← Book details Gobe Na Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 70 OF 136

Sashe 70

Gobe Na Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read

Bayan na gama sallah isha'i ina rike da wayata ina latse latsena kamshin turaren Abdallah yai min sallama kamin muryarsa ta daki dodon kunnena, a take na nemi natsuwata na rasa sai na ji duk na kwadaitu da son ganinsa fuskarsa a take na aje wayar na unkura ina gyara Hijab dina na mike tsaye ina juyowa sai nai arba da mutum, faduwar gaba ta same ni a lokacin wacce take yayin yin haka a duk lokacin da nai arba da Abdallah, abun ka da wacce ta rude sai na kasa komawa na zauna daman dakin babu kowa sai ni kadai da aljanuna idan ma ina da su, ratsawa nai gefensa na da zimmar na fita domin a bakin kofar yake tsaye ya zuba min idonsa kamar ya cinye ni, ban san yadda akai ba na kasa lura da kyau har na buga kaina da garun kofar a take goshina ya fara zogi ni kuma na saka hannu ina murzawa jikina na ta rawa kamar marar gaskiya, har lokacin be dauke idonsa daga kaina ba kuma be kauce daga kofar ba. A dole na koma na zauna saman kujerar da ke kusa da inda nai sallah, amman me sai na gagara samun natsuwa domin jikina na bani cewar idonsa na kaina. Sai da ya ji muryar Inna ta doso dakin tana masa lale marhabun sannan ya karaso cikin dakin ya zauna a saman carpet din da na tashi wanda nai sallah, idonsa ya koma gurin kafafauwa ya sakar musu ido kamar mai son tantance abu, ni kau na daga abuna sama na dora saman kujera na lullube su da hijab, sai kallon ya koma gurin hannayena, su ma na nade abu cikin hijab din sannan ya kalli Inna wacce ta shigo ta zauna.

“Abdallah yaushe rabonka da gidan nan”

“Bana samun zama ne sosai yanzu shiyasa aikin yana min yawa, ya gida ya kwana biyu?”

“Lafiya kalau ya gurin su Hajiya?”

“Tana lafiya tana gaishe ku”

“Muna amsawa mun kwana biyu ba muje ba itama bata zo ba, ina Suwaiba da su Inteesar?”

“Duka suna lafiya, na ga Baba a waje ai mun gaisa ina Mama?”

“Ta dan zagaya makota jikin ne idan yai mata nauyi sai ta zagaya saboda asibiti ma ance ta rika dan takawa tana shiga mutane”

“Allah sarki gidan yau ku ne akwai a ciki? Duk ina yan matan Baba?”

“Wallahi duk sun tafi wankin Amaryar da ake nan makota, kawarsu ce take aure kuma ta zama kamar yar gidan nan har yaran duk suna can shiyasa ka ga gidan babu kowa”

“Okay”

Ya amsa yana maida dubansa gurin wayata wacce ke kusa da shi, kamar na kai hannu na dauka sai ganin nai ya dauki wayar yana ta shafa screen din domin tana da password ba zai iya bude ta ba, ganin shiru yayi yawa yasa Inna ta tashi ta bar mana dakin daga ni sai shi sai fankar sama da ke ta aiki ba mu iska kasancewar akwai nepa.

“Zan nemawa su Namra transfer zuwa government schools”

Ya fada ba tare da ya kalleni ba, kamar yasan zan tambayi dalili sai ya ce.

“Saboda na san ba za ki iya cigaba da biya musu school fees a wannan private school ba”

Har ga Allah na ji babu dadi amman ban nuna masa ba, domin ban san dalilinsa na yin hakan ba, wata kila ya gaji da taimakon da yake ba ni ne a yanzu ganin kamar ba zan taba aurensa ba.

“Allah yasa hakan shi ya fi alheri”

Na fada da muryata da ke nuna lamarin be min dadi ba. Sai ya kalle ni kamar yana mamakin jin haka daga bakina.

“Ba zaki tambayi miyasa nai haka ba? Ba ki damu ki san dalili ba?”

“A lokaci da ka shige musu gaba har suka samu karatu a wannan makarantar ban tambayi dalili ba saia yanzu da zaka canja musu? Ka yi min alheri da yawa Abdallah wanda ni na san har na mutu ba zan taba iya biyanka shi ba.... Ba zan zarge ka da komai ba”

Mikewa yai tsaye ya jefo min wayata tare da jan tsaki.

“Ba ki hadu ba Halima....”

Yana fadar hakan ya fice, ban ce masa komai ba na fiddo hannuna dake cikin hijab na dauki wayata, ko da na kunna sai ganin screen din nai ya tsaga. Hakan da Abdallah yai be karamin komai ba sai kuzarin neman na kaina, kamin aikin ya samu ina son mai amfani da kudin hannuna na fara sa'a domin zaman banza ba nawa ba ne a yanzu.

Kwana uku da faruwar hakan ya kawo min takardar transfer dinsu har gida, a ranar Mama take tambayata dalilinsa na yin hakan nima na ce mata ban sani ba, sai da na labarta abunda ya faru asibiti.

“A duk yadda akai ba a iya yanke alakarki da Aminu saboda yaya sun shiga tsakaninku yaran har hudu ba ko daya ba”

“Za a iya yankewa mana Mama, Aminu ai be damu da yaran nan ba tun suna gidansa balle yanzu da ba sa tare da su”

“Ai yanzu ne yake sanin darajarsu Halimatu, ba ki lura da yadda Aminu ya canja ba? Ba ki lura da irin kulawar da yake bawa yaransa ba?”

Hafiza ta tsire baki.

“Ni fa ina ganin kamar so yake yace Halimatu ta koma masa...”

Ni ko nai karaf na ce.

“Allah ya kiyeye gatari da saran shuka, ni da Aminu a lahira idan na shiga aljanna wata kila na hango shi a bakin kofar wuta, dan yana da wahala idan Allaj ba kona shi ba akan zalincin da yai min”

“Halimatu kenan kina kara girma amman har yanzu hankali ya ki zuwa miki, kin kasa duban yaran dake gabanki ko dan su ai kya kyautata wasu kalaman akan mahaifinsu”

“Mama har yanzu ban gama warkewa daga tabun Aminu ba, saboda shi na samu kaina a duk wani hali da nake ciki a yanzu, mutumen da zai dube ni ya kira ni da mummuna yace ina ta haifa masa yara saboda na tsufar da shi, ya sake ni saboda na fada masa cewar dan'uwansa yana neman lalata yarsa? Sannan yai taraiya da kawata? Haba mama wace irin mutunci kike tunani zai shiga tsakani na da Aminu? Ni kadai na san irin kalubane da na fuskanta a gidansa”

Na karasa idananuwana na cika da kwalla, sannan na unkura na tashi na nufi inda jakata take na dauka daman da shirina na fito.

“Mama idan ko Hafiza idan su Namra sun dawo daga scul ki fada musu ba za su sake zuwa ba daga yau, saboda kar su saka rai, zan bawa Aisha kudin Napep ta je ta dauko su dan nasan kamin na dawo lokacin dawowarsu daga school yayi”

“To Allah ya bada sa'a ya tsare”

Cewar Mama. Hafiza kuma ta kalleni daga sama har kasa tace

“Allah yasa mai kamfanin yana kallonki yace ya samu mata”

Ni kuma nai dariya.

“Ai na girmi aure yanzu, ko nawa za a bani ba zan iya aure a yanzu ba, mun dai yi kuma gama da yarda Allah”

“Kara dai da kika ce da yardar Allah, aure ai shine martabar mace, kuma kin san ba ido zan saka miki kina zama a gida ba ko? Mutanen unguwa ma sai su yi ta yi da ke, musamman idan kika fara aikin nan wani ba tunanin alheri zai miki ba, yanzu sai ki ji an fara tsegumi, daman can ana lissafa mu na yan mata wai mun ki aurarda su.... ”

Mama ta tari numfashina tana ta kora bayani, ni dai kan uffan ban sake cewa ba, nai musu sallama na fice, har nai addu'a fita daga gida, ban daina mamaki da sake sake a raina ba, na kin ganin laifin da Aminu da Mama take da kokarin wankeshi a idanuwana, ga kuma zancen aure da take kokarin bijiro min da shi, anya ya gama da warke daga radadin azabar kunar da Abdulhamid da Aminu suka min da har zan yi tunanin aure? Ko da ma ace yana gabana ballantana yanzu da bana sha'awarsa.
  Na isa gurin da zanje cikin lokaci domin na tsarawa kaina isa gurin da misalin tara na safe sai ga ni na isa takwas da rabi da yan dakiku a kai, duk kuwa da kasancewar babu wanda ya san da zuwana a kamfanin hasalima ni kaina ban san mai kamfanin ba ban san tsari da dokokin kamfanin ba amman ina kyautata zaton a lokacin ne za a samu duk wani wanda ake tsammani samu a kamfani.
Chapter 70 · 0% Book details