← Book details Gobe Na Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 78 OF 136

Sashe 78

Gobe Na Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read

Ya fada sound so serious domin gani yake yau Siyana hauka take ji how zata kira company su tace kowa yai surprising dinsa, and now tana gaya mishi akwai celebration, shi rabon da yai celebration din birthday sa tun matarsa Halima na da rai.

“Tana da hankali she's just celebrating her brother birthday”

Khadija ta fada tana murmushi Siyama tace.

“Louder pls”

“No ina ganinki da hankali Khadija karki biye wannan”

Daga haka ya juya ya fice yana murmushi, sai kuma ya juyo yana kallon Hajiyarsa.

“A saka min cake dina a fridge pls”

“Okay Breakfast fa”

“Zanje office din na san kamin na dawo kun hada sai na ci, akwai wanda nake son meeting da shi a 8”

“Okay Allah ya tsare”

Sai da ya amsa da min sannan ya fice daga falon ya nufa haravar gidan gurin da ake aje motoci. He choose ya black kalar suit dinsa sannan ya shiga.
   Sai ya kusa isa kamfanin sannan ya rage gudun da yake, like always dan kawai ya gani idan ma din ma Halimatu zata bawa mahaukacin nan da be san alakarsu ba abinci, to his surprise yau be ganta ba sai dai mahaukacin na nan a zaune, haka nan kawai ya faka motarsa gefen titi yana ta kallon mahaukacin he just wanted to see idan zata ba shi abinci yau, ko ma bata ba shi ba shi miye nasa a ciki? Yaja tsaki a maimakon yaja motarsa yai gaba sai ya dauko wayarsa ya shiga whatsapp yana duba status din Siyama wacce ta sika status din da hotonsa tana masa kalamaina na kauna irin na yar'uwa da dan'uwanta, sai da ya dora hotonsa a status dinsa ya rubuta happy birthday to me sannan ya shiga duba na sauran yan'uwansa da abokansa, daga lokacin ne n banks dinsa suka shigo sai kuma fb da sukai masa happy birthday.
Ya fi karfin minti talatin a gurin sannan yai ma motarsa key ya karasa office din, hakan nan yaji baya son fita daga motar ma and he don't know why sai kawai ya ciro wayarsa amininsa kuma abokin aikinsa.

“Happy birthday Boss”

“Thank you, Salim ya ganar Inuwa? Kana ganin zai samu zuwa yau kuwa”

“Yes ai ba zai tsaba alkawari ba amman na san yau rana ce mai muhimmanci a gareka, zan masa jagoran komai kai sai ka huta”

“Thank you zan fito amman sai anjima”

“Okay”

Daga haka ya aje wayar yai reverse ya koma hanyar gida, still sai ya sake tsayawa yana kallon mahaukacin na tsawon five minutes sannan ya cigaba da tukinsa.

HALIMATU POV.

Bayan tafiyar Abraham wani tunanin ya fado min a rai, a iya tunani be kamata na kyale shi a haka nan yana ta bibiyar rayuwata ba, ya kamata na kai shi gurin yan sanda su mana tsakani ko ba komai zan samu salama kuma zan fada musu cewar dan fashi ne ko zai kashe ni sai dai ya kashe ni.
Ban sanarwa kowa ba sai dai na kudirci abun a zuciyata, a daren ban yi bachi ba sai pass 12, ina ta tunanin irin matakin da ya dace na dauk domin na san nan gaba kadan iyayena za su bukaci saninsa to sai na ce musu me?
  Da wuri na shiryawa yarana sannan na karya bayan su ma sun karya suka kama hanyar makarantar wacce ta kasance nesa da unguwarmu kadan, yau ban basu kudin tara ba saboda ina son dafa musu indomie tare da Kabir, da kaina na nufi shagon unguwarmu na siyo indomin sai ya rage naira goma ce kawai canji dan haka na bukaci ya bani chewing gum da ita idan ma na karbar na san rigima kawai zata zama tsakamin Namra da Aiman da Amal kara Adnan yana dan daga kafa wani lokacin baya biyesu.
  Sai da na dafa indomie na zuba musu a cularsu sannan na dauko leda na kwashe ragowar indomin na zuba ciki, a gaggauwace na nufi bandaki nai wanka na shirya sai dai hakan be hana ni shafa janbaki da hoda ba har da kwalli kamar yadda na saba,  riga da zane na atamfa na dauko na saka sannan na saka hijab dina ya saka wayata da a jaka na fito ina yi ma su Mama da Inna sallama.
Sai da na karanta addu'ar fita daga gida sannan na fita, ina karasa titi nai sa'a da mai adaidaita babu kowa a ciki bayan na tare na fada masa ya kai ni police station da ke can unguwar kwaza, wata zuciyar na fada min kar ka kai maganar gurin yan sanda saboda gudun abunda zata zame min, amman kuma idan ban kai ba me zan yi? Haka zan zuba masa ido yana ta bibiyata? Bayan na fada min ko na yafe masa idan ban aureshi ba ba zai daina bibiyata ba. Nesa da station din aka sauke ni domin masu napep ko abu hawa basa karasa har gaban gurin, bayan na bashi kudin na shiga ciki, gabana sai faduwa yake kamar marar gaskiya, abunka da wacce bata saba zuwa gurin yan sanda ba. Kai tsaye na shiga ciki har da yar sallama ta suka amsa min wanda na ganin da yar fuska far'a na nufa na fada masa abunda ya kawo ni a gurin, ba shi kadai ba ko su sauran da suke sauraren labarin nawa sai da sukai mamaki.

“Amman kuma ba ki san shi ba?”

“Ban san shi ba ba ni da alaka da shi, kawai dai yace yana so na ni kuma na nuna masa bana sonsa hakan kuma be saka shi ya daina bibiyata ba, and jiya ma sai ga kudi an aikowa mahaifina ina zaton shi ya bada yace a bashi amman shi mahaifin nawa be sani ba, kuma ni ina tsoro kar abun yai nisa ya zame min fitina”

“Kin ce kin taba ganinsa da bindiga?”

“Eh a motarsa ba, ina tunanin dan bashi ne”

“Ko dan kidnapped ba, wannan babban case ne gaskiya, ina ganin abunda ya kamata a fadawa PRo sai ta shiga tai masa bayani”

“No kai ta gurin oga direct zai fi, idan ya hannatawa Pro shikenan, mu sai mu rubuta statement”

Atsakaninsu su uku suke wannan shawarar, kamin dayan ya shiga ciki be dade b ya fito ya ce akwai case din da yake idan ya gama sai na shiga, haka na samu guri a gurin na zauna ina ta kallon wasu mutane da ke shigarda kara da wadanda ake saurarensu suna kare kansu.
Bayan kamar minti talati ya sake lekawa ya fito yace min na shiga, shi yai min jagora ciki har da bude min kofar na shiga sannan ya janyota ya rufe, mutumen da na tarar yana zaune a irin kujerar nan ta office mai lilo, ya bani baya wanda hakan ya bani damar daga kaina saman ina kallon office din, kamin ya kare wayar ya juyo ya kalleni arba nai da abunda ban tana tunani ba abunda ban taba tsammani ba, a take jakar hannuna ta subuce ta fadi, nai baya da sauri kirjina na mugun bugawa kamar zai fito.

“Ya akai?”

Ya tambaya ni fuskarsa ba yabo ba fallasa.

“Ni ban gane ba, tagwaye ne ku, kama ce, ko kuma kai din ne dai?”

Murmushi yai.

“Ni din ne dai, wa kika kawo kara? Ni ko wani?”

“Daman kai dan sanda ne kuma kake fashi da makami?....”

“Shiiiiiiiiiiiiiiiiiii”

Ya furta tare da saurin mikewa tsaye ya nufo inda nake, kan ya karaso har na kai hannu na bude kofar na fita da sauri jikina sai rawa yake, ina fitowa na nufi gurin kular abincin yarana zan dauka sai dayan yace.

“Kin masa bayani”

“No waya yake, yace naje na dawo, bari na kaiwa yarana abincinsu a makaranta na dawo”

“Okay ba matsala”

Daga haka na samu na fita daga station din, mamaki ya saka ni mike hanya ina ta tafiya ba tare da na tari abun hawa ba, sam hankalina be bani a gafen titi nake ba har sai da nake tsallakawa ba tare da na saurari horn din da motocin ke min ba. Ban ankara ba na ji abu ya buge bugu bana wasa ba, har sai da nai bayabaya na fadi kan kwalbatin da ke gefen titi.

“Ba ki da hankali ana miki horn amman sai kokari tsallaka titi kike kurma ce ke?”

Iyakar kokarin da nai na fita daga kwalbatin ne kamin na dago na kalli mai motar wanda ya rufe da fada babu ko tausayi. Muna hada ido yaja wani bugun tsaki ya koma cikin motarsa da ke bude ko inda nake be sake kallo ba.

“Wawa kai ne mahaukaci tun da baka iya tsayawa ka duba mutane ba, ko tokin be iya ba sai jin kai kamar wani Governor, ko titi na gidanku ne....!”

Be sake ce min uffan ba har yaja motarsa ya bar gurin.
Wani mai acahaba ne ya tsaya yana tambayar idan ban ji ciwo ba.

“Ban jimu ba faduwar kawai nai”

Na fada domin bana jin ciwo komai a jikina.

“Dan Allah ki rika kula idan za ki tsallaka titi irin wadannan ba imani garesu ba”

“Na gode”
Chapter 78 · 0% Book details