Sashe 130
Gobe Na Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Ba mu bar hotel din ba sai kusan la'asar a nan mu kai azahar da la'asar sannan muka koma asibiti, babu kalar albarka da be saka min ba babu irin godiyar da be min ba, each and every 30 minutes sai ya tambaye ni wai daman haka zauwara su ke? Shi ko yan matan da yake aure be taba arba da wacce ya samu abunda yake so a gurinta ba kamar yadda ya samu a gurina, har fada yake wai lallai mata suna suka tara.
Da muka dawo cikin asibitin tafiya kawai nake ina daure ina nuna kamar babu komai amman ni na san akwai komai ba irin na safiyar wacan daren amarci nawa dana kasa tafiya daidai ba ne, wannan kam ina tafiya sai dai ina jin azaba sosai da sosai.
Tun da Ahmad ya girma a nan sai yai wayo kusan kowace safiya sai mun tafi hotel din da sunan karyawa a can kuma bama dawowa sai dare, tun ina jin nauyin kar Hajiya ta gane har na barwa Allah domin na lura ko sau daya bata taba tambayar ko a waya yana ina ba? Ko kuma tace daga ina muka dawo idan mum tararda ita a asibiti, sai dai shi ne ma zai ce yau guri kaza mukaje na ga gari, alhalin ba gaskiya ba ne, idan na kalleshi sai ya kanne min ido daya ko ya daga min gira.
Satin mu daya a asibitin sannan suka sallame shi bayan sun yi bincike iya binciken su ba su gano komai ba, sai dai hakan be hana su dora shi akan magani ba, tare da wasu shawarwari ciki har da motsa jiki wanda suka ce yana da kyau ga lafiya.
Washe garin ranar da suka sallameshi ne muka kamo hanyar Nigerian cikin farinciki da kaunar juna, Hajiya kam tun kam mu dawo ta sanarwa kowa cewar danta ya samu lafiya, a raina nace ni kam ai na fi kowa sanin ya samu lafiya kam, ba mu bar kasar ba sai da Ahmad ya dauke mu ni da ita muka shiga wani shagon siyerda kayan sakawa da na ado muka siyo sannan muka shiga na yara na siyoma su Namra da Amal teddy Adnan da Aiman kuma mashin din wasar yara da wani madubi mai canja kala, Inna muka na siyo mata turare ita da Mama.
Sai a lokacin na gane ashe kayan mu na nan sun fi nasu na can arha domin duk abunda muka siya idan Ahmad ya fada min kudinsa a kudin Nigeria sai na jinjina abun.
Karfe 2:00pm daidai jirginmu ya sauka a Abuja babban birnin taraiyar kasa FCT.
_____________
Fatar kun yi sallah lafiya Allah ya maimaita mana 😍🙏
7/26/21, 1:29 PM - Buhainat: *GOBE NA...*
By Khadeeja Candy
6️⃣3️⃣
Mun iso Zamfara cikin aminci da farinciki, tun airport yan su Ahmad suka tarbo mu da muka iso sai muka tararda gidan kamar ana wani karamin ba a gaskiya na yaba da yadda yan'uwan Ahmad suke nuna kulawa da son zumunci.
Mun tarar an mana girki ga lemu kala kala gwanin sha'awa, a nan na kara sanin wadanda ban sani ba daga familynsa su ma muka suka san ni. Sai da na huta na ci abincin sannan Siyama ta shigo tace min Hajiya tace idan na kintse za a sauke ni gida, aiko da sauri na tashi daman tun dazun babu abunda nake sai tunanin gida da mamarin ganin nawa Familyn.
Direbansu aka saka ya kai ni har gida a nan wata murnar ta barka duk da kasancewar mun dawo Tuesday ne yara suna makaranta amman su ma manyan hakan be hana su murna da ihun ganina ba. Ban tabbatar da na yi missing gida ba sai da na ganni tsundun a ciki, wai har na yi tafiya na dawo sai abun ya koma min kamar a mafarki lallai rayuwa tana da ban tsoro kuma lallai duk abunda yai farko dole yana da karshe.
A nan ma an shirya min wani abincin irin namu na daidai gwargwadon hali bancin Kifin data saka a shimkafar jalof har da nama ta siyo ta soya min ta siyo min lemun Coke, a yadda naga tana ta murna da ganina ni kaina na san ta yi marmarina.
Gidan be kara haukacewa ba sai da su Namra suka dawo daga makaranta a nan wani sabon murna ya tashi suka dinga hawa suna sauka kowa Momy Oyoyo, wani irin farinciki naji ya baibaiyeni at least nima dai abun alfahari ce ga iyalaina duk da ban yi musu wani abun na gwaninta ba ko na azo a gani.
Ana gama sallah magari sai ga kiran Ahmad ya shigo wayata, bayan mun gaisa yake tambayar yaushe na tafi wai ban nemi izininsa ba ni kam dariya ma abun yaban.
“Ban fa tare ba”
“To miya raba dambe da fada? Ko baki tare ba ai igiyar aurena tana kanki, kuma tarewan zai wuce kwana biyu ne ko uku”
Na zaro ido.
“Wane irin kwana uku sai kace yar roba? Haba dai ina laifin wata uku hudu”
“What......! Ai ba zan iya barinki ko wata daya ki yi ba, kin san fa ina bukatar kusa da ni kuma ga wannan dan uwan naki zai iya zuwa fa”
“Haba dai ai mahaifiyarsa ta riga ta shiga tsakani, dazun Mama ke fada min wai karshen watan nan za a sake shiga kotu, ga Hajiyar ma lafiya bata isheta ba, yanzu ai ba ta nawa yake ba, ai na yi aure dole zai daga min kafa”
“Baki san halin Namiji bane Lims maza suna da wani irin hali, idan suna son abu ko?hmmmm ni dai gaskiya ba zan iya bari ki yi wata uku ba a cikin watannin nan Allah kadai ya san wanda zai ganki ko bayan shi Abdallah wata sani ko wani dabam na nan yana dakonki”
Dariya nai sai ya fara rantsuwa.
“Wallahi Allah kuwa ba zaki gane ba ne, ni kuma bana son ana ganinki kuma idan kina gidanku ba natsuwa zan yi ba kara dai na san kina dakina na rufeki abuna”
Na sake dariya, mun dade muna fira dashi kamin ya bijiro da fitinarsa nai masa sallama na tashi nai sallah isha'i...
Akwai wani irin natsuwa da kwanciyar hankalin da farinciki a cikin aure musamman idan ka dace, akwai akasin hakan kuma ga wanda be yi dace ba kamar yadda nayi da farko, ko da yake ko a yanzu ina kyautata zaton dacewar ne kawai da alamun da na gani a gurin Ahmad wanda ban gani ba a gurin wani namijin. Sati biyu da dawowata amman duk wanda ya gan ni a yanzu sai yayi magana cewar na canja jikina yayi kyau fuskata har wani sheki take, ramar da nai na cike ta a yanzu ni kaina na san na canja ban tare ba amman abinci da na sha sai wanda na zaba ni da yarana, ko wace safiya ka'ida ne sai ya kira ni ya tambayi yana tashi da rana haka kin ci abinci? Kina da wata damuwa haka yake min a kullum da dare kuma ko wace rana sai ya zo.
Tun satin daya shige Hajara ta kawo min kayan gyara jiki na kirji da wanda zai saka jikim tai ta sheki ga dilken da nake zuwa gidan Zil-touch tana min a duk bayan kwana biyu, na maida hankalina sosai gurin siyen wasu abubuwan da na ssn bana da su a gidansa dan aure ko kuma wandanda suka lalace cikin har da siyer da kayan dakina da zimmar yin sabbi.
Ranar wata lahadi ina zaune sai ga Siyama ta shigo bayan mun gaiss da gaisa da mutanen gida sannan na shiga na dauko mayafina domin ya fada min zata zo ta dauke ni muje gidan saboda na duba wallpaper da aka saka min idan ta yi, na nuna masa ba sai naje ba sai ya ta kura akan lallai sai naje a dole na amince.
Tare muka fita da ita bayan mun isa kofar gate din tai horn aka bude mata, mu na shiga cikin gidan na tarar an sabunta sabon fentin bangaren Hajiya gwanin sha'awa. Na yi zaton part din Hajiya za mu fara zuwa kamin mu shiga part din Ahmad din wato part din da zan zauna, amman sai Siyama ta fara shiga da ni part din Ahmad, an kawata gurin da sabon fenti sai kamshi yake, ina shiga falon nai arba da sabon cushion da curtains duka maroon color, dinning din na sabo, an zuba komai sabo a kitchen da bedroom din ma sabon furniture ne mai kyau, sauran dakunan ma duka sabin furniture ne. Gaba daya sai na ji kamar an sare min gabobin jiki na rasa abunda zance, sai a lokacin na gane abunda Ahmad yake nufi da cewar kar na wahalar da kaina shi baya bukatar komai ni yake so ba wani abu nawa ba.
“Komai ya miki? Idan akwai abunda be miki ba ki fada sai a canja ko a kawo kamin lokaci ta kure”
Siyama ce take maganar tana janyo kofar kitchen din. Tsaye nai a gurin kamar an dasani na rasa abunda zance wani guntun hawaye ya tsaya min a ido. Sai ta sa dariya
“Daman Wallahi Ya yace yanzu ana nuna miki sai kin yi kuka, har muka dinga dariya ashe da gaske yake”
Murmushi mai na share hawayen.
“Idan ban yi kukan farincikin ba Siyama na me kike son nai?”
“Kawai ki gode Allah”
“Al-hamdulillah”
Na furta fili da badini, sannan muka fito daga part din ina ta tunanin yadda zan labartawa su Inna abun, cikin tsananin kunya na shiga part din Hajiya, ko zaman ban yi ba Siyama ta labarta masa cewar na yi kuka sai yai murmushi yana kallona.
“Ni ai na san halin kayata”
Bayan mun gaisa da Hajiya ta sa aka kawo min lemu sannan ta fada min.
“Nasa Ril_kamshi ta hada miki turare kayanta suna da kyau”