuwansu india, ta fara samu sau™i duk da dai damuwa ta kasa barinta, a kullum zancen ta Waya. "'Yar uwata da nake ganin ko babu raina xata kula da nawa, ashe ita ce zata kashe nawa."

Haka Dad zai ta tausarta yana bata hakuri, shi kam Senate bai ma san bata da lafiya, kawai dai yana kira suna Gaisawa ta ce masa ta je india. 

Yau tin safe Senate ya tashi da son dawowa gida, gaba Waya ji yake idan bai je gida ba bazai iya duk wani aiki ba, haka ya sa Anas ya shirya musu flight. Anas farin ciki kamar ya kashe shi ya kira Mom ya sanar mata, wamda ita ma gobe zata dawo Nigeria, Dad kuma zai ce Rasha amma ta ce lallai ita ma Flight din yau take son bi. 

****

Bhatool kam kwana biyu wata irin soyayya ce mai dadi take faruwa tsakaninta da Ahamd, ko da yaushe suna tare a waya, ko aiki yake sai ya kirata ko abinci zai ci sai ya kirata, kullum suna cikim waya sannan basa Soyewa junamsu komai, duk abinda daya yake to daya ya sani, a yanzu Bhatool ji take ina ma ta haihu yau, a daura musu aure a washe gari. Zaune take a falo kan kujera suna faman waya da Ahmad da ya kwana biyu bai zo ba. "To yanzu yaushe zaka zo?." Bhatool ta tambaya kamar zata yi kuka. "Ko yanzu kike so ranki ya dade, zan iya ajiye komai na tawo." Murmushi ta yi sannam ta ce. "A'a kabari ka gama ayyukanka goben sai ka zo, me zan dafa maka?." Dariya ya yi sannan ya ce. "Kamar iyawa za ta yi." Itama dariyar ta yi sannan ta ce. "Zan iya mana, ai yanzu ya yi kwari yana barina na yi girki." 

"Au, aiki ne bai barinki ki yi sai girki?." 

"Ina fa aiki, jiya nina gyara Wakin gado gaba Waya fa, sannan na dafa Tea." 

"To waannan ne aiki?." Ya faWa yana dariya. "Kasan fa ni bana son aiki." 

"Nasani ranki ya daWe, 'yan aiki nawa kike so?." 

"Goma." Aikuwa ya yi dariya sannan ya ce. "Tom shikenan." 

"Shikenan kuma?." Ta faWa kamar zata yi kuka. "Eyh mana shikenan." Ya maimaita. "Ni wasa nake ma, bana son ko Waya." Daidai lokacin kuma akayi sallama aka shigo. "Waye ya shigo?." Ya tambaya. "Jannah ce." Ta bashi amsa. "Okay sannunta zuwa, mu yi waya anjima." 

"Okay." ta faWa tare da sauke wayar a kunnenta. "Ke da wa kike shan wannam soyayyar?." Jannah ta tambya tana zama, dariya Bhatool ta yi sannan ta ce. "Ahmad ne." Murmushin ya™e Jannah ta yi sannan ta ce . "Dagaske dai kin ha™ura da Senate ." 

"Har duniya ta naWe." Bhatool ta faWa. "Ai shikenan, Allah Ya sa haka yafi alheri." 

"Amin Amim Jannah, ya garin?." 

"Ke gari ya ci huta. An kawo kayana fa jiya, kuma kwana takwas suka sa." Jannah ta faWa. "Suka sa me?." Bhatool ta tambaya. "Auren."

"Ah Lallai baki da hankali, idan kin shirya to mu bamu shirya ba." Bhatool ta faWa, dariya Jannah ta yi sannan ta ce. "To ya zaayi, hutu ya samu ya dawo kuma yana so mu dan zuana ko kwana biyar ne anan kafin mu huce can Legos Win." 
Chapter 42 · 0% Book details