← Book details Billy Pinky Durlin Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 25 OF 49

Sashe 25

Billy Pinky Durlin Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Nan su Abba suka fice Billy ta kawo ma Naini abinci Bayan ya gama yace"pls ki sanar da Abba ina so zanje granny house, kuma gashi bai kar6i saqon da Abba yace na bashi ba.
Nan taje ta kira Abba daga nan ta wuce d'akin ta.

Washe gari da safe guraren 11:30,Naini ne ya shigo gidan ya sami Billy da Amjad a falo, umma ta riqe Billy ana mata allura sae kuka take.
Har cikin ranshi yaji abun amma yayi saurin hana kanshi sbd so yake ya cire Billy a ransa.

Sae da ya gaida su sannan umma taja Billy suka shiga daga ciki, Naini ya kalli amjad da ya sharewa en guntayen hawayen shi, Yace"Amjad lafiya"
Nan amjad yaja hannun Naini suka fito harabar gidan yayinda suka jingina a jikin motar Naini.
Cike da damuwa ya kalli Naini yace"na dad'e ina neman abokin da zai taya ni baqin ciki sae gashi Allah ya kawo ka, kai da nasan kayi zama na kusan wata d'aya a new Delhi tare da su pinky, zan fi jin dad'in wannan zancen da kai bcs har ko yaushe abin yana d'aure min kai sosai,shin ko kai kayi mamaki kan abinda ya faru tsakanin pinky da Hakeem? na me kenan? kar kace min baka san me yake faruwa ba,ni ban san wani abu da ya faru ba ina dai son na sani,,,,da kamar mamaki kuwa domin a yanda Abban Hakeem yaji baqin cikin faruwar abin na tabbatar ya sanar da mahaifin ka,,,ba mamaki ya sanar da Abbana amma banji a bakin shi ba kuma banyi mamakin hakan ba sbd Abba bai cika son gaya min abinda zai sani a damuwa ba bare a lokacin ina exams dole zai kiyaye abinda zai sa na kasa maida hankali na kan karatu,kuma muna gama exam yace zai aiko ni Nigeria banso hakan ba sbd wani abu da nake son hanawa zuciya ta,amma ba yanda na iya dole nazo.

Ajiyar zuciya Amjad ya sauke ya shiga sanar da Naini kaf abinda ya faru bayan dawowar su pinky.

Zaro ido Naini yayi yana kallon Amjad sae duk ya shiga damuwa sosai idanun sa suka cika tap da qwallah domin sonda Naini yake yiwa Billy so ne wanda baya son Billy ta rasa wani abun da take so, koda kuwa shi a gurin shi baqinci ne, yafi buqatar hakan.

Yace"Amjad saki fa kace kuma d'ai d'ai har uku Hakeem yayi wa pinky?sosai kuwa....no this can never happen bcs Hakeem yana son pinky sosai ni shaida ne... Hm ba don kafi ni kusanci da su ba,da sae dai nace nafi kowa sanin hakan,amma sae gashi naji labari a bakin wacce abin ya faru a gaban ta wato Feenah qawar pinky,amma duk da hakan naso ace naji ainihin yanda abin ya kasance a gun su umma amma kuma se naga meye amfani tunda aure ya riga ya rabu ba wani gyaran da za a yi a kai,kuma qarin takaici ne kawai idan na tuntu6e su da zancen,sbd kan takaici Abba fa ya kori Hakeem tun ranar da abin ya faru gashi yau sati d'aya bashi ba labarin shi,duk inda nake sa ran zan ga Hakeem na neme shi na rasa.
Naini yace"ya salam! wannan wane irin abu ne haka,nagode Amjad da ka sanar da ni wannan abun zan shiga daga ciki.

Koda ya shiga falon ba kowa yayi tsaye ya rasa me zaiyi duk tausayin pinky ya cika shi.
Fitowa yayi yaja motar shi ya bar gidan

2 days Naini na shigowa gidan baya samun pinky haka ko yau umma kawai ya samu a falo, sae da ya gaisa da ita yace"umma halan ina pinky take ne? Him!Billy tana 6angaren Hakeem nan ta mayar gurin zuwan ta ko yaushe hatta bacci da ace Abban Hakeem zai yarda da can zata riqa bacci,domin har fad'a yayi mata kan ta daina zuwa can,amma yana fita zata saci jiki taje.
Shiru naini yayi can yace"umma ashe wani abu marar dad'in ji ya faru tsakanin Hakeem da pinky shiyasa na sami pinky duk tabi ta rame,cike da damuwa umma tace"wai dama baka ji ba?eh umma sae daga baya nake ji a bakin Amjad,amma umma don Allah da kun haqura kun bar Hakeem ya dawo gida,,,,,
Naini ai Abban Hakeem ne yaqi haqura har yanzu,nayi ta bashi haquri,
yace wai na bar shi zai yi tunani akai, wanda duk a tunani na,zai ce Hakeem ya dawo amma naji shiru har gashi yanzu sati d'aya,amma inshaAllah yau zan tuntu6e shi da zancen dama nayi shiru ne kar yace na cika takura shi.
To umma ina ce an san inda yake koda Abba ya haqura, shine matsalar gsky bai fad'i inda yaje ba kawai yace yana jiran saqon afuwar Abban shi domin ya samu ya dawo, daga haka bai yi wani baya ni ba wanda koda Abban shi ya haqura za'a je a sanar da shi.
To umma inshaAllah ni zan shiga neman shi koma ina ne, domin a samu damuwar da pinky take d'auke da ita ko zata ragu,, him!Naini damuwar Billy damuwa ce da take bani mamaki ta riga tasan da sakin nan tun kafin suxo,amma sae zuwan su ne ta shiga damuwa sosai koda yake dole ta shiga damuwa sbd korar Hakeem da Abban shi yayi.
Haka ne zanje na ganta, yana gama fad'a ya fita bai zarce koina ba sae 6angaren Hakeem,da sallamar shi ya bude d'akin, Billy dake kwance ta tashi domin ganin wane ne, ajiye photon Hakeem dake riqe a hannun ta tayi.

Ta zauna da kyau tana mai kallon Naini,yace"pinky naji abinda ya faru na kuma yi baqin ciki sosai, na kuma yi mamakin yanda Hakeem ya aiwatar da hakan, amma ina mai jajanta miki kan kiyi haquri ki barwa Allah komai, kuma duk da nasan aure ya riga ya rabu tsakanin ki da Hakeem ya zama dole na nemo miki shi duk inda yake domin ko kad'an bana son ganin ki cikin damuwa, hakan nasa ni damuwa sosai.
Sosai taji dad'in kalaman Naini ta share hawayen da suka zubo mata tana ji kamar ta sanar da Naini ita ce ta rubuta sakin ba Hakeem ba, amma kuma tana fargaba sbd wani dalili da ta barwa kanta sani.
Godiya kawai tayi mishi, ta tashi suka fito daga d'akin suna cikin tafiya suka hadu da Abba a harabar gidan, nan Abba ya kira su, pinky taje cike da jin nauyin Abba sbd tasan ya hana ta zuwa d'akin Hakeem,nan ta duqar da kanta qasa bata yarda ta had'a ido dashi ba, yace"mamanah a ko yaushe lalla6ar ki nake kan ki cire damuwa a ranki kan wanda sam bai dace ace kin damu a kanshi ba.
Amma kije inshaAllah wannan damuwar ta kusa yaye miki domin na kusa kawo qarshen ta inshaAllah, wani irin dad'i Billy taji a ranta domin ganin take Abba zai ce da Hakeem ya dawo.

Hakan yasa ta d'an fara jin sauqi a ranta duk da tasan cewa ko ya dawo ba zai kula ta ba,amma tafi buqatar hakan da ace baya gidan.

Kwana biyu taci gaba da sakewa har tana fitowa shan iska yayinda Naini ke zama yana taya ta fira amma duk yanda yaso pinky tayi dariya baya samun hakan sae dai tayi ta sauraren shi ba eem ba um um.
Ko yanzu zaune suke sae labari yake bata tana sauraren shi,a cikin labarin ne ya d'auko zancen Hakeem hakan yasa ta qara maida hankalin ta tana kallon shi,nan ya bata labari kan wata rigimà da suka ta6a yi shi da team d'in sa da na Hakeem a new delhi kan ball.
d'an guntun murmushi ne ya bayyana a fuskar ta domin a cikin rigimàr su akwai dariya sosai har dai team d'in su Hakeem,sae duk taji tana son yin ball amma tana tuna Hakeem ya hana ta wasa da Naini nan tayi saurin cire ball d'in a ranta.
Abba ne ya biyo yana kallon su cike da jin dad'in ganin Billy ta fara sakewa nan suka gaida shi kafin yake shiga daga ciki.

Abba bai jima da shiga ba sae ga Feenah ta kunno da motar ta,bayan Feenah ta gaisa da Naini ne suka shiga daga ciki shi kuma ya ja motar shi ya bar gidan.

Suna shiga d'aki pinky ta duba fridge d'in ba lemu nan ta fito da niyar taje downstairs ta d'auko fad'an da taji Abba yana yi ne ya dakatar da ita inda umma ke masa magana kan Hakeem yace"ai ba qaramin yaro bane don haka sae na gama abinda ke gabana tukun, domin yanzu bani da burin da ya wuce naga mamanah ta gama idda na auradda ita,domin ta huce takaicin Hakeem,,,, Haba Abban Hakeem yanzu har sae Billy ta gama idda sannan za'ayi zancen Hakeem....to me ya rage ta gama idda in banda sati biyu da en kwanaki,tunda tun ranar da aka d'aura auren su ne ya sake ta, kuma a binciken da nasa kimin kince mamana ta sanar dake ba wani abu da ya ta6a shiga tsakanin ta da Hakeem har suka dawo,,,but Abban Hakeem dawa kake shirin had'a ta aure baka gudun abinda ya faru ya sake faruwa?
Ba abinda zai faru sai alheri inshaAllah domin wanda zan had'a ta aure dashi yana matuqar sonta kuma ita ma alamu sun nuna zata so shi,kuma nasan mamanah baza ta bani kunya ba ko don abin da Hakeem ya mata,,, amma Abban Hakeem wane ne kake shirin had'a ta aure da shi? Naini wanda ko yanzu na same shi da mamanah suna fira a waje sae murmushi take abinda na jima ban gani ba tun faruwar wannan abun,don haka da mamanah ta gama idda zan kira ta na sanar da ita abinda muka yanke shawara nida mahaifin ta da kuma mahaifin Naini......tamkar saukar aradu Billy take jin zancen da gudu ta koma d'aki ta fad'a jikin Feenah tana kuka.
Chapter 25 · 0% Book details