← Book details Gobe Na Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 124 OF 136

Sashe 124

Gobe Na Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Na lake kafada alamar ba zan fada ba, shi kuma ya kware min ido kamar mai yi da karamar yarinya. Sai da suka fice sannan na shiga bandakin nai alwala na fito na zauna bakin gado har sai da ya gama sannan ya tashi ya dawo saman gadon ni kuma na hau carpet din nai sallah, babu komai a addu'a ta sai nemawa Ahmad lafiya da rokon Allah ya tsare min shi. Sai da na shafa addu'ar sai ya miko min hannunsa na hagu, na rika na tashi tsaye sai ya dawo da ni kusa da shi na zauna, sai ya saka hannunsa saitin kwankwaso na yana ta wasa da shi, ya dora gemunsa saman wuyana sai yasa ta bakinsa ya janye mayafin kaina ya sauko kasa, bakinsa saitin kunnena.

“Na fadawa Hajiya ta sa a shirya miki ticket mu tafi tare”

“Amman Ahmad tun da ance ba a ga komai ba why not a yi addu'a kasan wani lokacin iska da kandu suna yin haka fa”

“Ba laifi ya zama iska ba, kin san Nigeria ba mu da irin wannan cigaban yanzu za a iya zuwa a can su yi gwaje gwajensu kuma a gano matsalar”

“No ba na asibiti ba ne”

“How do u know?”

Kamar mai rada haka yake min magana in each word sai ya tsotsi kunnena sannan yake fadarta wani sa'in kuma sai ya busa min iska a kunnen. A kalleshi a natse na ce.

“Baka fada min tun daga lokacin da ka gaisa da Abdallah ne abun ya same ka ba”

Sakina yai yasa hannun nasa ya rike fuskata.

“Ina kika je dazun?”

Na yi shiru.

“Ba gida kika je ba, na sani dominbda suka zo sun tambaye ki kuma Mama tace kin buga mata waya kina kuka, i suspect something fada min ina kika je? Don't lie to me”

“Magana nai da Abdallah....”

A take fuskarsa ta canja.

“As how?”

“Akan ciwon ka ne”

“Oh ya Allah, taya za ki je ki yi magana da shi? Kin san ko tunawa nai akwai son ki a zuciyarsa sai naji kamar na kone, akan me za ki je ki yi magana da shi? Lims why? Is not allowed ya ji muryarki ma ji drees dinki ma, gown ce fa sai mayafi Babe why?”

Ya karasa kamar yai kuka, hakan kadai ya isa ya karantar da ni irin zafin kishin da Ahmad yake da shi, so idan har zan zauna da shi dole nai tsaka tsantsan da rayuwarsa.

“Saboda na san shi yai maka kofi, kuma da na masa maganar ya amsa min da cewar shi din ne, tun da yana jin haushinka na san dole zai maka, shiyasa na ce maka ba na asibiti ba ne, ya yi ma dan'uwansa kuma ni ma ya sha min”

“Ba kofin ya dame ni ba, maganar da kika yi da shi ta dame ni, Allah kadai ya san abunda ya ce miki kila ma yace Halima ina son ki”

Na dan zaro ido.

“Aa be ce ba fada fa mukai da shi”

“Fada did he touch you”

“Oh oh No ba irin wacan fadan ba, fada na baki”

Ture ni yai daga jikinsa.

“Daga ni dan Allah”

“I'm sorry, amman na damu da halin da kake ciki ne”

Ya fada ina kada kafata domin tafiyar abu nake ji kamar ƙuda, ina jijjiga kafar na ji abu ya fado mai nauyi, saurin mikewa nai tsaye sai ganin kunamu nai har uku a inda kafafuwana suke, ban san lokacin da na daka tsalle na dale saman gadon ba ina ihu.

“Ka gani ko? Ya fusata da ni shine yai min kunamu nan”

“Shiiiiiiiiiiii karki bari Hajiya ta ji maganar nan”

Ya fada yana rufe min baki.

“Shiyasa na fada maka cewar ciwon hannunka nan ba na asibiti ba ne, ayi maka addu'a zai fi sai ka mu sauki”

Na fada kamar zan fashe da kuka, jana yai jikinsa ya rumgume.

“Amman kin san yanzu an riga an gama shirya komai Hajiya ba zata yarda a fasa ba, kuma zuwan ma yana da amfani ko ba kuma hakan zai kara tabbatar da maganarki kuma Hajiya ba zata zargi komai ba”

“Amman taya za a samu maganin kofi a asibiti? Ahmad kai tunani mana”

“Okay fine zan yi magana da Hajiya sai nace mata a hada da addu'a hakan ya miki?”

“Eh ni ma kuma za ki rika maka fatiha kafa bakwai kullum da safe a ruwa kana sha idan zaka iya shan yawuna”

“Hmmmm har abunda ya fi yawunki ma zan iya sha, kin san minene”

Ya fada yana shinshinata tare da dora hannunsa saman cinyata.

“A a bana son sani”

Sai yai murmushi ya sauka saman gadon ya dauki takalminsa da hannunsa na hagu ya kashe kumamun dake ta yawo a cikin dakin sannan ya dawo ya zauna a inda nake yana kokarin kai hannunsa kirjina aka tana kofar da sauri na dauki mayafina na rufe kaina shi kuma ya dauke hannunsa daga jikina.

Yunus ne ya shigo rike da ledodi a hannunsa, after sun gaisa da Ahmad ya gaisa da ni sai kuma ya soma zolayata.

“Amarya ashe ashe ba mu sani ba....”

Wani kallo Ahmad yai min hakan yasa ban biyewa wasan da yake min ba.

“Yunus ka fa san ni bana son wasa da iyalina please take note”

The way da yai masa maganar babu wasa ko kadan a tare da shi, sai dai hakan be hana Yunus din yin dariya ba.

“Daman na zo ne na dauke ta ayi mata hoto Hajiya tace a shirya mata komai da ita za a je”

“Ban gane ka dauke ta ayi mata hoto ba? Ta dai baka hotonka karami ko?”

“Ba shi kadai ba ka san za a mata passport”

“Okay kuma kai zaka kaita ayi mata”

“Alhaji bana da matsala idan kai zaka shige gaba ayi mata komai, yanzu dai ya jikin naka?”

“Al-hamdulillah zan mata komai”

Ya fada yana kallona. Sun dan dade suna fira kamin yai mana sallama ya tafi. A lokacin ne na zuba mana abincin a plate daya ni da shi, be wani ci sosai ba hakan yasa nima na ji ba zan iya ci ba, ya bukaci na hada masa tea.

“Shiyasa ka rame baka cin abinci”

“Sai na samu lafiya zan ci abinci na koshi na more”

“Ba gashi na zuba maka yanzu ba ka ci ba”

“Ba wannan abincin ba, wacan abincin wanda aka dade ba a hadu ba, kuma na yi marmari da yawa”

Murmushi nai ba tare da na kalleshi ba na cigaba da hada masa tea, da na kawo masa masa be karba ba sai yace na bashi da kaina, haka na rika ba shi tea kamar wani karamin yaro.

“Sha mana”

Na kurba kadan na bashi ya sha, bayan ya gama mukai sallah isha'i. Ban tashi daga saman carpet din ba sai ga Hajiyarsa ta shigo tana tambayar ko akwai abunda muke bukata.

“Sai dai ko shi ni ai gidan zan tafi”

“A a nan za ki kwana, wannan kuka da kuka min dazun idan kika je gida ai sai ki yi mafarkin kukan kuma”

Ta fada tana murmushi ni kuma nai kasa da kaina kunya ta rufe ni, Ahmad kan dariya yasa kamar ba shi ba.

“Ashe dai ana so na”

Kasakasa na wasa masa harara. Sai Hajiya tai murmushi.

“Allah dai yai muku albarka kuma ya ba ka lafiya ka koma gida cikin iyalinka”

Daga ni har shi muka amsa da amin, sannan tai mana sallama ta fice. Duk yadda na so ya kwanta saman gadon ni na kwanta kasa sai yaki, ala dole sai dai mu kwanta saman gadon a tare ko kuma shi ya sauko kasa mu kwanta.

“Gadon ai ba zai dauke mu ba”

“Ai ba dole sai mun wadata ba, ko kuma mu kwanta kasa”

“Ya za'ayi kana rashin lafiya ka dawo kasa ka kwanta?”

“Kin san dai ba zai yiyu mu kwana daki daya kuma a daban daban ma wannan ai haramun ne ma”

“Inji wa?”

“Inji ni”

Ya nuna kansa, ban san lokacin da na saka dariya ba. A dolen dole muka kwanta kasa ni da shi, muka lulluba da Bedsheet daya yadda ya rumgume ni a jikinsa yana shafa ni kai ka rantse da Allah ba ciwo yake ba.
Da asuba sai da na dumama masa ruwa yai wanka ni kuma na shiga nai alwala ko da ya fito na gama sallah na gaishe shi na shimfida masa carpet din yai sallah bayan ya gama na karanta masa fatihar ya sha sannan na hada masa tea.
Misalin bakwai da wani abu direbansu ya kawo mana breakfast ba laifi nan ma da na zuba mana ya ci wata kila saboda mun ci tare ne ko kuma dan na yi magane jiya yasa yau ya ci oho. Sai tara da wani abu mahaifiyarsa ta shigo, ni kuma na fita na basu waje. Ina tafiya wayata tai kara alamar shigowar sako, number Abdallah ce.

“Ina fatar mijin da kika aura ya rike ki amana Halima, i wish you all the best
....”

Shine abunda ke rubuce a cikin sakon, ban miya sa ba sai duk na ji wani iri. Har na koma dakin jikina a sanyaye yake.

“Na yi magana da Hajiya akan ko a daga tafiyar nan har gaba sai ce ba zai yiyu ba, amman dai ta aminta za a saka da addu'a din”

Ban ce masa komai ba na hau saman gadon na zauna na dora kaina sama wuyansa.

“Babe are you okay?”

Na kalleshi.

“I'm fine, Allah ya baka ikon rike ni amana”

“Amin”

Ya sumbaci goshina.

“Ba zako taba kuka da ni ba In-Sha-Allah i love you so so so much”

Ya fada try to hug me with both hands.

“Baka jin ciwo ne?”

“Da sauki dai gaskiya”

Murmushi nai na rumgume shi. Ban dauka da gaske yake ba har sai da muka je tare da shi aka min komai na tafiyarmu a yadda nake ganinsa na jidadi domin baya nuna alamar ciwon ko da akwai ma yana boye min, domin ya fada min duk bayan awa uku sai hannun ya taso masa da ciwo amman yanzu kam Al-hamdulillah.
Chapter 124 · 0% Book details