← Book details Gobe Na Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 50 OF 136

Sashe 50

Gobe Na Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Wani abu na ji kamar ya netse a kasa, saboda ya san people would think ko ya mata wani maganar banza ne. And she's right be kamata yai magana da matar aure ba, dan idan shi ne wani nai magana da matarsa zai iya masa komai ma, but shi ya manta da maganar aurenta ma.
Oh does she think sonta yake yi? Ko kuma ta maida shi wani banza ne take fada masa haka, har ya shiga motar be daina sake sake ba.

“She got lucky bana fada da mata, amman wallahi da namiji ne yai min haka sai an dauki gawarsa a nan i hate nonsense”

Ya fada yana fisgar motar kamar zai tashi sama, after few minutes ya bugu sitiyarin motar da karfi.

“Matar nan ba tai ba, i hate her so much, da ganinta mahaukaciya ce”

Ikilima dai bata ce masa komai ba bayan kallonsa da tai, tsoro dai ya gama kamata dan ta lura ransa ya bace sosai.

“Ai duk laifinki ne da kika kawo ni gurin nan, da ta isa tai min kallon banza ma, amman ji irin maganar da ta fada min son ranta, sai yanzu ai na gane bakar magana ta fada min”

Nan da nan jikin Ikilima ya fara rawa domin ta lura har fuskarsa ta canja sa gumi yake kamar marar gaskiya duk kuwa da irin ac da ke cikin motar.

“Har da wani wai kana jin kai wani ne, ai ni wani din ne ke ba kowa ba.... Mtchhhh”

Yaja tsaki yana jin kamar a gabanta ne ya rama, domin a duniyar nan yafi tsanar tsaki fiye da komai, da ka yi masa tsaki ko ka tofar masa da yawu kara ka mare shi ko ka zage shi.....
7/21/21, 10:44 PM - Buhainat: *GOBE NA...*

By Khadeeja Candy

2️⃣7️⃣

Na isa gida cikin bacin rai, ban taba jin na tsane wata halitta kamar yadda na tsani wannan mutumen ba, a yadda na fahimci rayuwata ina ta faduwa da mazaje marasa mutunci, maso sun su taka ni yadda ransu yake so, wanda ni kuma nake ganin ba zan dauki hakan a yanzu ba, na gama indai kuka ne akan wani namiji ko shiga damuwa akan wani namijin ba zan sake bari wani ya saka ni damuwa ba.
I can live without aure indai har zan iya tsare kaina da mutumcin na tarbiyantar da yayana, zan iya shiga aljanna, haka zuciyata ke raya min i feel like idan har Abdulhamid ya sake ni ba zan sake wani auren ba, zan cigaba da aikina ina kula da yayana, zan nemi ya sake ni bana bukatar sake zama da shi ji nai na tsani duk wani namiji a duniyar har na rika jin na matsu ya dawo gidan, kamar ance min da ya dawo zai rubuta takardarta ya ba ni.
  Maganin da na siyo dan na sha na samu bachi ne ammn sai bachin rai ya hana ni sha. Wani irin kuzari da karfin hali nake jin yana ratsa ni, i feel like ko da duniyar nan za su taru su tsane ni i can live, even for the sake of my children right? Yes this is right time da zan nunawa duniya wacece ni, wannan lokacin ne ya kamata na amsa suna, i don't know what the future bring ban ce ba zan sake facing wani challenge ba, but zan iya jurewa zan iya daurewa daga lokacin na fara rayawa kaina cewar gobena mai kyau ce. Na yi kuka a lokacin da na ke fuskantar wulakanci a gidan Aminu, na yi kuka a lokacin da akai ma Namra fyade, na yi kuka a lokacin da Aminu ya sake ni, na yi kuka a lokacin da akai min fyade, amman hakan yana nufi sai na zauna nai ta kuka akan komai akai min na bar damuwa a raina? No be kamata na karaya ba, be kamata na lauyewa kaina hakkina dan ina mace ba! I have to say it out loud, i have to fight for my right.

Kamin dare yai Abdulhamid ya shigo duk na matsu sosai, saboda irin abunda na kudirewa zuciyata, ban girka komai ba har dare, can bayan sallah isha'i sai gashi ya shigo gida kamar yadda ya saba, da ada ne ko be yi sallama ba ya shigo zan masa sannu da zuwa amman a yau sai na ji ba zan iya yi masa hakan ba. Ga duka alamu yau da yunwa ya dawo, domin yana dawowa ko dankinsa be shiga ba ya nufi dinning rike da wasu takardu a hannunsa. Ganin babu abincin a dinning din yasa ya juyo ya kalleni.

“Ina abinci?”

“Ban girka ba”

Daga inda nake zaune saman kujerana bashi amsa kai tsaye. Be sake cewa komai ba ya tashi ya nufi hanyar dakinsa yana shiga na rufe masa baya, sai na same shi yana kokarin cire rigar shaddar da ke jikinsa, hango shigowata ta madubi da yai ne yasa ya tsayar da cire rigar ya juyo ya kalleni

“Kina son wani abu ne?”

“Ina son sanin result din gwajin da nai nake son sani”

Juyowa yai da kyau yana kallona for like ten seconds sai kuma ha dauke idonsa daga kallon da yake min ya kalli wani gurin dabam.

“Positive....”

“Al-hamdulillah.... Abu na biyu kuma ina son ka san cewar komai yana da lokaci kuma yana da iyaka, a lokacin da na aureka babu wanda ya cilasta ni ra'ayin kaina ne, and now mun gaji we need some space”

Sake kallona yai a karo na biyu kamar wanda be fahimci yarena ba, wata kila kuma yana mamakin furucina ne.

“Saki na ke bukata...!”

I say it..

“Are you sure? Ba ki bukatar sake shawara ko tunani”

Shine abunda ya fito daga bakinsa, sai kuma ya matsa kusa da ni ya kai hannunsa biyu zai dafa kafadata, ni kuma nai saurin matsawa.

“Bana bukatar ko daya”

Sai da ya hade yawun bakinsa sannan ya furta.

“Shikenan zan ga abunda zan iya yi akai”

Yana fadar hakan ya juya ya cigaba da cire rigarsa ni kuma na fice na bar masa dakin. Ko kadan ban ji kuka a tare da ni ba kamar yadda na saba yin kukan a duk lokacin da wani abun bacin rai ya same ni, but i feel bad ina jin na yi abunda be dace ba, miyasa ba zan jira har zuwa lokacin da shi din zai bukaci sakina ba? Why? Bana da wata hanyar ne sai wannan idan har zan jira to zan cigaba da kashe kaina ne da rai na. Can bayan na yi sallah isha'i ina kokarin kwanciya ya shigo dakina ya aje min takeway ya fice.

AHMAD POV.

Hajiya na kallonsa ta san danta yana cikin bacin rai, sai dai ta yi shiru ne saboda ta saba masa haka a duk lokacin da yake cikin damuwa idan har taji bata ji yace mata komai ba sai ta tambaya.

“Hajiya yau ko?... No first of all ita wannan yarinyar da kika saka na kai gida wacece ita?”

“Sai ka fara fada min damuwar”

“Wallahi wata bad luck na hadu da ita yau, ban taba jin na tsani mace kamar yadda na tsani matar nan ba, i hate her... ”

“Me tai?”

Kadan ya gutsurawa Hajiya labarinta yana ta tsaki.

“Kai ma ai be kamata kai haka ba, ko dan yarta na abota da yarka, sannan matar aure ce akan me zaka tare ta a hanya da sunan ba ta hakuri? Kai yanzu yadda kake da kishin tsiyar nan wani ya isa ko kallon matar ka yai?”

Kallon Hajiya yake da mamaki he thought zata bashi gaskiya ta bawa wacan rashin gaskiya ne.

“Okay....”

Sai yai shiru, kamin ya sake tambayarta.

“Ita wannan yarinyar fa?”

“Yarinyar nan da ka gani bazawara ce”

“What....?”

Ya tambaya da mugun mamaki domin a tunaninsa budurwa ce, a yadda ya ganta yarinya karama.

“Yes ta yi aure bata dace ba mijinta har dukanta yake kuma ta hakura ta zauna har sai da yan uwanta suka kashe aure, sannan gidansu mahaifiyarta ita ce ta hudu, so ta san  halin rayuwa tun da ta taso a gidan yawa kuma duk mace da zata yi hakurin zama da miji mai duka zata iya hakurin zaman aure a ko'ina, shiyasa na ke son idan ta maka ka aureta”

“Aure yanzu Hajiya? Hajiya ba tai min ba, abu kamar ta tsinke ni bana son mace ramanmiya irin wannan, and kin san abunda ba zai taba yiyuwa ba ne na auri matar wani Allah ya sauwake, ba zan taba auren bazawara ba, ba zan iya auren matar da wani namijin ya aureta ya sake ta ba, ko kuma mijinta ya mutu har a bada, Hajiya ke ma kin san wannan”

“To wai miye a zaurawan nan ne? Haba Gwarzo, na aje wannan akidar dan Allah ni fa yan matan nan na yanzu ba yarda zan yi da su ba, kara wacce tai aure ta dandana dacin auren zata fi iya zaman aure a gidan nan”

“Ba dai bazawara ba Hajiya”

Ya sake nanatawa sannan ya tashi ya fice daga falon, part dinsa ya nufo har yanzu zuciyarsa cike da take da bacin rai abunda ya faru.

“Imagine wai ni matar nan ta tsaya ta fada wa maganar banza wai... Wani ni Ahmad hmmm”

Yayi kwafa sannan ya tura kofar falonsa ya shiga gumi na karyo masa, daman can haka yake da ransa ya bace sai ya fara gumi jikinsa yai zafi sosai kamar marar lafiya, idonsa ma a take suke canja, zuciyarsa kuma tai ta wani zillo kamar ta fito, shi kansa idan ransa ya bace baya iya controlling kansa, that's why yake taka tsantsan yana gujewa duk wani abu da zai kawo masa bacin rai.

AMINU POV.
Chapter 50 · 0% Book details