← Book details Gobe Na Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 121 OF 136

Sashe 121

Gobe Na Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

“Amman ba can yace min ya tafi ba”

Wani abu tai da ido tana yar dariya kamar marar gaskiya.

“Eh na tuna daga jos zai wuce can garin da yace miki zai tafi...”

“Wane gari?”

Na sake tambaya ina ta kokarin gano gaskiyarta, sai ta fara kame kame wanda hakan yasa hankalina ya kara tashi.

“Can inda yace miki, Kadu.... Na....”

“Ni Abuja yace min”

“Eh eh daga Jos din zai je Kaduna da Abuja, daman Abujar ya kamata nace tun dazun sai na fadi wani gari”

Ta karasa tana murmushin rashin gaskiya. Hannayenta na kama biyu na rike cikin wata irin siga ta magiya na shiga rokonta.

“Dan Siyama idan akwai wata matsala ki fada min”

A iya abunda zuciyata ta raya min Ahmad na cikin gidan yace ace baya nan, hakan na nufin Hajiyarsa ta hana shi ganina kenan ko kuma wata matsalar ce ta dabam daga sashenta. Sakin hannayen nawa tai tace.

“Ina zuwa”

Juyawa tai ta koma cikin gidan, ni kuma na tsaya a gurin zuciyata kamar zata fito, hawaye sai wanke min fuska yake ina sharewa, a yanzu kam idan har ta tabbata Hajiyarsa ta shiga tsakanina da Ahmad ban san ya zan yi ba, wata kila akwai matar da take son ya aura ba ni ba shi kuma ya aure ni ba d amincewarta ba, indan sabon da tsanar uwar miji na saba sai dai bana jin cewar zan iya jure wannan idan har ya tabbata abunda nake zargi ne.

“In-law Hajiya tace ki shigo”

Dagowa nai na kalleta idona da hawaye na girgiza mata kai.

“A a zan tafi dai, ki ce ina gaishe da Ahmad din”

“Ba zata jidadi ba idan kika tafi ba ki shigo ba, bayan kuma ita da kanta ta bukaci haka”

“Ina tsoro kuma ina jin kunya”

“Akwai maganar da Hajiya take son fada miki dan Allah ki shigo ko kuma naje na kirata”

Na yi saurin dakatarta ita.

“A a dan Allah”

“To muje”

A dole na bita a baya bayan na share hawayena, babu abunda zuciyata take raya min sai irin cin mutuncin da Hajiya zata min ko kuma gargadi, a lokacin ne naji ina ma ace ban zo ba, kamar wata marar gaskiya haka na shiga falon sai na tsaya daga bakin kofar na zauna jikin wata karanar kujera mai kamar ta kwalliya dake jikin kofar, ita kuma Siyama ta nufi dakin Hajiyar, ni kam gabana sai faduwa yake har yawun bakina daker nake hade su, ina jin motsin saukowar Hajiyar gabana ya kara faduwa.

“Ahhhh Haba dai Siyama ya zaki barta a bakin kofa? Yanzu idan Yayan ki yana nan Wallahi kin san sai yace mun wulakanta masa mata”

“A a Hajiya ita ta zauna a can daker ma fa ta shigo cikin falon nan”

Siyamar ta fada tana rigan Hajiya zaunawa. Hakan yasa na dan dago kadan na kalli Hajiya tare da mika mata gaisuwa sai ta amsa min da murmushi.

“Lafiya kalau taso dawo nan Yata”

Ta fada tana taba kujerar da take zaune wacce ta zaman mutum uku ce, ban iya musa mata ba na tashi na koma a inda ta bukata wato kusa da ita na zauna a kasa wata irin kunya na kara rufe ni, ai kam da kunya ace na so neman miji har gidansu!

“Kawo mata abinci da lemu Siyama”

Umarnin Hajiya Siyama ta bi a gabana ta jera min kula biyu wacce nake kyautata zaton tuwo da miya ne ko shinkafa da miya, sannan ta kawo min lemu da ruwa da kofuna ita da kanta ta bude lemun ta zuba min a kofi sannan ta koma ta zauna. Kunya ta hanani ko da kallon nemun balle na dauka na sha.

“Hajiya zan tafi”

Na fada ina mikewa tsaye cike da kunya.

“A a ko abincin ba ki ci ba?”

“A a koshe nake”

“Ba Ahmad kika zo nema ba? Zauna mana”

Hakan da tace sai yasa kunya ta kara rufe ni.

“A a daman... ”

“Zauna Yata ke ma kina da hakkin sani”

Cewar kina da hakkin sani yasa na koma na zauna cike da son jin ko minene.

“Yata... Mijinki ba shi da lafiya Siyama ta fada min cewar yace miki ya tafi Abuja, be je ko'ina ba yana asibiti, yace miki haka ne saboda baya son a tashi hankalinki, ni da Siyama duk ya roki kar mu fada miki halin da yake ciki, sai dai na fada miki ne saboda ke matarsa ce kuma kina da hakkin sani, na san ya mace na da kunya da kawaici tun da har kika iya zuwa nan dan jin lafiyarsa aiko kin nuna mana kauna, ya kamata ke ma ki san halin da yake ciki”

Tun da ta fara maganar na ji zazzabi ya rufe ni, a razane na kalleta.

“Hajiya me ya same shi? Dan Allah ku fada min”

Na juya gurin Siyama ina hawaye.

“Rashin lafiya ce ki kwantar da hankalinki da sauki ai sosai, yanzu haka na gama shirin fitar da shi waje jibi zamu tafi”

A take jikina yai sanyi gaba daya sai na nemi kunyar da nake ji na rasa na kama kafafuwan Hajiyar na rike.

“Dan Allah ku kai ni na gan shi, ina bukatar ganinsa dan Allah”

“Siyama tashi ki kaita”

Hajiya ta fada ita ma hawaye na sauko mata kamar yadda Siyamar ma take balle kuma ni da kuka ya zame min abinci. Da sauri Siyama ta tashi ta nufi dakin da nake kyautata zaton nata ne bata dade ba ta fito rike da dan mayafi da makullin mota, ni kam jiki na rawa na tashi na bi bayanta, kusan a tare muka shiga motar domin zuciyata sa ya soma raya min abubuwa marasa dadi. Wayarsa na soma kira wannan karon ma sai da tai ringing ta katse ba a daga ba.

“Idan yana cikin azabar ciwon baya iya daukar kira”

Siyama ta fada tana tuka motar tana kallon sunan yayanta dake gaban wayata, ji nai kamar ba zan iya hakura ba sai na sake kiran na ci sa'a ya daga.

“Hello Lims...”

Sai na kasa magana saboda bana son yaji kukana.

“Lims.... Lims.... Lims....”

Haka yai ta kirana amman na kasa amsawa daga karshe na kashe wayar gaba daya, sannan na kalli Siyama na ce.

“Tun yaushe ne ba shi da lafiya”

“Wacan asabar din da ta wuce, yace ya ji abun yana driving be ma iya kawo kansa gida ba sai da ya kira driver ya tuka shi ya kawo shi gida saboda hannun da ke masa ciwo, yace mana be yi kwana ba saboda azabar ciwo kuma da aka je asibiti aka auna sai aka ce ba a ga komai ba”

“Mi yake damunsa?”

“Ciwon Hannuna ne, wani lokacin har cikin jikinsa yace yana jin abu, idan ya taso masa sai an daure ko kuma an masa allura sannan yake samun sauki”

“Hannun ya bugu da wani abu ne?”

“Mu dai be fada mana ba gaskiya, yace cikin dare ya soma jin abun”

A gurin da aka tanada dan aje motoci ta aje motarta muka fita kusan har na fita sauri ma duk da ban san inda yake ba har sai da ta shiga dakin da kanta ina binta a baya. A zaune muka same shi an daure hannunsa na dama da belt dayan hannunsa kuma rike da waya. Yana ganina ya watsawa Siyama wata muguwar harara wacce ta saka ta kasa karasa cikin dakin.

“Zuwa kikayi kika dauko ta ko?”

“A a Wallahi ita ta zo...”

“Shut up.... Ban fada miki kar a fada mata ba? Ko ban fada miki tana da hawan jinin ba?”

“Yes amman..... ”

“Fita ki ba ni waje.... And if wani abu ya samu matata i swear sai kin yabawa aya zakinta”

Cikin tsawa sosai yake mata fadan ya ma kasa tsayawa ya saurareta, da sauri ta juya ta fice tana kuka. Nima da nake tsaye bakin kofar kuka nake ina kallonsa yayi wani irin mugun rama sosai kuma kana ganinsa kasan ba shi da wani kuzari.

“Kin gani ko? Saboda kukan nan yasa nace kar a fada miki yanzu sai ki tashi hankalinki....”

“Amman ina da hakkin sani, ni matarka ce, a iya tunanina babu wani boye boye a tsakaninmu, be kamata ka boye min wannan ba.... ”

Na fada cikin kuka, sai ya aje wayar ya miko min hannunsa na hagu, ni kuma na taka na karasa kusa da shi na kama hannun na rike.

“Can you please hug your husband”

Na rumgume shi kamar yadda ya bukata ina fashewa da wani irin kuka mai taba zuciya. Da dayan hannun ya rika shafa bayana yana min magana a hankali kamar yadda ya saba.

“Babe please kukan kin nan yana taba min zuciya, bana son wata damuwa ta same ki shiyasa na ce kar a fada miki”

“Daman na sani.... Shiyasa nake tsoron rabar mutane ko kuma mutane su rabe ni... Saboda wani.... ”

Ban karasa ba yasa hannunsa na hagu ya dago fuskata ya hade bakina da nashi, we spend more than 5 minutes muna abu daya kamin ya cire bakinsa ya hade goshinsa da nasa.

“I miss you....”

Ya fada cikin rada.

“Daman can ina fama da ciwon kirji kuma kin sani, to shine yanzu ya sauko min har a hannu, so ki daina canfa kanki idan kina haka haka ne zai ta sakancewa da ke, Allah yasa dai baki fadawa Hajiya wannan maganar ba? Kar ki sa ta fara zargi ta tsorata ta dauka da gaske ne”

Na girgiza kai a hankali hawaye na sauko min.

“Ban fada ba... Amman....”

“Amman.... ”

Yaja hancina sannan ya saka hannun ya share min shawaye.

“Karki sake irin wannan maganar, tun before na aure ki nake jin wannan ciwon yafi min tsanani a yanzu kawai pls smile”

Ya fada yana jan kumatuna, all what i try to do is na tsayardar zubar hawayena. Tashi nai na zauna saman gadon kusa da shi, a yau kam ni nake masa irin kallon da yake min wani irin jinsa nake a raina gaba daya tausayinsa ya gama mamaye min zuciya. Kissing forehead dina yai sannan ya saka hannunsa na hagu ya kama hannuna ya rike gam.

“Sarkin kuka i love you”
Chapter 121 · 0% Book details