← Book details Gobe Na Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 39 OF 136

Sashe 39

Gobe Na Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

“Ban maka magana tun jiya ba, ina son naje asibiti marata tana min ciwo tun jiya na yi zaton ko zan ji sauki kamin yau amman ban ji alamun haka ba”

Na masa maganar a yayinda muke cikin karyawa. Dagowa yai ya kalleni sai kuma ya kai fork dinsa ya dauki dankali ya ci.

“Kina Menstruation ne?”

“Yes”

Mikewa yai tsaye kamar ya nufi dakinsa ya dauko wayarsa kamin ya karaso kusa da ni ya kira Abdallah.

“Kana asibiti ko gida?”

Ban san mi yace masa ba na ji dai ya sake cewa.

“Okay ga mu nan zuwa, Halima ce bata jindadi zan kawo ta yanzu”

A take na ji gabana ya yanke ya fadi, gashi bana son ya zargi wani abun balle na ce masa bana son Abdallah ya duba ni.

“Bari nai wanka sai n kai ki gidan Abdallah ya dubaki”

Kai kawai na iya gyada masa ya juya ya koma ciki, har yai wankan ya shirya ya fito ban samawa kaina mafita akan abunda zan yi ko na ce da zai hana zuwan gurin dan'uwansa ba.
A dole tasa na saka hijab dina na na dauki jakata da wayata na fice ina gaba yana baya har muka fito daga falon, a gaban motarsa naje na tsaya ina jiran ya karaso ya cire key din na bude sai ji nai an rumgumeni ta bayana.

“I love you so much”

A hankali ya fada min haka sannan ya sake ni ya danna keys din hannunsa motar ta fita daga lock. Front seat na zauna shi kuma ya shiga driver seat a usual, sai dai har muka isa gidan Abdallah be kalli inda nake ba be ce min uffan ba kuma ban ga wata walwala a fuskarsa ba, hakan yasa na fi kyautata zaton wata kila rashin lafiyarsa ce ya saka a rai ta hana ni sukuni a take tausayinsa ya rufe har idanuwa suka soma cika da kwalla. Sai da na sauke ajiyar zuciya sannan na bude motar na fita, wannan karon shi ne a gaba ni ina baya. Mun dan jima tsaye a gurin kofar kamin Suwaiba ta bude mana. Na yi kokarin kirkirar far'a na yaɓa a fuskata duk kuwa da irin halin da nake ciki, sai dai yau na same ta akasin yadda na saba samunta ko kuma na ce nake ganinta, domin tun da na auri Abdulhamid ban taba zuwa gidan da sunan kawo mata wuni ba sai yau shi ma kuma wannan da daliline.

Cikin falon muka shiga na zauna a saman cushion Abdulhamid kuma ya zauna kusa da ni yana ta kallona kamar ba shi ba. Bayan kamar minti biyar Abdallah ya fito a daya daga cikin bedroom din da suke falon. Shi ma dai fuskarsa babu walwala kamar ta matarsa, sai da ya mikawa Abdulhamid hannu suka gaisa sannan ya zauna ba tare da ya kalli inda nake zaune ba.

“Ina kwana?”

Na mika masa gaisuwa ina ta kallon zoben hannunsa, zoben da ba kasa samun natsuwa da shi har yanzu.

“Ina kwana”

Sai ya dawo min da gaisuwar still be kalleni ba sai Abdulhamid yake tambaya abunda yake damuna.

“Mararta ke ciwo”

“Tun yaushe?”

“Tun jiya, magani nake son ka rubuta mata”

“Ya kike jin abun?”

Wannan karon ya kalleni a yayinda yake tambayar tawa.

“Ina dan jin tana min ciwo ne”

“Sosai ko kadan and tun yaushe?”

“Jiya”

Tashi yai ya shiga daki, be dade ba ya fito rike da takardar magani ya mikawa Abdulhamid.

“Dan Allah daga yau idan matarka bata da lafiya ka kai ta asibiti direct ba sai sai nan ba, ko ba komai zata fi sakewa idan tana ganin mace yar'uwarta”

Ba Abdulhamid kadai ba, ni kaina da nake matar Abdulhamid na yi mamakin jin furuncinsa, wanda na tabbatar hakan be yi ma Abdulhamid min dadi ba ko kadan. Uffan be ce masa ba bayan kallonsa da yai ya karbi takardar tare da ce min na tashi mu tafi. Daga gidan Abdallah kai tsaye gidan Hajiya ya wuce da ni, ban so haka ba amman ban isa na nuna masa ba kasancewar mahaifiyarsa ce. Ita kanta ta lura da yanayinsa na rashin jindadi daman can yana fama da shi balle kuma yanzu da Abdallah ya kara masa da wata maganar.
A gaban idona take tambayarsa abunda yake damunsa sai ya amsa mata da cewar babu komai, daga bisani ya kalleni ya ce.

“Ki zauna a nan idan an dawo aiki zan biyo miki da maganin sai mu wuce gida, Hajiya ba ta jindadi shiyasa na kawo ta nan ta huta kamin na tashi aiki”

Ya karasa yana fadawa Hajiyar.

“Allah ya saukewa”

Ta fada tana dauke kai irin abun be dame ta ba. Shi kuma yai mana sallama ya tashi ya fice. Da kallo Hajiya ta bishi har ya fice sannan ta kalleni.

“Ke me ke damun mijinki?”

“Kwana biyu nan haka yake, kuma yanzu muka fito gidan Abdullahi ya kai ni ya dubani shine ya ce karya sake kawo ni to ban san ko shi ya bata masa rai ba”

“Husaini ne ya ce masa haka?”

A take ta daga wayarta a gurin ta jira Abdallah ta fada masa tana son ganinsa, abun ka da mai jiran kiran uwa a ko da yaushe, sai gashi ya zo cikin kankanen lokaci dama can babu tazara sosai tsakanin unguwarsu Hajiya da ta Abdallah.
Fuska a sake ya shigo kamar ba shi ne na tarar a can ya hade rai ba, ko dan wannan mahaifiyarsa ce oho. Bayan ya zauka Hajiya ta sallame ni ta hanyar cewa na tashi na ba su guri.
Ba musu n tashi na fita daga falon sai an samu guri kusa da kofar falon na zauna ina ta sake sake a raina, ta wani bangare raina fes yake da zubar jinin da nake domin na san indai ciki na zube a yanzu, ta dayan bangaren kuma ina jin tausayin mijina. Ban san abunda Hajiya tace masa ba sai dai na ga ya fito ransa a bace har ya wuce ni sai kuma ya juya ya nuna ni da yatsa kamar ba Abdallah ba.

“Ina ta kokarin ganin na fita daga hanyarki, ya kamata ke gane ke matar dan'uwana na ce a yanzu, duk wani abu daya shafe ni ko kika san zai saka dan'uwana kusantar da ke a gareni ki yi kokarin kauce masa, idan ba haka ba ran mijinki zai yi ta baci fiye da yadda kike zato kuma za ki jawa mijinki shiga damuwa fiye da wacce yake ciki...”

Idanuwa ne suka fara yawo a fuskarsa.

“Baka da tausayi Abdallah ba ka da kirki, ba ka san damuwar kowa ba sai ta ka, kai baka tausayin dan'uwanka ma? Bayan halin da yake ciki na damuwa kake neman kara saka shi wani? Kamar ba uwa daya ta haife ku ba? Abun da ya kamata ace ka taya shi tausayin kansa da neman lafiyarsa amman sai neman kara jefa shi a damuwa kake?”

“Babu ruwana da matsalar mijinki, ba tausaya min ba, dan haka babu tausayi a tsakaninmu samun lafiyarsa ko zamansa haka har a bada be dame ni ba saboda shi ma be bar ni na samu farinciki na ba”

Kallon mamaki nai masa.

“Ya kake kokarin aron wadansu dabi'u da halaye marar kyau ka yafawa kanka Abdallah, kana abu kamar ba kai ba? Dan'uwanka jininka? Wallahi Abdulhamid ba zai taba yi maka abunda zai hana ka samun farinciki ba, ba ka da kirki da halin kwarai shiyasa baka taba burge ni ba, kana da son kanka da yawa shiyasa ban tana jin son ka a zuciyata ba....!”

Fadada fuskarsa yai da murmushi kamar ba shi ba.

“Wani lokacin Wallahi mata ba ku da hankali”

Yana fadar hakan ya juya ya nufi gurin motarsa.

AHMAD POV.

Tura kofar falon yai ya shiga da sallama, Momy ta amsa masa tana rike da wayarta.

“Dan halak, yanzu nake kokarin kiranka fa, tun da ka fita baka dawo ba”

“Ban dade da fita ba ai”

Ya fada yana kokarin zama.

“Eh na sani, bana son kana yawon nan idan ba aiki ba ko wani uzurin”

“Haba Momy sai kace wani karamin yaro”

“Ba zaka gane ba ne ai, yan mata yanzu shegen wayo ne da su a take za su ci maka kudi su gudu, kuma na sna indai ka bar gidan nan ba iya kula kake da kanka ba”

“Yanzu ni kamata yan mata za su yi wa wayo?”

Ya nuna kansa.

“Hmmm Baka san mace ba, har yanzu kai yaro ne, ka ci abinci?”

“Eh na ci abinci”

“Ka koshi?”

Murmushi yai yana ta mamakin yadda Momy take ta maida shi karamin yaro, sam ta ki yarda shi din namiji ne kamar kowa, sometimes har mamaki yake shi dai yasan ba girma ne be da shi ba balle ace tana ganinsa da karamin jiki, shiyasa wani lokacin ko yana bukatar baya nunawa saboda kar ta samu damar yi masa haka. Baby Namra ce ta fito daga bedroom dinta tana masa oyoyo.

“Daddy sannu da zuwa”

Ya mika hannunsa ya rikota.

“Yauwa darling y scul?”

“Fine Daddy wannan Name sake din tawa ta tafi”

“Yeah Momy ta zo ta dauketa did you miss her”

“Yes Daddy”

“Ke da kika ce ba ki sonta?”

“Yanzu kuma na ji ina sonta, daddy za ka kai ni gidansu?”

“Ban san gidansu ba”

“Pls daddy”

“I'm serious”

Ya fada yana kara gyara mata zama a jikinsa, har cikin ransa yake jin son yarsa fiye da komai a rayuwarsa, musamman idan ya tuna cewar bata da mahaifiya a raye.

“Idan kin je makaranta ki tambaye unguwarsu sai a kai ki”

Wannan karon Momy ce take maganar.

“Wane class take Momy?”

“4 tace min kamar 4 kamar 3 na manta dai ki bincika”

Da sauri ta gyada kai tana murmushi.
7/21/21, 10:44 PM - Buhainat: *GOBE NA...*

By Khadeeja Candy

*Gaba daya littafin nan Sadaukarwar ne ga Zainab A Baba💖*

2️⃣2️⃣

AHMAD POV.
Chapter 39 · 0% Book details