← Book details Gobe Na Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 110 OF 136

Sashe 110

Gobe Na Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Kamar mai rada yake min magana sai kallon cikin idona yake kamar zai cinye ni, kai na gyada masa alamar na ji sauki.

“Wani gurin na miki ciwo?”

Na girgiza kai.

“Can you talk?”

Nan ma dai kan na gyada.

“Then say my name”

“Ahmad... ”

Na fada cike da nauyin baki, murmushi ya sakar min.

“That's my girl”

Ya fada yana kara kashe murya sannan ya mike tsaye ya nufi inda nake zaton bandaki ne ya bude ya shiga sai gashi ya fito rike da karamin bokoti ya nufo inda nake, sannan ya dauko daya daga cikin ruwan gorar da suke saman drawer wadanda nake kyautata zaton shi ya siyo su ya bude daya.

“Za ki iya tashi ki wanke bakinki?”

Haka nan na unkura ba dan ina jin karfi ba na tashi na zaune na tara hannuna yana zuba min ruwa ina kaiwa a baki n kuskure na zubar, sannan na soma wanke fuskata.

“Ji yadda suka saka pretty face din nan na ki ya rame”

Ni dai ban ce komai ba, ko ban duba madubi na san na rame domin na ji fuskar tawa ta zurma. Yana aje ruwan ya dauki bokitin ya maida sannan ya nufi kofar fita yana.

“Bari na fara yin magana da Doc kar na baki wani abun ya saba doka”

Da kallo na bishi har ya fice kofar bata rufe ba aka sake turo ta Mama ta shigo tare da Mama Ramatu.

“Alhamdulillah Alhamdulillah, Allah mun gode maka”

Shine abunda take fada har ta iso inda nake ta zauna bakin gadon tana kallona fuskarta da murmushi.

“Ya karfin jikin Halimatu?”

Cewar Mama Rahamatu sai na amsa mata da Al-hamdulillah.

“Kina jin wani ciwon a yanzu?”

“A a”

Na fada ina kallonta babu komai a cikin idanuwa sai son mahaifiyata da kaunarta. Likitan nan ne ya shigo tare da Ahmad ya tambaye ni jiki na fada masa bana jin komai sannan yace a bani abinci na ci sannan a bani magani. Ahmad da kansa ya dauko ayaba ya mikawa Mama yace ta ba ni, ita kuma ta rika barewa tana saka min a baki ina taunawa a hankali har na koshi.

“A saka miki tuwo?”

“A a cikina ya cika”

A nan ma shi ya ballo maganin ya mikawa Mama ta bani na sha.

“Mama rumgume ta, idan mutum ba shi da lafiya yana jindadi a rumgume shi”

Ya fada yana kallona, Mama ta amsa da to tana dan kallonsa kamar yadda nima nake mamakin maganarsa sai kace wata karamar yarinya zai ce a rumgume ni, Mama ta kara haurowa kan gadon taja ni jikinta ta rumgume, hakan kuma ba karamin dadi yai min ba sai na ji natsuwa ta sauko min har na Lumshe ido.

“Am Baba daman ina son na fada muku wani abu, na yi magana da lauyana zai saka kara akan abunda akai wa Halima so i think ya kamata ku sani”

Ba shiri na bude ido na dago na kalleshi kamar yadda Mama ma take kallonsa.

“A a idan su idonsu ya rufe sun aikata abunda suka aikata, mu be kamata mu yi haka ba, ba a taruwa a zama daya, akwai zumunci mai karfi a tsakani, da mahaifin Abdallah da mahaifin Halimatu”

“Amman su basu san da zumuncin ba ne suka aikata abunda suka aikata?”

“Hankali da tunani ba daya ba, kuma ba a biye son zuciya kamar yadda tai”

“Ba ki ga yadda sukai mata ba? Zata iya rasa ranta fa sanadin haka”

“Tun da Allah yasa ba a rasa ran ba hakuri shi ya fi, amman shiga kotu a yanzu zai kara lalata zumunci ne kuma ka jawa Halimatu bacin suna a cikin dangi”

Wayarsa ce tai ringing kamar yana nema sai kawai yai picking call din ya fice daga dakin, a lokacin ne Mama ta dube ni cikin yanayin damuwa tace.

“Karki ba ri a kai matar yayan mahaifinki kotu, ita ma uwa ce a gareki, na sani da margayi yana da rai wata kila da yanzu kina can gidansa zaune yana kula da ke, inda yana raye da duk abubuwan nan ba su faru ba, idan kika bari aka saka Hajiya kotu saboda abunda tai miki Abdallah ba zai taba ganin farinki ba, ko dan shi kadai be kamata ki bari akai Hajiya kotu ba, domin zai kara lalata zumuncin ne, idan hankali ya gushe hankali ne yake dawo da shi, ki masa magana kar ya kai abun nan kotu dan Allah”

“In-Sha-Allah zan yi magana da shi Mama”

“To Allah ya miki albarka”

“Amin”

Tun da Ahmad ya fita ban sake saka shi idona ba sai washe gari da safe, misalin bakwai da wani abu. A lokacin ina zaune a dakin ni kadai domin ba sa barin kowa ya shigo da safe sai yamma ta yi. Ya shigo hannunsa rike da kwandon dake dauke da kulolin har kala uku dayan hannunsa kuma rike da filas din ruwan zafi.

“Ina kwana....”

Na mika masa gaisuwa sun kamin ya karaso, be amsa ni ba kuma be min murmushin daya saba ba har ya aje kayan.

“Ga breakfast in ji Hajiya”

“Ina kwana?”

Na sake mika masa gaisuwa a nan ma be amsa ni ba.

“Ya jikinkin na ki?”

“Al-hamdulillah”

Daga haka be sake ce min komai ba sai ya ciro wayarsa ya shiga dannawa. Kallonsa nai yanayinsa da yadda yai min sai ya sa na ji babu dadi.

“Kai hakuri na ja maka ba.....”

Kamin na karasa ya tari numfashinta.

“Ba ki ja min komai ba, ni na ja miki duk wannan abun daya same ki, ba ina fushi ne saboda abunda ya faru ba, kawai ina mamakin hali irin ba ku ne, taya za a ci zarafin mutum kuma ya hana a bi masa hakkinsa? Su ba su san da zumunci ba ne suka wulakanta ki? Har marinki fa aka ce yar sanda ta yi aka fito dake waje babu mayafi babu wulakancin da ba su muku ba, kin san abunda nake ji a zuciyata?”

Kai na girgiza masa.

“Babu wanda ya mare ni, kuma ba mu fito cikin gidan ba sai da mayafi, duk wanda ya fada maka tsabanin haka karya yake”

“Kanwarki ta fada min kuma baza tai karya ba, kina boyewa ne kawai”

Shiru nai ina tunani a cikin duka kanena babu wacce zata iya fadar haka sai Hafiza.

“A ina ka ganta”

“Na kira wayarki ta dauka, ita ta fada min komai”

Na yi shiru domin bana son karyata kanwata a gabansa, ko ba komai gobe ba zai sake ganin girmanta ba, balle har ya yarda da ita.

“Idan hankali ya gaushe hankaline yake dawo da shi, ita ita ta aikata kuskure mu be kamata mu aikata ba, ta aikata abunda ta aikata ne saboda tana tunanin ni ce silar batar danta”

“Amman miyasa ke kadai zata zarga? Ya akai ta san da maganar ma? After na fada miki wa kika fadawa?”

“Saboda bata so na, kuma ta fada tana tunanin na dauke Abdulhamid ne ko kuma na saka an dauke shi saboda zai yi aure, kuma saboda ya ki zama da ni, tana tunanin ni an saka Abraham ya dauke shi saboda na dauki fansa”

“Amman ba ita kadai ba har wannan Abdallah.... ”

“Abdallah ba zai taba min haka ba, i trust him, ba da sa bakinsa Hajiya tai min haka ba, ba zai taba bari ba, balle har shi yai min, kiyayyar da Hajiya take min a yanzu ta samo asali ne ta dalilin soyayyar da Abdallah yake min”

“Miya hana ki aurenshi?”

Ya aiko min da tambayar kai tsaye, kallonsa nai ina kokarin kawarda da hawayen da suke son zubo min.

“ A wacan lokacin Abdallah ya nuna min soyayya ne ta hanyar da be dace ba, shi yake yawan kawo min labarin abunda Aminu yake, yana son na kashe aure na na aure, wanda a musulunce haramun ne, domin Annabi yace baya tare da wanda ya so matar wani, ko ya zuga matar wani dan ta kashe aure ta ko da kuwa shi din zai aureta, a lokacin da aurena ya mutu, sai Abdulhamid ya fito so na bayan kuma Abdallah yana so na, amman shi Abdulhamid be san Abdallah yana so na ba, Abdallah kuma be taba sanin cewa na yi soyayya da Abdulhamid a lokacin da ina budurwa ba. A lokacin ina jin tsoron abunda ya kashe min aure kar na sake fada mishi, da kuma ganin da nai Abdallah yana so na tun ina a gidan wani sai nake ganin kamar idan na aure shi, aure ba zai dade ba hakan yasa na take aurensa na auri dan'uwansa, daga lokacin sai mahaifiyarsa ta fara kina, ashe Abdallah ya fada mata yana so na, sai take ganin kamar ni na ja hankali Abdulhamid ne na aureshi saboda na batawa Abdallah, saboda babu wanda ya san mun yi soyayya da Abdulhamid saboda a boye mu kai a wacan lokacin ya hana na bayyana soyayyar, wanda ban san dalilin hakan ba wata kila saboda ba shi da lafiya ne yana tsoron soyyayyar mu ta bayyana sirrinsa, a jiya ina jin tana fadar cewar na lalata zumuncin da yake tsakanin Abdallah da Abdulhamid, ban san iya abunda ya shiga tsakaninsu ba, kuma na san saboda ni ne, komai bana yinsa daidai, yanzu ma idan aka kai Hajiya kotu saboda ni Abdallah ba zai jidadi ba”

Dan murmushi yai ya tabe baki

“Kamar dai Abdallah nan yana da muhimmanci a gurinki”

“Yes, ya taimake ni a lokacin da nake bukatar taimakon, ya rike yayana kamar nasa a lokacin da ubansu ya guje su, kuma mijin dana aura wato Abdulhamid ya nuna min baya bukatarsu, duk son da Abdulllah yake min be tana neman yin lalata da ni ko sau daya ba, mi zai saka ba zai zama mai muhimmanci a gurina na”
Chapter 110 · 0% Book details