← Book details Gobe Na Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 57 OF 136

Sashe 57

Gobe Na Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Direct bangaren Hajiya ya nufa, sai ya same ta a falonta mai mata mopping na matsa mata kafafuwanta. A one seater ya zauna yana kallon fuskar Hajiya da ke cike da far'a, wanda yake kyautata zaton nasabar farincikinta da zuwan matar nan ta dazun.

“Ka ci abinci kuwa?”

“No kin san ai idan ina aikin nan bana iya tsayawa cin komai”

“Larai tashi ki dauko kulolin na zuba masa”

“No zan ci after magrib”

Ya fada zuciyarsa na ta yi masa sake sake akan farincikin Hajiya, baya son ya tambaya tai masa maganar Ikilima ko abunda ya shafeta so he decided ya kyaleta kawai idan ma maganar da ya kamata ace ta ji ce yana zaunesa za tai masa maganar. Hannu Hajiya ta kai ta dauko wayarta ta kira direban Baby Namra bugu daya ya dauka.

“Hello Almu kaje ka dauko Baby Namra”

“Ga ni a hanya Hajiya Alhaji ya fada min ai”

“Okay”

Ta aje wayar sannan ta kalli Ahmad tana murmushi.

“Ko dan Baby ai ya kamata ka auri yarinyar nan, dan nasan yadda Baby take da rigima kamar kai ita kadai zata iya zama da ku, Wallahi dazun da mahaifiyarta na ba ni labarin irin hakurin zaman auren da tai sai ta kara burge ni”

Shiru yai kamar ba zai ce komai ba, sai kuma ya kalli Larai ya ce.

“Za ki iya ba mu guri Larai”

Da sauri Larai ta mike tsaye sai Hajiya ta ce.

“Why?”

“We need privacy Hajiya, idan muka maganar Family be kamata wani ya ji ba”

“Aiko dai ina jindadin matsa min kafafuwan nan da take”

Tashi yai ya tare a gaban Hajiya kasan carpet yaja kafarta daya ya soma matsawa.

“Hajiya ki ce matar nan ta zo miki tallar yarta kawai, ai kamata yai ace ta bari wasu su fada, kuma ni babu abunda za ku fada min da zai saka na aureta, na fada miki bana son auren matar wani Hajiya you know it”

“Wallahi wannan yar albarka ce, irin wannan mai hakuri ba har tausa sai ta min ba”

Kansa ya daga ya kalli Hajiya, ya san suna da arzikin da za su iya yin duk yadda suke so, after masu mata girki da shara da wanke wanke da gyara harabar gida da mai bawa fulawa ruwa everyday, now sukukarta take son ta rika matsa mata kafafuwanta, he just don't know why Hajiya take son mulkar sukukanta da hana su yancinsu, be isa ya siyawa matarsa abu ba ba da sanin Hajiya ba ko da ko anko ne, balle kayan sallah komai sai ta zaba ake musu.

“Hajiya.....”

Sai kuma yai shiru ya busar da iskar bakinsa, ya san mahaifiyarsa so tana da right ta yi duk yadda take so da shi ko da iyalinsa, but this time around maganin kar ayi kar a fara ba zai yarda yai auren a yanzu ba, idan ma zai yi ba bazawara ba kamar yadda take so, domin shi dai a rayuwarsa yana kyamar ragin wani, ya fi son shi ya rage maka as long as mace ta auri wani ta fito ba zai iya aurenta ba ko wacece ita a duniyar nan and no matter how much he loves her.

“Ka amince kenan?”

Da sauri ya amsa.

“No Hajiya ba zan iya auren yarinyar nan ba, I Wallahi ko hannun macen da wani namijin ya aura bana jin zan iya rikewa balle kuma har na aureta”

“Wai wannan wace irin bakar akida ce?”

Hajiya ta fada a fusace tana janye kafarta.

“Wallahi Haka Allah yai ni Hajiya, ina da masifar kishi ina da kishin bala'i ni kadai na san abunda na ke ji”

“To Allah ya raba mu da bala'i.... ”

Kamin ya amsa da Amin Almu ya shigo jikinsa na rawa cikin falon har yana kokarin faduwa, ko sallama be yi ba abunda be taba tun da yazo gidan ba Hajiya ba ko Ahmad sai da ya firgita da yanayinsa.

“Alhaji....Hajiya... An jefa Baby...Na ji ana fadin Baby ta fada rigiya”

“Na shiga uku ban lalace ba”

Hajiya ta fada Ahmad kuma ya mike tsaye da sauri yana kallon Almu.

“Wace Baby?”

“Baby Namra Wallahi yanzu na ji ana fadar hakan ina tsaye kofar gidan na aika yaro ya kirata sai yaron ya shigo gida da gudu yan..... ”

“Almu Enough...!”

Be gama ba Ahmad ya daka matsa wata mahaukaciyar tsawar da ko Hajiya sai ta ta ji zuciyarta kamar zata fado, balle shi Almu da Ahmad yake kallo kamar idonsa zai ciro. Hannunsa ya saka aljihu ya ji babu keys juyawa yai da wani irin gudu da ya manta when last yai irinsa ya shiga part dinsa ga keys din a inda ya saba aje su amman ya kasa ganinsu sai da ya rumtse idonsa.

“Innalillahi wa'inna ilaihirraji'un”

Ya furta gabansa na kara faduwa, bude idon yai ya kai hannunsa ya dauki keys din ya fito da sauri ya nufi gurin motarsa, a yanayin yadda ya bar gidan da yadda ya hau titi duk wanda ya kalleshi ya san ba tukin hankali yake ba, ko dai ace yayi shaye-shaye ko kuma ba shi da hankali ko so yake ya kashe kansa. Cikin kankanen lokaci ya isa unguwarsu Halimatu, sau biyu kawai ya taba zuwa kawo Namra da kuma daukarta, ya san inda kofar gidan take amman be taba takawa ba sai yau, haka ya fita be ko kashe motar ba ya shiga cikin gidan su Halimatu kamar ba gidan matan aure ba.

“Ina yata take?”

Ita ce sallamarsa, sai aka rasa mai bashi amsa kowa yai cirkocirko.

“Ta fada rigiya Momy taje da ita Asibiti”

Adnan ya amsa masa.

“Wace asibitin?”

“Na ji tace fmc a napep suka je”

A nan ma Adnan ne ya bashi amsa, juyawa yai da sauri ya koma cikin motar, da wani irin karfi ya fizgeta sai da kura ta mamaye gurin. Yana shiga fmc ka tsaye ya wuce emergency ko'ina dubawa yake har ya hango Halimatu tsaye tare da kanenta biyu. Tun ka ya karasa ya rika ganinta kamar wani bakin maciji, yana isa gurin tana juyowa a take ya kifa mata mari, tangal-tangal tai tana kokarin faduwa sai mutane suka fara fadin a riketa Salma ta riko ta amman ina tuni ta kai kasa, hannunta ya daki wheelchair dake gurin.

Haba malam, haba bawan Allah Subhanallahi, sune abubuwan da suke fitowa a bakunan mutanen da ke gurin.

“Ina yata”

Ya tambayi likitan.

“Mahaifinta ne kai?”

Runtse ido yai kamar ba zai amsa masa ba, sai kuma ya gyada masa gudun bata lokaci.

“Muna bukatar jini”

“Ina take?”

Ya tambaya numfashinsa na fita kamar wanda yai wani aiki ya gaji. Da hannun likitan ya nuna masa kofar dakin.

“Tana ciki”

Da sauri ya shiga gurin, katon guri ne da ake aje mutane wasu kasa wasu saman gado ana shiga da su wani dakin likita na dubasu. Tsaye yai yana kallon yarsa kama da matacciya take masa domin bata motsi kuma babu alamar rai a tare da ita.

“Baby.... ”

Ya furta cikin tashin hankali.

“Tana da rai jini likitan ya ce a kawo sai a duba ta, sun tafi su dauko gado... ”

Be ko tsaya kallon mai matsa bayanin ba ya nufi yarsa yasa hannu biyu ya dauke ta cike da kuzari jin cewar tana da rai. Kamar wani mahaukaci haka ya fito da ita mutane sai kallonsa suke, ya sakata a mota sannan ya zagayo ya shiga mazauninsa da gudun tsiya ya bar cikin asibitin SJT hospital ya nufa da ita kasancewar ita ce asibitinsu kuma asibitin masu kudi wacce za a baka kulawa a take. Kamin ya karasa ya saka hannunsa aljihu ya lalaba wayarsa sai ya ji wayam babu komai sam ya manta da cewar a gida ya bar wayar sai yanzu da yake bukatar kiran family Doctor su.

Yana isa suka karbata a take suka fara bata kulawa, jini ne abunda suka bukata bayan sun shiga da ita ICU, kamin ya kai gurin da za a dibi jinin nasa jikinsa har rawa yake. A ana cikin dibar jinin sai ga family Doc su ya shigo gurin hankalinsa a tashe.

“Subhanallahi Gwarzo, yanzu ta kira tace na duba mata ko ka zo nan, na shiga emergency Doc Nura ke fada min an shiga da Baby ICU kai kuma kana nan, garin ya hakan ya faru...?”

Kai kawai Ahmad ya daga ya kalleshi, shi da kansa ya karancin irin tashin hankalin da Gwarzo yake ciki ya fi gaban kwatance. After an gama dibar jinin Ahmad ya riko rigar Doc Nura da idanuwansa da suka gama rikedewa ya ce.

“Dan Allah ka yi duk yadda za ka yi ka ceto rayuwar Baby, dan girman Allah”

Ba Doc Nura kadai ba duk mutanen da ke gurin sai da ta ji tausayin Ahmad, gashi dai ba kuka yake ba amman idanuwansa da jikinsa da fuskarsa sun nuna damuwarsa karara, even the way da yake numfashin kasan yana cikin tashin hankali. Doc Nura ya gyada masa kai.

“Karka damu In-Sha-Allah zata tashi”

Sai a lokacin ya sake shi, ya dafe kansa ji yake kamar ace yana da wani abun da zai yi yarsa ta dawo normal. Mikewa yai tsaye ya bi bayansa a bakin kofar dakin da aka shiga da ita ya tsaya ya jingina jikin bangon dakin ya Runtse ido, yana jin muryar Hajiya amman ja kasa daga kansa sai kokuwa yake da numfashinsa.

ABDALLAH POV.

Daure da tawul ya fito daga bathroom dan karamin tawul a kafadarsa yana goge ruwan da ke kansa.

“Waya kara ni”

Ya tambayi Suwaiba da ke zaune bakin gadonsa.

“Babu kowa”

“Amman na ji wayata ta yi ringing kuma na ji kin yi picking sai kuma kika fita”

“Ni ce na gwada kiran ina son na gane idan wayata tana aiki ne”

The way da tai masa magana sai ya ji be gamsu da abunda ta fada ba, if gaskiya ne then why da tai picking ya bar dakin? Be sake ce mata komai ba, ya zauna gaban madubi ya soma shafa mai, jin bata zo ta taya shi ba yasa ya juyo ya kalleta.

“Ba za ki taya ni ba?”

Bata bashi amsa ba, sai dai irin kallon kunar zuciya da take masa ya karantar da shi damuwarta.
Chapter 57 · 0% Book details