← Book details Gobe Na Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 73 OF 136

Sashe 73

Gobe Na Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Har lokacin da yake maganar ban kawo komai a raina har sai da ya fadi kalmarsa ta karshe, zuciyarta ta fara raya min wani abun da ban taba mafarkin faruwarsa, lalabe na fara yi a duniyar tunani na, sautin wacan muryar nake hada da wannan, ina ta kokarin siffanta surar wacan da wannan, farat daya na nemi duniyar tunanin nawa na rasa, abubuwan da nake kokarin hadawa duk suka watse, sai na ji kan nawa kamar babu komai a ciki. Tafiya nai bayabaya kamar zan fadi sai yai saurin kai hannunsa zai kamani.

“Dan.... Allah... Kar.. Ka... Taba... Ni... ”

Na fada a wahale, wasu zafafan hawaye na sauko min, kamar yadda shi ma idanuwansa suka fara fitar da hawayen.

“I can't hide it anymore yanzu, ba zan iya cewa ba da gangan na aikata ba, i rape you amman ban tsammanci zan dawo gareki ba, and on that very night da kika fada min kin samu cikina ban iya bachi ba a ranar saboda tunani da farinciki jin haka, daga lokacin na samu kaina da kaunar ki da kuma son rayuwa da ke, because my only hope and pray is na samu haihu kamin na mutu, na san zan iya mutu at any moment, but i want to make my parents proud, and ina son ko na mutu na bar carbon copy na....”

Ya karasa muryarsa a dakishe saboda kuka. Risinawa nai gabansa na hade hannayena kamar neman gafara.

“Why do you rape me? Mi mai maka?”

Sai shi ma ya risino saitin fuskata yana share hawayensa.

“I don't know why, na san dai mijinki na je nema a wannan daren.... ”

Be gama maganar ba na mike tsaye na juyo tafiya na fara yi kamar mai ciwon kafafuwa, ko wace dagawa da takawa tana min nauyi, ga nauyin zuciya da ya danne min kirji har yana neman numfashina, ina tafe wasu hawaye masu zafi suna sauko min yawun bakin gaba daya ya canja gumi na ta karyo min har kasan marata murdawa yake, ina ta girgiza kai alamar a'a a'a ban daina ba har sai da na hango Abdallah ya fito daga cikin emergency sanye da shadda hannayensa duka biyu zube a aljihu... Tsayawa nai cak ina kallonsa, a yau ji nai kamar an halittoni ne kawai domin kallonsa, kaunarsa da tausayin kazafin da nai masa wanda har ya kai ni ga furta masa. Babu kamar kai Abdallah Wallahi babu irinka, mutumen da ya kasa nuna min kyama balle yayana, mutumen da ke bani taimako da kowace hanya, mutumen da idan nai gudu naje gunsa da bukatuna da damuwata zai tara hannayensa biyu ya karbe ni, na yi kuskure tabbas na aikata kuskure na barin mutune da ya dace da zama abokin rayuwata....

“Kullum cikin kuka kike please smile....”

Maganarsa ce ta dawo da ni daga duniyar tunanin da nake, ashe ya karaso kusa da ni ya ban sani ba, fuskarsa da murmushi yana min alama da nai murmushi da yatsan hannunsa biyu kamar yadda murmushin yake a fuskarsa.
Ban tana jin kaunarsa Abdallah sai yau ban taba jin kimar Abdallah ba sai yau ba, ban taba jinjina abunda yake min ba sai yau. Murmushin nai ina hawaye.

“That's my girl....”

Ya furta sannan ya maida hannun aljihu yai gaba abunsa, kamshin turarensa ya daki hancina har sai da ma lumshe idanuwana....
Na samu dakika biyar a haka kamin na juya ina kallon tafiyarsa cike da kaunarsa, wata kila jikinsa ne ya bashi cewa ina kallonsa sai ya juyo ya kalleni tare da aiko min da kyakkyawan murmushin wanda ya sanyaya min zuciya ji nai kamar na ruga na rumgume shi na fada masa cewar yau Ni Halimatu ina kaunarsa.....

___________

Ana wata ga wata, ina masu team Abraham ashe abun na ku.....🤐😥
Team Abdallah
Team Gwarzo
Za mu ga team din da yafi yawa 💃💃
7/21/21, 10:46 PM - Buhainat: *GOBE NA...*

By Khadeeja Candy

3️⃣8️⃣

Ban koma cikin dakin ba, a harabar da amsu jinya suke zama na samu butar wata matar nai alwala ta bani carpet nai sallah nai addu'a sannan na tashi na nufi wani bangare na asibiti gurin da aka kawata da furanni da kuma hasken fitulun kasancewar hudu ya fara. Tsaye nai a gurin ina ta kallon sama wata iska mai dadi na kadawa hawayen idona na ta aikinsu, babu abunda nake tunani sai Abdallah babu wanda nake hangowa a tare da ni sai a yanzu nake ganin dacewar tarairaya ta da Abdallah.

“Uhmm na san na bata miki akan maganar da nai dazun amman iya gaskiyata nake fada, kina da damar da za ki ji haushi na ki tsaneni kuma zan jira har zuwa lokacin da zaki warke daga raunin da nai miki.... ”

Juyowa nai a hankali na kalli Aminu wanda ke min maganar, sai a yanzu nake kallonsa da kyau ya rame sosai ya dan yi duhu. Dan murmushi nai na nufi wata karamar balcony na zauna sai shi ma ya tako ya zo ya zauna kusa da ni. Magana na fara yi ba tare da na kalle shi ba

“A lokacin da nake budurwa idan mai ma mahaifiyata ko mahaifina wani aiki ko abunda ya faranta musu rai, sukan ce min Allah yai miki albarka ya baki miji na gari, ni kaina ina yawan addu'ar a sallah ta, a lokacin da ka zo kace kana so na ka aureni sai na ji cewar Allah ya amsa addu'o'inmu, bayan na yi haihuwar farko ka juya min baya, sai na fara addu'a ina ta fata da ganin kamar wata rana zaka daina, da nai haihuwa ta biyu sai na fara karaya, daga lokacin ne na dauka cewar aurenka yana cikin mummunar kaddarata, domin zama da mazinacin namiji ba abu ne mai sauki ba, kullum ina cikin fargaba, kullum ina cikin addu'a, kamin wani lokaci sai alakar auratayyarmu ta canja, na kuma maka kamar bakin maciji, idan nai kwaliya ina jiran ka dawo ka yaba min, ba zaka dawo ba sai tsakiyar dare, a maimakon idan ka kalleni kace na yi kyau sai ka fada min cewar siraran mata suna can suna can waje suna jiranka, a gabana kake yabon wasu mata a wayarka ko a tv saboda kawai na ji zafi, bayan ka san a lokacin da ka aureni ba haka nake ba, kyau jikina na daya daga cikin abunda ya dauki hankalinka har ka zo gurina ka nuna kana son aurena, a gidanka halitta ta canja Aminu saboda yayan da na haifa maka yasa jikina ya bude, halitta ta tashi daga budurwa zuwa matar aure, na bar iyayena na bar yan'uwa da kowa nawa na koma gidanka cikin yan'uwana da zama, amaimakon ka tausaya min ka mutunta ni sai na zama abar wulakantawa, kai ka yi min mahaifiyarka tai min yan'uwanka su yi min, ka dinga fada kana cewa na haifa maka yara da yawa zan tsofar da kai, hakan yasa na fara tunanin planning, kace na ciki kiba kai ba haka kake son mace ba ka fi son siririya, babu irin kudin da ban kashe ba akan nai slimming amman ban samu sa'a ba duka ka san saboda me? Saboda na faranta maka saboda na gyara rayuwar aurena, wani lokacin idan na unkura sai na ji kamar ba zan iya fita na bar yayana ba, hakan yasa na yarda aurenka yana cikin kaddarata, wasu akan jarabesu da kiyayyar uwar miji, ko yan'uwansa, wasu kishiya wasu mijin wasu yaya wasu rashin abinci wasu rashin lafiya, to sai aka jarrabe ni da abubuwada yawa, da gangan kake kin siyo mana abu mai dadi ko na marmari wanda za mu ci mu jidadi saboda kawai ka musgun min, ka dauki karan tsana ka dora min saboda kawai na aureka na haifa maka a yaya, a ranar da na tambaye ka 2k ka hana ni a ranar na ga alert dinka na turawa wata 30k+ ka tuna....?”

Tun da na fara naganar yake hawaye har na kai aya, be iya bani amsar tambayar ba ko kallona sai ya kasa yi. Hannu na saka na share hawayena ba tare da sun bar zuba ba.

“A kowa ce rayuwar aure akwai kalubale, na sani shiyasa na jure zama da kai a wacan lokacin. Amman wani abun mamaki a lokacin da kake ki na kaka nuna min kiyayya a lokacin ne Abdallah ya nuna yana so na, bashi kadai ba a duk inda na shiga maza basa dauke ido a kaina amman nawa mijin....”

Kasa karawa nai saboda kukan da ya ci karfina.

“Na yi miki abubuwa da yawa Halimatu, a lokacin ina jin kamar ke din matsala ce a rayuwata, ban gane muhimmancin ki ba sai bayan na rasu da ke, duk abunda zan fada miki a yanzu na san ba yarda za ki yi ba, amman Wallahi zuciyata babu wanda take mamari take kauna sai ke, na aikata babban kuskure na rabu da nai da ke, amman ko a wacan lokacin ina son ki Halima, kawai dai sherin zuciya ne da na shaidan. Amman a yanzu na canja Wallahi duk wani hali marar kyau nawa yanzu babu shi..... ”

Sai a lokacin ya kalleni ya sauko daga zaunen da yake ya risina gabana.

“Ki dubi girman Allah ki yafe min, ki duba yayanmu ko dan su ki yafe min, ni da Hajiya duka mun yi nadama, Wallahi babu daren da bana kukan rashinki Halima....”

“Kana son na yafe maka?”

Yayi saurin gyada min kai jikinsa har rawa yake kamar ba shi ba.

“To ka maka dan'uwanka a kotu, ka tsaya da kafafuwanka har sai ka kwatowa yarka yancinta......”

Ina fadar hakan na mike tsaye ina share hawaye na kauce daga gabansa na fara tafiya....

“Idan nai hakan zaki yafe min ki dawo ki zauna da ni da yayana?”

Juyowa nai na kalleshi.

“Wata kila dai zan iya yafe maka na goge sunanka daga bakar takardar da na rubuta shi, amman zancen zama aure a tsakanin ni da kai wannan har abada ne, sai dai wata mai sunana amman ba ni ba....”

Ban tsaya jiran abunda zai fito daga bakinsa ba na nufi dakin da su Amal suke, har a lokacin Mama da Hajiyarsa suna dakin a zaune, kusa da Amal na karasa na zauna ina tambayar Aisha wayata.

“Yaya Abdallah ya zo nan”
Chapter 73 · 0% Book details