← Book details Billy Pinky Durlin Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 9 OF 49

Sashe 9

Billy Pinky Durlin Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

_"calm down pinky,kar ki yarda plan dinki ya watse._wani 6angaren zuciyar ta ne ke tausar ta, sbd Hakeem ya kaita qololuwa ta yanda ya watso mata kayan, hakan ta dake ta qirqiro hawayen
qarya,cikin muryar kuka mai ban tausayi ga duk wanda yaji.
tace"haba Bobby meyasa baza ka haqura mu ajiye qiyayya, mu koma tamkar yanda iyayen mu ke so..... qarya kike sam ba hakan a ranki kawai don wata banzar manufa ce yasa kike min haka.
_Lallai kayi gaskiya da wata manufa nake maka duk wadannan abubuwan ba don kyautatawa ba ko kuma don na kasance mata a gare ka, sae dae manufar da kake tunani sam ba ita bace_
Tayi maganar ne a zuci kafin take cewa a fili"Bobby sam abinda kake tunani ba shi bane kawai dai yanzu na fahimci cewa qiyayya ba abu ce mai kyau ba shiyasa nake son kaima ka fahimci hakan.
Kuma duk abubuwan da nake ma ina maka su ne a matsayin matar ka,domin samun dinbin ladar da ke tattare da hakan.....qarya kike!kuma koda da gaske kike ki sani tun ranar da aka daura auren mu na rubuta na ajiye ke ba mata ta bace sam ba aure tsakani na da ke!
Billy taji zancen Hakeem tamkar wanda ke sanar da ita an mata bushara da gidan aljannah.
Hakeem yaci gaba da cewa amma tunda kika ce haka daga yau duk wani aikin da ke cikin gidan nan ke zaki riqa yinsa tun daga aikin kuku har kan gate man zasu ajiye aikin su ki dora inda suka tsaya, don haka tun yanzu kije ki dora min indomie na baki nan da minti goma!
_"this guy wan kill me but zan amince da hakan bcs hakan zai qara ma plan dina qarfi domin na fahimci plan dina ya fara aiki a kansa sbd alamu sun nuna tunda ya fita ya kasa cin ko wane irin girki a waje ya kuma dawo gida ya tarar da banyi ba shi ne ya wani dora min aikin gidan gabadaya just bcs ya riqa cin girki na!Brovo alaiki ya Billy u have really got dis drama_

Can ta dago ta kalle shi tace"shike nan zanyi duk abinda kace amma kayi haquri ka kar6i kayan nan da na wanke ma domin shima yana daga cikin aikin da zanci gaba dayi as ur wife.
Nan ta bashi kayan a maimakon ya kar6a sae ma ya maida hannyensa baya yana kallon cikin idanun ta domin kawai ya gano ainihin abinda ke cikin ranta,Billy ta fahimci hakan shiyasa tayi saurin kauda idon ta, yace"idan da gaske kike meyasa zaki bani kayan, ai ke ya kamata ki shigar da su da kanki.
Shiru tayi ta fahimci lallai idan tayi wasa Hakeem zai gano ainihin plan dinta, ya zama dole ta kiyaye.
Tace"Afwan but nayi haka ne sbd naga baka son ina shiga ma d'aki anyhow,bata jira me zai ce ba tabi ta gefen sa ta mayarda kayan a mazaunin su ta fito, Hakeem kuwa yabi ta da ido yace a ransa
_"duk abinda kike shiryawa baza ki ta6a cin ma burin ki ba_ domin ko da kuskure bazan sake ta6a ko yatsar ki ba bare har nayi kuskuren wuce gun"

*Billy gir[truncated by WhatsApp]
[9/22, 6:27 PM] ‪+234 810 038 8117‬: [8/7/2016] Billy giro😊:

*```👛BILLY PINKY DURLING ```👛*

*```Na Billy giro```😊*

*```page```*

*```👛19👛```*
Washe gari da asuba ta sallame sallah kenan taji Hakeem na mata knocking.
Koda ta fito ta same shi sanye da kayan exercise yace"kije ki wanke min mota kuma kar ki 6ata min lokaci domin zan fita da qarfe takwas.

Yana gama fada ya wuce Billy ta bishi da ido tace"da gaske yake son wahalda ni na ganin na kasa cimma burina,amma zan jure domin kaima naka lokacin zai zo da zaka shiga yanayin da baza ka iya fitar da kanka ba sae idan Allah ne ya fitar da kai,gwara ni kenan da in yanzu naso zan yakice wahalar.

Fitowa tayi harabar gidan da niyar tasa gate man yayi saurin wanke motar kafin Hakeem ya dawo daga gurin exercise.

Tsaye tayi cak tana kallon dakin gate man a rufe,
kenan Hakeem ya sallame shi, tace" laillai in yasan wata bai san wata ba ina da numbar gateman i will call him ryt now!....Hakeem ne ya katse mata hanzari da taga ashe cikin gidan ne yake exercise inda yake zagaye gidan da jogging.
_No prob pinky just go an wash d car zaki ci ribar hakan wata rana_.
Zuciyar ta ce ke bata hakan ta furta "OK"a fili,
ta shiga tunanin ta ya ma zata fara aikin da bata ta6a yi ba.

Komawa tayi daga ciki ta cire hijab ta dawo taje gurin motar ta dad'e tsaye tana kallon ta,
se can ta hango tiyo taje ta dauka tare da kunna fanfo ba shiri ta fara jin saukar ruwa a fuskar ta sbd kafin ta kunna fanfo bata lura da cewa bakin tiyon na facing din fuskar ta ba,a razane ta buga ihu tana ja baya yayinda ruwan ke ci gaba da watso mata a fuska har zuwa qirjin ta nan take ta jiqe kafin take fahimtar tiyon hannun ta ne ke watso mata ruwan domin ta manta cewa tana riqe da shi,
Jefar da tiyon tayi a qasa tana sauke numfashi hade da kallon tufafin ta da suka jiqe wato riga da wando na bacci,
rigar mai d'an siririn hannu wacce ta kai mata har guiwa wandon kuma dogo ne har qasa.
Guntun tsaki ta buga ta kama gashin kanta ta dunqule,sannan ta duqa tana nad'e qafar wandon ta,
sae dai tashin ta keda wuya qafar wandon ya walwale sbd sul6i ne da yadin.
A shagw6e take kallon qafar wandon fuskar ta kamar wacce zatayi kuka tace"oh no!

Duk abin nan da take Hakeem na kallon ta yana dariya cike da mugunta.

Suna hada ido tamkar bashi ke dariyar ba yayi mata kamar sam bai ma lura da abinda ke faruwa ba yaje kan resting chair ya zauna yana sauke gajiyar execise.

Nan taja tiyo ta tafi dashi gurin mota ta shiga watsa ma motar ruwa da taga koina ya samu taje ta kashe fanfo acewar ta gama wankin motar,domin tana kashe fanfo ta nufi qofar shiga gidan Hakeem yace ke zo nan,ba musu taje,yace me kike nufi da zaki fice baki gama wankin motar ba? Ai na gama wankin motar baka ga koinan ta ya sami ruwa ba... tsaki ya buga hade da jefa mata key yace dallah malama jeki bude gate man room ki dauko car wash da sosu ki wanke min mota!
Nan ta duqa ta dauki makullin ta 6oye damuwar da ke qoqarin bayyana a fuskar ta, ta qirqiro murmushi tace"sorry na manta ne.

Haka taje ta bude gate man room ta dauko abubuwan wankin mota har da qyallen gogewa.

Taje tana wankin motar cike da wahala sbd ta cika kumfa sosai,ga gashin kanta ya walwale sae faman wahalar gyaran sa take.
Da qyar ta kammala tayi tsaye riqe da qugu tana sauke numfashi,Hakeem da ke kallonta yace"indai wahala ce yanxu kika soma.

Bayan ta mayarda abubuwan wankin mota a gate man room ta rufe ta kawo masa key zata fice yace"kin manta da bawa flowers ruwa ne.... cak Billy ta tsaya tana jin kamar ta fashe da kuka domin bata ta6a wahala irin ta yau ba"tace a ranta"my plan gonna kill me amma wlh sae na jure domin bazan fara wahala a banxa ba.

Nan taje ta bawa flowers ruwa tana gamawa ta fice kitchen ta hada masa break fast dinsa sbd tayi zama d'aya ta huta.

Tana gamawa taje ta cire kayan jikinta ta bawa gado amana sae sha biyu ta tashi ta shiga toilet tayi wanka taje kitchen ta dora abincin rana.

Tana gamawa taje falo tayi zaune tana kallo.
Bata jima da zama ba ta shiga jin oda ba qauqautawa,
tsaki tayi sbd ta rasa inda oda ke fitowa.
Ba jinawa se ga Hakeem ya shigo gidan ransa baqiqirin ya kalli Billy da ke kwance tana hutawa Yace"be carefull kina wasa da aikin ki! kafin na bar gidan nan akwai abu biyu da bakiyi min ba,wato bani abinci da kuma bude gate sannan yanzu na dawo ina faman oda kika share ni!,, kayi haquri mantawa nayi bai ce da ita komai ba ya fice cikin 6acin rai.

Billy abin dariya ma ya bata tace"game din nan tamu da ban dariya take.

Hakeem kuwa da shigar sa daki ya fada toilet yayi wanka,ya shirya cikin kayan shan iska

Tana kwance taji fitowar sa ya wuce dauke da laptop yaje kan dining ya zauna ba 6ata lokaci ta bishi.

Hakeem ya wani hakince kamar wani Prince yana aiki da laptop Billy kuwa har ta zuba abinci a plate ta fara bashi a baki sae dae hankalin ta baya ga bashi abinci yana kan waya tana chat da qawayen ta.
Haka Hakeem kar6ar abincin kawai yake amma hankalin sa na kan laptop bai ankara ba yaji spoon kan hancin sa,
kai tsaye ya buge spoon cike da 6acin rai duk abincin ya watse yace"dama nasan qarya kike ba gaskiya a cikin zancen ki wace mace ce zata ce tana neman lada a gun mijinta amma tana bashi abinci hankalin ta na wani gun....sorry sorry please calm down, tabbas zance na da gaske ne,ka daina tunanin wani abu, fatana mu kasance kamar yadda iyayen mu ke so, amma kayi haquri da kuskuren da nayi a yanzu bada niya bane" ta fadi hakane yayinda ta langwa6ar da kai ta wani marairaice kamar da gaske.
Hakeem bai ce mata komai ba yaci gaba da aikinsa inda yake furta cewa a ransa
_"ai kuwa kaud'in bakin ki zai ja miki domin zan maida ke tamkar house girl_
Billy kuwa cewa take
_na fahimci kana min tsanani ne sbd na fara gajiya da hakan har ka samu ka gano ainihin plan dina ni kuwa bazan baka wannan damar ba duk abinda zaka min zan jure bazan yarda na nuna maka gajiyawa ta ba,domin nasan sannu sannu zaka nutse a cikin plan dina_.

Nan ta dauki wani spoon taci gaba da bashi abinci,
da ya gama ta kwashe kwanika ta kai kitchen bata fito ba sae da ta wanke su tas.
Chapter 9 · 0% Book details