Sashe 135
Gobe Na Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Ina kokarin zama yake ce min haka yana min gwalo kamar wani karamin yaro, fillon kujerar na dauka na jefa masa ina dariya sai ya shi ma yasa dariya yana zolayata.
“Yar Babyta idan fa zaki haihu ni zan miki nakuda”
“A ina a taba ganin namiji yayi nakuda”
“Ni dai sai na yi”
Ya fada yana daga min gira daya sai kace wani tsoron dan iska.
“Ni dai dan Allah Ya Omri ka daina jana ka bar ni na ji da yayanka”
Na fada ina nishi daker daman haka nake idan suka motsa sai su haye min zuciya daker nake numfashi, taso yai ya dawo inda nake zaune ya duka gabana ya bude cikin yana kallon yadda yake motsi sai kuma ya dora kansa sama ya lumshe ido yana murmushi, kamin ya ciro wayarsa ya fara daukata hoto.
Ko da na shiga watan haihuwa ta na zama wata abar tausayi, domin idan zan kwanta sai na nade wani zane sannan na dora cikin akai, dayan fillon kuma na dora kafafuwana sannan nai matashin kai da Ya Omri.
Ana sauran sati Edd na ya cika na je asibiti sai suka rike ni bayan sun min hoto sun dubani abunda suka fada min wai ba zan iya haihuwa da kaina ba, a lokacin na samu kaina a cikin tashin hankali marar misaltuwa, ba ni kadai ba har da yan gidanmu da kuma Hajiya da Ya Omri, sai a lokacin ne na san cewa abunda ke cikina hudu ne ba biyu ba kamar yadda Ya Omri ya boye min. Sosai ya so fitar da ni waje domin amin aikin acan amman naki domin ganin nake ko mutuwarce kara dai na mutu a kusa da mahaifiyata. Be ki amince min ba sai dai kuma be min yadda nake son din ba domin a cikin kwanakin ya sa aka shirya min komai muka tafi Abuja wata private hospital mai shegen tsada da kyau ga kula kamar za su cinye mutum, yawancin ma turawa ne suke duba matane sai kwararun likitoci.
Duk kwana daya a dakin 170k ake biya bayan sauran responsibility na asibiti.
A ranar Likitan aka min theater kamin a shiga da ni babu wanda ban nemi yafiyarsa ba babu wanda ban yi ma kuka ba, har da amanar yarana na bada hakan yasa hankalin kowa ya tashi, ba ma kamar Ya Omri da har wani rama yai, ni kam har ga Allah na dauka mutuwa zan yi domin duk haihuwa ni nake yi da kaina na tiyata ba, kuma ban tana shan wahala irin na wannan ba.
Sai dai cikin ikon Allah da iyawarsa da yardarsa sai aka min theater ban san ma anyi ba domin hankalina baya jikina a lokacin, sun dade suna kira sunana kamin na amsa musu domin numfashina yayi nisan zango ga jikin ina jinsa kamar ba nawa ba. Al-hamdulillah likitar da fada tare da sauran nurses da kuma wata likitar ita ma mace Nurses din ma dukansu mata ne. Sun dade a kaina kamin dauko baby dora min a kirji.
“Duba ki gani me kika haifa”
Cikin lumsasun idanuwana na duba na ce
“Mace”
Suka sake dora min dayan
“Namiji”
Suka sake dora min wani.
“Namiji”
Na fada idona na cika da kwalla, sai musulmar cikinsu tai hamdalla suka canja min gado suka dora ni akan wani sannan suka rufe min jiki suka turo ni akan gadon aka fito da ni. Mama da Hajiya da Ya Omri ne rike da yaran uku babu komai a fuskarsu sai farinciki. Wani dakin dabam aka kai ni suka jona min gorar jini suka saka min iskar da zata taimaka min gurin numfashi sannan suka min Sannu suka fita. Sai ga Ya Omri na ya shigo rie da Baby fari sol cikin kayan sanye masu kyau da tsada. Gefena na aje baby sannan ya doko ya sumbanci goshina ya rumgume ni hawaye na sauko masa.
“Thank you so much, Allah ya miki albarka”
“Ya Omri nawa na haifa?”
“Four amman guda ya koma”
Yana rufe baki sai ga Nurse ta shigo da daya Hajiya kuma rike da daya, wani karamin gado dake kusa da ni na asibiti aka jera su, Hajiya ta matso kusa da ni tana min sannu da jiki.
Naga kulawa na ga gata ba a gurin mijina ba, ba a gurin Hajiya ba duk wani abun da ya take bukata a gurin uwa Hajiya tana min shi, Ya Omri na kam Wallahi yadda yake dawainiya da ni da damuwa har tausayi yake ba ni. Sati na daya suka sallameni muka dawo gida, a nan aka ce min ban ga komai ba indai gata ne da kulawa, daga gurin yan'uwan Ya Omri kamar wandanda basu taba samun haihuwa ba a dangi sai a a kaina haka suka rika kula ni kamar zasu dafa ni su cinye.
Madara aka siyo ana hada musu da ita domin nonon baya isarsu bama kamar mazan da ba su iya sha kadan ba. Kayan barkar da Ya Omri yai min sai kace hauka ne ko kuma be san zafin kudi ba, ban cin wadanda nai ta samu gurin yan uwansa da kuma nawa dangin domin kowa ya ji na haifi yan uku sai yayi mamaki kuma ya zo ganinsu.
Har abokansa ba a bari a baya na gurin bawa yaran kyauta da zuwa ganinsu ga su farare sol gwanin sha'awa ni kaina burgeni suke balle kuma ubansu da ya rasa inda zai dauka ya aje su wanda hakan shi yafi komai yi min dadi, at least na haifa wa wanda yasan darajar yaya kuma ya san kimata domin kullum a cikin tausayina yake da nuna min kauna.
Ranar wata Monday akai suna wanda ya kama sati biyu kenan, dayan aka saka masa sunan mahaifin Ahmad wato Muhammad wanda akai wa lakabi da Sudais dayan kuma aka saka masa sunan mahaifin Hajiya Abubakar aka masa lakani da Shuraim, mace kuma aka maida sunan Namra, sai dai ita ana kiranta da Little Namra.
An yi shagali iya shagali har abunda ban taba mafarkin za a raba ba anyi, a ranar daga ni har su mum sha bachin gajiya daman tun da suka zo dubiya ba su da aiki sai bachi sai kuma shan nono.
Kusan rabin rainon su a hannun Ya Omri na yake indai yana gida to babu ruwana da su sai idan nono za su sha ko madara, idan kuma baya gida ga Baba mai kula min da su ba ni da matsalar daukarsu dan wani lokacin shi da kansa zai musu wanka ko ya wanke musu kashi ko tsarki.
Sai da su kai shekara biyu da wata biyar sannan Ahmad yasa aka maido da su Namra da Amal da Aiman da Adnan a gidan, sai dai matan dakinsu dabam mazan ma haka, hakan kuma ba karamin faranta min rai yai ba, hakan ne ya kara tabbatar min da cewar lallai Ahmad ya rike yayana kamar nasa, lokaci lokaci Aminu kan kira shi ya tambayi lafiyarsu wani lokacin kuma sai ya aiko da mota a dauke su ya tafi da su yai musu shopping ya dawo da su, shi kansa rayuwarsa abar tausayi ce a yanzu domin matarsa bata haihuwa ba har yanzu wata kila ma su Namra da yak wulakantawa a baya su ne kadai ya'yansa tun da ita wacce yake aure ta riga ta lalata mahaifarta. Ga dan'uwansa wato Sadi ya zama aban tausayi domin ciwo ya kai shi kasa babu kyau gani, sam ba zaka ganshi kace shine ba, nikam hakan dadi yai min domin kuwa Allah ne ya nuna masa iyakarsa tun a yanzu kamin ayi wani hisabin a lahira....
Kiri da muzu Ya Omri ya hana ni zuwa barkar haihuwar da Suwaiba ta sake yi na macen da Abdallah baya so, duk kuwa da kasancewar ita din ta zo a lokacin dana haifi yan uku, sai dai mijinta be zo ba kuma be aiko ba be kuma kira ba. Sai na rasa yadda zanyi taya zata haihu na ki zuwa bayan kuma na sani, ai sai ga rashin kyautawa ta, da na san zai hana ni tun farko da ban tambaya ba sai na masa wata karyar na tafi.
“Idan ban je ba ba zata jidadi ba ko Mama ba zata jidadi ba kuma Wallahi ban kyauta ba, komai fa ta wuce abunda ya faru duk a baya ne”
Banza yai min yana ta wasa da yaransa sai kyalkyalar dariya yake shi da su kamar ma be san ina zaune a dakin ba. Can ya dago ya kalle ni.
“Magana kike?”
“Barkar Suwaiba”
“Idan ba bacin raina kike son gani ba ki daina min maganar nan, haka kawai ki taka ki tafi gidansa yai ta kallonki”
“Ba zanje lokacin da yake nan ba”
“Na ce ba za a je din ba, ko a munafunce ban amince aje ba”
Ya fada fuskarsa babu alamun wasa, har yanzu yaki yarda Abdallah ya daina so na ya kasa manta abunda ya faru na rasa wane irin kishi ne Ya Omri yake fama da shi ko mai sunan Abdallah baya so, Aminu ma dan ya zame masa dole ne. Duk yadda na so nai convincing dinsa ya amince fir ya ki a dole na hakura sai dai na siye abubuwa na bada nace a kai mata wanda na san hakan ba zai mata dadi ba.
Ranar wata Lahadi ina zaune dakina rike da waya ina chat ya shigo rike da wasu takardu ya zauna kusa da ni yana fadin.
“Ina tunanin bana da mu za a yi hajji”
Ban san lokacin dana jefar da wayar hannuna ba na tashi na fuskance shi baki sake ido har gurin gira.
“Da gaske?”
“Yes tun da yara sun yi kwari ai ya kamata ke ma ki kai ziyara, sai mu koma tare, idan Allah kuma ya amince mana kuma sai mu yi ummara idan lokcin yayi”
Rumgume shi nai cikin wata irin murna marar misaltuwa sai ya fara dariya yana fadin.
“Idan mun dawo zaki karo min yan uku”
“Har yan goma zan karo maka”
Ya fara dariya yana rumgume ni.
“Kamar gaske, salon kukan ya dawo ta fitina ko”
Murmushi nai sai ya rike fuskata yana kallon cikin idona kamar ba gobe.
“I love you so much”