← Book details Gobe Na Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 66 OF 136

Sashe 66

Gobe Na Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

“Idan ba a karbe yaran ba taya za ayi? Ta dawo? Ai sai an karbe yaran shaukin sonsu da kaunarsu ya shiga zuciyarta sannan ta san muhimmancinsu ta dawo maka”

“To Hajiya idan Murja bata yarda da zamansu ba ai dole na hakura har ta dawo gaba daya..... ”

Ya karasa yana ciro wayarsa dake ringing daga cikin aljihun gaban rigarsa, ganin daga gurin aikinsu ne yasa shi hanzarin daukar wayar. After sun gaisa mutumen yake sanar masa ya zo yanzu ana nemansa.

“Okay gani nan zuwa, amman lafiya dai?”

“Ka zo dai”

Ya sake amsawa da okay sannan ya kashe wayar gabansa na mugun faduwa kamar yadda jikinsa yake fada masa ba lafiya ba.

“Wato yanzu sai ta aminta sannan yara za su zauna gidan lallai Aminu, kamar ba kai ba kamar an sauya ka Wallahi”

“Rayuwa dole ai tana sauyawa Hajiya, yanzu dai bari naje gurin aiki ana nemana”

Ya fada yana mikewa tsaye, Hajiya kam da kallon mamaki ta bishi har ya fice. Direban Hajiya yai ma magana ya sauke shi a gurin aikin na su da zimmar idan ya gama abunda yake sai ya samu wani cikin abokan aikinsa su sauke shi gida, tunda abun ya zame masa haka mota bata kaunarsa sabuwar da ya siya ya kashe mata kudi har ya gaji bata gyaru ba, idan ma ta tashi cikin kwana biyu zata sake samun wata matsalar.
Cikin tsoro da tunani kala kala ya shiga ofishin shugaban na su, ya tararda wasu mutane a ciki hakan yasa shi neman guri ya zauna har sai da ya sallami bakin nasa sannan ya karasa gurin teburin ogan yaja kujera a daya daga cikin kujerun da mutanen suka tashi ya zauna yana mika masa gaisuwa.

“Makullin office dinka nake son ka ba ni da duk wasu takadar da suka shafi ma'aikatar da wadanda suke hannunka...!”

Tas tas tas gabansa yai mugun bugawa.

“Ranka ya dade lafiya dai?”

Wanda ya kira da ranka ya dade ya dauko wata takardar ya mika masa, sanyi jiki Aminu yai gurin karba kamar yasan abunda ke ciki ba alheri ba ne.

“Ranka ya dade takardar me ce?”

“Ka karanta ai ka yi boko”

Ya hade yawu yafi a kirga sannan ya bude zungureriyar takadar wacce ya kasa fahimta abunda aka rubuta a ciki ba dan kuma be iya karanta turancin ba sai dan baya cikin natsuwarsa.

“Innalillahi wa'inna ilaihirraji'un, ranka ya dade me nai aka kore ni? Kamar kora na ke gani ko?”

Ya tambaya jikinsa na bari bayan ya karanta takardar a galabaice ga wata uwar gumi daya tara a goshi.

“A gaskiya ni kai na ba zan fadar dalili ba abu ne daya taso daga sama”

“Amman ana sallamar mutum ba tare da yayi laifin komai ba ranka ya dade? Idan wani laifi nai a fada min sai na gyara, aikin nan shine rayuwata”

“To ina ganin abunda yafi ka koma gida sai ka rubuta apology letter sai ya aiko min ni kuma zan tura ta sama In-Sha-Allah, amman dai sun fi zarginka da wasa da aikin ga kuma rashin zuwa aikin akan lokacin”

“Allah yasa hakan shi yafi alheri, na gode”

Ya fada yana mikewa tsaye jiki a sanyaye zuciyarsa a daure. Office din nasa ya nufa a lokacin daya shiga sai ya rasa abunda zai yi a ciki sai kawai ya nemi gurina zauna ya rumtse ido, tunani yake son yayi ya kasa tunanin me zai yi? Kayansa da suke office din ya kwashe ko kuma tunanin gobensa? Ko tunanin laifin da ake tumarsa da shi? Anya wannan kawai ya isa ya saka a koreshi daga aikin da ya shafe shekaru yana yi? Ko dai akwai wani wanda yake masa makarkashiya yake bibiyarsa da sheri? Shigowar abokinsa ne yasa shi dago kai ya kalli kofar da idanuwansa da suka gama sauya kala.

“Tahir kaga abunda mutanen nan suka min?”

Ya fada yana nuna masa takardar kamar ya fasa kuka.

“Aminu sai hakuri idan mahassada suka saka mutun a gaba sai addu'a tun jiya aka bada takardar nan amman kowa ya kasa kawo maka shine yau bayan ka bar office yace a kira ka shi zai baka”

Ya busar da iskar bakinsa.

“Yace na rubuta takardar bada hakuri”

“Kai share banza ai duk da shi akai maka wannan sherin budurwarsa yake son dorawa a kujerarsa”

“Wacece Habiba?”

“No Jalila dai ba tare yake da ita ba”

Duk wata magana da yake yana yinta ne kawai cikin karfin hali amman ba dan yana da kuzari da karfin zuciya ba. Da taimakon Tahir ya hada duk wani abu daya san na shi ne ya kwashe a office din ya saka a kwali Tahir ya saka masa a motarsa, sannan ya koma office din shugaban na su ya mika masa keys din da wasu abubuwan da suja shafi ma'aikatar yai masa sallama ya fito.

Tun da suka kamo hanyar gida Tahir ke ta ba shi magana yana nuna masa hanyar da zai bi a maida shi aikin da kuma manyan mutane da ya kamata yai ma magana. A cikin motar Tahir ya bar komai nasa ya fita daga motar ya shiga gidansa cikin damuwa da tunani kala kala, he wasn't surprised ganin motar Sadi a harabar gidan daman can ya saba zuwa gidan idan an kwana biyu wani lokacin kuma yana shigowa tare da shi, suna da kyakkyawar fahimta tsakaninsa da Murja ba kamar Halimatu da daman can tun a farkon fari basa samun jutuwa wanda ya samu asali daga Hajiya wacce bata son Halimatu. Tafiya yake yana jin kamar ba kasa yake takawa ba saboda damuwar data cika masa ruhi, a yau kam ba tare da ya kira murja ya sanar mata da zuwansa ba zai shiga gidansa duk kuwa da kasancewar tai masa gargdin cewar karya dawo gida babu notice, sai dai tashin hankalin dake tare da shi a yau ya mantar da shi dokarta, shi yanzu ma tsoronsa daya kar ya fada mata gaskiya ta guje masa, ko kuma ta juya masa baya, anya ma zai iya fada mata cewar an koreshi daga aiki bayan ko amarci bata gama ci ba? Duka duka ko shekara batai ba tana tunanin jindadi zai bijiro mata da wannan maganar? Har ya tura kofar falon ya shiga be yanke shawarar fada mata gaskiya ba ko kuma boye mata idan ma ya boye mata me boyewar zai haifar tunda dole ne wata rana sai ta san gaskiya. Ganin babu kowa a falo sai tv dake aikin watso labarai yasa shi mamaki, sai dai be kawo komai a zuciyarsa ba ya leka kitchen din dake bude nan ma wayan babu kowa kai tsaye ya nufi dakin Murja yana tabawa ya ji shi a kulle an saka masa key daga can ciki. Hakan yai mugun daga masa hankali har ya kai hannu yai knocked sai kuma wata zuciyarta hana shi, to ko dai Murja bata nan ne? Ta rufe dakin ta manta bata rufe falon ba? Idan kuma bata nan mi ya kawo motar Sadi a cikin gidan? Kuma ina Sadin yake? Juyawa yai da sauri ya fice daga falon ya zagaya ta can gurin windows dakin Murja da zimmar ya leka dakin sai ya samu windows din suma a rufe.

Dawowa yai falon ya zauna ya zubawa kofar dakin ido, yana ta kokarin hana zuciyarsa zargi yana ta kokarin kyautatawa matarsa da dan'uwansa zato! Sai me? Sai ya kasa natsuwa ya kasa sukuni gaba daya sai ya manta da zancen sallama hankalinsa gaba daya ya dawo a nan. Wata dabarar ce ta zo masa sai ya fita harabar gidan daga can inda ba za a jiyo muryarsa ya kira line ta da sunan da yai saving number ta sweetheart ringing tai har sai da ta kusan yankewa sannan tai picking.

“Hello Baby”

“Na'am ykk zan dawo gida yanzu”

“Okay sai ka iso i love you”

“I love you too”

Ya amsa mata yana maida numfashi. Sannan ya maida wayar aljihu ya nufo falon, har lokacin ba a bude dakin ba kuma be ji motsi ko alamar za a bude din ba hakan yasa shi jin sanyi a ransa sai hankalinsa ya fi karkarta da yarda cewar wata kila ta fita wani wajen ne? But wait idan ta fita ina Sadi? And me ya kawo motarsa a nan?
Ganin ba shi da amsar tambayar yasa shi sake nufar kofar dakin da zimmar knocked sai dai kamin ya karasa aka bude kofar daga can ciki ga mamaki Sadi ya fito daga dakin sanye da shadda yellow hullarsa a hannu yana gyarata. Kamar hoto haka Sadi yai tsaye a gurin ganin Amnu, kamar yadda Aminu ma yai tsaye kamar an dasa shi a gurin sai dai hakan be hana shi murmushin mamaki ba.

“I...na.. Mu...rja...”

Ya tambaya maganar na fitowa daga bakinsa daker. A rikice Sadi ya nuna masa dakin daya fito a take gumi ya karyo masa.

“Tana..... Ta... Na... Ci... Ki.... Al.... Al... Aljannunta.... Ne suka... Taso.. So... So... So”

Murja kamar jira take tana jin haka ta buga wani mahaukacin ihu ta fadi kasa ta soma murje murje....

HALIMATU POV.

Ban jidadin yadda na amsawa Abdallah cewar yes kaunar Aminu nake ba, bayan kuma ni kaina na san karya na fada na fada ne kawai cikin bacin rai sanadiyar maimaita min tambayar da yake ta yi, sai dai a yanzu ina jin cewar ko kallon banza be kamata ace ina yi ma Abdullah ba balle har na fada masa wata maganar marar dadi, na ji babu dadi sosai haka yasa na yanke shawarar kiransa idan na natsu na bashi hakuri, sai dai kuma ya cancanci na kira na bashi hakurin? Hakan ba janyo min wani abun ba? Idan kuma ban bashi hakurin ba zai iya daukar da gaske son Aminu nake, halin a yanzu ko sunansa bana son ji balle har a alakanta kalmar so da shi, no ba sai na kira shi ba indai Abdallah ne da zarar ya gama fushinsa ya sauka zai koma kamar komai be faru ba.
Haka dai muka isa gida a napep da sake sake kala kala a raina, na kulla wannan na kwance wacan har na fita daga napep din.

“Mai motar can fa tun dazun yake biye da mu”
Chapter 66 · 0% Book details