← Book details Gobe Na Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 47 OF 136

Sashe 47

Gobe Na Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

“Wallahi na aiki Musa direba da ita Mafara sako zai karbo min, ka kira Sadi ya kawo maka motarsa daya mana ai mota biyu ne da shi”

Ba musu ya koma ya zauna ya ciro wayarsa ya kira kanensa Sadi. Ringing biyu zuwa na uku ya daga.

“Sadi kana ina?”

“Gani kusa da gidan Hajiya”

“To ina gidan karaso ka sauke ni gida”

“Okay”

Bayan na sauke wayar, Hajiya ta cigaba da yi masa maganar so take ta karkarto hankalinsa da barin zancen maido Halimatu domin ita a ganinta ba mafita ba ce, zuciyarta ta fi natsuwa da sammu akai masa ko dai Halimatun tai masa ko kuma wani dabam, ba a wuce minti ashirin ba Sadi ya shigo gidan cikin sabuwar shadda light yellow da hula kubu sai kamshin turare yake. S tsaye ya gaisa da Hajiya domin shi ma a hanya yake akwai inda yake son zuwa.

“Gida zaka sauke shi”

“Ina motarka ne?”

Sadi ya tambaya yana barin kallon Hajiya wacce tai masa maganar.

“Wallahi ta samu matsala wai engine dinta ta buga”

Aminu ya fada cike da damuwa a fuskarsa.

“What, motar da ka siyo satin nan ko dai wacan tsohuwar”

“Tsohuwar ai siyar da ita nai, wannan dai sabuwar”

“Garin ya?”

“To ni ina ma zan iya cewa ga dalili, abubuwan ne dai sai hamdala”

“Allah ya kyauta, tashi muje”

Sai da Aminu da Hajiya suka amsa da Amin sannan ya mike tsaye suka fice tare. Har gida Sadi ya kawo Aminu, bayan ya bude motar ya fita Sadi ma ya bude ya fito wai bari ya gaisa da Madam. Aminu na shiga cikin falon Murja da taso da sauri ta rumgume shi tana masa oyoyo sai shagwaba take zubawa kamar wata karamar yarinya.

“Ina tare da shi fa Hajiya”

“Dan kana tare da shi sai ya hanani nunawa mijina soyayya?”

Murmushi Sadi yai ya dauke idonsa ya nufi kitchen.

“Bari na sha ruwa”

Kitchen din ya shiga da kansa ya dauko cup ya bude freezer ya dauko robar ruwa ya bude ya soma bulbulawa. Kamar daga sama ya ji am rumgume shi ba shiri ya dire ruwan da yake sha ya juyo da sauri yana kallon kofar kitchen din.

“Kai dan Allah sarkin tsiro, ya shiga dakinsa”

“Amman ai zai iya saukowa yanzu kuma ya shigo nan”

Ya fada da rada hankalinsa a tashe yana kallon kofar kitchen din dan ya san the worst thing da zai aikata shine ya bar dan'uwansa ya san alakar da ke tsakaninsu.

“Ka daina zuwa kwana biyu, i miss you”

Ta fada tana dora hannunta a saman lips dinsa sai lumshe ido take da fake eyelashes dinta.

“Murja alakar mu ta da ba kamar ta yanzu ba ce fa, saboda dan'uwana kike aure dole nai tsaka tsantsan”

“Auren dan'uwanka ya hana alakar mu cigaba ne? Tun farko ba kai kaja ba, da aka aurena zan auri yayanka ne, sai wani kwana kwana kake min jikina kawai kake so”

Saurin turarenta yai daga jikinss ya fito daga cikin kitchen din jin kamar motsin fitowar Aminu a falo, kai tsaye ya nufi kofa ya fice daga falon gaba daya. Dariya murja tai ta nufi dakin mijinta, da taimakonta yai wanka ya shirya cikin farin yadi marar nauyi sannan ta gabatar masa da abincin rana. Cin abincin suke yana ta sake2 yadda zai bullo mata, so yake ya fada mata cewar yana son ya dawo da yaransa a gidansa amman yana jin tsoronta, baya son bacin ranta idan ranta ya bace ji yake kamar zai mutu, ko motsi dai sai ya rasa natsuwarsa saboda tsoron abunda zai fito daga bakinta, haka Allah ya saka masa tsoronta kamar mutuwarsa, idan ranta ya bace har kuka yake mata gurin bata hakuri abunda be taba yi ma wata mace ba, ko Hajiyarsa baya tsoro yadda yake tsoron Murja.

AHMAD POV.

“Na dauko Baby Namra daga gidan Hajiya, ka dawo gida da wuri karka wuce 8”

Sai da ya hade yawun bakinsa sannan ya amsa mata ta okay.

“Yayi Mommy's Boy”

Rahim ya fada yana dariya.

“Ba fa abun dariya ba ne seriously bana jindadin abunda kake min”

“Okay sorry but abun nan yana ba ni dariya”

“Ba abun dariya ba ne, abun nan gaba yake kara yi ba baya ba, na rasa yadda zan bullowa lamarin nan, yanzu fa ta kai har wayata Hajiya ta ke karba ta duba, irin ita bata yarda da ni ba,kullum ganin take kamar yan mata wayo za su min”

Rahim ya kara matsowa kusa da shi ya da fashi.

“Magani kawai kai aure Gwarzo, matukar ba aure kai ba zai Hajiya ba zata daina ganinki a yaro ba”

“Auren ba mafita ba ne, yaure uku nai kamin na auri Halima amman ko wace ta kasa zama da ni sai Halima ita ma kuma saboda ta yi hakuri ne, bayan rasuwarta mace biyu na aura Hajiya bata barin na zauna da mata, tun da idan bata ga dama ba sai ta hana ni cin abincin mace ta ce bata yarda da shi ba, kuma ko yarinyar na nemo idan bata gamsu da ita ba ba zata bar ni na aureta ba”

“Wata mace zaka aura ba yarinya ba, mace mai hakuri da sanin ya kamata, kuma kamin ka aureta ka fara gabatar mata da Hajiya ka fada mata komai na ka karka boye mata, kai idan ta kama ma kai auren a boye kai yi dan samawa kanka mafita, dan Hajiya har yanzu bata daina ganinka a yaro ba, bata yarda ka girma ba”

“Wallahi abunda take min ko Baby Namra albarka, dan yau idan Baby Namra ta ga dama zata iya zuwa wani guri a cikin familymu tace can zata kwana kuma Hajiya ta barta amman ni ban isa ba, abun da Hajiya take min har dauren min kai yake wani lokacin har daure min kai yake”

“Ka samu wata ka aura, irin macen nan da ta saba shan wahalar gidan aure, ka aureta kuma ka fada mata komai karka bi soyayya ka auri yarinya ta zo tai ma Hajiyarka hauka ko ta kasa hakuri da kai, iirin dai mace mai yaya biyu uku aha”

“Kai ba zan iya auren macen da wani ya aura ba, you know ina da kishi sosai, ba zan iya zama macen da wani ya aura ba balle ma wacce tai aure har fiye da daya”

“To ai kaji matsalar ka fi son ka auro yan matan nan na zamani kansu na hayaki dole su ce ba za su zauna da Hajiya ba, ba wai dan kana sonta zata aureta ba, kai ko auren kwangila ne kai kawai da zarar ka samu yancinka gurin Hajiya sai ka rabu da ita ta auro wacce kake so, ya kamata ka amsa sunanka na Gwarzo fa, na san baka daukar rainin kowa a kamfani, idan ka bawa mutum umarni jikinsa har rawa yake ya cika maka aikinka, to ko a gida ya kamata kana motsawa”

“Da Halima na nan da yanzu na amsa, Ba zan taba son wata ba Rahim, ni mijin matacciya ne, na riga na auri Halima kuma na auru, duk mace da zan aura zan aureta ne kawai dan samun mafita amman ba dan kauna ba”

Yayi maganar cikin sanyayyiyar murya, yana sotsa lips din, zuciyarsa na sosuwa da kauna Halimatunsa Uwar Baby Namra.

“Halima ta yi min abunda wata macen bata taba min ba, ta haifa min Baby Namra, ta yi hakurin zama da Hajiya har na tsawon shekara biyu...”

Rahim ya soma lura da yanayin abokinsa, daman ya saba shiga a irin wannan yanayin a duk lokacin da aoa dauko maganar Halimatu, a kokarinsa na kawar da maganar ya dauko masa maganar kamfani.

“Yauwa na manta ban fada maka ba, sun fa turo takardun nan ta mail din kamfani amman sai mun yi printing out....”

Mikewa Ahmad yai tsaye cikin damuwa.

“Dan Allah ka daina maganar wani kamfani a yanzu, lemme go and rest...”

Fita yai daga gurin ya nufi motarsa, yana shiga ya dauki hanyar Exclusive City.

HALIMATU POV.

Na yi kuka iya wanda zan iya, na yi na gaji na rarrashi kaina domin ba ni da mai rarrashina a wannan lokacin. Daya daga cikin waitress din dake gurin ne ya zo yana tambaya idan ina bukatar wani abu?

“Bana bukatar komai, akwai wanda na ke jira ne”

Juyawa yai ya koma gurin da yake tsaye, ya cigaba da danna wayarsa, binsa nai da kallo kamin na ji wata murya mai cike da bacin rai tana min magana.

“Waya aje wannan matar a nan?”

Juyowa nai na kalleshi da kumburarrin idanuwana, mutunen nan ne daya taba ture ni a keke, kuma shi ne wanda na gani a lokacin da naje kai Namra School, kuma shi ne mutumen da ya tsinci Namra. Da saurin waiter din dazun ya zo yana tambayar ba'asi.

“Taya za a bar wata ta zauna a seat din nan? Me ke damunku? Da alama kai bako ne, kuma laifin ba na ku ba ne laifin shugabanku ne, for more than ten years ina biyan kudin gurin nan saboda tsabar rainin hankali yau za ku bar wani ya zauna? Oh haka kuke idan bana nan daman you're very stupid”

Sauran waitress din suka zo suns bashi hakuri, wanda ni ban ga dalilin hakan ba, ko da yake na ji ya ambaci sama da shekara goma yana biyan seat din da alama baya son kowa ya zauna ne.

“Ke dalla malama tashi ki rasa kujerar da za ki zauna sai wannan”

Ko kadan maganarsa bata 6ata min rai ba, da alama macen da yake biyawa kudin kujerar tana da muhimmanci a gareshi, ba kamar ni ba. Mikewa nai tsaye na kalli kujerar sannan na kalleshi na ce.

“Ka yi hakuri ban san cewa kujerar ta ka bace, ban san alakarka da mai seat din ba, mata, yar'uwa, uwa, ko ya ko kanwa, amman ka bata hakuri a madadina, domin ko wacece duniyarta kyakkyawa ce, kuma mai fadi ce shiyasa tai dace da mai kare martabar gurin zamanta ba ma ita din ba”
Chapter 47 · 0% Book details