← Book details Gobe Na Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 118 OF 136

Sashe 118

Gobe Na Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Ya fada bakinsa na taba nawa murya can kasa kasa kamar mai rada, saurin lumshe idona nai muna ta shakar numashin juna....

___________________

Ayi hakuri two days mun yi biki shiyasa ban samu damar typing ba 🙏

Gashi nan na yi muku 5k words na biya bashi 🏃🏻🏃🏻🏃🏻

*Where are are the classy ladies 🤔 mata yan kwalissa ga awwaba scent tazo maku da hadadun turarukan wuta humra body oil turaren jiki na tsuguno da kayan gyaran jiki kaman dilka scrub organic soap 🧼 da sauransu akan farashi daidai aljihu say no karnin da warin damshi na lokacin damina zaaiya samunmu a wannan lambobin 09137294470 08034236800*
7/21/21, 11:10 PM - Buhainat: *GOBE NA...*

By Khadeeja Candy

5️⃣8️⃣

Raba jikina nai da nasa.

“Mutane za su iya ganinmu”

Be ce min komai ba yaja hannuna ya karasa gurin motar da ni ya bude gidan baya na shiga sannan shima ya zagayo ya shigo ya rufe sannan ya rika hannayena ya soma murzawa yana kallon fuskata.

“Ban miyasa nake jin ki a zuciyata fiye da kima ba, ina jin cewar na fi kowa dace a duniyar nan, a yanzu bani da wani buri sai na aurenki kuma ya cika ina son sosai, irin son da bana jin wani namiji ya taba miki shi, bana tunanin akwai namijin da ya fi ni son ki”

Ya sumbanci hannun nawa.

“Kamin na aureki, idan wani ya fada min zan aureki zan karyata shi kuma na fusata, amman a yau da Yayan mahaifin yai min albishir da cewar an daura aurena da ke sai na rasa inda zan saka kaina dan murna, na rasa abunda zan bashi na kyautata masa na goron abunda ya fada min, na gode da kika amince min na gode da kika ba ni damar shiga rayuwarki, na gode da kika karbe ni a duniyarki”

Ya karasa tare da kai hannunsa yana shafa fuskata, sai kuma ya jani jikinsa ya kwantar da ni ya rumgume ni sosai kamar ba gobe.

“I love you so much Lims”

Ya fada calmly kissing my forehead, dayan hannunsa kuma yana mutsa yan yatsun hannuna. Mu kai shiru kamar babu mu a cikin motar baka jin komai sai saukar numfashinmu, can ya saka hannunsa ya dago kaina ya dora bakinsa a saman nawa kamar zai tsosa sai kuma ya bar shi a haka yana ta kallon idona da na rufe, ji nai an busa min iska a saman idon hakan yasa na bude muna hada ido sai ya hade bakinsa da nawa, a hankali yake kissing din lisp dina sai kuma ya cire bakinsa a nawa ya kai gurin tsinin hancina ya tsosa sannan yai kissing forehead dina ya sake rumgume ni a kirjinsa tsantsa yana sauke ajiyar zuciya.

“What else i can say more than Al-hamdulillah, you're finally mine”

Muna haka na hango mota ta faka a kofar gidanmu, ina ganin motar na san cewa Abdallah ne, Ahmad kam be gane shi ba har sai da ya fito daga cikin motar ya jingina yana lasa. Wayar da ke hannuna tai ringing kiransa ya shigo, kallon wayar nai na kalli Ahmad sai na kasa daga kiran.

“Me ya zo yi?”

“Wata kila yana son magana da ni ne”

Bude motar yai yace min na fito muje, abunda ban so ba ke nan domin nasan ganin mu a tare da Ahmad ba karamin bata ran Abdallah zai yi ba, ba zan iya musa ma Ahmad ba kamar yadda ba zan so Ahmad yai abunda zai kara batawa Abdallah rai ba. Ya rufe motar sannan ya rika hannuna muka nufi gurin da Abdallah yake tsaye, daga inda yake tsayen ya dago idonsa yana kallon mu har muka iso, na kasa ce masa komai shi ma be ce min ba Ahmad ma be masa magana ba, sai kallon juna suke kana ganinsu kasan da akwai abunda kowa ya aje kasan zuciyarsa, Ahmad murmushi yake yana ta lilo da hannuna duk yadda na so na kwace hannun sai ya ki saki, na yi tunanin Abdallah zai yi wani abun ne ko kuma ya fada masa bakar magana amman ga mamakina sai ya sakar wa Ahmad murmushi ya mika masa hannunsa.

“Congratulations, that's good daman ka ce zaka nuna min ko waye kai a gurin Halimatu ko? Na gani yanzu ina taya ka murna”

Sai da Ahmad ya kalli hannunsa nasa sannan shima ya mika masa nasa.

“Thank you”

A lokacin ne Abdallah ya kalleni da murmushin a fuskarsa yace min.

“Ina taya ki murna”

Ni kam kasa amsawa nai sai Ahmad ne ya sake ce masa

“mun gode”

Sai ya bude motarsa ya shiga yai ribas ya juya ya bar mu a gurin tsaye ina bin motarsa da kallo.

“Kun taba yin wata magana ne da shi?”

“Eh lokacin da mahaifiyarsa ta saka aka kamaki ba, yace min wai ni waye ne a gurinki da har zan nuna masa isa, sai na ce masa zan nuna masa ko ni wanenen nan da dan lokaci”

Na yi shiru bance komai ba, hakan yana nufin shi da Abdallah sun yi sa'insa kenan, wata kila shiya saka Abdallah ya nemi na bar aikin a kamfanin dan ya nuna masa ya isa da ni. Ji nai ya saki hannuna ya juyo gabana yana kallona.

“Bari na barki ki huta, ki yi list din duk abunda kike so kin san yanzu hakkinki da na yaranki yana kaina, da safe zan zo na karba”

Ya fada sannan ya shafa fuskata, har ya juya sai kuma ya juyo.

“Ba ni line wayarki”

“Why....”

“Just”

Ban musa masa ba na ciro line ya mika masa.

“Amman akwai numbers din yan'uwa da kawaye na a ciki”

“Okay idan na dawo gobe zan zo da sabon line sai ki dauki numbers din a ciki”

Kai na gyada masa sai ya juya can kuma ya sake juyowa a karo na biyu yai min alama da na zo, sai na karasa kusa da shi kamar yadda ya bukata, saitin kunnena ya kai bakinsa ya rada min

“Muje ki min sallama”

Ko be fada kai tsaye ba na san abunda yake nufi maybe he want to kiss me or hug, ko something like that, ni kuma bana son mutane su fara saka mana ido ace mun fara yin abunda be dace ba a bainar jama'a.

“Akwai mutane fa”

“To muje zauren gidanku”

“Nan ma za a iya saka mana ido, ka bari har ka dawo”

“Ba zan bari ba....”

Ya fada yana wuce ni ya nufi cikin zauren gidan a dole na bishi a baya, ko da na shiga har ya jingina da bangon gurin yana jiran shigowata, hannunsa ya kai ya kama kwankwaso na ya rike ya hade fuskarsa da tawa.

“So this woman here is mine”

Ya fada da sigar da babu wanda zai ji sai ni, ni dai hankali yana kan kofar gida kar wani ya fito daga cikin gida ya gan mu. Bakinsa ya saka cikin nawa ya tsosa iya yadda yake jin ya samu natsuwa sannan ya sake ni, kamar an masa shocking haka ya zabura da karfi ya bankare sai kuma ya runtse ido, kamin ya bude su a hankali ya kalleni.

“Good night Sweetheart”

Ya fada yana kissing kumatuna sannan ya juya ya fita daga zauren, hakan kawai na samu kaina da son kallonsa, haka n leko a zaune ina ta kallonsa har ya karasa gurin motarsa ya bude ya shiga yai mata key ya fice.
Wata irin natsuwa da sakewar zuciyata da nishadi ne suka ziyarce, rumgumar da yai min sai na ji kamar mu kasance a haka har a bada, gaba daya jikina kamshin turarensa yake murmushi ya maye gurbin hawayen da nake, ina jin a raina kamar na yi dace duk da ban tabbatar din ba, sai a yanzu nake jin wata irin natsuwa da farincikin amincewa da nai, wata kila dazun ba kukan bakinciki nake ba, kukan farinciki nake ban gane ba, da kuma yadda abun ya zo min a bazata.

“I love you so much Lims”

Na yi murmushi ina jindadin tuna kalmar daya fada min a dazun, har yanzu bana jin ina son sa kamar yadda bana jin tsanarsa ko kasan a raina, amman am happy I'm now officially Mrs hakan ma wata martaba ce babba, na juyo na nufo cikin gida, sai da na gama sallah isha'i sannan na bude ledodin da ya kawo min, kaza ce babba har guda biyu da lemu sai kayan tea da katon burodi da kuma ku a cikin farar takarda 20k.
Washe garin ranar na tashi cikin walwala ba laifi ina ta jin nishadi a raina, bayan su Namra sun tafi Islamiya sai ga Aminu ya sallamo ya shigo cikin gidan, kamin ya karaso falon Mama nai saurin dauko Hijabinta na saka ya rufe jikina sannan na dawo falon na zauna. Ya shigo da sallama na amsa masa ina murmushi kamar ba ni ba. Shi ma murmushin ne kwance a fuskarsa sai dai ba irin murmushin nan na jindadi ba irin murmushin nan mai kamar na dole.

“Ina kwana”

“Lfy kalau”

Ya amsa yana ta kallona kamar be taba ganina ba, a raina na raya cewar da ace Ahmad nan Aminu yake min kallon nan da yanzu wani abun ya faru, ban san lokacin da wani murmushin ya subuce min ba har sai da na ji Aminu na tambayar.

“Me kike yi wa murmushi?”

“Ba komai”

“Na ga alamar dai kina cikin farinciki”

Na yi kasa da kaina ban ce masa komai ba.

“Daman na zo ne na taya murna, na ji abunda ya faru ance kin yi aure jiya, shine nace abun babu gayyata”

“Nima abun ya zo min bazata ne shiyasa”

“To congratulations Allah yasa alheri Allah yasa wanda zai rike ki amana ne”

Yanayin yadda maganar ta fito daga bakinsa kana ji kasan ba dadi ya fade ta ba. Ni dai na amsa da Amin.

“Nima na zo na fada miki ne zan maida Murja”

Kallon Mamaki nai masa.

“Murja da wacce ta ci amanarka?”
Chapter 118 · 0% Book details