← Book details Gobe Na Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 108 OF 136

Sashe 108

Gobe Na Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Har muka isa gurin ban daina tunanin abunda na aikata wanda zai saka ayi min wannan kamun ba ban san na yi fada da kowa ba, ban san na yi wa wani kazafi ko kage ba, ban san mi na tarewa wani ba. Abun da kamar wulakanci domin muna isa suka saka ni a cell suka rufe, ko minti biyar ban yafe ba ba na hango Inna tare da Aisha da Mama da, like ten minutes wani kanen mahaifin mu ya iso gurin tare da yayansa.
Na yi minti talatin a ciki sannan aka fiddo ni aka nufi wani office da ni, ina shiga na samu Hajiya a zaune tare da yan'uwanta, kallo daya na yi mata na gane dalilin kamoni da akai. Mutumen da ke zaune a gabamu yana karanta min abunda ake zagina da shi dan Hajiya Altine wato yayar Hajiya, na san shi ya san ni amman a yau sai kamar be taba ganina ba.

“Ni ban san inda Abdulhamid yake ba, kuma ban san inda Abraham yake ba, nan fa cid ce babba kuma kai police ne Yusuf kai baka sani ba ni ya za ayi na sani?”

“Karki fada min maganar banza karki sake kiran sunana ki dauka ba ki taba ganina ba a rayuwarki”

Shine abunda ya fada min a tsawace, sai na kalli Hajiya na ce.

“Ba kiyayya ta shiga tsakanina da Abdulhamid ba, soyayyah ce kuma shi ya ji ba zai iya zama da ni ba ya rabu da ni, me zai saka ki yi min wannan zargin? Me nai miki Hajiya wannan maganar wace irin kiyayya ce?”

“Au baki sani ba? Munafuka, ai auren da kika masa ba na Allah bane, kin janyo hankalinsa saboda ki ci dukiyarsa tun da kin ga shi yafi dan'uwansa kudi, to shi aiki yake yana sai da motoci, dan uwansa kuma likita ne kawai, ko cikin nan Allah kadai yasan gaskiyarsa kin dauka ba zai yarda ta magana tun da kin shanye shi kamar yadda kika yi ma Abdallah, duk yadda akai da hadin bakinki aka sace min d'a, tun da kin ga zai yi aure kin ji bakinciki, wai dan har baki da kunya kike soyayya da kanensa? Kin taba ganin inda aka auri yaya kuma yana da rai a auri kane? Wato gaki autar mata ko, ban cin kin raba kansu kuma ki shiga ki mulke mu son ranki ga bayi, kin ma ci uban rainin wayo Wallahi”

Haka tai ta jera min bakaken maganganu sai abunda ta mance, jikinta har rawa yake kamar zata dake ni. Ban taba jin nadamar aikata wani abu ba kamar auren Abdulhamid a wannan lokacin, sai dai bawa be isa ya wuce kaddararsa ba.

“Za ki fada mana da arziki ko kuma sai cilasta ki?”

“Ban san komai a kai ba”

Na fada ina hawaye, bana son fadar komai saboda kar na jefa Ahmad a matsala, kuma idan Hajiya ta san ta dalilina ne zata kara zargina ne.
Haka aka raya aka kada aka juya aka na tsaya kai da fata ina fadar ni ban san komai akai ba. Daker aka bawa kanen mahaifina damar shigowa cikin office din wanda shi ma kanene ga mahaifinsu Abdallah, babu irin maganar da be yi da Hajiya ba amman ta ki saurarawa ita ala dole sai na fadi inda danta yake.

“Hajiya zumunci kike kokarin lalatawa, abunda kike yi be kamata, da uban yarinyar da mijinki uwarsu daya ubansu daya, akan me za ki yi wannan abu? Idan Alhaji yana da rai ke kin isa ko hararar zuri'arsa ki yi? Wallahi na tabbatar da ace Alhaji yana da rai yau ba za ki kwana a gidansa ba”

“To sai kaje ka taso da shi a yanzu ka saka ya sake ni, ni ba ku ga abunda tai min ba ta raba kan yayana, da gangan ta kulla soyayyah da Husaini yanzu kuma ta zo ta auri Hassan, yaro ya bata ga ayoyi tambaya akanta sai ku ce na kyaleta saboda ni ban san zafin haihuwa ba? Wallahi ko Alhaji ne a raye ba zai yarda a taba masa yayaba”

Kamar wacce take fada a ciki unguwa haka ta rika daga muryarta tana fadi abunda ranta yake so, Baba Buhari sai yai shiru kawai yana mata kallon takaici. Muna office din har la'asar, ganin na ki amsa laifina na ki na fadi komai yasa Yusuf din yace a shiga da ni wani daki, sai ya hada ni da wasu mata police suka tafi da ni wani bangare na gurin, suka shiga da ni cikin wani daki mai hudu, a yadda na fahimta abun kamar hadin baki ko ma nace cuta ce zallarta domin a iya sanina ko maza sai idan an dokesu kuma an kwana biyu ba su fadi kowa ba sannan ake saka a gurin, amman ni kamar daman can suna jira na ne. A rayuwata ban taba ganin inda aure ya zama kiyayya ba kamar nawa da ya zame min haka da Hajiya.

“Ba zaki fada ba?”

Dayar ta fada min cikin tsawa.

“Ni ban san komai ba”

Na amsa ta har lokacin zuciyata bata ayyana min na fadi komai ba. Wata hula suka saka min a saman hijabin da ke kaina, sai kuma suka cire min Hijabi suka saka min hular, wani namiji dake gafena na ga ya kunna wani abu sannan na daki hular kan nawa, a maimakon na fara bayani kamar yadda aka ce min mutane suna yi sai na nemi hankalina na rasa.

AHMAD POV.

Murmushi yake yana kurba tea dake hannunsa, ya nade kafafauwansa yana zaune gaban Hajiya, ita ma murmushin take tana fadin.

“Haka nake son mace tana da tsantsaye da rayuwa, kasan da wata ce kana bata motar nan zata hau murna ta karba jiki na rawa”

“Sosai ma Hajiya, kuma Wallahi wannan abun ya kara min kirmarta sosai a idona, sai na ji ta kara shiga raina sosai Wallahi”

“Amman ka mata magana kuwa?”

“Har ynzu dai, ki taya ni da addu'a, tana da dan taurin kai dan kadan kuma tana da wuyar sha'ani shi ma kadan, saboda tana tsoron rayuwa”

“Allah ya tabbatar da alheri yasa kuma ya karba maka”

“Amin Hajiya Amin”

Ya amsa cike da jindadi addu'ar mahaifiyarsa, sannan na aje mug din ya mike tsaye.

“Bari naje office”

“To Allah ya tsare, ka dai kusa zama babban mutum kamar da”

Murmushi yai ya fice yan shafa kansa. Driving yake zuwa office cikin nishadi da annashuwa, haka nan kawai idan ya tuna yayi waya da Lims da daren nan sai yaji wani dadi ya lullubeshi. He arrived in time just to see her face yana son yadda yake tsawa jikin windows yana hangota musamman idan zata bude windows din office dinta. Haka yai ta tsaye a gurin tun yana duba agogon ya ga nine saura har ya koma ya zauna can kuma ya taso ya tsaya ya koma ya zauna har kusan 11am abunda bata taba ba, domin duk dadewarta bata wuce 9 ko 9:30.
A take ya ji duk ya damu, wayarsa ya dauka ya kira wayarta sai ya jita kashe, a lokacin ne ya fara tunanin ko dan abunda ya faru jiya yasa yau ta ki zuwa aiki kuma ta kashe wayarta? Sai duk yaji ya shiga damuwa, har kusan 3pm ba wani labari, line ta ya sake gwadawa, sai yai sa'a wannan karon ya shiga, kamin a dauka duk ya matsu.

“Hello Lims”

“Ba Halima ba ce kanwarta ce Hafiza, Halima tana gurin yan sanda”

“What? Miya faru?”

“Dazun suka zo suka kamata da safe, ba irin wulakanci da ba su mana ba nan gurin wai suna zarginta da hannu a batan tsohon mijinta, tana can hannunsu sun kulleta”

“What? Wane station din ne?”

“State cid office”

Kashe wayar yai ya mike tsaye cikin zafin rai da rashin natsuwa na kira lauyansa, sai da yai masa bayanin komai sannan ya fada masa cewar su hadu a can din.
@360 na isa gurin, ko motarsa kadai ka kalla kasan babban mutum ma'ana mai ji da naira balle kuma shigarsa ta suit da yai, yana shiga cikin gurin lauyansa ya iso, duk wani shiga da fita da ake ciki lauyansa ne yake magana bashi ba, suna shiga office din aka kira Hajiya ta iso tare da Hajiya Rukaiya, ba su zauna ba Abdallah ya shigo office din shima.
Ahmad na kallonsa ya watsa masa wani mugun kallo.

“Kai kasa aka kamata kenan?”

Abdallah yai kamar be ganshi ba ko inda yake zaune be kalla ba balle har ya amsa shi. Hajiya ta kalli Ahmad da kyau tace.

“Waye kai? Ko kai ne Abraham din? Ni na saka aka kamata ba shi ba”

“To kina nan zaune za a fito da ita, kuma idan akan Abdulhamid ne ni zaki saka a kama ba ita ba, nine silar kama shi da akai yi ba ita ba”

“Kai Malam karka fada mana maganar banza, idan baka san darajar iyayenka ba ni san nawa, karka ce zaka yi ma mahaifiyara rashin kunya”

Abdallah ya fada a fusace. Sai Ahmad ta tabe baki yana kallonsa.

“Kasan darajarta ka bari ta ci mutuncin wacce bata da laifi?”

“Hey my friend don't tell me rubbish”

“An fada maka who are you?”

“Ai kai za a tambaya, ka so nan kana wani nuna isa wa kake a gurin Halima? Wallahi idan na so ko kallonka Halima ba zata sake yi ba stupid human being”

“Oh really? Ni ko zan nuna maka wani abu ne a gurinta, ka jira nan da one month sai na nuna maka waye ni a gurin Halima, sai ka gane darajata ta fi taka a gurinta”

Yana fadar haka ya mike tsaye da zimmar zai fita sai ga lauyansa ya shigo yana fadin su tafi gata can an saka a mota. Ba shiri Hajiya ta mike tsaye.

“Ina Yusuf din yake? Ya za a saki yarinya bata fadi komai ba? Ni ina dana yake”

Juyowa Ahmad yai ya kalleta.

“Dan ki yana Abuja hannun DSS kije ki yi fada da su idan kin isa, and idan wani abu ya samu Halima dukanku ba zan kyale ku ba har kai”

Ya karasa yana nuna Abdallah. Abdallah ya masa wani mugun kallo.
Chapter 108 · 0% Book details