← Book details Gobe Na Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 109 OF 136

Sashe 109

Gobe Na Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

“Look at you fool sai na nuna maka baka isa da Halima ba trust me.... ”

Ahmad be sake ce masa komai ba ya fice. Abdallah kuma ya hau rarrashin zuciyarsa domin ji yake kamar ya hau Ahmad da duka, Hajiya kan jikinta gaba daya ya gama sanyi jin Abdulhamid yana hannun DSS.

_________________
Guess what will happen next.
7/21/21, 10:48 PM - Buhainat: *GOBE NA...*

By Khadeeja Candy

5️⃣4️⃣

Yadda kafarsa take taka kasa da karfi ya isa ya isar maka da cewar ransa a mugun bace yake, balle kuma kai arba da kyakkyawar fuskar nan tasa wacce ta koma kamar bakin hadari idanuwansa gaba daya sun gama canja kala daga fari zuwa ja. Wani irin nishi yake irin wanda bacin rai ya dannewa numfashi, gumi kawai ke karyo masa daman can haka yake idan ransa ya bace sai gumi da dannewar numfashi.
Tare da barrister suka isa gurin motar, sai ya kai hannunsa ya bude gidan baya inda aka saka Halima, hannunsa ya kai ya taba fuskarta zuwa hancinta dan tabbatarwa idan tana raye, tabbas yaji tana numfashi sai dai kana kallonta kasan bata cikin hayyacinta.

“Wai hula suka saka mata”

Barrister Nuhu ya fada yana tsaye bayan Ahmad, dagowa Ahmad yai ya kalleshi da wata irin murya marar dadi saurari yace.

“Barrister ka shigar da karar matar nan da dan sandan da yai mata wannan abun, zan kaita asibiti yau yau nake son ka fara komai, ba zan iya yafewa ba, ba zan iya kyale wannan abun ba”

Yana fadar hakan ya zagaya zai shiga motarsa sai ga Inna da Husna sun iso.

“Mun gode Allah ya saka da alheri”

Be iya amsa su ba sai kawai yace.

“Asibiti zan kaita yanzu, asibitin Dr Nura za ku iya samun mu a can”

Yana fadar hakan ya bude motar ya shiga, yai mata key, kamin ya isa asibitin ya sake kiran wayar Halima duk da yasan bata hannunta amman yana son magana da Hafiza ne, akai sa'a wayar na hannunta domin ringing daya ta dauka.

“Hello, ke ce kanwar Lims ko?”

“Eh”

“A gabanki abun ya faru?”

“Eh komai a gabana akai, Mama ta hanani binsu ne can station din, baka ga wulakancin da sukai mata ba har waje suka fita da ita ba Hijab sai da na bita na saka mata mutane sai kallonta suke kamar ta yi sata, tun cikin gida ma yar sandar guda ta fara marinta”

Juyawa yai ya kalleshi Halima wacce idonta ke rufe sannan ya ce.

“Zan tura miki number wani barrister amman ki kira shi da line ki ba line Lims ba ki fada masa duk abunda ya faru zai shigar da kara akan case din”

“To ina ita Halima take?”

“Gata nan zan kaita asibiti”

Yana fadar hakan ya kashe wayar, ya sake waigawa ya kalli Halima, sai duk yaji tausayinta ya kara kamashi, da wani irin karfi ya daki sitiyarin motar, yana wani irin nishi kamar zai ciro zuciyarsa daga kirjinsa.
Yana kunna kai cikin asibitin wayarsa tai ringing kamar jiran kiran yake yai picking da sauri.

“Barrister”

“Na'am Ranka yadade ina son na san cewar shin abunda ake zarginta da shi, bata aikata ba din gaske? Kuma bata da hannu a batan mutumen?”

“Bata da alaka da shi mutumen yana hannun DSS, bata da hannu a batan sa ko wata mu'amala da shi”

“To ya akalarka take da ita?”

Juyawa yai ya kalli Halima sannan ya amsa ma Barrister.

“Matata ce....!”

“Za a shigar da karar a madadinta ne ita kanta ko kuma....!”

Shiru yai for a moment, yasan dai kotu ba a mata wasa, kuma shi din be riga ya auri Halima ba, idan aka shigar da sunan shi din mijinta ne kotu ta gano babu auri a tsakaninsu zai iya kawo musu matsala, how he wish ace ya aureta, ya tabbatar da yau Hajiya ko Abdallah basu yarda ko yatsa sun daga sun nuna mata ba balle har su saka a kamata.

“A madadinta zaka shigar, mutanen nan sun wulakanta ta Barrister i want them to regret, su nemi yafiyarta da kansu kuma kotu ta yanke musu hukunci so that's su san ita ma din mai matarba ce, har marinta sai da yar sandar tai kanwarta ta fada min komai, zan tura mata number ka zata kiraka ta maka bayanin komai, an ji hular da suka saka mata ko criminal sai wanda ya kai kololuwa ake yi ma haka, it's just like plan sun tsara kasheta ne kawai Allah be basu sa'a ba”

“Karka damu za ayi duk abunda ya dace”

Ya sauke wayar daga kunnensa daidai lokacin da ya isa harabar asibitin, sai da yai parking a emergency sannan ya fito yana kiran wayar Dr Nura, sai kuma yai rashin sa'a Dr baya cikin asibitin a lokacin sai dai ya saka ayi mata duk wani abu daya dace kamin ya iso. Gurin Ahmad ya samu ya zauna ya jimke hannunsa ya dora a saman bakinsa yana wani irin kashe ido zuciyarsa sai tafarfasa take.

“Sokon banza wawa”

Ya furta tunawa da kalaman Abdallah da yai.

“Daga ganin matar nan yayanta duk ba na albarka ba ne”

Ya mike tsaye yana jin wani irin tsanar Hajiya da Abdallah, daman can ya tsani Abdallah tun abunda ya faru a kamfaninsa wanda matar Abdallah tai yi ma Halima wulakanci.

“Saboda suna ganin bata da gata kowa ya kwaso hararsa sai ya zuba akanta”

Ya fada yana safa da marwa a gurin. Dr nura be dauki dogon lokaci ba ya iso gurin ya shiga bata taimako da kansa.
  Inna na isowa Mama ma ta iso tare da kanen mahaifin Halima, kana ganin fuskarsu kasan hankalinsu a tashe yake. Dukan yadda Ahmad yajin zafin zuciya sai ya dannen shi yana kokarin kwantar musu da hankali.

“Ku kwantar da hankalinku, zata samu sauki likita yana ciki yana dubata”

Mama ta gyada kai hawaye na sauko mata.

“Dukanta su kai?”

Inna ta tambaya.

“Ban sani ba tukuna sai likitoci sun gama bincike su”

After like 40 minutes Dr Nura ya fito daga dakin ya nufo inda suke. Ahmad sai kallonsa yake ya kasa tambayar komai.

“Ba wata matsala a yanzu nan da awa uku zata farka”

A hankali Ahmad ya cikawa bakinsa iska ya busar, ya Lumshe ido ya bude sannan ya mike tsaye ya bi bayan Doc Nura. Mama da Inna da Husna kuma suka nufi dakin da aka wuce da Halima.

“Ka tabbatar babu wata matsala Doc”

Bayan sun shiga office din Ahmad yake tambayarsa domin gani yake kamar ya boye ne ganin iyayenta. Sai da Doc Nura ya zauna sannan ya amsa masa.

“Babu wata matsala, abunda aka buga mata akan ne ya mata nauyi shiyasa hankalinta gushewa, amman babu wani matsala”

Ba zai iya zuwa dakin ya zauna ba bayan Mama da Inna ya san suna ciki kuma zuciyarsa ta ki aminta ya tafi ya barta cikin asibitin sai kace bata da kowa ko kuma bata san kowa ba, so he decided ya zauna a office din Doc Nura yai jiran awanin da Doc yace zata farka, da kansa ya kira Hajiya sanin cewar zata kirashi idan an yi magariba be dawo gida ba.

“Hajiya yau ba zan dawo gida da wuri ba”

“Why?”

“Lims ta samu matsala ne”

“Wacece lims?”

Runtse ido yai ya bude sai a lokacin ya tuna da Hajiya fa yake waya, duk da ba kunyarta yake ba domin ta zama kamar friend dinsa amman duk haka ita bata san yana kiran Halima da Lims ba duk kuwa da irin yadda sunan da yai mata ya bi bakinsa, duk da haka be kamata ya fadi haka a gaban Hajiya ba.

“Halima i mean”

“Subhanallahi matsalar me ta samu?”

“Kanta ya bugu da wani karfe muna asibiti yanzu haka, so ba zan bar asibitin ba sai ta farka”

“Allah sarki, babu matsala Allah ya bata lafiya”

“Amin thank You Mom”

“Se ka dawo”

Ya sauke wayar yana murmushin jindadim yadda Hajiyarsa ta amince a take ba kamar yadda take masa ba a da, ko kuma dai dan yana Halima ne oho.

HALIMATU POV.

Ba zan iya kiran bachin da nai da suma ba, ba kuma zan iya cewa ban suma ba, sai dai abunda na sani hankalina ya bace na dan lokaci a lokacin da aka saka min abun da, sai dai ina jin hayaniyar da suke kamar cikin mafarki kuma kamar a wata duniyar, har dauko ni da akai aka saka ni a mota zuwa asibiti har shigowa asibiti duk ina ji sai dai ba ji irin na mai rai ba kuma bana iya bude idona balle nai motsi, hakan ne ya tabbatar min da ba suma nai ba domin wanda ya suma baya sanin abunda ke kansa, sai dai daga lokacin aka suka min allura sai hankalin nawa ya tafi ban farka ba sai da aka sauko daga sallah magariba.
Na farka cikin rashin kuzari yawun bakina ma ba dadi kamar wata mai ciki, ba na wahala ne kawai ba wata kila har da yunwa domin ko karin safe ban yi ba.

“Sannu Halimatu”

A hankali na daga kai na kalleta wacce ita kadai ce a dakin, sai ya gyada mata kai alamar gamsuwa, sannan na maida idona gurin kofar da aka turo. Ahmad ne ya shigo hannunsa rike da ledodi tun da muka hada ido yake sakar min murmushi har ya aje ledar yana fadin.

“Ga kayan marmari na gani a gate na riko muku”

“Allah ya saka maka da alheri”

“Amin, ya jikin nata?”

“Al-hamdulillah yanzu ta bude ido”

“Okay, Baba babu ruwan shayi ko?”

“A a babu su yanzu kam, ga dai tuwo nan da aka kawo”

“Shayin dai zai fi, ko zaki kira gida ki ce a kawo mana ruwan zafin in yaso sai na karbo kayan tea nan waje, Doc yace idan ta farka a bata tea”

Da to Inna ta amsa sannan ta tashi ta fita daga dakin, kamar jira yake ta fice sai ya nufo gadon da nake kwance ya kwanto da fuskarsa daf da tawa.

“Na ji tsoron sosai da na ganki a galabaice dazun, na dauka ba za ki yi saurin farkawa haka ba, ya jikin naki”
Chapter 109 · 0% Book details