← Book details Gobe Na Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 76 OF 136

Sashe 76

Gobe Na Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Wani irin dadi nake ji, a taimakon abincin da nake bashi a yanzu, ina jin cewar na bawa wani mai bukatar taimako taimako na, a kamfanin ma kowa yana mutunta ni kamar yadda nima nake bawa kowa girmansa, bana da matsala da kowa ga wasa da dariya sai kace daman can mun dade tare a aikin, bana fuskantar wata matsala a aikina sai dai fargabar abu daya, wato Mahaifin Baby Namra, tun daga lokacin da na fara aiki a kamfanin aka bani takardu da da magazine din kamfanin sai na gane cewar shine mai kamfani kamar yadda na lura da cewar shine mai makarantar da can da Abdallah ya cire su Namra domin a can mna ganshi kamar yadda na taba ganinsa a wannan kamfanin aau daya, domin hotonshi ne a jiki an rubuta masa shugaban kamfanin Ahmad Muhammad Gwarzo, sai dai ba kowa ya san haka ba kasancewar ba a saka hotonsa a kamfanin ba balle sunansa, kusan tun da na zo ban taba ganinsa ba, sai wacan ganin da nai masa a farkon zuwana kamfanin neman aiki.
A yanzu kam kullum a cikin fargaba nake ina karanta masa hasbunallahu da rokon kar Allah yasa ya ganni har na samu wani aikin na bar masa kamfaninsa, domin ina ji a jikina cewar duk ranar da ya gano ina aiki a karkashinsa sai ya wulakanta ni ya ci min mutumci kamin ya koreni.
Bayan shi ba ni da wata fargaba kuma ina jindadin aikina, ko ba komai kamfanin yana kusa da inda Abdallah yake aiki, hakan yasa na daukarwa kaina kullum da misalin karfe biyu na rana sai saka order an kaiwa Abdallah abincin rana a office dinsa, tun ina zuwa kullum na kai kudin har na fara biyan na wata wata, sai dai duk da haka Abdallah be taba kira wayata da sunan ya min godiya ko ya nuna min ya jidadin abunda nake masa ba, ko kuma ya gargade ni akan na daina ba, sai dai mai kai abinci ya fada min be taba cewa a daina kawo masa ba, tun daga lokacin da na fara aiki a kamfanin kusan kullum sai na turawa Abdallah sakon Barka da Safiya abun har ya xame min kamar ibada sai dai shi be taba maido min da amsa ba, idan na masa magana a whaspp ko fb sai ya karanta amman ba zai ce min komai ba, tun ina jin babu dadi har na soma sabawa da wannan sabon halin nashi.
Haka zai shigo gaishe da su Mama da Baba gida, ba zai ko kalle inda nake ba haka ba kuma ba zai hana na yi masa magana ba, wani lokacin ya kan amsa min sai dai idan na matsa da magana sai yai mana sallama ya tafiyarsa.
Gaba daya ya canja min taimakon da yake ba ni ya daina, sai dai ba shi ya dame ni ba kamar rashi sakin fuskarsa da kula ni da yake a yanzu, ga shi Allah ya dauki soyayyarsa da kaunarsa da tausayinsa ya cika min zuciya da su. A yanzu ta kai idan ba zancen Abdallah ba bana son labarin ko wane namiji, duk wata soyayya da nai wa Aminu da Abdulhamid a baya ashe ta karya ce a yanzu nake soyayyar da gaske, haka zan raya dare da begensa a zuciyata da tunanin abubuwan alherin da yai, da girma da yaraba hudu amman tunanin soyayyar wani ta hanani sukuni, idan na ga wani da sunansa sai na ji ya burgeni saboda kawai Abdallah.
Sai a yanzu na gane cewar na aikata kuskure babba na zabar Abdulhamid na bar Abdallah, a yanzu kam ina ganin laifin Abdallah kadan na cewa yana so a lokacin da igiyar aure take saman kaina, da farko ina daukar cewar fushi yake da ni daga baya kuma sai na fahimcin cewar kamar kokarin cireni yake a ransa ya nesanta kansa da ni, wanda hakan ba mai yiyuwa ba ni a tsakanin ni da shi, har ga Allah na tabbatar Abdallah yana so na, kamar yadda nake jin a yanzu da a raba ni da soyayyarsa kara a raba ni da raina.
Ko da Abdallah ba zai aureni ba ina son na saka masa da soyayyar da ya nuna min ni da yayana.

“Wai da gaske kike za ki shiga gasar nan?”

Kaina na dago na kalli Hafiza wacce tai min maganar ina murmushi domin na lura kamar bata yarda da zancen da nai na cewar zan shiga tare da yara a wasar da za'ayi Next Week ta children day ba.

“Why not? Ko dan farincikin yarana ai zan shiga, bani da matsala da kowa yanzu ba aure ke kaina ba balle na ce”

“Amman gaskiya matan hausawa ba sh cika shiga irin wannan ba”

“Ai dai mata suna shiga ko? To nima zan shiga idan na saka wando zan dora abaya a sama na saka karamin hijab dina”

Na fada ina jin cewar har a raina zan yi domin farincikin yarana kawai, domin a yanzu bani da damuwa sai ta yarana da iyayena sai kuma tawa, na tattara komai na aje a gefe, Aminu ma da ya matsa min na fada masa kotu zan kai shi idan be daga min kafa ba, sannan na jadadda masa matukar be saka Sadi a kotu an kwatarwa Namra hakkinta ba ba zan taba yafe masa ba, wanda nake tunanin abu nai wahala yai hakan ko dan Hajiyarsa na san ba zata bari ba.

“Yes Momy kuma mu za mu cinye....”

Aiman ya fada yana daga hannu tare da dariya, sai na gyada masa kai.

“In-Sha-Allah kuma idan mun yi ta daya, zan yi amfani da kudin na saka ku a wata makaranta private school so that ku samu karatu mai kyau, sauran kudin na rika juyawa ga aikina kamin lokacin biyan wasu yai na san zan samu na biya”

Namra ta yi karaf tace.

“Momy pls ki siya mana kayan wasa kuma pls”

“Zan iya muku, ki yi addu'a Allah yasa mu yi na daya”

“Amin kullum zan yi addu'a idan na yi sallah”

“Da alama dai wanda ya siya miki ticket din nan ke da yaranki yana ji da ke sosai, ko mother letter din nan fa kusan 20k ake bada ita”

Hafiza ta fada tana dago min wata farar takardar mai zagen kamar abun zinari.

“Kuma kin ga ticket ma na shiga gurin kawai 10k ne na shiga game kuma 30 domin ko baka ci ba za su baka wani abu wanda kuma yai na daya million daya da award da kallon azurfa, haka dai na biyu har zuwa na biyar, muma na ga alamar shi wannan bawan Allah da yake ta wahala da ke kamar ba ma sonshi kike ba, oh maza akwai daukarwa kai wahala”

Ta sake fada tana tabe baki

“Baki san waye shi ba, kin taba ganinsa?”

“No kawai dai naga yana ta kashe miki kudi ne hakan nan, ko jiya sai da Mama tai magana har tace zata same ki ku yi magana indai a aurenshi za ko yi ba, to ki sallame shi kar dawo daga baya yace sai an biyashi”

Shiru nai na dan wani lokacin, idan har Mama ta same ni da zancen ban san me zan fada mata ba, idan har taji cewar kafiri ne zata tsorota ta kuma nemi hanani kulawa wanda na daina tuntuni amman shi ya kasa janye kansa daga jikin kullum sai neman kara shiga jikina yake, na rasa yadda zan yi da shi babu bakar maganar daban fada masa ba babu irin gargadin da ban masa ba amman babu abunda ya canja.

“Yana da kyau Momy amma yana saka sarkar cross kuma yana sawan cin chewing gum....”

Na yi saurin rufewa Namra baki.

“Kar naji maganar nan gurin wani, duk wanda ya fadeta a cikinku sai na dokeshi, tashi ku shiga ciki... ”

A tsawa na yi musu maganar fuskarta babu alamar wasa hakan yasa duk suka tsorata har Amal suka tashi suka shige daki suka bar mu a waje ni da Hafiza, a kokarin dauke hankalinta daga zance na dauko mother letter din na rike ina tambayarta.

“Me ake da wannan hala?”

“Uwa ce zata rubuta tahirin rayuwarta da kuma yadda take kula da yayanta daga karshe sai ta rubuta daga uwar su wane da wane, sai ta saka a cikin dan box din wasika, idan mc ya zo shi zai karanta sai ya fada cewar daga uwar su wane idan anji an san ko su waye ake nufi”

“Wow abun ya kayatar”

Na fada ina jin cewar ni ma zan rubuta komai na rayuwarta a cikin wasikar da kuma yadda nake kula da yarana sai dai na zan fadi sunan da suna yara ba ba, ba so nake a san ni ba kawai dai ina son nao sharing tarihin rayuwata ga wadansu iyayene musamman abunda ya shafi Namra domin kawai ya zame musu darasi su kula da yaransa da kyau, ba kamar yadda ni nai sake har haka ta faru da yata ba, zan rubuta komai nawa a cikin har da rayuwar aurena a gidan Aminu da auren Abdulhamid da soyayyata da Abdallah, haukacewar da Kabir yai da kuma mutuwar Baby Namra fyaden da akai min akaiwa yata, sai dai ba zan fadi sunan kowa a ciki ba.

“Ke fada min ina kike hadu da shi?”

Ta tanbayeni daman na san za a rina, a banza ma Hafiza tai gulma balle wannan mai dalili. Abunka da yar'uwa duk kuwa da kasancewar ba uwar ma daya ba uba ne kawai amman bama boyewa juna abu idan ma ba wanda ya sani ba ba zai taba sanin cewar ni da Hafiza yan uba ne ba, domin a gidan m ba zaka taba sanin yan dakin Mama da kuma yan dakin Inna ba, kowa uwarmu ce idan Mama bata nan bama da matsala ko damuwa mun san Inna zata mana kamai, kusan Hafiza ma a dakin Mama take komai nata a can take yi wani lokacin ita da Mama har sirri suke babu wanda ya sani sai idan sun fada.
Kamin na gama bata labarin har mararta ta cika da fitsari, tsoro duk ya bayyana a idonta da jikinta.

“Bari nai fitsari na dawo”
Chapter 76 · 0% Book details