← Book details Gobe Na Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 43 OF 136

Sashe 43

Gobe Na Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

“Momi Daddynta yana sonta sosai komai siya mata yake, kuma har shi yake zuwa daukarta idan zata koma gida”

“A ina kika hadu da ita?”

“A school din mu take ita ce tana so na friend tace ita bata da friends kuma Momi ita ma sunan Mominta Halima, amman ta rasu.... ”

Hannu na mika mata alamar ta zo, sai ta taso daga inda take zaune a kan Center tebur ta nufo inda nake sanye da English Wears dinta kanta babu dankwali balle ayi maganar hijabi.

“Kin ganeni?”

Na tambaya bayan na rike hannunta, sai ta gyada min kai tana murmushi irin murmushin nan na yara masu kiriniya.

“Momi na fada mata yau za mu zo gidanki shine tace tana son ta ganki, tace daddynta ya kawota kuma ya kawo ta”

Namra ta fada da mamaki a fuskarta, domin ita bata tashi cikin irin wannan gatan ba, da mahaifinta zai mata abu ko kuma ya nuna mata kula balle har ya dauketa ya fita da ita.

“Daddynta yana sonta sosai Momi har da waya ya siya mata, yana bata chocolate komai siya mata yake, kuma gidansu har da motar wasan yara ya siya mata da lilo irin an scul dinmu”

Ta sake fada, ni kuma sai nai murmushi na shafa kanta domin na san abunda yata take ji, kwatankwacin abunda nake ji idan na ga wata mace ta yi dacen mijin aure.

“Kin yi dacen uba, Allah yai miki albarka ya jikan mahaifiyarki”

Da kanta ta amsa min da Ameen kamin ta saki hannuna ta nufi gurin su Adnan, da alama dai ta sake sosai da su kamar wasu yan'uwanta.

A gidan suka wuni tare da Hafiza sai dare suka tafi, duk yadda ta so na labarta mata damuwa ban yarda na bude mata cikina ba. Tafiyarsu da minti ashirin Abdulhamid ya dawo a lokacin ina zaune falo, bai yi knocked ba daman yanzu ya gane sai dai ya saka key ya bude kofar falon ya shigo. Na masa sannu da zuwa ya amsa min irin amsawar nan kamar an masa dole, a yadda na lura Abdulhamid yana zaune da ni ne irin zaman nan kamar na dole domin ba zaka ga zamantakewar aurenmu ka ce zaman ne na masoya ba. Na so na gabatar masa da zancen zuwa gida duba Abbah a wannan lokacin sai kuma wata zuciyar ta hana ni, na yanke shawarar da safe zan fada masa idan ya gama karyawa.
Ashe abunda ban sani ba Abdulhamid tafiya zai yi a garin da ban san ina ba ne, sai da safiyar ta waye bayan na gama hada masa abun karyawar na yi ta jiran ya fito shiru be fito ba, har tara da rabi ganin be saba kai wa hakan ba yasa na shiga dakinsa sai na samu dakin wayam babu kowa a ciki sai wata farar takardar a saman gadonsa, karasa nai na dauki takardar wacce ke saman kudin da ban san na minene ba har sai dana karanta takardar.

“Tafiya ta kamani zuwa Kaduna, zan dawo on Tuesday ko Wednesday ga kudi nan ki yi amfani da su.....”

Ina gama karanta takardar hawaye ya wanke min fuska, a yanzu bana da martabar da Abdulhamid zai kalli ya fada min cewar zai yi tafiya? Zauna nai bakin gadon ina tuna irin rayuwar da nai a gidan Aminu, a da na yi tunanin komai ya wuce, ashe abubuwan da zan fuskatanta suna da yawa, ko wace mace da irin jarrabawar da take tsintar kanta a cikin a gidan mijinta, wata mijinta neman mata yake, wata ya hana ta ci da sha, wata ya hana ta lokacinsa, wata ya hana ta kudin kashewa. ni kuma irin tawa kaddarar kenan.

“Al-hamdulillah”

Na furta sannan na share hawayena na taso na fito daga dakin, dakina na dawo na bude drawer ta na dauko maganin bachi na kurba kadan na kwanta, da niyar nai bachin kadan sai ga shi na zarce da dogon bachi ban farka ba sai la'asar. Azahar ma sai da na ramata sannan na dora da la'asar din, haka kuma be min dadi ba domin ban saba ramuwar sallah ba, idan ba da wani dalili mai karfi ba. Ganin ni kadai ce a gidan yasa ban wahalar da kaina wajen girka komai ba, daman can ba ci nake ba saboda shi nake girkawa kuma yanzu baya ma garin.
Wayarta na dauko na kira layin Baba, ringing biyu ya dauka na gaishe shi cikin girmama da kauna ya amsa min da kuzarinsa.

“Baba ya jikin?”

“Al-hamdulillah jiki da sauki sosai sai da suka fada miki ko?”

“Hafiza ta zo jiya ta fada min, Baba ciwo ba abun boyu ba ne, musamman irin naka da idan kafafuwan suka tashi baka iya takasu, ya kamata aje asibiti a sake dubawa”

“Kafafuwan da sauki fa, yanzu nan ma Abdullahi ya dawo da ni gurin gashi, shi ke kaini aka gasa kafafuwan kullum, da sauki sosai ki kwantar da hankalinki”

“To Baba na so na shigo sai Abdulhamid yai tafiya, amman idan ya dawo ko kuma na yi waya da shi na nemi izininsa zan zo na dubaka”

“Allah ya miki albarka Halimatu, karki zoba da izininsa ba, ayi ta hakuri”

“To Baba Allah ya kara maka lafiya”

Da amin ya amsa na sauke wayar ina hawaye, duk yadda na so na daga waya na kira Abdulhamid na tambayi izininsa na zuwa gida sai na kasa, daga karshe na yanke shawarar tura masa sako. Ko minti biyu ba ayi ba ya dawo min da reply har da kalmar da nake zaton zolayace kawai ko kuma ya rubutu min ne saboda ya saba rubuto haka a karshen ko wane irin text da zai min.

“Subhanallahi Allah ba shi lafiya, ki je gobe, kuma idan na dawo zamu je mu duba shi, zan kira shi na masa ya jiki.

Ki kula da kanki i love you.....”

Daker na iya hadeye yawun bakina tare da wani abu da na ji ya tsaya min a makoshi. Sannan na tashi na shiga gyara gidan domin yau ban yi gyaran safe ba tunda wuni nai ina bachi.

Sai na kimtsa ko'ina na gyara komai sannan na shiga nai wanka, sai kuma na dawo gaban madubi na zauna ina ta kallon kaina, ni kaina ban lura da na yi rama sosai haka ba sai yau, ban ɗaga daga gurin ba sai da na ji wayata na ringing, number mama ce cikin sauri na dauka tare da sallama, bayan mun gaisa na sake mata ya jikin Baba ta amsa min da sauki tare da kara fada min Abdallah yana ta hidima da shi.

“Allah ya saka masa da alheri ya biyaki”

“Amin. Halimatu me ke damunki?”

“Me ya faru mama?”

“Kin daina zuwa gida, kuma Hafiza ta fada min kina cikin damuwa amman kin ki ki fada mata”

“Babu komai Mama kawai dai bana jindadi ne kwana biyu”

“Halimatu, ni fa mahaifiyarki ce, ko ms ke damunki ni ya kamata na fara sani kamin kowa, kuma idan ba ki fada min damuwarki ba wa kike da shi da za ki fada masa?”

Hawayen na ji ya cika min ido, tabbas ina bukatar mahaifiyata a kusa da ni kamar ko wace ƴa.

“Mama idan na zo gobe zan fada miki komai, maganar ba zata yiyu ta waya ba”

“To Allah ya kawo ki lafiya”

“Amin”

Na sauke wayar sannan na tashi na nufi wardrobe na dauko kayan bachina wando da riga na saka. Da kaina na tafi na rufe gate din gidan saboda yau ni ce kadai a gidan daman Abdulhamid ya saba rufewa yau kuma ba ya nan, bayan na rufe gate a dawo na rufe kofar falo na kashe kayan kallo da wutar falon sannan na shiga dakina na kwanta ba dan bachi ba domin na san bachi ba zai dauke ni haka nan kawai ba sai idan wani abun na sha.
Data ta na kunna na shiga media rabon da na yi chat ma har na manta, na samu sakkwanin da yawa musamman ta whatsapp, na groups da na private har na gaji da bibiyar grps din na kashe datar.

Misalin daya da yan mintuna da na ji kamar ana taba kofar falonmu, da farko tsoro ya kamani a tunanina ko aljanuna, sai da na jai motsin yayi yawa har da saka abu aka dukan kofar ana kokarin ballanta sannan na taso na fito daga dakin cikin karfin hali. Isowa falon tai daidai da balla kofar da akai domin kadan ya rage ba su cireta ba har ginin gurin sai da suka taba gurin balle kofar. Wadancan mutanen ne dai wadanda suka zo wacan karon, masu sanye da mask da kuma bingogi. A take a nemi tsoron da ke cikina na rasa, ashe akwai ranar da ko mutuwa za kai arba da ita baka tsoronta.

“Waye ku? Me kuke nema agurina? Waya turo k? Shi wanda ya turo ku me na tare masa?, miyasa ba ku zuwa sai a lokacin da mijina baya nan? Fyade kuka sake zuwa min? Ku sake sakawa mijina ya ki yarda da ni kamar wancen karon? Ku saka bindiga ku harbe ni zai fi min jindadi da kwanciyar hankali sama da ku same min wani cikin, ko waye kai ka san ni kuma ka san cewa mijin ba shi da lafiyar da zai iya kusantata shiyasa kake min haka saboda ka tarwatsa rayuwata, to Allah ba zai barku ba sai ya saka min.... ”

Ina rufe bakina daya daga cikinsu ya karaso kusa da ni ya buga min kan karamar bindigar da ke hannunsa abaki, wani azababben zafi na ji kamar babu bakin ma, ko kuma wacce aka cirewa hakora, a take jini ya samu hanya. Uku suka zauna a kujera yayinda sauran suke a tsaye.
Ban iya sake cewa komai ba, dan ban yi zaton bakina yana ajikina ba har lokacin, faduwa nai zaune na tara hannuna jinin dake zuba daga bakina yana ta tsiyayomin.

“Yau ba gurin mijinki muka zo ba, kuma ba mu san cewar mijinki baya gari ba, ba turo mu akai ba zuwan kanmu ne, kuma baki san daya daga cikinmu ba, sai dai na lura zuciyarki tana da tauri a yanzu”
Chapter 43 · 0% Book details